BABAN KAWATA

Chapter 23

by @smauta




Duk suna gaban ICU zaune da sauri suka nurses nata shiga da kayan aiki Dr ne tsaye kan kaka bani na'urar caji jini yana sauka daga zuciyar ta ne zuwa huhunta sauri da gudu wata nurse ta fito khalil yasha gabanta lafiya,sir lafiya kadan ta farfaɗo amma jini na sauka huhunta zan iya shiga???yayi tambayar a rude no ICU ne bazaka iya shiga ba.............




Dede tana rike da manar dukkansu suna wani irin kuka mai tsuma zuciya dede ce ke sabbatu Allah kabarmu da yaya itace gatanmu ba uwa ba uba ita muke gani muji dadi,kawu labaran ba abinda yakeyi sai aikin salati yana fareti bakin ICU.........




Sautin Beep Beep Beep sannan ya tsaya layi madaidaici



A hankali Dr ke fitowa duk sukayo caaaa akan shi dr lafiya a hankali ya sadda kanshi kasa yace munyi iya bakin kokarin mu dede ce ta fadi kasa manar ta rufe bakinta da hannu idanunta sun fito waje sosai jawur Khalil sumar tsaye yayi kimmm kamar dutse bai iya magana ba,dede ya kalla sannan ya kalli manar duk wani kwarin gwiwa ya rasa shi a lokaci daya 🥺 likitan ya cakuma karya kake bata mutu ba bazata mutu yanzu ba..............




Likitoci ne wannan yashiga wannan ya fita duk suna kan kaka kaka da zuciyarta ke bugawa a hankali karar na'urorin daya karade kunnuwan likitoci da Beep Beep Beep dr ne da sauri yace ta dawo ta dawo dukkansu sujuda sukayi a wurin suna godema Allah......





Dukkansu suna cikin dakin ICU tun bayan farfaɗowar ta,kaka na bacci mai nauyi hancinta na like da oxygen kawu labaran na rike da hannunta yaya ki tashi karki tafi ki barmu daga gefe guda kuma dede na hamdala Allah yaji addu'ar su,manar kuwa zaune take a gefe idanunta sun kumbura........




Kakace ta bude idonta a hankali manara ta zo kusa dani daga Dede har kawu labaran sumar zaune sukayi da gudu manar ta iso bakin gadon tana share hawaye kaka nice manarar ki ce kaka kin tashi??wannan yaron na waje wanene sai lokacin suka kalli kofa Khalil na tsaye yana kallon su kaka shine wanda ya ceceni ya ceto rayuwar ki da taimakon Allah, lumshe ido tayi ta bude kice yashigo shima yazama iyalinaaaa.............




Manar na hawaye tace naji kaka,manar kice masa nagode ya dauki nauyin daba nashi ba dede,labaran yadda zaku rike manar amana ku rikeshi amana bacci ya kara daukar kaka shuru sukayi,sai lokacin kawu labaran ya mike yaje bakin kofa Khalil shigo a'a girgiza kanshi yayi alamar a'a................




Ka shigo kaka ce tace ka shigo a hankali ya karaso amma yana nesa da gadon manar ta kalleshi hawaye cike da idanunta sannan tace nagode nagode,a hankali Khalil ya kalli dede yace nagode...........




Dashi da manar sukaje office din dr yana masu bayani,sir ta tsallake mafi hatsarin amma zata kwana daya anan ICU kafin mu kaita ward kuma idan akwai hali tayi recovering akwai wani gashi da akeyi a Germany indai akai mata shi ita da ciwon zuciya har abada,manar ya kalla ta gefen ido sannan yace dr duk abinda yakamata acan din kayi mana booking na likitan zamu fara processing visa..........




Batasan lokacin da takai masa wata wawar runguma hannunshi biyu ya saka yayi folding dinta da kyau yana shafa bayanta tausayinta a yanzu shine raunin shi,dr ficewa yayi yabar masu office din,dago kanta yayi MANAR why are you doing this????bansan dawane baki zan gode maka ta kara rungume shi sosai yakan jiyo bugun numfashi ta akan kirjin sa.............




Ta dora hannunta kan nashi ni marainiya ce banida kowa sai kaka ciwo yazo mata a bazata a lokacin da nake ganin rasa ta shine abu mafi sauki gareni Allah ya jefoka cikin rayuwar mu ka taimakemu kayi mana abinda mu bamuyi ma kanmu ba,to ya isa haka karki godeman ki godema Allah kuma yanzu nazama ahalin ku inji kaka,muje ki huta nizanje gida akwai aikin da zan kammala a gidan zamu tafi da kawu labaran shima ya huta da dare saimu dawo ko..........




Wajen ICU suka samesu dede tace yaron nan bayan wannan dawainiyar kuma wata za'a kara mana yanzu likita yake fadama nagode bata karasa ba ta fashe da kuka, bakomai mama kawu zanje gida idan ba damuwa muje tare ka huta zuwa dare saimu dawo ai kawu labaran kamar jira yake yayi tari eh da kyau hakan muje mu huta gobe mun dawo🤣🤣🤣🤣