CHAPTER 23
Wata irin dariyar mugunta ya yi ya ce, "Koma me za ce ba zan damu ba, hasali ma kwarin gwiwarki da jarumtarki birgeni take yi,amman ki sani ranar wanka ba a ɓoyon cibi, sannan akwai ranar ƙin dillanci,haka kuma ba a iya cin tuwo sai miya tai dadi."
Tsaki tayi ta ce, "ga fili ga mai doki." Ta ƙarasa Maganar tana bangaje shi tare da wucewa.
Binta ya yi da kallo yana dariya ya ce, "Tabbas sai sukuwa."
Sai da taje gidan Marayu kafin ta wuce Zeeyter Oil And Gas.
Gaɓadayan ya kara canjawa musamman bangarenta da aka yi dana Haiydar wanda yake kallon juna, kowanne dauke da sunansa asama, Na Haiydar din ta fara shiga ta gani kafin nata, komai sak iri ɗaya Khaleel ya tsara , ba karamin kayatarwa ya yi ba,in ba ka fito ba kai kace acen kasar waje kake.
Anata faman aiki kuma komai na tafiya yadda ya dace, tsintsiya ta dauka ta fara shara da sauri yaran suka zo zasu karbeta fur taƙi basu sai da ta share compayn nan tsaf wani ma ya shigo ya dauka yar aiki ce.
Yusuf ne mai karban Robobi da mutane ke kawowa.
An yi Layi sosai ,Matan Aure,Yan Mata,Samari,Da sauran Yara.
Gwanin ban sha'awa kowa na badawa ana bashi kudinsa nan take ana tarawa a store.
Harira da Hurera da tun zuwanta an guwar suke biye da ita ne suka fara gulma, "Ni Wallahi na rasa wannan wace irin Aljana ce, ko mun mata abu in ya kamata sai ya saketa fa, nikam na gaji wallahi kullum sai dai tana ci gaba, ina ga musa mata guba a abinci kawai."cewar Hurera.
Harira ta numfasa ta ce, "Humm ki bari ni Wallahi don bakin ciki da hassada ma ji nake kamar in kashe kaina,ko me ya gani jikinta ma yake so oho shi mijin nata, gata baƙa ga jiki,fuska ba wani kyau ba,mu ga farin,ga kyan amman an rasa me cewa yana so bare auren watakila sai mun tsufa, mun girmeta fa duka amman ki ga."
Hurera ta ce, "Wallahi yau kan ta bar anguwar nan sai nasan inda na bi na illata ta ko ta ina ne ma in ji dadi araina."
Harira ta ja hannunta tana, "Za mu je in fada miki abun da za mu yi."
Zuwa suka yi suka dibo karkashi, suka daka shi a turmi,iya ruwan yauƙin suka matse daidai stais din da zeeyter zata taka in zata fito gidan mai suka zuba.
Hurera ta ce, "Kin ga tana taka abun nan zata karye wlh,kuma tana karyewa kan ta warke ma wani abune ko ba komai ai mun ɗana,kuma mun illata ta zata koma tafiya ɗingishi."
Dariya Harira ta yi suka tafa, "Wallah kina wuta kawata shiyasa na ke sonki kin san salon mugunta."
Zeeyter zata fito kenan saboda Madame Naddja ta zo zasu fara karatu, har ta sanya kafarta Daidai wajen sai ta maida azuciyarta ta tuna cewa bata yi addu'a sai da tayi addu'a kafin ta taka gefe.
Tsabar gulma da gudu hurera ta karaso tana son bige zeeyter yadda dole ta kafa, maimakon zeeyter ta taka ai kuwa sai hurera tim a kasa, kuka ta fara da majina domin ba karamin faduwa ta yi ba, gaɓadayan kofofin biyu sun goce ta kasa motsasu.
Zeeyter ce ta dauketa ta kaita asibiti nan aka tabbatar masu cewa ta samu matsala a kafarta ta karye ɗaya,ɗayar kuma gocewar ƙashi ne.
Harira kuwa tun da ta ga hurera ta faɗi ta gudu.
Sai da zeeyter ta biya kudin komai da za ayiwa hurera kafin ta bar Asibitin wajen yamma.
Pleatau ta fara wucewa ganin yamma ta riga tayi.
Tana tafiya tana jin wani taku a bayanta ana Binta kamar na daren jiya,tana juyawa kuma ba za ta ga komai ba, ci gaba da tuƙa kekenta tayi tana tsaki, har ta isa gida kuwa ba a fasa bin bayanta ba.
tana zuwa ta samu daidai inda haiydar ke parking mota ta ajiye kekenta
Shigewarta ciki ba dadewa shi ma ya dawo.
Ganin keke agun yake parking ya sa shi fitowa ya cilla keken gefe.
Ashe tana gani da gudu ta fito ta maida keken tana masifa, "Abun hawa ai bai fi abun hawa ba, parking nayi kuma kaima ban hanaka kayi agefe ba ai ga waje nan."
Kara fisge keken ya yi zai wurgar ta rike tana, "Wallahi agun zan sa,kuma a kuma cire mun aga masifa da bala'i a giddanan." Ta ƙarasa maganar tana zane da chalk
"Ga shi nan kowa yana parking agunsa kuma kar a shiga na wani,ban shiga naka ba, nima kar ka shigan mun nawa."
Tsayawa haiydar ya yi a zuciyarsa yana, "Oh ni da gidana za afi karfina, ko wace irin mahaukaciya aka hadani oho,inna biyewa wannan nima haukar zan yi ina ga."
A zahiri kuma ya ce, "Yoo daman kowa ya ga keken nan ai sai ke har kama kuke, gun parking kam gashi in zaku cinye gidanma." Ya fada yana shigewa mota domin gyara parking.
Ba yadda ya iya agefen kuwa ya yi.
Zeeyter ta ce, "Oho dai duk hawa ake,kuma Gwanda ni ban da katon kai ma."
Ta fada tana shigewa cikin gidan.
Shi kuwa da ya fito ƙadangare ya gani a bango, Murmurshi ya yi ya ce, "zan yi maganin mahaukaciyar nan yau."
Gari ya yi duhu tana ganin ya shige daki ta fito ta fara bincika motarsa,kwalbar giyan da ya siyo ya boye dauka ta zuba.
Domin tunda yasan in ya shiga da shi ta gani sai ta zubar ya sa shi fara bari amota ko da zai sha ma saidai yazo mota,dowawar shin nan ta fahimci cewa ya sha,hakan yasata bincika motar wanda kuwa cikin sa a ta gani.
Tsaki tayi ta zubar kafin ta koma ciki
Tana komawa ta shiga wanka.
Yana ganin ta shiga wanka yaje ya ajiye mata wannan makeken ƙadangaren.
Ta fito kenan ta zauna kan gadon ta ji kamar wani abu na hayewa jikinta tana dubawa me za ta gani ban da ƙadangare, wata irin gigitacciyar ƙara ta sake wanda saida dukka bangaren gidan ya dauka.
Haiydar har ma ya manta yana jiyo kararta da gudu yaje dakin
Kanƙame shi ta yi tana kuka jikinta na rawa, "Bana so,bana son abun cen,bana son shi,jikina zai hau."
Kallonta ya yi,ya kalli ƙadangaren kan ya tuna mai zaiyi ban da dariya, saketa ya yi ta kara kankame masa wuya, tana kuka.
Dariya yake kamar zai shiɗe ya matsar da ita gefe ya dauke ƙadangaren ya fita yana dariya.
★ba abun da zeeyter ta tsana kuma take tsoro kamar kaɗangare Domin,domin tana yarinya in ta gan shi har suma take.
Gaɓadayan ta birkice ban da shssheƙar kuka ba abun da take.
Dawowa da ya yi dan ci gaba da dariya sai kuma ya ji tausayin ta ganin yadda jikinta ke rawa,tana shiɗewa,ga zazzaɓi ya lulluɓeta.
Kwantar da ita ya yi ya lulluɓa mata bargo kafin ya dauko maganin zazzaɓi ya bata.
Zai tafi ta riƙe hannunsa,haka ya zauna gefen gadon har sai da tayi barci.
Tana yin barchi ya cire hannunsa a hankali ya fita.
Mota yaje don ya dirƙa abun da ya saba, Amman ina neman duniyar nan ya rasa giyarsa, mai gadi ya tambaya kan zeeyter ta fito dazune.
Ya tabbatar masa da eh.
Tsaki ya yi ya ce, "wannan mahaukaciyar yarinyar bata ji."
Komawa ya yi falo ya dauki wayarsa data ya kunna ya shiga Group dinsu na 5stars Hira suka yi sosai musamman Farouk da ke ba sa labarin YEL.
yana jin haushin Rashin giyarsa amman tunda suke maganar YEL hankalinsa ya kwanta wani farinciki na musamman ya ziyarci zuciyarsa.
"Wai Yau Ina Gimbiyata ne? Ban ji motsinta ba."
Farouk ya katse masu hira da hakan.
Tsaki Haiydar ya yi ya ce, "Yau ta taro abun da yafi karfinta tayi barcin dole."
Deejerh ta ce, "In in fa Aboki fada Gaskiya."
"Ko dai kai kasata barcin ba." Khaleel ya fada.
Zahra kuwa dariya tayi.
Shima Haiydar ya yi dariya yana, "Wannan ai tafi karfina."
Washegari.
Zeeyter na fitowa falo ta ci karo da Haiydar mai zaiyi ban da dariya.
Yana kallonta yana ƙara dariya.
Tsaki ta yi ta wuce sa ko kulashi ba ta yi ba.
Kitchen ta nufa tana, "Ina ni kakewa dariyar mugunta? Zan rama wallah sai na rama."
Sai da ta gama shirinta tsaf ta rigasa zata fita ma ya ci gaba da dariya yana, "Abun ya dawo kuwa?"
Ko kulashi ba tai ba ta fice.
Tana ficewa ta je daukan kekenta ta ciro wani karfi ta sace masa tayar mota.
Leƙawa ta yi ta ga baya zuwa hakan yasa ta jan kekenta a hankali ta bar gidan.
Da saurinsa ya fito zai tafi office, ya shiga mota,ta tashi amman sam taƙi tashi cikin ɓacin rai ya fito yana tambayar me gadi.
"Wane ne ya taba motar nan?"
Mai gadi ya ce, "Yallaɓai Madame ce."
Da fa kai ya yi yana, "Againa? Yarinyar nan fa bata jin magana, wallahii ta gama rainani,tana ganin ina wasa ne da ita ."
Ya fada yana kallon motar, tunani ya fara ga shi ba wata motar a gidan wannan ce kadai duk sauran suna company,ɗayar ma da zeeyter taƙi karba jiya anzo an daukata.
Tsaki ya yi ya fice a gidan yana tafiya da kyar domin ba saba tafiyar ƙafa ya yi ba, ga anguwar ba abun hawa kasancewar duk manyan mutane ne da motocinsu.
Sai da ya jigata kafin ya isa wajen wani bakanike suka tawo tare domin a gyara.
Gabadaya lokaci ya kure sai wajen 12 ya samu aka sa iska a motar kafin ya nufi company.
Zeeyter kuwa tafiya shirgin gabanta ta yi, ranar bata koma gidan ba sai cikin dare,duk jiranta da ya yi sai da ya gaji ya yi barci.
Haka suka ci gaba da rayuwa,kowanne ya yi abu,sai ɗayan ya rama, mota kuwa ba yadda Haiydar ya iya haka ya koma parking awajen da zeeyter ta ce,amman kullum cikin daru suke kowa damuwarsa ya rama abun da aka masa.
Wasa wasa har an gama gyaran zeeyter Oil And Gas Ranar Haiydar za shi gani.
Ba karamin kyau ƙauyen da ma compayn ya yi masa ba,domin in ba kasani ba ka shiga cikin compayn ka ce a kasar waje ne.
Zeeyter bata ma san da zuwansa ba,tana can tana harkar gabanta.
Halliru ne yake zagawa da shi yana nuna masa ko wani bangare na compaynin.
Suna zuwa daidai Office dinsa ya ga abude.
Da mamaki ya ce, "Ya Aka yi nan abude waya bude?"
Halliru dai bai ce komai ba suka shiga.
Suna shiga zeeyter ce ta baje a office din dan jaraba akan table take gyaran wayar wutan soket.
Fita Halliru ya yi ya basu waje.
Haiydar ya karasa gabanta, "Kamar dai na ga nan ba office dinki bane ko? Me yasa ba za ki je can kiyi kayan haukan naki ba sai anan wato ga marainin wayo ko?"
Ta dago ta ce, "Eh anan na ga dama, in ka so kai ma ban hanaka shiga nawan ba ai,ni nan nake ra ayin zama."
Ta karasa maganar tana ci gaba da aikinta.
Tsaki ya yi, ya fara kokarin janta yana, "Ki fita mun anan tun kafin ranki ya ɓaci."
Maƙewa tayi tana, "wallahii na rantse ba inda zani,sai dai a zauna duka ayi aikin anan amman ni kam ba inda zan fita."
"Au ba za ki fita ba ? Ki ka ce haka? Ni kuma bazan je nakin ba nan din zan zauna."
Ya karasa maganar yana janye kujerar da take kai, ya zauna yana ciro files din da Halliru ya ba shi zai duba.
Tsaki tayi ta janyo dayar kujerar ta manna jikin na shi ita ma ta ci gaba da haɗa wayoyinta.
Kowa na aikinsa amman duk bayan mintuna suna dagowa sai su haɗa ido dukansu su saki tsaki a tare kafin kowa ya ci gaba da harkar gabansa.
Tusar bazata ce ta suɓucewa Haiydar, ya yi saurin dagowa a tunaninsa zeeyter ba ta ji ba.
Mai za ta yi ita kuwa ban da dariya tana, "Sannu da aiki Oga, wannan kamshi haka ai ko turare ma ya sara maka."
Makewa ya yi ya kawar da kai ya ci gaba da aikinsa.
Halliru ne ya shigo ya kawo masu abinci kowa na shi .
Da sauri Haiydar ya dauka zai fara ci don tun tuni yunwa ke dukan cikinsa abun ka da acici.
Har zai kai baki ta fiske.
"Miye haka ?" Ya fada cikin zafin rai.
"Ba ka yi Bismillah ba,ko ka manta da hakan ne?"zeeyter ta fada tana kallonsa.
Tsaki ya yi kafin ya ce, "Bismillahir-Rahmanir-Rahim."
Mika masa tayi tana dariya, "da ba ka yi ba kuwa da yau wani ya wuni da yunwa Yasin."
Shi dai cin abincinsa yake ko kulata bai yi ba.
Ko da suka gama aiki ranar a tare suka nufi hanyar gida,yana mota ita kuma tana kekenta, gashi ta masa ɗare-dare agaba,ba daman ya yi gudu.
Gabadaya takaici ya gama cikawa Haiydar ciki,duk inda ya yi don ya wuceta sai ta katange.
Da haka har suka isa gida tare kowa ya yi parking dinsa,yadda ya juya mota, haka ita ma ta juya kekenta.
Ganin komai ya kammala aka fara shirye shiryen shagalin da za ayi wanda ya hada da zuwan Elon Musk da ke America domin Duba yanayin yadda kasuwancin nasu zai kasance.
Babban tunanin Haiydar da damuwar sa shine zeeyter, ka da suje ta bashi kunya, Mussamman tun daga shigarta ma , da haukarta acewarsa.
Ga shi an gayyato manyan mutane sosai wasu har daga ƙasashen waje.
Yana kwance sai saƙe-saƙe yake aransa ko ya abunnan zai kasance ga shi ga mahaukaciyar yarinyar nan sai Allah, "ba don ya zama dole ba, Wallahii ba zan bari taje gunnan ba." Ya fada yana sakin tsakin takaici.
Bayan kwana biyu
★★★★
Ranar Taro da sassafe Haiydar ya fita yana dawowa ya sameta a falo,wurga mata wata leda ya yi yana, "Wannan kayan za ki sa,don na san ba abun mamaki bane kije gun shagalin nan da kayan haukarki."
Kallon raini ta masa kafin ta ce, "ni nace ma ina da bukata? Ko nace ma ban da kudin siya? To bana so, kuma baza asa ba,inna sa kayan haukan na je a koreni kar abarni in shiga."
Ta fada tana wurga masa ledar.
, "In kin ga kin fita agidannan to wallahi kin sa kayan nan,ki tabbatar kin sa na fada miki."
Ya fada yana shigewa daki.
Cikin shigarsa
Na three pics suit tailor made ba karamin kyau ya yi ba, ban da kamshi ba abun da ke tashi.
Cike da takaici ya kalleta yana, "wai ba za ki sa kayan bane?"
Tashi tayi tana kokarin fita ta ce, "Eh baza asa ba, na ce bazan sa ba ai ba a dole ko."
Da sauri ya damkota yana kokarin cire mata kaya ya ce, "Ni ko zan sa miki da kaina, wannan ai iskanci ne,wawiyar yarinya kawai,ko ina sai kin nuna halinki."
Bangaje shi tayi ta fice da gudu tana, "A hakan dai za ni,nan gani nan bari."
Binta ya yi,amman ina ta riga ta tsere.
Takaici kamar zai kashe Haiydar haka ya hau motar shi ya nufi office.
An gama shirya komai kuma duk baƙi sun hallara amman ba Zeeyter ga lokaci na tafiya.
Farouk ne da ya yi connecting ta internet yana ganin komai domin ganin yadda shagalin zai kasance ya ce, "Oga wai ina ka boye mana Madam ne?"
Tsaki Haiydar ya yi azahiri ya ce, "To waya san mata ne."
A azuciyarsa kuma yana addu'ar Allah sa kar tazo.
Ganin lokacin zai ƙure suka fara yunƙurin fara shagalin.
Wani kamshi da ya daki ɗakin taron ne ya karkatar da hankulansu duka ga hanyar shigowa.
ZEEYTER ce cikin wata irin fitanniyar riga dogowa, dinner gown, tamkar ajikinta aka yi rigar,fuskarta kuwa tamkar an dasa mata Kwalliyar, ba karamin kyau tayi ba.
Gaɓadaya duka mutanen wajen suman zaune suka yi suna kallonta, musamman Haiydar, Farouk da ke screen da kuma Elon Musk.
BARA MU DANYI WAIWAYE
A lokacin da Deejerh ta cewa ZEEYTER tayi kwalliya ta ce baza ta yi ba,daga nan deejerh ta dunga bata shawarwari yadda za ta kara darajarta da kimarta wajen Haiydar da ma al'umma a wannan taron, hakan yasa deejerh ta turo mata mai gyarata yadda zata bawa Haiydar mamaki.
Ci gaba....
Tsayawa tayi ganin gaɓadaya sun zura mata ido, ga shi ba sabawa tayi ba sai duk jikinta ya yi sanyi.
Wani irin kishi ne ya damƙi Farouk ganin gaɓadaya sun zuba mata ido .
Cikin karfin hali ya yi gyaran murya wanda dukansu sai da suka juyo ga System din da yake kallo ta ciki.
"Barka da zuwa Gimbiyata."
Ya fada.
Haiydar ne ya tashi ya riko mata hannu tare da zaunar da ita.
Gabatar masu da ita ya yi a shugabar ZEEYTER Oil And Gas.
Sannan kuma ya tabbatar masu cewa wannan ne company na hudu da suka haɗa alaƙa da shi, dake reshen jahar Nijar,duk jawabin da ya yi bai ce ita matarsa bace a iya abokiyar Kasuwanci ta tsaya.
Dukansu Mamaki suke ganinta karamar yarinya kuma mai fasaha.
Sai ma data fara jawabi, gaba-daya idanunsu da kunnuwan su suka miƙa gareta.
Dukkanin bayanan suke ina fitowa screen din projecter da Farouk ya hada.
Harda bayanin yadda suke hadda man fetur da kuma bayanan yadda Haiydar ke sarrafa motoci.
Cikin tsari suna jawabi rubutun na fitowa.
Sai da suka gama kafin Zeeyter ta fara binsu suna gaiswa dake kai tsaye taron aka fara ganin lokaci ya kure.
Ko da ta fara gaiswa da kowa tana zuwa gun Elon Musk, a hankali ya furta, "U Look So Beautiful Madame."
Murmurshi kawai tayi, daidai a idon Farouk da Haiydar.
Kawar da kai Haiydar ya yi, Farouk kuwa sai da ya yi tsakin da ya amsa dakin taron.
Suna gamawa aka fara cin abinci, table din da ZEEYTER take Elon Musk ya zauna, Haiydar kuma yana na kusa da su.
"Madame I want a very strong patnership between our companies, I'm overwhelmed that people like you do exist in this universe though you're still very young, but I'm impressed with you and your performace."