BIYU A ƊAYA

Chapter 15

by @barista

BIYU A ƊAYA 
    (Don't judge a book by its cover)


Page 15
Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
TEAM FIVE INK LEGENDS 


Bata ƙarashe faɗin sunan ba, Maman ta ce

"Ya isa haka Bilqees, ki kwanta ki huta duk kin gaji"

"To Mama"

Ta maida wallet ɗin cikin jakarta, ta kwanta, nan da nan ta yi bacci ....

********************************
WASHEGARI 

Da kyar ta farka a barci, duk jikinta yana yi mata ciwo, ga ciwon kai da ta tashi dashi, da ƙyar ta mik'e ƙafa ta ce yi tafiya mu gani, da ƙyar ta fito ta shige toilet ta ɗauro alwala ta dawo ciki ta idar da sallah, ta juyo ta kalli Mama dake zaune kan dardumar sallah tana lazimi..

"Barka da safiya Mama"

"Bilqees an tashi lafiya"

"Ƙafata ciwo take yi min"

"To an ya ba za ki zauna ki huta ba?"

"Haka nake ji, ko za ki faɗawa ALAJA ƙafata ke min ciwo ba zan iya tafiya restaurant ba"

"To bari na je na sanar da ita don kada ta fice bamu sani ba"

Maman Bilqees ta mik'e ta fito ta wuce ɗakin ALAJA ta tadda tana ƙoƙarin fitowa ta ce da Alaja

"ALAJA barka da safiya har an yi shirin fita aiki?"

ALAJA sake kulle ƙofar ɗakinta ta kammala ta juyo tare da cewa 

"Yawwa Maman Bilqees, gari ya waye za a koma bakin aiki"

"Ah to madallah ubangiji ya yi jagora"

"Amin ina Bilqees? t
Ta fito mu wuce"

"Ai Bilqees ƙafarta tana ciwo ba zata iya fita ba"

Sai a lokacin Alaja ta tuna da abin da ya faru jiya, amma ta basar tare da cewa 

"Ciwon ƙafa kuma? Me ya samu ƙafar?"

Maman Bilqees ta san halin ALAJA da maida abu kamar bata sani ba, ta sauke numfashi tare da cewa 

"Lafiya fah muka kwanta da safe ƙafa ta tashi da ciwon"

"Mu je na gani"

Suka shigo side nasu, Bilqees da bacci ya soma satarta, jin motsin shigowa yasa ta buɗe idanunta. ALAJA ta zauna kusa da ita tare da duba ƙafar da gaske ta kumbura, nan Bilqees taga tashin hankali wajen Alaja, ta riƙe ƙafar tana

"Bilqees sannu, haka ƙafarki ta kumbura? Ya ki ke ji? Me ƙafar take miki? Ba za ki iya tashi bane?"

Mamakin yanayin da Alaja ta shiga ne Bilqees ke yi, a take ta kiɗime, hankalinta ya tashi, Bilqees ta buɗe idanunta ta zuba su kan Alaja, jiya fah tana magiya akan ta taimaka mata amma fir taƙi yanzu kuma ta tashi hankalinta, a hankali ta furta 

"Maa"

"Yes Bilqees how are you feeling?"

"I'm feeling better now"

"Sannu tashi muje chemist na Dauda, ana samun shi da safe, da wuri yake fitowa"

"A'a Maa, i can't walk"

"Don't worry Bilqees, I'll take you there"

Ta cicciɓi Bilqees kamar jaririya ta fito da ita a lokacin su Majada, Laraba da Jummai suna tsaye suna jiran fitowar Alaja su wuce aiki ganinta ɗauke da Bilqees a hannu yasa suka taɓe baki. ALAJA bata bi ta kansu ba tayi ficewarta waje, tana isowa chemist ɗin ta ajiye Bilqees kan kujera tare da cewa 

"Dauda ka duba ƙafarta, duk abin da ya dace ka aiwatar"

Bilqees sai bin ALAJA take da idanu, ganin tausayi da tashin hankali a idanu da fuskar Alaja yasa ta soma hawaye, kamar ba Alaja ba..

"Maa"

"Bilqees sannu za ki samu lafiya, ki daina kuka"

"Thank you"

ALAJA ta dube ta sosai tare da sake cewa

"Yanzu Dauda zai duba ki"

Dauda ya duba Bilqees sosai yaga ganin abu ta taka, yasa ya yi mata allura sannan ya basu magani, Alaja ta sake kinkimo Bilqees ta dawo da ita gida, sai da ta saka ta cikin ɗakinsu ta kwantar da ita sannan ta ce

"Zan wuce aiki Maman Bilqees ki kula da ita"

"To ALAJA an gode"

Cewar Maman Bilqees amma Alaja ta fusata cikin ɓacin rai ta ce

"Is she not my child? Da za ki ce kin gode Bilqees is mine"

"Uhm haka ne Allah ya bata lafiya"

"Yawwa that's right"

Ta fice, Bilqees ta lumshe idanunta tana tuno abubuwa da dama, wasu al'amuran rayuwarta na ɗaure mata kai, tabbas Mama ce ta haife ta amma me yasa Alaja ke jin raɗaɗin ciwon dake jikinta...

"Bilqees ko na haɗa miki kunu ki sha"

"A'a Mama bani sha'awar cin komai"

"To ai ba za ki zauna da yunwa ba"

Shigowar Majada yasa Maman Bilqees cewa

"Majada ke ce?"

Don kai tsaye suke ɗaga labule su shigo, babu sallama ko neman izinin shigowa.

"Ya jikin Bilqees"

"Da sauƙi"

"Ga wannan in ji Alaja"

Ta ajiye ta fice, maman Bilqees ta buɗe abubuwan sha ne da ciye-ciye, Bilqees bacci ya ɗauketa ba tare da ta ci komai ba...


International hotel

Buɗe idanunsa ya yi ya kurawa fankar dake kaɗawa a hankali, ya ɗau tsawon mintina a haka, sannan ya duba wayar sa yaga time 9:30 am, tun da ya idar da sallah asuba ya kwanta sai a wannan lokacin ya farka daga bacci. Ya yi miƙa ya tashi ya sauƙo daga bed ya faɗa toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya yayi kyau sai ƙamshi yake yi....

Nocking da aka yi ne yasa ya buɗe ƙofar ganin Dr Faisal ne, ya dawo ciki ya zauna bakin bed tare da cewa 

"Morning Faisal"

"Morning sarkin bacci"

Murmushi Dr Waahab ya yi, tare da cewa 

"To me zan yi in ba bacci ba"

"Matsalar gauranci kenan"

"Eh naji, me labari ne?"

"Za mu je restaurant"

"A'a ku tafi kawai ni ba zan je ba"

"Don mesa?"

"Bana buƙatar komai"

"Ba dai saboda abin da ya faru jiya da daddare bane?"

"A'a in zai yi kawai nayi order"

"To in mun je sai ayi maka order"

"Hakan zai fi"

"To bye Beb tana jin yunwa"

"Sai kun dawo"

Ya koma ya zauna, ya fiddo waya yana kiran mutanen Nigeria, Maiduguri suna gaisawa ya jima a haka sannan yaji an yi nocking, ya buɗe na miji ya gani sanye da kayan ALAJA restaurant ya bashi damar shigowa ya shigo ya ajiye mishi abinci tare da cewa 

"Sannu da hutawa Yallaɓai"

"Yawwa sannu na gode"

Ya fice Dr Waahab ya rufe kofar ya buɗe abinci yaga an shirya masa lafiyayyen breakfast ya zauna ya ci sai dai kuma yaji yana buƙatar shayin gargajiya da ake dafawa a RESTAURANT ɗin. Ya ɗau waya ya kira Dr Faisal bugu biyu ya ɗauka tare da cewa 

"Breakfast ya iso ka ko?"

"Eh amma ina buƙatar shayin gargajiya"

"To bari na tambaya"

"Ok"

Ya katse wayar, minti biyar Dr Faisal ya kira, ya ɗauka tare da cewa 

"An samu shayin ne"

"Eh yanzu za a kawo ma, already na basu room number ka"

"Ok thanks"

Ya katse wayar, bayan 10 minutes aka yi nocking, ya buɗe sai yaga mace ce da ɗauke da basket, bai bata damar shigowa ba ta raɓe ta shigo, yayi matukar mamaki har ta ajiye tare da zaunawa bakin bed ta ce

"Yallaɓai ga shayin gargajiya da kake buƙata"

"Na gode"

"Uhm suna na Majada, zan taya ka hira, na ɗebe maka kewa saboda kaɗaici"

"Tashi ki fice"

Ya faɗa cikin ɗaga murya, ko gizau bata yi ba, ta kurawa kyakkyawar fuskar ido ta sakar masa killer smiling tare da cewa 

"Baka buƙata tane?"

"Kin san Allah zan gaura miki mari in dai baki fice min ba"

Ta mik'e tana taku irin na ƴan duniya ta iso kusa dashi tana fari da idanu, tayi magana a hankali 

"Be a man please"

Ya buɗe mata ƙofa tare da cewa 

"Ki fice min da gani"

Ta danƙara masa harara, tare da murkuɗa baki ta fice, ya maida ƙofar ya rufe ya zauna bakin bed yana maida numfashi tare da furta wa a hankali 

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun"

Ransa ya mugun ɓaci, wannan wane irin abu ne mace take kawo kanta wa namiji, shi bai taɓa ganin irin haka ba. Ya mik'e ya zuba shayin kurɓa ɗaya ya tabbatar da ba wacce take dafawa ɓace ta dafa, ya maida ta ajiye. 

Ya dawo bakin window, yana kallon wajen hotel, ya hango yaran da suke zuwa wajen suna wasa ya yi suna zaune, ya sauke numfashi zuciyarsa ta raya masa yaje wajen. 

Ya ɗauki wayar ya ɗaura jacket akan kayansa tare da sanya wayar a aljihu ya ɗaura a gogon hannunsa ya fito tare da rufe ƙofa. Yana fitowa daga cikin hotel ɗin ya iso wajen yaran ya kura musu idanu na wani lokaci, a hankali ya tako ya zauna kan dakali, bai ce dasu komai ba, Muneef ya ce

"Ba kyakkyawar Aunty ta ce mu dinga gaisar da manyan mu ba"

"Barka da safiya"

Suka haɗa baki wajen faɗi, ya amsa cikin sakin fuska 

"Sannun ku yara, wasa kuke yi"

"A'a sadaka muke karɓa"

Da mamaki yake binsu da kallo ya furta

"Sadaka!"

"Eh sadaka"

Cewar sauran yaran, ya kurawa ƙaramar yarinyar cikinsu idanu, ya miƙa mata hannu ta iso ya zaunar da ita kan cinyarsa tare da cewa 

"Ya sunan ki"

"Aicha"

"A'isha! Nice name"

"Ina tattawan (kyakkyawar) Aunty"

Cewar Aicha ta kurawa sajensa idanu tare da kai hannu tana taɓa kwantaccen gemunsa, ya yi murmushi tare da cewa 

"Wace ce haka"

"Kyakkyawar Aunty ita mu ke jira"

Cewar Haneef, Dr Waahab yana kallon Aicha ya ce

"Yayar ku ce?"

"A'a zuwa take yi ta bamu Alawa da biscuit"

"Ok"

Ya faɗa tare da duba a gogon hannunsa kusan 12:00pm ya sauke Aicha tare da miƙa wa ya ce

"Ina zuwa"

Ya bar wajen ya nufi bakin titi, ya tadda shago, ya sayi BOBO da biscuit ya dawo sai dai chak! Ya tsaya saboda hango wannan matar da take zuwa musu, gani ya yi sun rungume ta suna murna suna tsalle tana hana su, ta ce

"To kowa ya zauna"

Suka zauna cikin kulawa ta ce

"Yau na jima ko?"

"Eh kyakkyawar Aunty har zamu tafi ma"

"Wani abu ne ya riƙe ni amma ba zan sake jimawa ba"

"Har wani uncle ma yazo"

"Uncle?"

Ta tambaya cike da mamaki, suka amsa da 

"Eh amma ya tafi"

"To ku sani ba kowa ne za ku yarda dashi ba"

"To kyakkyawar Aunty"

Ta raba musu Alawa da biscuit, ta ce

"Zan koma ana jira na, sai gobe"

Ta mik'e ta barsu zaune suna shan Alawa suna murna.

Dr Waahab ya sauke numfashi, ganin ta bar wajen yasa ya tako a hankali ya iso wajen yaran tare da cewa 

"Yawwa na dawo"

Suka nuna masa Alawa da biscuit suna murna, ya ce

"A ina ku ka samu?"

"Kyakkyawar Aunty ce tazo ta bamu"

Suka faɗa, ya jinjina kansa tare da cewa 

"Sunanta kyakkyawar Aunty?"

"Ba mu san sunanta ba, muke kiranta da kyakkyawar Aunty"

"Don me yasa ku ke kiranta da sunan?"

"Saboda kyakkyawa ce"

"Oho! Ya yi kyau"

Haneef ya sake cewa

"Fuskar a rufe"

"To yayi kyau, ni ma na kawo muku abin sha"

Ya nuna musu nan murna ya raba musu, su ka yi godiya da gudu suka bar wajen. Ya mik'e ya dawo cikin hotel ɗin, a lokacin su Dr Faisal sun dawo ya dawo ciki ya buɗe laptop nasa yana duba wasu abubuwan......


*******************************

A hankali ta shigo cikin gidan tana ɗingisawa, ta shiga madaidaicin palourn su ta zauna, Mamanta dake zaune ta ce 

"Sannu har kin dawo daga tattakin?"

"Eh Mama sai naji ƙafar dama dama ciwon ya ragu"

"To Allah ya sawwaƙa, shine fita da jaka ai sai tayi miki nauyi"

"Mama akwai abinci?"

Bilqees ta faɗa tare da sauya zancen, Mama ta amsa da

"Akwai mana, bara na zubo miki"

Maman Bilqees ta mik'e ta zubo mata abinci taci, ganin lokacin sallah azahar ya yi ta mik'e ta idar sannan ta ɗauko wayar ta tana game.

Har dare Bilqees tana ɗaki har Alaja ta dawo ta shigo ta duba ta sannan ta wuce side nata. Washegari sassafe Alaja ta ɗaga musu hankali akan lallai sai Bilqees ta biyo ta, duk da bata jin daɗi amma haka da daure ta shirya suka fito. Tare suka iso restaurant ɗin ta ce Bilqees taje ta huta.

Tana nan zaune taji hayaniyar shigowar baƙin da suke zuwa cin abincin safe, ta fito ko zata hango wannan mutumin amma baya cikin su, Alaja tayi kiranta tare da cewa ta dafa shayi za akai hotel. Bata ɓata lokaci ba ta dafa aka bai wa waiter Isyaku ya kai, Bilqees ta dawo ciki tana mamakin me yasa wannan mutumin likita bai zo yau ba, Allah yasa lafiya ga wallet nasa yana wajenta.....


********************

DR Waahab yana zaune yana jiran isowarsa breakfast nasa, yaji an yi nocking ya buɗe ganin breakfast ɗin ya iso yasa ya karɓa ya dawo dashi ciki, ya zauna ya soma karyawa ganin harda shayin gargajiya yasa ya zuba kaɗan don ya ɗanɗana wanda yake so ɗin ne ko ba shi ba, aiko yana kurɓa ya ji shine, nan ya sha bana wasa ba. Ya kammala ya duba a gogo tare da leƙowa ta window ko yaran nan sun zo, ga mamakinsa suna nan zaune, ya ɗaura jacket nasa akan kayansa tare da sanya wayar cikin aljihun wondon sa, ya duba wallet nasa babu don akwai cash a cikin zai yi amfani dashi wajen sayawa yaran BOBO.. haka ya fito yana mamakin a ina ya yada, ya iso wajen yaran ya tadda wannan wannan Auntyn tasu ta iso tana raba musu Alawa, shiru yayi yana kare mata kallo, yau ma cikin baƙaken kaya take kamar kullum, ya sauke numfashi ya kalli hannunta da take bada Alawa fari tas dashi, ɗan ƙarami, jikinsa ya basa bata da shekaru, ya iso ya tsaya daga ƙarshen layin yana jiran ta iso kansa.

Kyakkyawar Aunty bata an kara da mutum a saye ba saboda rage tsawonta da tayi, tana bada Alawa da biscuit, sai da tazo na ƙarshe taga Alawa ya ƙare kuma yaran basu ƙare ba, tunani ta faɗa kenan yau ba daidai aka bata Alawa da biscuit ba, daman takan saya har da nata to natan ne ya saura, ta yanke shawarar ta hakura zata bada natan.

Tana ƙoƙarin miƙe wa ta hango an miƙa mata babban hannu, tabi hannun da idanu ganin agogo a ɗaure a hannun ga kuma tulin gashi yasa cikin sauri ta ɗago sai taganta a ƙasan mutum, ta ɗan yi baya tana kare masa kallo, ya sakar mata da murmushi yana sake miƙa mata hannun shi ma a bashi, ta ɗan waro fararen idanunta da suke ciki niqabin tana sake kare masa kallo........





Comments and share fisabilillah