JA DA BAYA...

Mara gaskiya

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 23✍️*  

***

"Whattt!"  
Alhaji Gali ya furta cikin wani irin yanayi da ya sa Hajiya Kaltum ta dago kai daga kallon talabijin.  

"Me ya faru Excellency?"  
Inahh, Alhaji Gali kamar bai ji ta ba, hankalinsa yayi mummunan tashi, sunan Ayzaan ma kadai baya kaunar sake jinsa. Ya tsaya cak kawai yana kallon Meerah, wacce ta dago tana kallon sauyin da baban nata yayi nan take, mamaki takeyi ganin yadda yake ta zufa duk da AC da ke aiki a falon.  

"Ayzaan Muhammad Mai Rabo, yasake tambayar meerah dan gasgata wa?"  
Meerah kuwa ta gyada kai cikin rashin fahimtar abin da ya canza masa yanayi tace.  
"Eh Dad. Shi nake nufi, I really love him"  

Ya juya ya kalli matarsa.  
"Wai kodai kunne na baiji abinda meerah tace bane hajiya kaltum?"  
Hajiya Kaltum ta kalleshi tace.  
"Me tace ne Wanda ba daidai ba?"  

"Sunan Wanda ta keso tagaya maka zabinta yayi matukar Yi domin Dan babban gidane, sannan shi kansa yaron Wani ne, duniya ta San dashi to ni Kam zabinta yayi min sosai."  

Alhaji Gali ya koma ya zauna a hankali. Fuskar da take cike da walwala kafin yanzu ta canza zuwa tsantsar fargaba da damuwa, aranshi yake fadin "lallai bakisan wa yarki take so ba, Baki San hadarin Wanda take so ba, bakisan barazanar sa ba ga rayuwata, bakisan abinda yake boye ba da Baki furta hakan ba."  

Numfashi ya sauke mai nauyi kafin yace.  
"Kin san wane ne Ayzaan Muhammad Mai Rabo kuwa?"  

Meerah ta yi murmushi, tana fadin  
"Eh mana dad nayi bincike akansa, na gaya maka ai, Ayzaan Mai Rabo The Lion, shahararren Dan kwallon da duniya ke alfahari dashi,my champion.tafada cikin sauki."  

"Kin san gidan da ya fito kuwa?" ya tambayeta har zuciyarsa Yana fatan ace ba wancan Ayzaan din bane, sai dai yasan sam ba abinda zai yuwu bane.  

"Yes dad Mai Rabo Estate mana."  

Hajiya Kaltum kuwa ta lura da yadda mijinta yake magana, da Kuma yadda yanayinsa ya sauya hakan yasa ta tabbatar akwai abinda ya faru, to Amma miye shi Wanda bata saniba?  

Kallon Mai gidan nata tayi tace  
"Me yafaru ne excellency? meyasa sunan ya baka irin wannan mamakin?"  

Alhaji Gali bai amsa mata ba. Wani tinani kawai yake aransa dole yaiwa tufkar hanci cikin gaggawa kuwa.  

"Maganar Ayzaan ta dawo masa arai kamar yanzu yakeyinta(nafita a rayuwarka ayanzu,na yadda kunyi nasara,Amma duk sanda kasake kuskuren shigo da kanka cikin komata,a sannan zan nuna maka Ainayin wanene AYZAAN!!!)

Ya sunkuyar da kansa Wanda abinda ya faru yake ta kokarin dawo masa sedai yanata Hana faruwan hakan.  

idan Meerah tashiga rayuwar Ayzaan,menene zai faru kenan?
Shin Ayzaan ya manta dasune ko kuwa dan ya Zubar da makaman yakinsa kamar yadda suka shaida?
Kokuwa Wani shiri yake akansu?


Mai Rabo Estate, shidai wannnan family sun Zame masa bala'i a rayuwarsa. Bayan abinda ya faru yanzu Kuma hirar da sukayi da inarah agidan jaridarsu tunda yaji sunan Mai rabo, da Kuma irin kallon da yarinyar take masa, yadda Sam Babu tsoro a cikin Idanunta, ya tabbatar jinin Mai rabo ce.  

Kuma tundaga ranar Bai Kara bacci Mai dadai ba domin suna bukatar kawar da ita Dan gudun bayyanar sirrin su, hakan yasa sukayi zaman meeting akan yadda zasuyi da rayuwarta, yanzu Kuma ga wata masifar ta kunno Kai.  

Meerah da ke kallon mahaifin nata ganin yadda yake ta sharce zufa yasa ta matsa kusa da shi, ta da fa shi tare da fadin  
"Dad, me ya faru?"  

Dagowa yayi ya kalleta, kafin ya sauke numfashi yace.  
"Meerah, A'ina kika san wannan yaron?"  

"Dad a Social media nafara ganinsa some months ago, sai Kuma na taba ganinsa."  

"Kin taba magana da shi?"  
Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan tace  
"Dad Bai kulaniba sannan nagaya masa Ina sonsa sedai ko kallo baiyi ba ya wuce," ta karasa maganar hawaye na zubo mata.  

Alhaji Gali ya numfasa, kafin ta.  
"Karki sake ki nuna fuskarki garesa kiyi Nisa dashi."  

"Dad!"  

"Ki saurare ni dear, Ba wai na ce ki manta da shi bane Amma akwai abubuwan da ba ki sani ba, Dan haka karki kusanci inda yake ki buya daga gare sa meerah, domin daga ranar da ya waiwayeki to muna cikin gagarumar matsala"  

Meerah ta kalli mahaifiyarta hawaye na zuba tace.  
"Mommy, ki gaya masa Ni Ayzaan nake so, Taya dad zaice Karna bayyana soyayya ta Kuma nayi nesa dashi?"  
I love him so much fa mommy.

Hajiya Kaltum kuwa waigawa tayi ta kalli mijin nata, sannan ta kalli 'yarta ta cikin sigar rarrashi tace.  
"Abin da mahaifinki yake nufi dear shi ne, ki bari mu fara bincika komai kafin ki yi wani hukunci."  

Meerah ta turo baki.  
"Amma Dad kome zaka bincika gaskiya kayishi cikin one week or three days..."  

Alhaji Gali katse ta yayi cikin sauri yana fadin  
"Za'ayi hakan my dear."  

"I love you dad" ta fada tana rumgumesa.  
Shafa bayanta yayi cikin rarrashi tare da yi mata peck a goshi yashige bangarensa da saurin Dan yana bukatar yin wayar gaggawa.  

*Aina sukayi kuskure ne da abubuwa suke dame musu haka?* Shine abinda alhaji Gali yake tambayar kansa.

---

*MAI RABO ESTATE*  

 Mai rabo estate kuwa Inarah ce suka tafi supermarket tare da Hibba, Zaitoon sai Kuma Ameerah da Afeef, Ameer Yana bacci lokacin, ita kuwa Ameerah sarkin naci tana tare aunty's din nata,Dan basu so tafiya da itaba tace ita se taje,har ta kwanta tace gurin lilly zata,hakan yasa Yaya Khalid da kanshi yakaita bangaren Ammie Wanda lokacin su Kuma su Inarah zasu fita

Suna tafe a mota suna shirmen basu da suka Saba hibba ce ke tuki Dan tace bazata yadda inarah tayi driving dinsu ba ta dinga sharara gudu.  

Yanzu ma da kyar Ammie ta barsu suje Shima da sharadin rashin tukik na Inarah Dan baa so ta cika tuki.  
Sannan Kuma akwai abubuwan da suna bukatar siyowa wanda har ita kanta Ammie zasu tawo mata da wasu abubuwan hakan yasa ta barsu da gargadin Karsu Dade.  

Sam Ammie bata so fitarsu ba haka kawai gaban ta ke Faduwa Amma ta kawar da hakan a zuciyarta ta barsu ganin sun dage.

Hibba na gabanta tana kallon kayan da ke kan shelves, Zaitoon kuwa tana ta zaɓar abubuwan da take so.  

"Inarah, zo ki ga wannan," hibba tafada tana kokarin nunawa inarah Wani 
Zobe.

Ta karasa wurin Hibba tare da kallon abinda take nuna mata.  
"Wow gaskiya ya hadu?"  

"Ga wannan ma na rasa wanne zan dauka ni, Lily Kalli wannan Dan Allah Ba shi da kyau?" Tafada tana nunawa inarah zoben Wanda yai matukar kyau da daukar hankali  
"Gaskiya yayi kyau masoyiya, sedai kamar zai Miki yawa"  

"Ke dalla bani ce dama zan sa ba, ruhie zan sayawa, nasan zaiyi matukar kyau a hannunsa" tafada tana Kaiwa bakinta tayiwa zoben kiss.  

"Ba naki ba ne?"  
"Yaya mahbub Zaki siyawa?"  
"Aahhhhh lallai naga masoyan asali kaunar Ayyyyy," tafada tana dariya.  

Hibba ma dariya takeyi tana fadin.  
"Fadi ki Kara kaunar Ayyyy."  

Dukkansu suka yi dariya. Tare da cigaba da siyayyar da suke.  

Wani na hango ya zuba Ido Yana ta kallon wacce aka Kira da inarah din, sunan ya maimai ta azuciyarsa Yana fadin nice name.  
Inarah wacce take rike da hannun ameerah kuwa bata San yanayi ba, Wanda shi Kuma duk Wani motsinta akan Idanunsa ne.  

"Aunty Inarah." ameerah tafada tana kallon inarah  
Waigowa tayi ta kalleta tare da rage tsawo tana shafa kan yarinyar tace.  
"Na'am princess?"  

"Aunty lily wancan mutumin se kallonki yakeyi" tafada tana nuna bawan Allah da ameerah tamasa tonon silili.  
"Kin sanshi ne aunty lily..?"  

Inarah ta tsaya cak, tare da waigawa taga mutumin Wanda har zuwa lokacin kallonta yake Yana murmushi.  
Hibba da Zaitoon suka kalli juna. Sannan hibba taja hannun inarah sukayi gaba.  

"Ina son ki tun da ga ganin farko Dana Yimaki Ban taba menan abu na rasa ba haka kema bazan iya rasaki ba, I love you" mutumin yafada Yana Sakin murmushi.

Lilly kinyi Wani shiru tundazu,da alama kin sace zuciyar Wancan bawan Allahn yadda ya zuba Ido kawai Yana kallon ki kamar solo,ta karasa maganar tana dariya 

"Ni... ban san me zan ce ba,Kuma ni banson shi," inarah ta fada cikin sigar maganar ta tayau da kullin wato shagwaba.  
"Ke dole ki so shi atam,inkuma ba shi ba gayan Wanda kike so,kodai Yaya Zaki ne?." Tafada tana cigaba da duba kayayyakin.

 Lumshe idanunwa tayi tare da Sakin Wani kayataccen murmushi,Allah yasani ko sunansa aka fada hankalinta kwanciya yakeyi,bare Kuma maganar sa ya Allah 🥰.

Ci gaba suka Yi da sayayyar ta su, Wanda kowa ya kusan gama abinda zai yi.  

---

Nan ɓangaren kuwa, mark ne yana zaune shi kaɗai a cikin motarsa, yana kallon wani abu a cikin wayarsa, Wani killer smile ya sake.  
Kawai yana kallon hoton.  

Bayan ɗan lokaci ya kashe screen ɗin.  
Wayarsa ta sake ringing.  
Cikin izzah da matukar aji Ya ɗaga ba tare da yace komai ba.


Muryar da ke ɗayan ɓangarenne ta ce,  
"Mun samu sabon bayani."  
Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba,dakyar ya Bude Baki yace.
"Game da me?"  
"Game da mutumin da kake nema."  

Idanunsa yasake lumshewa sannan yace.
"Ka tabbatar da bayanin?"  
"Dari bisa dari."  
Ya yi shiru.  
"To turo min."  

"Amma akwai wani abu."  
"Me?"  
"Mutumin da muka gano... yana da alaƙa da Mai Rabo Estate."  


"Mai rabo estate Kuma like what?" ya tambaya cikin mamaki,  

Daga dayan bangaren aka bashi amsa.
"Eh sir tabbas Yana cikin Mai rabo estate,sannan game da asibitin ma munfara bincike akai Kuma tabbas abinda kake zato hakane,sedai da alama suna da matukar wayau domin gaba daya sun lullube hakan,ta yadda bazaka gane cewa da hannunsu aciki ba, yanzu dinma information daya muka samu.

Shikenan kaje asibitin gobe, gurin mutumin da nagaya masa,sannan kukai wannan mutumin ku ajesa.
Abinda yace kenan ya kashe wayarsa Yana sake fadin.

"Mai Rabo Estate."