5STARS CHRONICLE Book 1 YEL

CHAPTER 13

by @xayyeesherthulhumaerath

Durƙusawa gaban Maman Yusuf ya yi yana, "Na san na zalinceki , kuma na cutar da rayuwarki,amman Don Allah ki yafe mun, daga yau na miki alƙawari zan baki farinciki wanda bakya tsammani,zan baki ikon daga darajarki na 'Ya mace dana durkufe shekarun baya, cikin kankanin lokaci tare da dunkulallen jawabin yarinyar nan ya sauya mun komai na rayuwa, tabbas 'Ya mace ba abar wulaƙantawa bace."

Ya karasa maganar yana hawaye.

Murmurshi ta yi ta ce, "Babban burina bai wuce ashe ka fahimci darajar 'Ya mace da Ahalinka ba,kuma ka fahimta Alhamdu Lillah,na yafe ma duniya da lahira."

Daga wannan lokacin salon ya fara canjawa.

Zeeyter na komawa gida Madame Naddja ta sanar da ita za a fara taronnan nan da kwana ɗaya domin ta yi wa wani magana wanda shi ne farkon target dinsu.

Hakan yasa suna gama karatu Madame Naddja ta tsaya sai da suka gama shirya yadda komai da komai zai kasance tun ranar kafin ta tafi.

★★ Kwance Farouk yake amakeken gadon dake dakin wayarsa yake dannawa can kuma ya tsaya tamkar an bashi umarni kamar wasa ya yi creating sabon account a facebook, ba hoton shi sai zallan suna kuma ba details din komai da za a iya gane wane ne searching sunan Zeeyter ya fara yi ,ai kuwa sai ga shi ta fito,ko da ya duba dpn ta ita ce kuwa sanya da kayanta digijari-digijari, Friends request ya Tura mata, da mamaki har ta amsa.

"Hi." Ya Tura mata

"Hi ya tafi koyo Sallama da kan ka agun kamar gwanda." Ta fada da emojin harara.

Dariya ya yi kan ya ce, "Oh Oh Sorry Madame Assalam alaikum."

Emojin Murmushi ta dauko tare da fadin, "Wa alaika Salam."

"Ya ki ke? Ya jin dadi? Ya zafi,ya kuma sanyi." Ya fada.

Emojin bata rai ta tura, "Wanne zan amsa ciki?."

"Duka mana." Farouk ya fada.

Daga nan suka ta dariyamarsu abun mamaki har tayi saurin sakewa da shi sunata hira yana bata dariya.

Dariya.

Daga karshe Farouk ya ce, "zamu iya zama kawaye? ."

"Sosai ma mai zai hana?"

Ya ce, "To Shikenan daga yau Zanna ce miki kawata ni kuma me za ki na kirana?"

"Aboki mai kan gwanda." Ta fada cikin zolaya.

Dariya suka yi dukkaninsu.

Har suka yi sallama Ba karamun dadin hirar nan Farouk ya ji ba, ban da ita ba abun da yake hangowa a idanunsa har barci ya dauke shi.

Ita kanta mamakin kanta take ya akayi tayi saurin sabawa da mutum da bata sani ba a lokaci kadan?

Tsaki tare kawai ta tashi cikin darennan ta shige toilet, tayi wanka sannan ta kara Sadiq (saurayin da ta saba kira in tana da bukata) tare suka kwana har sai asuba da ta tashi sallah ta tada shi ya tafi.

★★Zaune suke dukkaninsu kowa na aiki Deejerh ta fito, "Hi Guys ku duba mun wandon nan ya yi fasali kuwa?"

"Woooo My Deejerh ke ta Mussamman ce, ban jin cewa a yanzu zan iya sa wani kaya da ba designing ɗinki ba, wandon nan ya bala'in yin kyau ba kadan ba,wannan nasan yana fita kasuwa sai an nema an rasa." Zahra ta fada tana kara duba wandon.

Farouk ya ce, "Eheen na fada maku muna da sarauniya komai nata na musamman ne "

"Kullum cikin fito da salo mai ban mamaki kike Deejerh." Khalil ya fada yana karewa wandon kallo.

Cikin zolaya Haiydar ya ce, "tunda abun wariya ne maimakon ayi na maza sai na mata to bai mun kyau ba."

Dariya suka yi dukansu Deejerh na, "Mai kake ci na baka na zuba, na mazanma na loading kasan ko wani irin kaya sai dai afara gani a jikinmu."

Wani irin wando ne golden colour, gabadaya botira ne jiki anyi kamar ado dasu har wajen shafe din,kasan kuma anyi wani irin tattara kanana mai step-step.

Ba karamin kyau ya yi ba,yanayin yadda kowacce mace xa ta iya sawa kuma zai mata kyau, lutiye ko sirara.

★★Zeeyter ganin cewa bata da abun yi ga shi Madam Naddja bata zuwa ran Sunday,gidan mai kuma an fara gyara masu aiki ne da su Halliru ke lura da gun kawai.

Tattara kananun yaran unguwar tayi ta ba kowa littafi da pencil,da kaloli.

Tare da fadin, "Kowa ya gina gida mai kyau duk wanda na shi yafi kyau zan ba shi sweet,."

Ita ma ta fara zanen ba tare da tasan abun da take zanawa ba, zuciyarta kawai take ba sai da ta gama ta ga YEL .

Ba karamin kyau da sheƙe zanen nata ya yi ba, tamkar a kirata ta fito.

Suma yaran duk sun dage kuma kowanne zanen gidansa ya yi kyau,suna gamawa ta ba kowannensu chocolate tare da fadin, "Kowa ya je ya ajiye littafi da kalolin agida, ranar da ba makaranta sai mu kara."

Dukansu suka fita suna dariya.

Harira da hurera ne suka shigo suna leƙe.

Zeeyter na ganin su ta ce, "Ku shigo mana,da matsala ne? Ko xan iya taimakon ku?"

Shigowa suka yi suna Murmushin munafurci.

Hurera ta ce, "Umm umm wallahi za mu fita anguwa ne kuma bama da kudin mota."

Murmurshi Zeeyter tayi ta ciro dubu biyu ta mika masu.

Godiya suka mata suna kallon juna da ido.

Suna fita Harira ta ce, "Banza bata san cewa inda za a illatata zamu ba, har tana bamu kudi."

Dariya Hurera tayi, "Bar jaka ai za muyi maganinta."

Suna fita kuwa ta nufi gidam marayu hira tayi sosai da yaran suna murnar ganinta sannan tayi masu sadakar da ta saba masu a kullum.

Washegari

Da Sassafe Zeeyter ta tafi gidan abinci domin dafa abincin da xa aci wajen taron wayar da kai.

Madam Ayshe da Madam Naddja kuma suka tsaya tsara gun.

Misalin karfe 10:00pm aka fara.

Wanda haiydar ne ya kasance bakonsu na ranar.

Tun daga zuwan shi yanayin ƙauyen ya birge shi,duk da cewa bai taba zuwa ba sai dalilin Madam Naddja da ta gayyace shi.

Ba ɓata Lokaci ya fara jawabi kamar yadda aka umarta kan Ilolin shaye-shaye da ma shi kan shi shaye-shaye menene kuma taya ake farawa.

Bayan ya yi sallama da gaisuwa ya fara da, "Kwaya ko magani shine duk abinda idan ya shiga jikin dan adam yake kawo chanjin yanayi cikin kwakkwalwa ko jikin sa ta kowani fanni, misali ko ta hanyar sha ne, shaƙawa ne ko kuma ta yin allura.

Miyagun shaye-shaye

Shan maganin da doka ta hana ayi anfani da shi.

Shan magani barkatai ba tare da ixinin likita ba.

Wuce umarnin likita gurin shan kwayoyi.

Shan abubuwan da addini ya haramta.

Dalilan da ke sanya matasa afkawa cikin shaye-shaye.

Jahilci, matsalolin rayuwa kamar ace damuwa tayi wa mutum yawa ko kuma ya tuna wani abu da bai son tunawa da ya shafi rayuwarshi, nan take mutum kan iya shan komai ma, hada-hadar siyasa, hulɗa da abokan banza, sakacin iyaye wajen tsawatawa yara, a fannin sakaci yana nufin kowanni fanni ke nan Mussamman masu kudi da suke sakarta yaransu ,ba tsawatarwa kullum sai dai anuna masu cew suyi abun da suke so,su ji dadin rayuwa,talakawa kuwa hakan na nufin halin ko in kula da wasu iyayen keyi kan 'Ya'yansu,sannan kuma da yanayin wurin zama, da dai sauransu.

Wasu daga cikin miyagun kwayoyin da aka fi amfani da shi gurin shaye shaye.

Hodar aljanu (cocane), tramol, kashin kadangare, afarci kasa (pemoline tablet), hodar iblis (heroine), maganin mura da ake sha ba bisa ƙa'ida ba (emzolynn, tutolyn, codine, benelyn) Alkaho,da dai sauransu.

Matakai na soma shaye-shaye

Gwaji mutum ya soma kusanta ko mu'amula da masu shaye shaye daga nan kuma sai mutum ya ce bari ya gwada yaji mai ake ji.

Masu shaye shaye akai akai.

Shine matakin kama shaye shaye a kai a kai, wanda ya kai wannan matakin ba zai iya komai ba sai ya sha idan bai sha kwaya ba ba zai zauna lpy, wanda ya kai wannan mataki zaka sameshi kullum cikin maye, a wannan matakin yana iya yin sata domin ya siya kwaya.

Alamomin gane mai shaye shaye kuwa,

Rashin natsuwa,talauci, kora daga gurin aiki ko makaranta, yana kawo haɗari ga wanda suke yin tuƙin motar ko babur, yana kawo ciwon huhu, yana kawo ciwon hauka, yana kawo lalacewar mazakuta, yana kawo cutan kanjamau saboda idan hankali ya gushe yana kawo jima'i barkatai ba bisa ka'ida ba, yana kawo lalaci yadda mai shaye shaye bai iya yin komai sai ya sha kwaya.

KAƊAN DAGA CIKIN HANYOYIN DA ZA ABI DOMIN MAGANCE SHAYE-SHAYE

Ya zama wajibi Iyaye su tashi tsaye domin lura da 'Ya'yansu, abokan su,wajen da suke zuwa da duk wani abu da ya shafesu, sannan Al'umma suba jami'an tsaron goyon baya wajen hukunta duk wanda aka kama da wannan badakala , haka kuma iyaye su kasance suna yawan nusar da 'Ya'yansu kan iloli kamar wa inda na gabatar.

Ba yara kadai ba,duk wani babba ya kamata ace ya lura sannan ya kiyaye da tsarin rayuwarsa domin bai san me zai zama nan gaba ba,kuma bai san ya iyalansa zasu kasance ba."

Tsayawa ya yi a daidai nan wajen, jikinsa ya yi sanyi, ya tafi wani guntun tunanin dake cewa wannan jawabin tamkar da kan shi yake.

A zuciyarsa ya furta, "Allah ka bani ikon gyara rayuwata nima."

Ya numfasa kafin ya ci gaba da cewa, "mu daure, mu cije, duk da cewa sabo na da wuyar dainawa amman haka zamu danne zuciyoyinmu mu gyara,fatana anan kowa ya fahimta masu yi su daina wa inda basu fara ba su kiyaye, Allah ya bamu ikon gyara rayuwarmu da ta al'ummarmu,sannan ka da ku manta ba 'Ya'Ya maza kadai ke shaye-shaye ba har da wasu 'Ya'ya matan, jawabin mu na dauke da kowanni bangare nr."

Da haka Haiydar ya kammala jawabansa.

Gaɓadayansu jikin mutanen wajen ya yi sanyi daga iyayen har yaran,batun ya shiga jikinsu matuka.

Yana kammala ya nemi ixinin tafiya Amman Madame Ayshe da Naddja sun hana kan dole ya tsaya ya ci abinci.

Ko kudin da Zeeyter ma ta tanada kan abashi sam yaki karba ya ce arabawa mabukatan wajen sadaka.

Ganin cewa su Farouk nata kiranshi ne ya basu hakuri ya fita da niyar tafiya daidai lokacin da Zeeyter ta tawo da abincin d za a raba agun.

Ya juya kenan sai ga kira ya shigo wayarta ta koma gefe.

Shi kuma yaja motar shi ya tafi.

Tana sa wayar a kunne ta ji, ".........

Muryar Dpo ta ji yana, "Madame barkanmu Dai."

"Barka." Ta furta.

"Uhumm Madame ke nan, daga tafiya sai mantawa dani kuma? To ya ki ke."

"Lafiya." Ta amsa a gajarce.

Ya ci gaba da magana , "Madame kamar bakyason yin magana."

Katse wayar tayi tana tsaki kawai.

Shiga cikin wajen taron tayi aka fara raba abinci, hatta Maman Yusuf da Babanshi kuwa sun zo, sai da kowa ya ci ya koshi kafin aka watse.

Madame Ayshe da Madam Naddja suka sanar da ita Haiydar yaki karban kudi, da kuma abun da ya ce.

"Allah sarki bawan Allah, Allah ya saka masa da gidan Aljanna, Madame ku bawa duk wanda ya dace kamar yadda ya bukata."Zeeyter ta fada tana nuna farincikinta ƙarara saboda hukuncin da Haiydar ya bada,duk da cewa bata san waye ba amman ta ji cewa ya birge ta cikin zuciyarta.

Zaune take tan hutawa kamar an ce mata ta dauko wayarta tare da leƙawa facebook.

Sakon Farouk ne ya fara shigowa, "Hy Kawata, barkanmu da rana."

Gyara zama tayi kafin ta ce, "Barka dai Aboki, fatan kana Lafiya?"

"Alhamdu Lillah kamar yadda kike."

Da, "Ma sha Allah ." Ta maida masa.

Ya ce, "Ni Ko inyi tambaya mana Kawa."

Zeeyter ta ce, "Bismillah za ka iya, Allah sa ina da amsar."

"Kina ma da shi,Don Allah me kika fi so aduniya?" Farouk ya tura mata dauke da emijin tunani.

"Farincikin Al'umma a ko ina na fadin duniya, wannan shi ne abun da na fi so."

Har ya fara typing ya tsaya yana kallon haiydar kan ya ce, "Abokina Kasan cewa aduniyar nan tamu akwai wata 'Ya mace ɗaya tilo tamkar da maza? Rayuwar tamkar Don al'umma take, za a iya cewa ita tazo duniya ne kawai domin taimako,da kudinta,da karfinta da basirarta tana kokarin maida ƙauye birni,tunaninta a kullum shi ne ya za ta taimaki Mutane ba bambamci tsakanin makiyanta da masoyanta, na tabbata za ka ji mamaki in kaga abubuwan da take kirkirowa a duniya, wannan duk abun mutum dole ya sara mata, dama ace zan iya mallakar ta da nafi kowa jin dadi arayuwa, Wallahi duk wanda ya samu yarinyar nan ba karamun dace ya yi ba, yarinya ce fa karama,abun nata bani mamaki."

Haiydar na kwance sai da ya tashi, "Daman da gaske akwai mata irinsu aduniya? Ban santa ba amman har kasa mun cewa nima na ji tana birgeni, ace za asamu irinsu d yawa aduniyar nan ai da munji dadi mun huta,ba wai komai ace namiji ba,komai na miji,ko ba komai ka ga yarinyar da kake faɗa ta nuna cewa mace za ta iya gyaran al'umma da ɗaukan dawainiyarsu har ta gina su, Amman ina yarinyar nan take da zama ne? Yar wace kasa ce?"

Haiydar ya fada cikin zakuwar yana son sanin wace ce.

Dariya Farouk ya yi, "Yoo to wannan ai shine babbar Matsalar kowa ya kasa ganota." Ya karasa maganar a zuciya yana, "In sha Allah tawa ce."

Haiydar ya yi Murmurshi, "aiko nayi alkawari da ikon Allah sai na nemo yarinyar nan aduk inda take ko da kuwa a karshen duniya take rayuwa."

Cikin dariya Farouk ya ce, "Mamaki yau kai ne wata ta burgeka kuma kake alwashin nemanta? Don ma ba ka ji Tarihin Rayuwarta Gabadaya ba,abun al'ajabi, tausayi da mamaki, Lallai to mu zuba mu gani za aga wanda zai riga nemota, amman da kashedi, duk Wanda ya riga shi zai dauketa."

Dariya suka yi dukkan su.

Farouk ya ci gaba da danna wayarsa domin ba wa Zeeyter amsa.

"Ummm Lallai kin ji dadi dama nine, ni fa ban damu da kowa ba,kuma bana damuwa da damuwar kowa."ya tura mata.

Zeeyter ta turo emijin bata rai, "ni kam bana son mutum haka, ka kasance mai son mutane ko da basa sonka,taimakonsu ko da basa godewa, a gun Allah muke nema kuma dominsa mu ke yi domin ya biya mu da AlherinSa,za ka ga kullum zuciyarka ta kasance fayau ba tare da daukan nauyin komai ba, sannan duk wani ƙalubale da zaizo ma a rayuwa zaizo cikin sauki, komai za ka yi, kasa Allah a gaba domin kuwa shine Mahaliccin mu duka duk duniya."

Farouk ya ce, "Haka ne dukkanin jawabinki gaskiya ne, zan kokarta ko da kadan ne daga ciki in fara kwatantawa."

"Yafi dai kam Abokin Dole." Ta karasa maganar da emijin Murmurshi.

Dariya ya yi, "Wato ma abokin dole, Okay byee ina da wani aiki yau."

"Byee A yi aiki Lafiya." Ta fada.

Chating dinta ta ci gaba da yi tana dube dube.

Wani messege ne ya shigo mata.

Tana dubawa ta ga Namijine ya Turo mata hoton gabanshi yana, "Yane?."

Tsaki tayi kawai ta shiga duba profile dinsa da komai na kan facebook din sai da ta bincika

Tana ganin numbersa

Fita tayi a facebook din ta shiga facebook Tracker ta rubuta

Sannan ta dawo facebook ta kwafe URL dake profile dinsa.

Ta koma Facebook Tracker tayi paste din URL din, daga nan ta shiga Hack Account.

Processing ya fara sai da ya kai 100% sannan ya nuno mata Password dinsa.

Copyn password din tayi kafin ta kara komawa facebook tayi logging din account din na shi.

Duk abun da ta gani ban da sexy chat ba abun da yake yi da yan mata , Murmushin takaici tayi a zahiri ta ce, "Yanzu na ga Account din da zai kara shiga har ya nemi rainawa mutane hankali karamin Dan Iska kawai,indai za ka bude Account da number nan niko sai nayi hacking."

Fita tayi tana kokarin shiga gidan marayu shan gabanta da aka yi yasa ta dagowa.

Dpo ne yana sakin Murmurshi.

"Haba Madame Meyasa ki ke son bani wahala ne? Baki san yadda nake sonki bane wai? Zan iya mutuwa fa a kan ki."

Kallon shi tayi ta kyalkyale da dariya kafin ta ce, "Mutuwa ko? Ah lallai za ka iya mutuwa akai na, to bama nan ba indai kana so in kara tabbatar da hakan ka ga rijiyar cen?"

Ta fada tana nuna masa da hannu.

"Eheen." Ya fada

"Ok to ina so ka yashe mun cikinta daman ina neman masu yasa." Zeeyter ta fada.

Cikin Mamaki ya kalleta, "Yasa kuma? Ni? Madame ki bar irin wannan wasan zan dai sa yara suyi."

"Aa ni kai nake so kayi,in ba haka ba kuma kar in kara ganinka anan."

"To to naji zan yi Amman zan kira yara su tayani." Ya fada cikin wani yanayi.

Murmurshi ta yi, "Yawwa to Bismillah a kira su."

Kira ya yi aka turo masa da Yara Biyu daga Office.

Zigidir ya tube daga shi sai singileti da gajeran wando

Kayan aiki ta dauko masu ta ja gefe tana rufe baki da hannu don dariya.

Domin Dpon irin Samudawan lutayennan ne, Mussamman da ba kaya in ka kalli cikinsa kadai ya isa ba da dariya.

Suɓutur-suɓutur shi da yara duk sun ɓaci da laka mai Zeeyter za ta yi kuwa ban da dariya.

Gabadaya yara da manya duk anzo ganin Dpo yana Yasa gaɓadayan su Mamaki suke sun zubawa sarautar Allah ido kawai

Suna gamawa Zeeyter ta fara tafi ganin haka sauran yan ƙauyenma suka biye mata tana, "Maddalla da shugaban kwarai, ace wai har da kanka za ka zo kana bincika matsalolin al'umma kuma kuma ka gyara? Anya akwai sauran irinka aduniya kuwa? Muna alfahari da Dpo Khalid." Ta fada cikin zaƙewa.

Suma sauran yaran suka fara ihu, "sai DPO Khalid."

Shi kuwa Dpo mutuwar tsaye ya yi,yana kallon Zeeyter kawai.

Dariya tayi ta karaso inda yake ta dauko kayansa a inda ya ajiye ta mika masa tana, "Oga Khalid Wannan tunbin naka na da ban dariya."

Ta kunshe baki

Kan ta ci gaba da fadin, "Wannan ita ce soyayyar da tafi ta komai aduniya ka nunawa al'ummarka kana tare da su duk tsiya duk rintsi hakan zai sa su alfahari da kai, ace cikin mune wani ya yi wannan aikin ba mai damuwa da nuna jin dadi,amman su dubi fuskokinsu?"