Chapter 22 (KAKA A ASIBITI)
by @smauta
***
Group na littafin BABAN KAWATA BY SMAUTA 🖌️
Manar ce zaune kusa da jakar kayansu da kaka akan stretcher kaka kiyi hakuri munzo inda zaki samu lafiya hawaye na kufce mata,a hankali kaka ta kalli manar dinta daidai lokacin dede ta iso itama rike da jakar kayanta hannun dede kaka ta saka cikin na manar ta fara cewa ku rike juna ku so juna karku rabu da junanku,yaya dan Allah kibar wannan maganar cuta fa ba mutuwa bace da yardar Allah sauki zaizo kiyi rayuwa kema kamar kowa..........
Khalil ne suka fito shida kawo labaran daga ambulance din da sauri jude ya karaso wurin shi oga sannu da hanya yawwa ga likitan nan zuwa ok,kawu labaran kyaun asibitin kadai ya tabbatar masa da wannan fa asibiti idan ba mai hannu da shuni ba babu mai iya tako ta Alhajin Allah, na'am kawu me kake nema daga garemu,dariya ma khalil tambaya ta bashi ya kwantar da murya a hankali kawu bana neman komai na rasa iyayena da kakannina nasan yadda rashin kulawa yake tunda Allah ya bani abinda zan taimaka dashi zanyi nima bansan inda Allah zai taimake ni ba............
Gaba ɗaya maganar nan dasukeyi suna jinsu dede ce ta kalli khalil sosai Allah ya saka maka da alheri Allah yajikan magabanta ya hanaka ganin bakin cikin duniya dana lahira yaro yadda ka farantama kaima Allah ya faranta maka kaji dukkansu suka amsa da Amin,da sauri likitan ya iso aka shige dasu dakin da za'a ajiye kaka...........
Oxygen suka fara daura mata likitoci 7 ke kewaye da kaka,wani daga cikin likitocin ne ya fito ya dubeso cirko cirko oga yayima khalil magana muna bukatar CT scan,blood test,heart test,dole mu fara sanin mene matsalar kafin mu dorata kan magani,khalil yace duk abinda kuke buƙata ga jude nan kar a tsaya jiran komai ayi komai cikin gaggawa pls kudi ba matsala bace.......
Kawu labaran ya marshe kasa ya daga hannu sama Allah ka anshi addu'ar mu dun surutun dede jikinta yayi laasar saishi dake zuba kamar radio galla masa harara kawai tayi ita da anbi shawarar ta wallahi bazaa taho da labaran ba abinda zai masu nan sai abun kunya,manar na gefe daya ba wanda take kallo sai Khalil tana kallon alheran shi gareta shima duk baida natsuwa ganin baby girl a damuwa daga mata gira yayi alamar what's wrong?????
Saddar da kanta kasa tayi ya tako har gabanta cikin taushin murya zatayi lafiya In Shaa Allah,ta gyada kai Allah ya amince
Har 11 na dare bawani labari kowa yagaji su zauna su tashi aikin kenan,kawu labaran kuwa yayi male male baccin shi kawai yakeyi kan kujera,likita ne ya fito fuskar sa cikin damuwa suwaye dangin kafin ya karasa karaf dede tace gamunan,muna bukatar muyi mata aiki na gaggawa zuciyar ta nada matsala sosai akwai ruwa dake taruwa a cikin huhu idan baayi mata aikin ba nan da 24hours za'a iya rasa ta........
Komawa dede tayi ta zauna dabas tana Innalillahi wainna ilaihir rajiun
Khalil ya matso nawane kudin aikin Dr?
25 million naira manar dake gefen Khalil ta kara sautin kukan ta jin wannan uban kudi da aka kira duk wannan abun kawu labaran baccinsa yake hankali kwance 🤣🤣 sai dakai kawun mu na zudda mutunci😹😹💔.................
Khalil yace hurry up dr ayi mata aikin yanzu zamu biya kudin jude ya kira yaje yayi payment komai da komai nan take, addu'a dede ke kwararama Khalil bakomai mama labaran dede ta kalla har minshari yake ta tafka mashi bugu a kafa tashi aikin baccin kazoyi kanada marar lafiya irin haka,kudin aiki miliyan ashirin da biyar kai bacci kakeyi,wata wuntsila yayo yace ke dede ba kyau tayarma da ɗan uwanka hankali yanzu ina yayar??????
Tana ciki za'a fara aikin ina aka samu kudin Khalil ne ya biya,khalilu kaine ka biya kudin nan anya kai mutum ne kuwa?me yasa kake mana wannan dawainiyar ,manar ya kalla kawu saboda ita ne kuma ta cancanci farin ciki kuma ya tsaya bai idasa mai zaice ba🥹
Saida ya tabbatar da anshiga aikin yayi masu sallama dan yanaso zaije gida ya huta,manar ya kira sulum sulum ta biyo bayan shi wata leda ya dauko ya bata waya ne a ciki akwai number na a ciki duk abinda kuke bukata ku kirani jude zai tsaya daku anan ga abinci nan an kawo pls ki natsu kici a hankali tasa hannu ta karba nagode nagode nagode shiiii ya dora hannun sa a bakinta kije ciki banda kuka kinji ko...........
Haske mai haske ya haske ko ina an ɗora kaka a gadon aiki likitoci 4 ne akanta ga nurses suna ta sauri,kawu labaran ya zauna kasa tasbihi yake tayi Allah ya baki lafiya yaya banda ke bamuda wani gata,idanun dede dake jawur ta kalle shi labaran kabar kukan nan dan Allah addu'a take buƙata ke dede yanzu uwaki nakeyi ehhhhh,manar ta cukunkune kanta cikin cinyoyinta ya Allah ka ba kaka lafiya ya Allah karka sakani a cikin maraicin daba zan iya jurewa ba,wayar daya bata ce ta dauki ringing ta kara a kunne,har yanzu kukan kikeyi?ina tare dake ba abinda zai faru da kaka wani sanyi ya mamaye zuciyar manar nagode kawai ta iya furtawa wayar ya fiddo a kunnen shi jin kiran da ake masa ZAINAB ya fada cikin ranshi a hankali..............
Idon Dede nakan manar sarai tagane da wa take wayar Allah mungode maka daka aiko mana wannan yaro cikin zuriyar mu bayan awa hudu nurse ce ta fara fitowa dukkansu sukayi tsalle suka mike nurse lafiya?
Alhamdulillah anyi nasara a aikin amma har yanzu tana ICU tanada 24hours idan ta tsallake su aiki yayi ta tafi ta barsu nan tsaye cirko cirko..........
Masallaci kawu labaran ya tafi sallah yayi raka'a biyu da zummar Allah ya tashi yayar shi,dede ce ta rungume manar alhamdulillah Allah Allah yasa mu cigaba da jin alheri amin,dr ne ya fito dede tace likita lafiya eh lafiya lau take hajia amma bazaku iya ganin ta ba sai gobe ga nurses nan zata raka ku dakin da zamu kawota goben sai kwana a wurin,ka tafaren daki ne mai dauke da ciki da parlour har biyu kai kace hotel ne suka ba asibiti ba jakunkunansu manar takai dayan dakin ta fito kawu labaran na parlour anan zai kwanta dede ta kalli manar ke manar jeki ki wanke fuskar ki kizo kici abinci,dede banajin yunwa eh nasani bakyaji amma sai kinci abincin nn..............
Da safe wurin 10 Khalil ne da kanshi ya iso asibitin bayan sun gama gaisawa yake tambayar manar me zakuyi breakfast nidai na koshi,umarni nake baki akan cin abinci ba neman shawara ba fita kawai yayi yaje ya saka masu order abinci,
Fitar sa keda wuya dede ta kalli manar a hankali manara meke tsakanin ki dashi?
Firgita manar tayi Ba bakomai shine kawai nace maki ya taimakeni,naga yadda kuke kallon juna kiyi hankali da yarintar manar mutumin nan na lura zuciyar shi a karye take dake karki idasa karyata,manar ta kasa ansawa a cikin zuciyar tace dede bakisan nice tawa zuciyar a karye ba🥹🥹🥹🥹🥹🥹