5STARS CHRONICLE Book 1 YEL

CHAPTER 27

by @xayyeesherthulhumaerath

Kafin ita ta shige ciki domin karasa haɗa takardun waje ɗaya.

Tana gamawa ta kira Deejerh ta fada mata cewa tana bukatar wasu kayayyakin domin za ta yi tafiya na kwana biyu.

Da farinciki ta kunna data ta fadawa Farouk cewa ai abokin aikinta ya cika masu Humanitarian Award kuma sunyi nasara zasu tafi singafur.

Ba karamin farinciki Farouk ya yi ba, ganin yadda Zeeyter take Farinciki,domin hakan shine burinsa a kullum.

"Iyeee kice zamu singafur, Ma Sha Allah na miki murna ko zanzo nima a sakayani ne." Cewar Farouk.

Zeeyter tayi dariya tana, "Eh mana kazo ko a cinya nasaka ai."

Sai Dare Zeeyter ta kara komawa gida ta dibo wasu abubuwan bukatan saboda anan bobiel takeso ta kwana domin kammala aikinsu yadda ko sun tafi singafur babu Matsala.

Har cikin dare Haiydar bai dawo ba,aiki ya masa yawa shi ma a Office.

Hakan yasata daukan takarda ta rubuta masa cewa za ta yi tafiya na kwana biyu ta aje kan table kan ta tafita a wannan tsakar daren.

Tana tafiya ana binta kamar yadda aka saba, tana kunna torchlight sai agudu.

Can kuma taji an damƙe mata wuya ana ƙoƙarin rabata da numfashinta.

Wani irin karfi ne yazo mata,ta mauje mai bin nata tana kokarin makuresa shima.

Fisgewa ya yi y gudu,ita kuwa da kyar ta seta numfashinta kafin ta ci gaba da tafiya.

Haiydar na zuwa yaga takarda dubawan da zaiyi azahiri ya ce, "Mtsw Allah sa ma karki dawo, mahaukaciyar banza da wofi."

Wani takaici ne ya ƙufulesa domin ya tawo da bukatarsa,haka ya shige ya yi wanka kafin ya yi barci kawai.

Ya shige ya ci gaba da aikinsa.

Kwanan Zeeyter biyu A bobiel kafin su tafi har an fara kanun maganganu ai ta kashe auren daman ba iya zama za ta yi ba,ya korota ne.

Wasu ma agaban idanunta suke fada ita kuwa ko a jikinta sai dai ta sake masu Murmurshi, tayi gaba.

Daren yau jirginsu na singafur zai tashi, hakan yasa suka shirya ita da Halliru suka nufi airport.

Haiydar kuwa gabadaya ya ƙosa hakan yasa a daren bayan ya dawo daga Office yaje ya dauko Meenoh.

Amman abun mamakin shi ne sam ta kasa gamsar da shi,tamkar totuwar masara haka ya jita.

Wani irin tsaki ya yi yana hankaɗata gefe.

"Dallah matsa mun kauce anan, abu sai kace rijiya, fita mun agida ki tafi karki ƙara dawowa wannan ba dai ki kawar mun ba sai dai ki zuba mun takaici."

Ya fada yana shigewa toilet.

Tagumi tayi tana mamakin wai ita ce yau Haiydar baya marari ,duk maganin matan da take amfani da su,duk yabonta da yake ya tashi a banza.

"Tabbas wannan munafukar matar ta shi ce sanadi kuma zan dau mataki." Ta fada cikin bacin rai.

Tattara kayan ta tayi ta maida jiki, haka ta bar gidan domin ta san halin Haiydar sarai indai ya furta baya son abu to fa baya so.

Yana fitowa ya fita waje ya siyo giya,ya dawo zai sha kenan har ya zuba a kofi ya kasa sha zeeyter kawai yake tunawa da maganganunta.

Daga karshe ma tashi ya yi yaje ya zubar.

Ya kasa shan giyar kuma ya kasa barci.

Gaɓadaya gidan yaƙi masa dadi.

Tunaninta da kewarta ya fara

Yana, "Ko ina wannan mahaukaciyar yarinyar ta yi oho."

SINGAFUR.....

Suna isa kai tsaye suka riski driver har ya iso yana jiransu .

Masauki ya kai su.

Zeeyter ta shiga toilet tayi wanka a hotel din,haka ma halliru dake ɗayan dakin.

Bayan sun fito ta duba riga acikin kayan da deejerh ta hado mata ta sa, duk da cewa ba ta yi wata kwalliya ba,amman ba karamin kyau tayi ba, Mussamman yadda rigar ta tafi da jikinta.

Abinci ta zauna ta ci kafin Halliru ya shigo kan cewa suna da interview da su kafin afara taron.

Gabadaya kowa ya halla illa su Zeeyter, suna shiga wajen kuwa sauran turawan suka fara binsu da kallon banza.

Wata a gefe suna haɗa ido ta gallawa Zeeyter harara.

Murmurshi tayi kafin daga baya ita ma ta bita da hararar tana mika mata hannu su gaisa.

Sai da ta gama gaisawa da sauran,su doctors ne, Engineers ba irin mutanen ba a tara agun ba duk suna cikin participant ita kadai ce Yar Afrika.

Bayan sun gama ta koma wajen alkalan suka gaisa.

Sai da akayiwa kowa tambayoyi kafin aka zo gun Zeeyter.

Da mamakinsu yadda ta tashi tana jawabi da confidence dinta sannan kuma tana zubo turanci tamkar ba Yar kasar Nijar ba, kai kace wacce tayi jami'a abun ya matukar birgesu ba kadan ba.

Ana gama tattaunawar wannan baturiyar na kule da Zeeyter hakan yasata zuwa ɗakinta ta kulle mata kofar ta baya sannan kuma ta dauke keyn.

Halliru yazo kiranta domin tafiya dakin taro amman ina sam ta kasa buɗe kofar domin wannan ba irin mutane wacce ta saba buɗewa bane.

Lokaci ya kure har an shiga dakin taro.

Cewa tayi Halliru yaje kawai ta zauna a dakin tana zubawa sarautar Allah ido.

Kamar daga sama halliru ya ga Farouk gabansa yana, "Ina Madame din? Lafiya dai ko."

Jiki a sanyaye Halliru ya yiwa Farouk bayanin komai.

Gashi har an fara kiran sunan Zeeyter Amman babu ita.

Cikin takaici Farouk ya shige ciki, wani ma'aikacin hotel din ya samu ya karbi wani keyn awajensa ya budeta.

Za a wuce kenan ganin cewa bata zo ba sai ga sautin muryarta tana, "Here Am I."

Tsaki wannan baturiyar tayi tana jin takaici tamkar ta kufule kanta.

Tashi tayi zata fita, Zeeyter ta karasa daidai kusa da ita a hankali ta ce, "Thank you Mah." Ta karasa tana sakin Murmurshi.

Kallon tayi tana sakin tsaki kafin ta wuce.

Abin mamaki kuwa Zeeyter ce ta cinye aduk cikin kimanin Mutane dari da dauri dake kasashen waje.

Farinciki ya sa ta gagara rufe baki,yan jaridu,gidan Tv gabadaya sun baibayeta,ba abun mamaki da ya wuce karancin shekarun ta da kuma kasancewar ta 'Ya mace amman

ta take manyan maza da manyan matan kasashen ketare.

An bata makuden kudade kimanin 3 thousand Dollars da wasu yan kyautuka, certificate da Award, gaba-daya abu ya gama karade duniya cikin kankanin lokaci

Sujjada tayi afilin tana mika godiyar ta ga Allah.

Farouk da Halliru ban da washe baki ba abunda suke, tsabar farinciki Zeeyter bata san lokacin da ta rungume Farouk ba.

Bayan an gama taro an watse Suka zauna Zeeyter ta kalli Farouk ta ce, "Ya akayi haka? Me ka zo yi ko kaima kana ciki ne?"

Murmurshi Farouk ya yi ya na nuna halliru , "Abokina ne ya fada mun kunzo ni ko na ce dole inzo in ga Gimbiyata."

Halliru kuwa a zuciyarsa ya ce, "Madame duk wannan nasarar ta mu shine sila,shine silar Murmushinki a yau,ban da kuma wasu abubuwan da baki sani ba."

Suna cikin hira Zeeyter ta miƙe zumbur tana, "Ni fa yau nake son komawa gida, ince zamu samu jirgin da zamu hau ai."

Farouk ya tashi yana, "Haba Gimbiyata ba za ko ki bari mu kwana muna hira ba, kamar ana korarki? Ko dai kina kewar Haiydar ne?"

Tsaki ta yi ta ce, "a kan me zanyi kewarsa? Shi baiyi tawa ba sai ni, lallai kunci kai kai da abokinka,ni dai ina son komawa gida idanuwana sunata saƙa mun wani abu mai mahimmanci da ya kamata inyi shekara da shekaru ban samu dama ba, Amman yau kam Alhamdulillahi In sha Allah kowa zaiyi Farinciki bani kadai ba,kuma ba mu kadai ba."

"Ban fa yarda ba,na san duk wannan damuwar taki bai wuce ace ki ga Haiydar ba, na san abokina da shiga rai."Farouk ya fada yana dariya.

"Eh din naji ma shi nake son gani,ko ba komai mun kwana biyu ba mu yi rigima ba, nayi kewar rigimarmu amman ban da shi,don haka ina komawa shi zan fara tsokalowa."

Zeeyter ta fada tana dariya.

Farouk ya ce, "alright tun da kin dage bara naje inyi magana mu ga ko za asamu."

★★★

"Zoe Wake-up, Wake-up Please Baby." Wata matashiyar baturiya ta fada tana dan bugawa Yarinyar ta ta filo a hankali.

Cikin Muryar Barci ta ce, "Mom Live me please I'm feeling Sleepy."

"Baby ki tashi Sorry wasu ne suke buƙatar Ki tukasu zuwa Nijar."

Zoe ta ce, "Mom su nemi wani barci nake ji sosai ku barni mana,hutuwa nake,ina bukatar hutu."

Jan filon ta kara yi ta Ci gaba da barcinta, sai da tayi mai isarta can kuma kamar an tsikareta ta tashi da sauri ta shige toilet tayi wanka ta fito.

★Zoe matashiyar budurwar mai shekara ashirin da shida cif aduniya. aduniya,babbanta Hamshakin mai kudine a singafur, bata da sha'awar komai da ya wuce tuƙin jirgin sama, wanda take ason ranta kawai ba wai don kudin ba,domin in dan kudin ne tana daga zaune sai dai tayi umarnin abata, Yar Gayace takin karawa sannan kuma kyakkyawa ajin farko,bata cika shiga sabgar mutane ba sai dai in taku tazo ɗaya,ita kadai mahaifinta ya haifa hakan yasa shi sakaltata ta kowanni bangare,sannan Christen ne su,tun tana karamarta take da burin zama matukiyar jirgi hakan kuwa ya kasance tun kan ta girma ta fara, tana karatu tana tuƙi har ya kai ga ta girma kuma ta gama karatu.

Zeeyter, Farouk da Halliru suna zaune a airport har Zeeyter ta fara ƙula.

Tawowar Zoe ne ya dakatar da su daga maganar da suke, tafiya take tamkar ba za ta yi ba, Farouk gabadaya ya tafi da kallonta,suna haɗa ido ta galla masa harara, maimakon ya maida mata hararar sai ya sake tsaki.

Zuwa tayi ta karbi wani file ta nufi jirgin da kwarin gwiwarta zata tayar Amman ina sam jirgi yaƙi tashi,fitowa tayi tana ma ma'aikatan gun magana, "waya shiga cikin Jet din nan yau."

"Nobody Mah" suka fada.

Tsaki tayi ta koma ba inda bata duba ba, Amman sam ya gagara.

Zeeyter ce ta tashi ta bita Farouk ma ya bi bayanta.

Tana shiga jirgin ta ce, "taimake ni da box din cen naki."

Mika mata zoe tayi kawai ta tsaya.

Tana budewa ta fara gyara ashe wata waya ce ta harde, Farouk ya ce, "Gimbiyata ni kam mene ne baki iya ba arayuwarki?"

Zeeyter ta ce, "Kisa amman watakila shi ma zan fara akanka."

Dariya ya yi yana, "Ba matsala ai indai kece."

Zoe aranta take fadin, "Ina ga wa innan mata da mijine."

Zan kuma ta ce, "Mtsw to ma ni miye damuwata da su in ma mata da mijinne."

Ganin yadda Zeeyter ta duƙufa tana gyaran sai taji gabadaya ta birgeta,binta kawai take da kallo cike da mamaki, gata bakar fata.

Zeeyter na gamawa ta ce, " Ma sha Allah Madame xa ki iya tadawa yanzu mu ga."

Da mamaki tana tadawa kuwa ya tashi.

Dawowa tayi wajensu ta ce, "Sunana Zoe ni ce wacce zan tuƙaku zuwa Nijar can we be friends?"

Ta fada tana mika mata hannu.

Zeeyter ma ta mika mata, "why not? Nayi Farincikin haduwa dake ni kuma Zeeyter."

Karaf Farouk ya katse su da fadin, "Ni kuma fa? Anyi ƙawance da Gimbiyata saura ni."

Dariya suka yi duka zoe ta ce, "Kai ma Abokine daga yau."

Sai da suka yi exchanging numbers kafin suka yi sallama da Farouk ya koma hotel don shi ya ce sai washegari zai koma Malaysia.

Cikin kankanin lokaci zoe har ta sake jiki da Zeeyter sun saba.

Haiydar na zaune falo ya yi tagumi, Girmankai ya hanasa kiran wayar Zeeyter ga zuciyarsa fal take da kewa da muradinta.

Kamar daga sama ya ji an turo kofa, yana daga ido sai ga Zeeyter gabansa.

Kamar zaiyi magana kuma sai ya yi tsaki yana kokarin shigewa ɗaki.

Janyo shi tayi tana, "Kawu ko Oyoyo ba za amun ba,wai shin baka yi kewata bane?"

Fincike hannunta ya yi anasa yana, "Wane ne kawun? In rasa kewar wa zanyi sai ke,tur."

Zeeyter ta ce, "Oh ba ka yi kewata ba? Zanyi maganinka kuwa ni ce ai, bara inyi wanka inzo ."

Tsaki ya yi ya koma kujerar ya zauna yana duba wayarsa.

Tana shiga tayi wanka tayi sallah tukun tasa kayan barci ta fito.

Zama tayi daf da shi tana, "Har wani ramewa ka yi fa,ko dai da bana nan kayi ciwo ne? Ji goshin yadda ya kara fitowa kamar jirgi."

Karasa maganar tayi tana dariya tare da taba goshinsa da hannunta.

Bige mata hannun ya yi ya ci gaba da danna wayarsa.

Karaf ta fara yi masa kiss gaba-daya ta gama sakar masa da jiki, sai da ta gama tsokanosa ya sake yana mai da martani ta tashi da gudu ,bin ta ya yi,amman ina har ta shige daki ta kulle kofar.

"Ba za ki bude ba wai? Wannan wace irin mugunta ce, kin san......"

Sai kuma ya yi shiru.

Dariya Zeeyter ta fara tana, "ni ba sa'arka ba ce ai na faɗama daman zan yi maganinka,maza kaje ka kira wannan yarinyar nikam ma nayi barci."

"In baki bude ba wallahii sai na sa miki kadangare ta window na fada miki,kin san bana wasa da ke."

Zeeyter na jin hakan ta bude masa tsilif don tasan zai aikata Gwanda ta ƙara gumamai ta wani bangaren.

Gaɓadayan su cikin bagen juna suka raya wannan daren, Mussamman Haiydar.

Washegari da sassafe Zeeyter ta fita.

Zuwa tayi ta samu masu yin aikin titi,ta masu bayanin tana so ayi titi a bobiel da ƙauyuka biyu da suke cikin garin.

Nan take suka gama tsara yadda komai zai kasance suka yi lissafi sannan ta daura Yusuf a kan wanda zai lura da hakan.

Ta ce sam ba za ta ci wannan 3Thousand dollars din ba, sanadin al'umma ta samu,kuma su za ta yiwa aiki,hakan yasa bayan sun gama lissafi ta duba sauran ƙauyukan da ke fama da wahalar ruwa ta sanya a masu bohol.

★★

Zaune yake a office yaron da ya saba kawo masa jarida ya yi sallama kafin ya shiga ya ajiye masa kan table.

Daga kan da zaiyi Shafin Farko ya ga hoton Zeeyter dare dare.

Tashi ya yi tsaye cikin mamaki dauke da jaridar a hannunsa.

Kara kallo ya yi ya tabbatar dai ita dince kafin ya zauna ya fara karanta tarihinta.

Yana karantawa maganganun Farouk na mai yawo a azuciya, sai yanzu ya fahimci tafiyar da tayi da kuma inda taje. a zahiri ya furta , "YEL." nan take kwakwalwarsa ta fara tunano masa abubuwa da dama har ma ranar da suka fara faduwa suka bangaje juna,ranar da ta hau kan motarsa ta zauna,da kuma farkon zuwanta Compaynin sa.

"Ba musu Zeeyter ita ce wacce Farouk ke bani labari,amman Meyasa ban fahimci hakan ba?"

Ya yi shiru can kuma sai ya ci gaba, "To taya ma zan fahimci wannan mahaukaciyar yarinyar."

Murmurshi ya yi kawai ya dauke jaridar ya mai da cikin dirowa sannan ya ci gaba da aikinsa.

Dare na yi ya koma gida, tun daga bakin get yake jin sautin kiɗa na tashi, da hanzari ya shiga don atunaninsa ta tara masa mahaukata ne irinta a gidan.

Ita ɗaya ce tanata tikar rawarta.

A fusace ya karasa ya kashe yana, "ke wai Mahaukaciyar ina ne? Baki san cewa dare bane zaki sake wannan uban karan."

Tsaki tayi, "ina ruwanka dani? Ina ruwanka? Kai ma ka kunna mana kowa ya yi rayuwarsa ba matsi."

Ta karasa maganar tana kuma kunnuwa.

Kashewa ya kara yi

Ta kunna.

Ganin ba za ta fasa ba yasa shi shi ma dauko ɗayar speaker ya kunna ya ƙure volume din kamar nata.

★★★

Ita kuwa ko ajikinta rawarta ta ci gaba da tiƙa, daga karshe ya tsaya yana kallonta kawai.

Sai da tati mai isarta kafin ta kallesa tana gwalo ta nufi ɗaki.

Shiga ɗakin da zata wata irin gigitacciyar ƙara ta ƙwala wacce ba iya gidan ba sai da anguwar ta amsa.

Cikin sauri Haiydar ya ƙarasa kan kace miye har ta sume agun.

Ƙadangaru ne fal tsakar ɗakin irin jajayen nan manya-manya.

Daukanta ya yi ya nufi ɗayan dakin da ita kafin ya dawo ya kulle wannan.

A hankali ya shafa mata ruwa afuska,cikin razana ta farfaɗo tana,"Bana so na ce Wallahi bana so,ka daina samun wannan abun kasheni za suyi bana son su,bana so."

Ta fada tana fashewa da kuka tare da matsawa daga garesa.

Kokarin riketa yake amman ina sai rawan jikinta yake tana kara matsawa.

"Mugu bana son ganinka ka bar nan mugu kawai,bana so,ni nace bana so,kuma wallahi sai na rama."

Tsawa ya daka mata, "mahaukaciya kawai ki barni inyi magana ma ba za ki iya ba tsabar hauka? To sai kita yin, kiyi abun da zaki yi nasa miki din."

Ko kallonshi ba tayi ba, ta kara matsawa can karshen gadon,tana rufe ido ba abun da take gani sai wannan kadangarun gabadaya ta birkice ta fita a hayyacinta.

Tsaki ya yi ya tashi ya fita yana, "sai kita haukar taki ke ɗaya ai wawiya kawai."

Ta kasa sakewa sam, ko kyakkywan motsi ta kasa,ita kadai sai firgita take tana hawaye.

Ga wata irin yunwa da ta fara ji, har yaje ya zauna zai ci abinci sai zuciyarsa ta fara raya mai, "Yanzu haka wannan Mahaukaciyar ma ko abincin bata ci ba."

Kitchen ya shiga ya dibo mata,kafin ya bude kofar dakin ya wula mata Plate din ya fice abinsa.

A hankali ta rarrafo ta dauka tana murguda baki, "ai wallahii sai na rama nima, mugu kawai."

Zagewa tayi ta ci abincinnsn tamkar sabuwar kamu,tana gamawa kuwa barci ya kwashe ta.

Cikin daren Haiydar ya samo wasu maza suka kwashe ƙadangarun duka,yana mamakin yadda aka yi suka shiga dakin kuma da uban yawa haka.

"Dole akwai wani boyayyen lamari." Ya furta a zuciyarsa.

Ɗakin da take ya koma, ganin yadda ta kanƙame a karshen gadone ya matukar basa dariya.

Ganin baya jin barci hakan yasa shi bude data, yana budewa kuwa sai ga sakon Farouk.

"Hello Friend, Ya Gimbiyata ta isa gida Lafiya? Muna taya murna Allah kara daukaka."

"Gimbiyarka? Na bi gimbiya da gudu ka kiyayeni da gimbiyar nan fa tom." Cewar Haiydar dauke da emojin kashedi.