JA DA BAYA...

MUTUWAR INNOCENT AMEERAH😭

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 25✍️*

***

Alhaji Gali ya amsa mata, amma zuciyarsa cike take da wani irin tashin hankali da bai taba nuna wa Meerah shi, murmushi ya kakalo na dole ya daura a fuskarsa.  

Meerah itama Maida masa da martanin murmushin nasa tayi tana fadin.  
“Thank you Dad. Na san kana son farin cikina, Kuma duk abinda nakeso zakamin shi ko menene shiyasa nake sonka dad.”  
Ta karasa maganar tana rumgume shi.  

Hannunsa ya ɗora a bayanta, yana shafa bayanta a hankali, amma hankalinsa yana can wani wuri.  
A cikin zuciyarsa kuwa tambaya ɗaya ce kawai ke yawo.  
Ta yaya zai hana Meerah kusantar Ayzaan ba tare da ta gano dalilin hakan ba?  
Domin ya san 'yar tasa kome takeso bata tsaya jinkirin, ita duk abinda takeso akwai ta sameshi sannan tun tasowarta batasan ace kartayi abu ba, kome tace tana so kawai Yi mata sukeyi.  

“Dad?”  
“Na'am.”  
“Me yasa ka yi shiru, kamar kana tunani?”  

Ya yi murmushi ya kalleta, sannan yace.  
“Babu komai dear. Kawai ina tunanin inda zan fara.”  

“dad Ka fara da Samo min number ɗinsa please dad.”  
Alhaji Gali ya ɗan tsaya, jim sannan yace  
“Number kike so dear?”  
“Eh dad, Duk wani abu dai da zai sa na samu damar magana da shi.”  

Ya kalleta na ɗan lokaci.  
“Meerah, ba ki saurari abinda na gaya miki ba kenan?, Amma zan kawo Miki number din kamar yadda nace, Amma karkiyi wani abu akai, sannan karkije inda yake?”  

Ta turo baki cikin shagwaba tace.  
“Amma Dad...”  

“Ki bar komai a hannuna. Zan yi miki bincikenki. Amma ki yi min alƙawarin ba za ki yi wani abu da kanki ba ?” ya katseta cikin rarrashi  

Ta yi shiru bata iya cewa komai ba.  
“Meerah,” yafada Yana kallonta.  
“To Dad, na yi alkawari.”  

“Good that's my baby”  
Ta sake rumgume shi tana fadin.  
“I love you Dad.”  
“I love you too, my princess.”  

Ta yi murmushi sannan ta tashi ta fita daga bedroom din nasa.  
Murmushin da ke kan fuskar Alhaji Gali ya gushe kuwa bayan fitar meearah Nan take ya gushe  
Ya tsaya cak.  

Tashi yayi ya shiga bandaki aransa Yana fadin zama Bai ganni ba dole nasan abinyi.  

---

Inarah kuwa suna tafe a hanya, Amma gaba daya hankalinta Yana kan zancan da zarah ta kira ta gaya mata, sannan haka kawai taji wata faduwar gaba Mai tsanani ta riske ta.  

Zaitoon ce take tuki, hibbah tana zaune gefen Mai zaman banza, itakuwa inarah tana baya tare da Ameerah da Afeef, duk surutun da sukeyi inarah bata sa Baki ba tayi shiru tana tunani.  

Kalaman Zarah suna ta dawo mata, inda ita kanta take tuna irin manyan sirrikan data gano game da lamarin.  
“tabbas wannan karon abin ya fi wanda muka zata girma,” shine abinda ta fada azuciyarta tare da juyawa ta Kalli window.  

Hibba dake kallon ta, ta madubi, ta Bude Baki tace.  
“lilly najiki shiru bakiji abinda nace bane?”  
“Na'am, banjiba mekika ce?.”  
“No, naga duk kindamu ne sosai, kidena takura kanki fa.”  

Inarah ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan tace.  
“sanin kankune bana boye muku abubuwa dayawa da suka shafi aikina, Amma tundaga kan mutuwar jikar babah adama nasa ma abun ayar tambaya, duk da a bune daya Saba faruwa Amma nasan tabbas akwai Wani a bayan lamarin, Amma Ban sani ba akwai wani abu da nake jin ba daidai bane tabbas.”  

Sannan ko jiya Ankara samun batan yara har guda shida, Wanda gawar daya kawai aka samu, Shima anyake wasu sassan na jikinsa, har idanuwan sa ancire, wannan rashin imani da me yayi kama? kokuwa Mulki haukane? Masu aikata wadannan muggan abubuwan suna cikin al'umma sanye da lullubi na Kamala, ni Kuma nayi alkawarin sai na binciko kowanne me hannu aciki, Kuma dole hukuma ta hukuntasu." ta karasa maganar Kai daji kasan abin Yana mata ciwo sosai.  

Zaitoon ta juya ta kalle ta sannan tace "kibi komai a sannu dai lily, kidena matsa ma kanki kodan ciwon ki baya bukatar damuwa, duk masu aikata irin wannnan abubuwan Ina mamakin Kuma suke iya rayuwa da wannan hakki akansu?.  

Hankalina yatashi wlh jiya ganin labarin wata mata tana ta kuka sosai, yaronta daga aikensa siyan Omo aka dauke sa, kwana biyu Babu shi Kuma duk inda zasuyi cigiya Babu karshe fa a Wani kangon aka gansa anyanke masa gaba, wannan zalinci da me yayi kama, Kuma duk akan duniya duniyar da barinta zamuyi ko munshirya ko bamu shiryaba". hibba takara maganar cikin jimamin abinda yake faruwa.  

Inarah ta sauke numfashi tace inshallah zanyi kokari na kiyaye.  
Amma abinda ya fi bani tsoro shi ne, idan har bayanin da ta samu gaskiya ne game da abinda muke nema, to wannan ba case ne da za mu iya ɗauka da wasa ba, domin kuwa babban lamari ne Mai girma.”  

Zaitoon ta rage gudun motar tace.  
“Ki yi haƙuri Lily. Inshallah komai zai zo da sauki, nibansan meyasa kike daura ma kanki matsalar wasu ba ni aganina wannan ba damuwarki bace, Amma dai inshaallah akomai kece da nasara.”  

Inarah ta jinjina kai tace.  
“Allah ya sa hakan,” tana ci gaba da fadin, "nikam zaitoon shiyasa banson driving dinki ayi ba ayi ba, ko sauri bakyayi  
Keni motar ce ma naji kamar ba daidai ba, dakyar nake tuka ta fa.  

Ameerah wacce ke gefenta ta ɗaga kai daga kallon game din datakeyi da wayar inarah da ke hannunta, tace.  
“Aunty Lily.”  
“Na'am princess?”  
“bana gaya Miki ba, waccan motar fa tun daga kusa da supermarket take binmu, Amma Baki yadda ba.”  

Duk waigawa sukayi gaba daya suna so suga abinda Ameerah din take nuna musu.  
“Wace mota,” duka suka hada Baki suna tambaya?  
Ameerah ta nuna ta taga tace.  
“Waccan baƙar.”  

Hibba wacce gabanta ya Fadi ta duba motar, sannan tace  
Da gaske ne fa  
Baƙar mota ce a baya.  
Ta ɗan yi shiru.  

Zaitoon kuwa cewa tayi  
“Ko dai hanya ɗaya ne kawai ya hadamu, Amma inba haka ba me zaisa wata mota tayi ta bibiyarmu ?”  

Hibba ta sake kallon madubi sannan tace  
“Ban sani ba gaskiya, Amma nima yanzu nayi tunanin hakan, Amma da wlh har gabana ya fadi”  

Inarah ta kalli motar wacce suke magana akai, tinted ce shiyasa Ba ta iya ganin fuskar ko ma waye aciki, bare Kuma agane me akeyi a ciki.  
Sedai wani irin yanayi ne ya risketa Nan take Wanda batasan dalili ba Sam, da kyar ta iya Bude Baki tace.  
“Kar ki tsaya zaitoon ki Kara gudu kokuma ni nazo na cigaba da driving din.  

A wauta irin tasu maimakon suyi kokarin Kiran wata lamba Amma Ina Sam basuyi wannan tunanin ba.  
Hibba ce ma ta kalle ta tana kokarin fadin "kodai nakira ko Abbah ne ko Yaya sadeeq? sedai bata Kai ga karasa maganar da take kokarin Yi ba kawai sukaji karar harbi ta setin bangaren inda inarah take.  

Ido suka rintse gaba dayansu cikin matukar gigicewa da tashin hankali, Wanda idanuwansu yake rufe basusan meyake faruwa ba, kokuma wa aka harba din acikinsu, domin kuwa abune da Bai taba faruwa a rayuwarsu ba basu taba hasoso hakan ba, shiyasa duk suka kame kamar wasu gumaka.  

Sedai Kuma a bangaren bayan ma inarah ce wacce ida nuwanta suka kafe kaf akan fuskar ameerah domin ita ta kasa rufe idanun nata sedai kamar bata numfashi itama, babban abinda baaso agareta shine Kara Mai tsanani sabida lalurarta, to da alama karar Harbin da akayi ya jefa INARAH cikin Wani hali.  

Sedai idanunta abude suke tar akan fuskar ameerah wacce jini ya wanke wa fuska, da alama dai Babu numfashi ma ajikinta.  

Abinda ya faru shine ameerah Wanda ta dago da niyar nunawa inarah abinda take kalla awaya, kasantuwar Afeef shi Yana kwance Yana baccine a sit din bayan, ita kuwa ameerah tana ta game dinta tana dariya, to  
Yunkurowar datayi tana fadin aunty Liliy kalla, yayi daidai da Harbin da akayi daidai setin inarah din sedai dagowar da Ameerah tayi shine yaba harsashin damar sauka a tsakiyar goshin ta, Wanda bata Kara Koda motsi guda daya ba, maganar da ta Bude Baki zatayi ta tsaya cakk.  

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.  
Shine abinda hibba ta samu damar fada cikin dimuwa, dawani irin tashin hankalin da bata taba riska ba arayuwa.  
ita kuwa inarah har zuwa lokacin bata motsa agurin, idanunta dai na kame kam, akan fuskar ameerahn.  

Ko karar motar jami'ai da suka karaso wurin basujiba, Wanda har Abbah ya karaso gurin cikin matukar tashin hankali Amma gaba dayansu basusan da hakan ba hasali ma hibba ce kawai nake ga kamar Mai rai acikin motar, domin shi Afeef dayake kwance a kujerar Banga motsinsa ba.  
Haka zaitoon wacce take tuki harzuwa lokacin itama Banga ta motsa ba.  

Muryar hibba ce kawai cikin tsananin kuka take fadin.  
"Princess?"  
"Ameerah..."  
Zaitoon....  
Inarah...  
Afeef.....  
Wayyoooo Allah na shiga uku na lalace innalillahi WA inna ilaihi rajiun, bawani anan yataimaka mana. take fada cikin ihuu ta kasa ko kwakwkwaran motsi  
"Ameerah, ki tashi mana..."  
Muryarta ko fita batayi sabida kukan datakeyi  
"Princess... kina ji na kuwa?"  
"Lily.. me yake faruwane kina jina?"  
Ina ba amsa.  
Zaitoon kibude idonki Dan Allah bawani Wanda yake jina ne, zaitoon, Afeef!, lilyyyyy wayyoooo  
"Ameerah... don Allah ki buɗe idanunki."  

Abbah ne tare da jamian da suka zo gurin yayi Maza cikin matukar gigicewa ya Bude motar, yadda yagansu Babu Mai motsi Banda hibba yasa yaji Wani irin faduwar gaba har Jiri Yana neman Zubar dashi.  

Hibba kuwa ai da gudu tafito daga cikin motar ta kankame Abba cikin gigicewa da sambatu take fadin sun mutu, Abba lilly ta mutu zaitoon ma haka, inarah Abba, ameerah Afeef, Abba duk sun mutuuuuu.  
"Ya Allah! Ya Allah!" ya Allah!  
Innalillahi WA inna ilaihi rajiun shine kawai abinda ya fitowa daga bakin Abba.  

Wanda cikin gaggawa ambulance din data karaso akadaukesu gaba daya zuwa asibiti, Abba yarasa tunanin dazaiyi shiga motar ambulance din yayi tare da hibba wacce ita ma dai ta sume masa  

"kai mu asibiti! Da sauri!, Yi Maza kakaimu" shine abinda Abba yake iya fada kawai cikin firgici, Babu inda baya rawa ajikin nasa hannayensa sumu rawa sukeyi.  

Isarsu asibitin na Mai rabo cikin gaggawa aka karbesu, kasantuwar su sanannu Kuma asibitin nasune.  
Mahbub yafi Abbah shiga cikin tsananin tashin hankali yarasa Wani irin taimako ma zai basu kokuma wa zai fara taimakawa, gaba daya ma ya koma kamar ba likita ba.  

Haka dai likitoci suka hadu akansu Wanda sungano firgici ne yasasu Suma sedai ita ameerah tuni Rai yariga yayi😭 halinsa, Wanda izuwa lokacin wasu daga cikin ahalin sunsan abinda yafaru, sedai Kuma duk sun Farka Afeef ne kawai yake bacci kasantuwar ko lokacin da abin yafaru shi bacci yake yi, karar harninne yatasheahi har yakaisa ga Suma.  

Kuka sukeyi sosai da sosai game da mutuwar yar karamar yarinyar da bataji ba bata gani ba.  
INARAH kuwa da Wani irin azabbaen ciwon Kai ta tashi Wanda anyi mata allura Amma baccin yaki daukarta, ameerah kawai take kira cikin fitar hayyaci  
fuskar yarinyar da ta saba yi mata surutu kawai take gani tana tunawa da kalamanta na ƴan mintuna da suka wuce.  
"Aunty Lily... waccan motar fa tun daga supermarket take binmu."  

Hawaye suka ƙara zubo mata masu matukar radadi  
"Kin faɗa min... kin faɗa min Ameerah... Kin fada, Amma meyasa ban saurarekiba?  

Ameerah ta kasance yarinyar da ba ta san tsoro ba. Ƙaramar yarinya ce da kullum bakinta cike da magana. Duk inda Inarah take muddin sunzo garin to tana tare da ita.  
"Aunty Lily..."  
Muryar ameerah tasake dawo mata a cikin kunnenta.  

Inarah ta fashe da Wani irin matsanancin kuka tare da rike kanta Wanda yake barazanar rabewa biyu, ko idanuwanta bata iya budewa sabida azabar radadi dasuke mata.  

Irin yadda taki kwantar da hankalinta yasa dole gaba daya suka hadu suka tafi gida, tare da gawar ameerah wacce har lokacin jini Bai Dena zuba ba.