CHAPTER 21
Zeeyter ta ce, "Eh sosai gaskiya, Don ko da naje yau sunyi nisa a aikin sosai kuma komai ya tsaru yadda ya dace kai dai sannu da kokari."
"Maddalla,daman ina so in nuna miki wasu Injina wanda zasu maku amfani sosai, sannan a fadada ma'aikatan nan sosai ta fannin kawo gorina,yadda har wasu matan gidan zasu rage zaman banza."
Ya karasa maganar yana nuna mata hoton wasu injinan tace mai.
"Eh Sunyi kyau Sosai Muna da bukata,maganar ma'aikatan kuma na sa asanar da wannan ma In sha Allah, tunda yanzu muna bukatar kayan aiki da yawa ba zaiyu ace a tsaya iya yaran ba, harda mata masu zaman gida, dama samarin duk mai ra ayi."Zeeyter ta fada.
Farouk ya ce, "Weldone Madam aikin na kyau kuma yana burgeni, abokina ya kayi shiru ne ko duk tunanin computer ne?"
Ya karasa maganar yana kallon haiydar.
Dariya ce zata subucewa Zeeyter ta danne, suna haɗa ido da haiydar ya hararata ita ma ta rama, Murmurshi Khaleel ya yi ya ce, "Wato tsabar Soyayya duka kun bar gun aiki kafin Lokacin tashi kun dawo gida kuna kallon juna, bama wannan ba ya kamata a fara shirin taron bude haɗakar kasuwancinmu Kafin a gama gyaran companyn tunda ina zaton sun kusa kammalawa, bangaren office din ka da nata ne kawai ya rage."
A tare dukkansu suka kalli juna...
Khaleel ya ce, "Oh Oh Dis Luv na ga alama yau kuna jin shaukin Juna, To Ni dai kar a manta da batun taron, Byeebyee."
Yana fada ya katse kiran.
Haiydar Da Zeeyter kuwa basu ma san yana yi ba,gabadaya sun tafi wata duniyar, ganin abun ba yi yasa haiydar fara rabata da kayan jikinta, ya yinda ita ma nan da nan ta fada cikin shauƙi, Lulawa suka yi cikin wata duniya ta ban, Mussamman Haiydar da ban da sambatu ba abun da yake yi.
Sai da suka tabbatar sun biyawa juna bukata kafin suka tsagaita,kowa na saukar da Numfashi.
Zeeyter ce ta fara tashi ta shige Ɗaki.
Bin ta kallo Haiydar ya yi kawai a azuciyarsa yana sakawa, "Ban taba jin irin ta ba, Daman Akwai mata kamar haka A duniya? Lallai Meenoh bata da komai kuma bata shayar dani komai,kuma bata iya komai ba,tamkar a mafarki, na kasa yarda." Wani irin kayataccen Murmurshi ya Sake a zahiri ka fin ya ci gaba da saƙawa, "Ina son yadda take, Amman yarinyar mahaukaciya ce." Ya karasa yana tashi tare da sakin tsaki kuma yana tuna wacce Farouk ke ba shi labari da yayiwa lakabi da YEL, a zahiri yake fadin , "Nasan sai ta fi mahaukaciyar cen komai."
Dakin da ta shiga ya bita, daidai Lokacin da ta fito daga wanka shi ma wankan zaiyi yana zuwa daf da ita suka bangaje juna tare da yin tsaki a tare.
Kafin ya fito har ta shirya ta fita waje tana jagaya unguwar duk da kasancewar dare ne amman ko ajikinta, ita kan ta azuciyarta jin hakan take ana Mussamman tamkar karonta na farko a kasancewa wannan duniyar.
Ji tayi wani na binta a baya tana juyawa kuma sai ta ga ba kowa, hakan ya sa ta tsaya cak tana tunanin ta ina za a bullo, ganin cewa taƙi motsawa yasa a turo mata wani baƙin basamuden kare, da gudu ya nufo gareta yana kokarin cizonta,dakyar ta samu ta kauce tana gudu yana bin bayanta, ta fadi,ta kurje, ta tashi ta ci gaba da gudu,da kyar ta koma gida tana shiga mai gadi ya rufo kofar da gudu.
Shi ko Haiydar in ya hango kasancewar ta su ba abun da yake sakewa ban da Murmurshi,Amman in ya tuna zeeyter kuma sai ya sake tsaki.
Yana fitowa ya ganta zaune duk ta kurkuje riga duk ta yage mai haiydar zai yi ban da dariya,har yana riƙe ciki,ƙula tayi kamar zata fashe cikin zafin rai ta ce, "Imbécile (Iskanci) Banza mai kan gwanda kawai Ido Kamar Gujjiya."
Tsaki tayi ta wuce daƙi tana tafiya da kyar.
Shi ko Haiydar ya kasa daina dariya sam Mussamman in ya kara kallonta tana tafiya da kyar ga jiki ko ina na girgiza.
Shigewa tayi ta shige ɗaki domin gasa jikinta ko zata samu ta yi barci.
Shi kuma zama ya yi yana dauko System dinnan ransa ya jagule ya ɓaci har ya manta da cewa ya yi wata dariya, gabadaya damuwa ya shiga ganin cewa gobe yana da meeting,kuma komai na baya nan meeting din na ciki.
Number Farouk ya kira don ya masa bayani ko da taimakon da zai iya masa amman kirin yaƙi shiga fir.
Kansa ne ya fara sarawa tuni ya dauko kwalbar giya ya fara sha, zeeyter daga ɗaki ta fara jiyo warin giya da sambatunsa yana, "Meyasa System dinnan za ta mun haka, Why? Why? Why?."
Yana sha yana dafa kai da sambatu.
Tana fitowa fisgar system din tayi a hannunsa, nan take ta bude, sannan ta ƙara fisge Kwalbar giyar, ya jefa masa system din tana, "Sam baka son Rayuwarka da ta Al'ummar da ke rayuwa karkashinka."
Waje ta fice ta zubar kafin ta dawo.
Cikin maye ya kalli system din yana ganin komai ya dawo tuni ya ware,ko kulata baiyi ba, ya fara aiki.
Daki ta koma ta ciro wayarta ta fara chatting,Yau Sakon Deejerh,da Zahra ne ya fara zuwa mata kafin na Farouk domin yanzu kusan kullum sai sunyi hira.
Deejerh ta ce, "Hello Kawata Ya Kike? ya Aiki Ya Oga kuma."
Zeeyter ta ce, "Lafiya lau, Alhamdulillah fatan kema haka? Ya fama da Ado da kwalliya?"
Murmurshi Deejerh tayi ta ce, "Anata fama, ya shirin Shagali,munyi magana da Khaleel ya ce mun an kusa kammala komai,ina fatan kin tanadi irin kayan da za ki sa da kwalliyar da za ki yi?"
"Hmmm kwalliya Kuma? Kaya ma sai na zaba, ina tunanin ai basa da matsala da yanayin shigata ko wani abu so ni simple zan je abuna."zeeyter ta tura Mata.
Kafin ta duba Sakon Zahra da ke cewa, "Hy Mrs Haiydar, ya ki ke , fatan abokina baya takura miki?"..
Murmurshi zeeyter ta yi da alamar zolaya ta ce, "Eheen ya ma takura ni mana da ko na masa duka kuzo jinya."
Dariya zahra ta yi Sosai ta ce, "Aa fa kar ataba mun Aboki mun tuba, fatan business komai na tafiya kan tsari?"
"Alhamdu Lillah komai na daidai In sha Allah." Zeeyter ta tura tana kokarin bude sakon Farouk.
"Kawar Dole,Mai Mijin Dole, Ya kike? Ko dai yau Ogan ne ya rike ki?"
Tsaki zeeyter ta yi ta ce, "Na bi Oga da gudu ba takalmi, in baka bar mun maganar mashayin giyar nan ba sai na kamaka na ma duka."
Dariya Farouk ya yi suka ci gaba da hirar.
Ji tayi kawai an fisge wayarta dagowan da za ta yi Haiydar ne tsaye kamar an aiko shi,sai da ya gama aikinsa zuciyarsa ta samu sukuni kafin ya tuna da maganar giya.
"Ina kika Kai Mun Abuna? Wai ban hanaki yi mun wannan iskancin ba? Ke uwata ce? Na ce ke uwata ce da za ki hanani sha."
Hannun da yake nuna mata ta rike kafin ta ce, "ni ba uwarka ba ce,kuma ba komai ba,kamar yadda nake ba kowa ba a duniya, abu ɗaya na sani na tsani shaye-shaye ko in ce duk wani abu da mutum zaiyi na illata rayuwa bana gani in kyalle,in zaka siyo sau goma ka sha sai na zubar in dai zan gani sai dai komai zai faru ya faru."
Ɗayan hannunsa ya kara kokarin dagawa cikin zafin rai da niyar kai mata mari shi ma riƙesa ta yi, ta ce, "Kamar ranar na faɗa ma,amman yau ma bara in ƙara tunama,babban kuskuren da za ka yi arayuwa shi ne Duka,Mari,Ko Wulaƙanta wata 'Ya Mace A duniya ka kiyaye,kuma Giya ce dai wallahi sai na zubar." Ta karasa maganar tana sake shi tare da murguda masa baki tana gudu.
Tsaki ya yi a fili ya ce, "Ai ba sai ta duka ba, amman ina tabbatar miki da cewa sai nayi maganin ki yadda ko guba ki ka ga zan sha baki isa ki tanka mun ba."
Komawa ya yi ya ci gaba da aiki a laptop dinsa.
AMERICA
Elon musk, Babba kuma fitaccen Dan Kasuwa Mai ƙyera motocin da ke amfani da cajin Sola irin Haiydar,amman shi babbban company garesa wanda yake ƙetare kasashe daban-daban,sannan yana zaune a America, bincike yake yana neman wani Company da zai iya samu a Afrika wanda zai iya zuwa daidai da nasa compayn ya siya ,
Domin Complain da yake samu agun consumers dinsa na Afrika,ana bukatar ya bude factory na maintenance wanda ba sai sun je America ba.
Da kuma maganar gidansa da ya bude mai kimanin Farashi Ten Thousand dollars,wanda Farouk zai iya lura da hakan a bangaren shi.
Five Star's Expensive company ya fara cin karo da shi, kuma duk ya fi masa sauran Companies din,nan take Bayanan su ya fara shiga ya Duba, Khaleel, Farouk, da Haiydar sune abu mafi wanda ya fi bukata, Zane,Na'ura da Kuma Motoci.
A lokacin ya ji yana da bukatar mallakar Compayn su domin suna da duk wani abu da yake da bukata.
A lokacin ya dauki Email dinsu ya tura saƙo ga Manager.
Sakon na zuwa gun Manager driect ya turasa zuwa wajen Khaleel, sai Khaleel ya duba sosai ya nazarci lamarin kafin ya kira meeting din gaggawa.
Gabadayansu suka hadu A Video Call Ta sykpee a system.
Khaleel ya tura masu komai sun gani sai da suka yi shawara kafin aka hada call din Elon musk.
Ko da yazo kawai nuna masu kudirinsa ya yi na siyan companynsu.
Wanda sam suka nuna masa basu amince ba sai dai ya kasance sun haɗa alakar cinikayya ta yarda zasu na cire masa nasa shares din, a hakan suka samu matsaya inda ya aminci kuma zai zo Nijar ya fara duba yanayin aikin Haiydar kafin na su Farouk da Khaleel.
A cikin daren suka gama komai, suna kokarin yin sallama Farouk ya ce, "Malam baka tambayeni YEL ba yau, ko dai Gimbiyata ta fara zautar da kaine."
Dariya Khaleel ya yi yana, "Eheen Now."
Deejerh ta ce, "Ango da Amaryar zamani ba,shown su na birgeni."
Sai a lokacin Haiydar ya yi magana, "ba dai ka ki nemo mun ita ba,zan baka mamaki One Day One time."
"Na ji dai agaida mun Gimbiyata kuma ana kula da ita." Byeebyee Cewar Farouk.
Da haka suka yi sallama dukan su.
Tana tashi da safe bayan tayi sallah ta nufi kitchen kasancewar ba saba barcin safe ta yi ba.
Lalle, bagaruwa da kanin fari ta Hada su tukunya guda ta dafa, da ya yi , ta diɓa kadan ta sha, sannan taje toilet ta zuwa wani a bahun, sauran kuma ta sa acikin ruwan wankanta shiga cikin bahun din ta yi na yan Mintuna kan ta fito ta fara wanka.
Bayan ta fito kuma ta dauko Water Meloon a fridge,ta yayyakan shi, ta zuba a blanda sannan ta zuba madara, Zuma da dabino tukun tayi blanding.
Da shi ta yi break abin ta.
Wani zubin kuma tana amfani da Albasa ta jiƙa a ruwa sannan tasa gishiri.
Sannan tana yawan Shan Rake da duk wani kayan Fruit da ke gyara mace, ta zaɓi da tayi haɗin gargajiya fiye da na magungunnan matan nan don acewarta bata yarda da su ba,sannan wani bangarenma yana da illa domin yana sauyawa mace asalin ta wanda ba za ta taɓa komawa ba.
Sannan tana Yawan Shan Gwanda Gudun Tunbi, wanda yana taimakawa sosai wajen rage tumbi in mutum na da shi,in kuma bai da shi hakan zai hana tumbin fitowa ko yana da niya.
Sannan tana amfani da Cloves ta dafa shi a wuta da lemon tsami, su jima suna dahuwa a wutar, sannan tana yayyakan lemun ta zuba acikin ruwan clove din, sai ya dauki wajen 10hours kafin ta zuba a gora,sannan tana sha kamar kwana uku arana safe kafin ta ci abinci da kuma dare bayan ta ci abinci.
A kowani wata kamar sau biyu take wannan.
Haka kuma tana tsarki da clove din domin shima yana dauke warin gaba,sai dai ana jin kamshinsa sannan yana iya kare mutum daga daukar infection, ko da ma ya dauka in baiyi karfi ba zai taimaka masa wajen fitarsa Nan take.
Wannan shi ne sirrin Zeeyter da ke birkita duk wani Ɗa namiji da ya taɓa kasancewa da ita.
Kayan shirginta ta fara haɗawa tana shirin fita, saƙon da ya shigo wayarta ne yasa ta komawa ga wayar.
Sakon kudi ta gani ya shigo account dinta wanda wannan shine kusan na Uku da take gani ba tare da tasan me turowa ba, aduk sanda aka turo sai dai ta ga wani saƙo kamar haka, "Ki yi aikin Alkairin da kika saba da shi,wannan sadaka ne fissabillah."
Ko da tabi number baya shiga sannan kuma ko da ta maida sako ba a Reply.
Murmurshi kawai tayi a zuciyarta tana fadin, "Allah ka sakawa duk mai wannan aikin da albarka."
Zata fita kenan sai ga Haiydar ma ya fito, dukansu suka ci karo a kofa.
Wurgo mata keyn mota ya yi yana, "Ga shi nan sai ki dauka."
Kallon sama da ƙasa ta masa kafin ta ce, "An ce ma ban da kudin siyane ko ina da bukata? Ban da ra ayi kuma ba za a hau ba."
Ta fada tana murguda masa baki.
Fara tawowa inda take ya yi,da gudu ta fita a gidan tana, "ba aso, ni ban ce ina so ba, na fi so in tafi a kafa ina ganin gari,bare ko da ina bukata ma ni da kudina zan siya."
Ganin ta fice da gudu yasa shi yin tsaki,daukan keyn ɗayar motar ya yi yasa a jaka Kafin ya shiga ta shi motar.
Tafiya take tana yan waƙenta kwatsam ta ga wajen masu sai da keke, ƙarasawa ta yi agun ta tsaya tana, "tabbass zan nuna masa ni ma ai zan iya siyan abun hawan ba sai ya bani na shi ba."
Ciniki tayi da su, na wata tsohuwar keke da taji jiki kaco-cinta duk sunyi tsatsa amman haka ta siya ko a jikinta,ta hau tana tafiya, wanda tafiyar kafa da wannan tsohuwar keken ba maraba.
Ban da kallonta ba abun da mutane ke yi.
Ita kuwa ko a jikinta.
Tana cikin tafiya kaca na tsinkewa tana tsayawa ta gyara kamar dole ta ci gaba da tafiya, wasu har dariya suke mata,amman in suka haɗa ido maimakon ta ji haushi sai ta bisu da dariyar ita ma.
Kana tuƙa Yar ƙwakur din kekenta tana leƙe-leƙe har ta isa unguwar da tasa aka tonawa rijiya da bohal,ganin yara da manya na ɗiba cikin kwanciyar hankali,da ka gansu zaka tabbatar da farincikin da ke fuskokinsu,ba karamin dadi ta ji ba, a zuciyarta tana ƙara godewa Allah.
Kamar ance ta kalli gefe, Wani masallaci ne ƙarami wanda ake sallah a ciki,wani matashi yazo zai shiga toilet din masallacin amman ya rasa buta, sai wata mattaciyar gora ya dauko ya zuba ruwa kafin ya zaga.
Girgiza kai kawai ta yi,a lokacin ta nufi kasuwa, buta,moɗa,tsintiya harda bokitin ruwa ta siyo, ko da tazo ta ba ladanin ya ce, "Waya baki ki kawo."
Murmurshi ta yi ta ce, "nima ban san waye ba, kawai dai an aiko nine."
Dafa hannunsa ya yi akanta yana fadin, "Da ke,da duk wanda ya siyo kayyakin nan har ma wanda ya sa aka mana bohol da rijiya, Allah ya maku albarka,ya inganta Rayuwarku,ya daukaka ku,ya haskaka ku,sannan ya mutunta ku,ya kare ku, kuma ya tsare ku aduk inda za ku kasance."
Da "Ameen." Ta amsa kafin ta hau kekenta ta ci gaba da faman tafiya har ta isa bobiel.
★★MALAYSIA
Farouk ne zaune yana bincike A system dinsa.
National Humanitarian Award ya fara cin karo da shi an fara sanarwa kan kowa ya fito ya fikrarsa,basirar da ma azancinsa.
Nan take zeeyter ce ta fara zuwa masa a rai, har ya dauko waya zai kirata sai kuma wata zuciyar ta hanasa, Number Halliru ya dubo ya kira.
Cikin sa'a kuwa ya amsa, tambayoyi ya kara yi masa dangane da Zeeyter Sosai ya bashi amsa sannan ya umarce sa da ya tura masa wasu details din ta waya ko System.
Sannan ya tabbatar masa da cewa kar ya bari zeeyter ta san ya tambayesa wani abu da ya shafeta.
Shiga Page din ya yi ya cike mata komai da komai.
Yana gamawa ya dauko wannan vedion da ya mata tana rawa, aduk sanda yake kallon wannan vedion ba karamin nishadi yake har sambatu yake, "Gimbiyata ke ta musamman ce,a komai,kuma a ko ina, da ikon Allah sai nayi nasara a kan ki arayuwata."
★★Zeeyter na zuwa Bobiel da shagon Nasur ta fara zuwa, ba abun da yafi faranta mata irin yadda yaja kananun yaran unguwar sunata aikin gyare gyare yana nuna masu.
"Ah barka da zuwa Madame." Maganar Nasur ne ya katse mata duniyar tunanin data lula.
Murmurshi ta yi ta ce, "Barka Da aiki Nasur,ina fatan komai na tafiya daidai?"
"Lafiya lau Madame, komai daidai in sha Allah."ya fada
yana kallonta.
"To Alhamdu Lillah, Allah ya bada sa'a." Ta fada tana tafiya.
Ji tayi Mutum ya sha gabanta,dagowan da za ta yi sai DPO.
Wata irin dariyar Mugunta yake yana fadin, "Na fada miki duk rintsin wuya sai na mallekeki ,sannan in baki mamaki wajen daukan fansa,ba a taɓa mun abu na kyale ba,ba kuma zan fara a kanki,tunda nake arayuwa ba a taɓa cin Nasara akai na,ko in samu abun da nake so ko kuma kowa ya rasa."
Ya fada yana lakacin hancinta.
Ko gezau maganarsa batasa ta yi ba, cikin izza ta kallesa ta ce, "wani abu da ba ka sani ba, Batutuwan mutane sam baya taɓa damuna a rayuwa, atakaice ma in ban dau abu da mahimmanci ba alokacin da aka yi,kuma a wajen nan nake bari duka in karkade jikina in tafi, zai fi kyau in ka maida hankali kan aikinka da na iyalanka na gida,Sannan kuma daga karshe ka tuna cewa ba abun da mutum ya isa yi wa dan uwansa in ba Allah ya ƙaddara ba."