INARAH NA CIKIN HADARI🥺
*JA DA BAYA...*
*Book 1*
*Page 24✍️*
***
“Mai Rabo Estate?”
Ya maimaita a hankali, kamar yana son tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiye masa.
Adayan bangaren kuwa cikin tabbatarwa aka bashi amsa.
“Eh sir.”
“Wane irin alaƙa?”
“Har yanzu ba mu gama gano komai ba. Amma sunan gidan ya fito ne a cikin wasu bayanan da muka samu.”
Ya yi shiru, na Wani lokaci tabbas yasan hakan zata iya faruwa Amma tayaya?
Idanunsa ya lumshe Yana Kara Tino abubuwan da suka faru.
Ahankali ya Bude bakinsa yace.
“ku dakatar da bincike, sannan kubar komai a hannu na. Kada ku yi kuskuren yin abinda ban sakaku ba.”
“Yes sir.”
"Yanzu abinda zaku Maida hankali akai shine gano wannan dayan address din, sannan
“Da zarar kun samu wani sabon bayani, ku sanar da ni.”
“Okay sir.”
Sannan ya katse Kiran.
Ajiye wayar yayi a gefensa, sannan Bai ko motsa daga yadda yake zaune a motar ba.
Kallon gidan da ke nesa yake yi.
Yazo da niyar haduwa da wasune game da wani bincike, saidai ayanzu akwai bukatar yasake sabon shiri akan lamarin.
“Me yasa duk abinda yake bincike akai yake komawa wannan gidan?”
Tambayar dayake yiwa kansa kenan Wanda bayi da amsar wannan tambayar tasa, hakan yasa yaja gwauron numfashi tare da daukar wayar tasa Wanda bansan Mai yayi da ita ba, nagadai ya aje tare da murmushi a fuskarsa.
Tabbas ya cancanci akirasa da kyakykyawan dattijo kuwa, sedai ya amsa sunan nasa na mask shadow, domin kuwa nima inuwar tasa kawai na samu damar gani, shifa ko a yanzu dayake cikin mota shi kadai, hakan Bai sa naga Wani abu daya dazai bayyana mana jikinsa ba, yanzu Dana samu na gano muku fuskarsa,sedai yana da kyau na hakika,sedai itama din ba sosai na iya gano ta ba, sedai kamar yadda yan kungiyar black mafian suke neman sanin waye shi, nima haka nake ta kokarin ganin na gano waye shi.
---
A cikin supermarket kuwa, Inarah da su Hibba sun kusa gama siyayyarsu.
Bangaren kayan Maza inarah tayi rike da hannun Ameerah, sabida akwai kayan datake so ta siyawa zakin ta.
Hakan yasa taje ta zaba duk kayayyakin daxata Siya masa, harta juya, se Kuma ta koma tace.
"Bari na daukar wa Yaya mahbub wannan agogon Shima kar na koma gida ya kasa jarida ta atoh," takara maganar ta tare daukar agogon da Kuma zobe taja hannun Ameerah wacce itama take ta janyo hannun nata Dan nuna mata abinda tagani, wacce ita inarah dinma bata Lura ba.
“Aunty inarah”
“Na'am my princess?”
“Kin ga mutumin can kuwa?”
Inarah ta kalli inda yarinyar take nunawa.
Amma ita dai bataga kowa agurin ba, hakan yasa ta shafa kan yarinyar tace nibanga kowa ba.
“Ya tafine.” shine a inda Inarah ta fada
Ameerah ta ɗaga kafaɗarta, cikin iyayi irin nata, Wanda hakan seda yasa Inarah tayi dariya.
“lily Yana ta kallonki fa, kamar ma mara gaskiya Allah.” ta fada Kai bazaka ce yarinya ce yar shekara biyar ba.
Inarah ta yi dariya sosai sannan tace.
“Ke dai kin cika magana princess, har kinsan mara gaskiya ma,” takarashe maganar tana dariya tare da rumgume yarinyar
Hibba wacce ta karaso gurin, ganin sun Dan jima basu tawo ba yasa ta biyosu aikuwa ta fashe da dariya.
“Wallahi Ameerah photo copy dinki ce lily, Sam bakinta ba full stop, ga Dan banzan surutu kamar aku.”
“ina ruwanku yan sa ido?” inarah takarasa maganar suna barin bangaren gaba daya suka tafi domin biyan kudin
“aku da aku anhadu ai mu gidanmu yanzu ba shiru.” zaitoon ta fada tare da yiwa inarah gwalo ganin irin hararar data wurga mata tana fadin "eh din.
Inarah ta harare ta.
“Hibba!”
Dukkansu suka yi dariya.
Zaitoon ta ɗauki wata jaka.
“Mu je checkout kafin Ammie ta kira ta tambayi ina muka tsaya, Dan yanzu ma se tace mun Dade, na rasa me yasa Ammie yau Sam bataso futowarmu ba.”
Hibba ta jinjina kai.
“Gaskiya Kam, gara muyi mu koma.”
Suka fara nufar wajen biyan kuɗin.
Kafin su isa, wayar Inarah ta fara ringing, dayake wayar na hannunta dubawa kawai tayi taga number din zarah ne, wayar tasa a kunnen nata tace.
“Hello Besty?”
Muryar Zarah ta fito cikin sauri.
“Naam ykk, Lilly kina Ina ne?”
“munje Supermarket tare da su hibba, meyafaru me naji muryarki haka?.”
"Ba komai lilly ki kula dakyau, ki gaggauta komawa gida zan biyo ta gida muyi magana.
“meyake faruwane besty, naji muryarki Wani kala, akwai matsala ne?”
“Ba zan iya gaya miki ta waya ba, lilly, Amma wannan karon abin ya fi wanda muka zata girma, Ashe abun ba karami bane, gaskiya hankali na ya tashi lilly, kiyi sauri ki koma gida.
Inarah ta sauke numfashi, sannan tace.
“Game da yaran nan ne?”
“Eh.”
Fuskar Inarah ta canza.
“Yanzu zan dawo inshallah.”
Ta kashe wayar.
Hibba wacce ke ta kallonta tunda ta fara wayar tace.
“Me ya faru?”
“Zarah ce ta kirani Wani sabon bayani ta samu game da case ɗin da muke bincike.”
Zaitoon ta tambaye ta ganin yadda take ta saurin sauri,
“Case ɗin yaran nan da kike bamu labari?”
Inarah ta jinjina kai tace.
“Eh.”
Ameerah ta kalli fuskarta tace
“Aunty Lily, yanzu office zaki tafi?”
Inarah ta sunkuya ta shafa kanta, sanan tace.
“ba office Zan tafi ba princess gida zamu koma.”
Haka suka fito sukaje suka biya kudin komai Sannan suka fito daga cikin super market din, suka shiga mota.
Suka bar harabar super market din sun dau hanya naga wata bakar mota ta mara musu baya.
---
Alhaji Gali ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa, jikinsa har rawa yakeyi.
Nan take ya ɗauki wayarsa ya kira wata lamba.
“hello ranka ya dade, Anyanka ta tashi fa.”
Daga Dayan bangaren aka bashi amsa Wanda banji me aka ce ba.
Muryar ɗayan ɓangaren taci gaba da magana wacce banji me aka ce ba
Alhaji Gali ya sauke numfashi.
“hakan za'ayi gaskiya kakawo shawara, duk yadda zaayi ayi gaggawar daukar mataki.”
Shiru. Yayi nadan lokaci kafin naji ya sake cewa
“Ayzaan Mai rabo babban baraza ne ga rayuwarmu, a wanann karon akashesa kawai,duk da a yanzu baishiga harkarmu ba Kuma ba wata a tsakaninmu Amma tabbas ni Ina tsoron sa duba da wahalar da muka Sha akansa ,Sannan. Akwai bukatar asake zama gaskiya, duk da nasan yanzu mungama dashi, Amma asake Wani sabon...”
Bekai ga karasa maganar tasa ba yaji karar kofar, anbude anshigo kamar ko yaushe Babu sallama
Da sauri ya katse wayar ya daga Ido Yana kallonta yace
My dear me yafarune?
“Dad...”
Ya kalleta.
“yaakayi dear, me ya faru?”
Cikin shagwaba sosai da sangarta ta budi Baki sannan tace.
“Na zo ne in tambaye ka dad... shin ka fara bincike akan Ayzaan?”
Fuskarsa ta sake canzawa.
Wannan karon kuwa sai ya gane cewa...
ba Ayzaan kaɗai ne zai iya kawo masa matsala ba.
Saboda 'yarsa ta riga ta fara shiga cikin wannan sirrin da ya dade yana ƙoƙarin binne shi.
A hankali ya ce,
“Eh... zan fara.”
Amma a ransa kuwa cewa yake:
“Allah ya sa ban makara ba.”
Amma tabbas se na raba Meerah da wancan mara kunyan yaron,inya tuna yadda yashuka musu rashin mutunci ya Hana su bacci da fargaba har se da sukayi maganinsa,Kuma basu sake fuskantar matsala daga bangarenba hakan yasa suke cin karen su Babu babbaka,Amma yanzu anbatar Ayzaan da Meerah tayi se yake ganin kamar Wani tarko ne Ayzaan din yayi musu da hakan.
To Amma dai koma menene zamu gani dai.