CHAPTER 29
Dariya Farouk ya yi yana, "Eheen Gimbiyata mana,ko taka ce? Na ga business Marriage ne bare ace za a kafa mun sharadi."
"Oho dai,ni dai na fada ma ka kiyayeni da wannan sunan."
"Gimbiyata sai na fada fa,ba ma wannan ba,maganar da nake so muyi shine,tun da naga tana ta kokarin daga wannan ƙauyen nasu mai zai hana ka sai fili babba acen Khaleel ya tsara maku gida da makaranta aciki yadda komai zai wadata,ina tunanin hakan ba karamin faranta mata rai zaiyi ba,sannan kuma kun ƙara daga ƙauyen a takaice ka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya."
"Kuma ka yi tunani mai kyau fa,don ni ƙauyen ya birgeni sosai ko da naje yafi wani cikin garin ma,basu da matsalar wuta bare kuma ruwa, Ma sha Allah,in sha Allah zan yi Magana da Khaleel din,amman kar ka bari ta sani ya kasance abun yazo mata ba zata." Haiydar ya rubuta yana kallon Zeeyter da ta jima da lulawa duniyar barci.
Farouk ya ce, "Owk As You wish."
Daga nan suka nufi Discussion group din su, gabaɗaya sai murna suke taya Haiydar da Zeeyter kasancewar abun ya karade duniya duk sun ji labari.
Daga nan yama Khaleel maganar yana son siyan fili a bobiel da kuma yanayin gidan da yake so a Private.
Khaleel ya ji dadi sosai hakan yasa da kan shi ya bada umarnin aduba masu babban fili wanda zai isheshi wajen fidda duk wani abu na bukata.
WASHEGARI
Kafin ta tashi har Haiydar ya ya yi sallah ya fice training.
Ita ma tana sallah tayi wanka tare da sanya kayan sport dinta ta fita.
Yana cikin gudu ya ji karaf an bangajesa.
Zeeyter ce tana sakin tsaki.
Ta ci gaba da gundunta.
Binta yayi shima da gudu zai bigeta,ta bangaje shi ya fadi a kasa sai da ya bige kai.
Dariya tayi ta tafi abun ta.
★tana komawa gida suka ɗaura kayan breakfast ita da mai aiki.
Sai da suka kammala ta ci kafin ta wuce bobiel abinta.
Haiydar ne yasa wani dan sanda yana binta a baya ba tare da ta sani ba,domin kwana biyu sam bai yarda da yanayin ba,ya fara fahimtar akwai wani boyayyen lamari.
Tana zuwa Bobiel suka fara shirye-shiryen taron wayar da kan da suka saba don ranar ne za aci gaba, tattaunawa kan mahimmanci sana'a, tare da karatu ga 'Ya Mace.
Madame Ayshe da Naddja sun gama tsara komai.
Don haka Malamar da aka kirawo ta fara jawabinta.
"Assalamualaikum barkanmu da kasancewa a wannan rana mai daraja, sunana Madame Surayyah sannan zamu tattauna kan mahimmanci sana'a da kuma karatu ga
'Ya mace ne, abun na matuƙar sosa mun rai ko ince bani mamaki wai ace karatun 'Ya mace bai da amfani ko kuma yin sana'ar ta baya da amfani,
a aurar da ita ta zauna tayiwa miji da 'Ya'Ya bauta Shikenan rayuwar 'Ya mace? Aa sam ban yarda ba,kuma ba zan taɓa yarda ba ko da kuwa acikin mafarki ne, don kina
'Ya mace baki zama bola ba,kuma ba ki zama baiwa ba,mutumce kamar kowa,nemi ilimi ta kowanni bangare yadda da an taɓaki zaki kare kanki,
babban kalubale da ke kanmu matan musulmai ya fi afkuwa a asibiti yadda ake wulaƙanta mu ake disga mu cikin jama'a don kawai bamu yi karatu ba,shin ba za kiyi zuciya ki nemi ilimi ba?
Ba za ki tashi tsaye domin inganta rayuwarki da ta iyalanki ba? Wai ace in mace tayi karatu bata auruwa ai idonta ya waye to wallahi ban yarda ba, zauna da jahilci ya maidaki baiwa sai ya gama maidaki ba komai ba ya koroki gida,yi karatu kuma kiyi sana'a yar uwa indai baki auru ba to wallahii Allah ne bai kaddara ba,
amman karatu mai zirfi ba shi zai hanaki samun miji ba,ban ce kar kiyi aure ba don karatu aa in miji ya fito yi aure Amman da sharadin zanyi sana'a kuma zanyi karatu ,ina mai tabbatar miki da cewa ba ke kadai ko danginki zasu amfana dake ba,har da shi da na sa dangin har ma ki zam abar alfahari,
sanya aranki ba wanda ya isa ya yi miki abun da Allah bai miki ba,kina zaune rajab agida ba karatu ba sana'a kullum sai tambayar miji kudi,tun yana bada na marmari har sai ya gaji kun fara samun saɓani,haba! Gyara rayuwarki 'Yar Uwa canja tunanin ki, in ma karatun bai samu ba fara sana'a fi karfin bukatunki da na danginki har ma da 'Ya'Yanki, zaman lafiya zai samu cikin gidanki baki da wata matsala sai dai wacce ba a rasa ba, mu tashi mu gyara rayuwarmu domin 'Ya mace haske ce da zata iya haskaka duniya da ma mutanen cikinta da ikon Allah,da wannan nake kira a gare mu da mu yi nazari domin zaɓawa rayuwarmu mafita mafi cancanta."
Bayan ta gama jawabanta, gwanin sha'awa Zeeyter ta bada kudi dubu goma-goma na mutane goma wa Madame Naddja domin ba wa inda basa da karfin kasuwanci jarin da zasu dogara da kansu.
Sunyi murna Sosai anci an sha taro ya watse.
Ban da albarka ba abun da Madame Naddja da Madam Ayshe ke sanyawa Zeeyter.
Ƙwana biyu gaba-daya daga Zeeyter har haiydar sun shiga rububi busy kowa na aiki ba zama, hakan yasa ko haduwa basa yi, tana komawa gida ta shige ɗaki take kulle kofa ko yazo ya buga sai dai ya gaji ya tafi.
Hakan yasa ya fita sabgarta.
Aiki ya kankama domin kuwa cikin wata hudu an gama ƙera makeken gida mai dauke da makaranta, wajen koyon sana'o'i, gun abinci da kuma wajen sheƙatawa,uwa uba bangaren marayu.
Ba karamin tsaruwa ya yi ba,kullim Zeeyter ta zo wucewa ta gun sai ta yi addu'ar, "Allah ka bani ikon yin ko da kwantankwacin wannan ne,tsarin ya mun komai ya mun."
Wata safiyar Lahadi zaune take tana chatting afalo kasancewar tunda aka shiga satinnan sai wannan ranar ta samu hutu shi ma haka Haiydar din.
Fitowa ya yi yana, "Ki shirya za mu je anguwa."
Zeeyter ta kallesa tana murguda baki, "ni ba inda zani hutawa nake,yoo ban da gulma ma yaushe muka taɓa zuwa wata anguwa da kai."
"Ni dai nace ki shirya za mu je anguwa, in kuma kinki to zan ba ki mamaki kuwa."
Tsaki tayi ta ci gaba da danna wayarta can misalin karfe Biyu bayan anyi sallar azahar Haiydar ya fito yana, "Jiran ki nake fa ko haka zaki fita da kayan zaman gidan?"
Bata ce komai ba ta sharesa.
Fita ya yi ya gyara motarsa kan yana shigowa Ya cinciɓeta tana wutsilwutsil yaki saketa ta galla masa cizo shi ma ya rama,kuma ya ki saketa,bai direta a ko ina ba sai cikin mota ya rufe.
Ta fara masifa, "wai ana dole ne? Na ce ni ba inda zani amman sai anmun dole zanyi maganinka wallahi kuwa."
Ko kulata Haiydar baiyi ba,ba inda ya nufa sai bobiel ganin hanyar da ya bi ne yasata yin shiru tana mamaki tare da tunanin mai ya faru haka, bugawa zuciyarta ta fara yi tana addu'ar Allah sa ba wani abu ya samu madame Ayshe ba ko sauran yaran.
Ganin ya direta daidai get din makeken wannan gidan ne ya dakatar da ita.
Bude motar ya yi ya cirota tare da shigar da su ciki.
Tana shiga tayi suman tsaye ganin yadda gidan yake kowanni ɓangare da sunanta.
Bata san lokacin da ta rungume Haiydar ba tana kuka, "Thank you, Thank you so much can't believe this oh oh."
Ta karasa maganar tana ƙara shigewa cikin gidan tare da ƙarewa kowanni part kallo.
Bangaren abincin ne farko restaurant ɗan daidai wanda zai dau mutane kimanin ɗari.
Sannan makaranta Babba bangaren yara da manya komai na bukata na gun hatta gun kayan wasa.
Gidan marayunma ya tsaru, sannan bangaren sana'o'i a gefe.
Gidansu kuma yana can karshe agefe.
Haiydar ya ce, "wannan shi ne inda zamu zauna daga yanzu zaki iya kawo duk wanda kike so, sannan ki tsara komai yadda kike so,mallakinki ne,dominki ne in kin so Ma ki tara harda mahaukata irin ki."
Murguda masa baki tayi kan ta ce, "Eh din dadinta ma a mahaukatan harda kai duk zan rene ku."
Ta karasa maganar tana kara shigewa cikin gidan tare da tsalle, kamar zai bita ganin mutane kawai ya yi tsaki ya shige ciki.
Bangaren su ya shiga ya zauna.
Zeeyter kuwa aranar taje ta tattaro su Madame Ayshe suka dawo gidan tsabar murna.
Ita ma da Haiydar agidan suka kwana ranar.
Ammman ita sam ta kasa barci tsare-tsare kawai take da neman yadda gidan zai Kasance Mussamman bangaren school din boko da islamiyya.
Karfe hudu na asuba,Kamar daga sama suka jiyo ihun mutane ta kowanni ɓangare.
A birkice suka fito ita da Haiydar.
Me za su gani?......
★★★
Gidan mai ne yake kamawa da wuta.
Jama'a na ta ihu ai Zeeyter zata kashe masu 'Ya'ya .
"Ni fa daman ban yarda da yarinyar nan ba,sam ban yarda da ita akwai wata boyayyar munaƙisa a zuciyarta."
"Wallahii ba za mu yarda ba,ba zai saɓu ba,ganin idonmu a kashe mana 'Ya'ya sannan a illata mana wasu ba, ba za mu lamunta ba."
"Ni nafi zaton mayya ce ma,mu kasheta kawai mu huta daman in ban da anso mugunta ina ƙauyennan ina gidan mai da har za azo a maka mana shi tankarere a mana Wayo a dauke mu da Yaranmu aiki ashe duk don aga bayanmu ne? To wallahi ba zai saɓu ba,kuma ba zamu taɓa yarda ba,sai mun kasheki kuma mun ga bayanki."
"Sai mun kashe ki, Wallahi sai mun kasheki kamar yadda kikai silar mutuwar wasu daga cikin 'Ya'yanmu."
Gabadaya yan kauyen suka birkice da maganganu daban daban.
Zeeyter ta ma rasa abun cewa kawai kallon yadda ake fito da gawar wasu da wa inda suka samu rauni take.
Mata da mazan ƙauyen suka hadu tare da ɗibo Petrol da ashana wai zasu konata.
Ko gezau ba tai ba tsabar tayi suman tsaye.
Haiydar ne yajata bayan sa yana fadin, "In kuka kuskura kuka taɓata ba shakka sai kunyi danasanin zuwa duniya ma gaba-daya, kada wani ya ƙara kusantota in ba haka ba kuma kuna kirawa kanku mutuwar ne kafin ta mutu duk sai naga bayanku."
Tsagaitawa da maganar ya yi yana kiran Babban Dpo da ke Plateau.
Nan take yan sanda suka cika wajen aka yi masu bayanin komai da yadda abun ya faru,babban abun mamaki shine ba asanma ta inda hutar ta kawo ba,domin duk matasan aikin wanke gorina suke awannan lokacin.
Yana gama bayani ya janye Zeeyter ya shigar da ita gida.
Madame Ayshe ban da kuka ba abun da take ita ma ta koma bangaren su kasancewar ta hana yaran fitowa.
Suna shiga zeeyter ta fadi tana kuka, "ba zan iya ba,ba zan iya ba,na gaji Wallahi ba zan iya ba,da gaske nice silar komai,komai ya faru nice sila,abar su sumun hukuncin da ya dace,yau nice silar mutuwar mutane? Ba zan iya ci gaba da rayuwa haka ba,na hakura da komai ba zan iya ba,nikam na hakura, ku barsu su kasheni indai zasu ji dadi aransu."
Tashi tayi zata fita, Haiydar ya falla mata wani gigitaccen mari yana, "ke baki da hankali ko? Na ce baki da hankali? Ko me zai faru ba kaddara bane daga Allah? Shin kin san hakan zai faru ne? Ko kuwa Mutum yana taɓa rayuwa babu jarabawace? Wannan ita ce jarabawa mafi girma arayuwarki amma ba hakan na nufin ki manta da nasarorinki bane, godewa Allah aduk yadda kika tsinci kanki."
Faduwa tayi gabansa tana kara fashewa da kuka, "ni ce silar komai,ko basu kasheni ba,ni zan kashe kaina ba zan iya ba ina ganin rasa rayuka sanadi na."
"Komai da kike ba don su bane? Na ce komai da kike don su waye? Ko tunda kike arayuwa kin taba yin wani abu don farincikin kan ki kawai? Iye? Na ce kin taɓa yin wani abu don kiyi farinciki kawai? Don su kike, don yau an samu akasi sai su butulce miki? Rayuwa ta taɓa tafiya babu ƙalubale ne? "
Durƙusawa ya yi yana dafa kafadarta, "Ko da kowa ba zai bi bayanki ba,nikam a yanzu ina bayanki ɗari bisa ɗari,ko da kowa zai nisance ki nikam ina tare da ke,in duka duniyar nan zasu fito su nuna cewa basa son ganinki nikam zan so ganinki har karshen numfashina."
Ya dan yi shiru kafin ya ci gaba da magana.
"In kowa zai tsaneki aduniyar nan nikam zan so ki har bayan raina indai ana so, na so ki tun kafin nasan ke ce,kuma tun kafin in ganki,sannan tun kafin in san ina tare da ke, ina sonki tamkar rayuwata zan iya komai domin ki kuma domin Farincikinki,ba za ki fasa komai ba, zaki ci gaba da komai yadda kika fara,ina bayanki ɗari bisa ɗari na kara maimaitawa ko da kuwa kowa zai juya miki baya ya butulce miki."
Rungume sa tayi cikin kuka tana, "Amman ba zan iya komai ba,ji nake duk karfin gwiwata ya sace, komai ya fita mun arai,ba zan iya ba."
Bayanta ya fara shafawa a hankali yana, "I may not get the time to tell you this everyday, but I just want you to know that you mean the world to me. If I ever get a chance to relive my life, I would start it from the day we got married.
I cannot survive without your love. I feel suffocated when you are not around me. I love you so much. In your love, I think of nothing but love.
I often pinch myself to check if I am dreaming. It's unbelievable for me to have such perfect life and a perfect wife like you. I love you darling."
Ya numfasa kan ya ci gaba da faɗin, "za ki iya kinji za ki iya in sha Allah, ki sa aranki komai mukaddari ne daga Allah kuma ba wai baya sonki bane ya kaddara miki hakan aa hakan ma wata nasarace domin gwada imaninki,
Ina tare da ke kinji a ko ina kuma a komai You will have my support In sha Allah, zan gyara komai kuma in tabbatar komai ya tafi kan tsari Just ki yarda dani ."
Haiydar yanata babatunsa ashe har wani rikitaccen barci ya yi awon gaba da ita.
Juyowan da zaiyi yaga ta jima da lulawa.
Murmurshi ya yi kawai ya dauketa ya kaita daki ya kwantar akan gado.
Ranar ko office bai je ba police station din Pleatau ya nufa domin cike wasu takardu kafin suka nufi asabiti kasancewar ankai wa inda suka samu ƙuna.
Wa inda suka rasa rayukansu kuwa har an gyara su an kaisu makwanci.
Gaɓadaya Haiydar bai zauna ba,babbar damuwarsa fitar da Zeeyter a case ta yadda baza a tuhumeta da laifin aikata komai ba.
Tafi sati ko kofar get din gidan bata zuwa Gaɓadaya tayi sanyi kullum sai dai kawai ta zauna tayi shiru .
Haiydar ma ya zamana baya zama a office ko ya fita yana yin abubuwan da ya kamata yake dawowa gida,sai da ya tabbatar komai ya daidaita an kashe case din amman bincike ya nuna dole akwai sa hannun wani a cikin lamarin,kuma an sa tsaro domin tabbatar da ko wane ne..
Sannan ya sanar da su Farouk.
Nan take Khalil yasa aka fara gyaran gidan man da ke ma ba wani konewar azo agani ya yi ba,illa mutanen da suka rasa rai.
Ta kai ga har abinci Haiydar ke yi agidan, ya zo sai ya lallabata ma kafin ta ci.
Zaune suke ya gama abun break
Ya ce"Oyaa Gimbiyar Farouk ki zo ki ci kinji."
Dariyar da ta jima ba ta yi ba tayi ranar , "ni ba gimbiyarsa ba ce sai dai taka."
Haiydar ya ce, "Aa ni Aguna Bright Eye kike agunsa kuma gimbiya kin ga kowa da na shi kenan."
Sai ranar ne ya samu ta fara sakewa yanata Tsokanar ta.
Mutanen gari kuwa anata gulma ai tunda asirinta ya tonu ta buya ta daina fitowa.
Haiydar nata kokarin kammala komai kafin Zeeyter ta gama dawowa daidai,ya dauki malamai ya sa a school din har an fara karatu sosai har wasu marayu daga wani ƙauyen duk ya dauko su,sannan gidan abincinma Zahra ta aiko masa da ma aikata ana abincin kyauta kowanni lokaci indai mutum zai je to zai ci abinci kyauta har sai ya tashi ya bari.
Ganin yadda komai ya kammalu data fita ta gani taji dadi Sosai Mussamman yadda taga kannenta marayu su baby da booboo nata farinciki.
Ga wajen abinci ma mutane nata ci.
Ganin cewa har yanzu ta kasa sakewa ta koma kamar yadda take dane ya sa shi yanke shawarar tafiya Indonesia da ita domin wannan shekarar taron su acen za ayi gun Zahra anan suka samu Compayn da zasu tallafawa.
Ya gama masu passport da visa komai da komai ya kammala.
Khalil ya riga kowa zuwa Indonesia da Yaronsa ƙarami Noor.
Deejerh da Farouk ma nata shirye-shiryen tafiya.
Zaune take da daddare tana kwance tunani kawai take ba abun da take gani a idanunta sai gawawwakin mutanen da suka rasa rayuwarsu sanadin gidan manta,kamar kullum da tunanin take kwana kuma take hini.
Haiydar ya shigo yana, "Madame ki tashi zamu tofi Indonesia."
Cikin mamaki ta bude baki tana, "Indonesia yin mene kuma?"
Haiydar ya ce, "Mu je zaki gani."
"Owk to bara in dibo kaya ko."
"Aa nasa deejerh ta je miki da kaya." Haiydar ya fada.
Matukar mamaki Haiydar ya ji karon farko da ya cewa Zeeyter tayi abu tayi ba tare da musawa ba.
Ba musu ta dauki jakarta kawai suka tafi airport suna zuwa kuwa jirginsu ya tashi.
★★INDONESIA
Balikpapan shine inda zahra take da zama,kuma yana ɗaya daga cikin manyan birni biyar da ke cikin Indonesia.
Suna da kasuwanni da gurare na ban sha'awa.
Tana zaune a babban gidanta wanda Khaleel ya tsara masu tare da yaranta guda biyu duka mata Anushka da Anitha.
Khalil, Farouk, Deejerh duk sun hallara illa Haiydar da ke kan hanya.
Noor suna ta wasan guje-guje su Anusha a falon Khaleel ya fito yana, "Wa innan yaran basa jin magana fa zan yi zana."
Dariya zahra ta yi tana, "Sai dai Azane Su Anushka amman ban da babyna (Noor)."