CHAPTER 39
Ya dubi Zeeyter kafin ya ci gaba da magana, "Madame Wannan shine Babana,ga Antouna kuma da kaninne na Deedarth da Unaisa."
Kara kallon Deedarth ta yi wanda ba musu kana yi masa kallo ɗaya ka kalli wannan dattijon da Haiydar ba su da maraba ko kadan tamkar an tsaga kara.
Sabanin Unaisa da tai kama da Mahaifiyarta sak.
Kitchen Zeeyter ta nufa ta dibo masu ruwa da abinci ta jera.
Tana Tsokanar Deedarth , "To Mijin azo aci abinci ka ci abincina daga yau ba za ka kara cin abincin wata awaje ba."
Dariya Deedarth ya yi yana, "Ah haba dai Anty? Za mu gani kuwa ,don ni dai na san babyna ta fiki iya girki."
Ko da suka gama cin abincin tare Deedarth da Zeeyter suka tattara Plate din ya tayata suka gyara komai kafin aka dawo ana hira.
Haiydar ya ce, "Mamaki nake Ji yadda ka girma Deedarth? Ji Unaisa? Wannan da an kara shekara biyar ina ga ban isa in gane ku ba."
Baba ya ce, "Ai kuwa kam tun ba Unaisa ba da har tana kokarin fin yayan nata ma."
Unaisa ta kalli Antou tana taɓe baki, "Antou kin ji Baba ko?"
Wani irin murmushin munafurci ta ƙaƙalo tana, "Ai daman 'Ya mace sai da girma,kai Haiydar wai ina yaran gidan ne?" Ta fada tana waige waige.
Haiydar ya ce, "Yara kuma? Suna bangaren gidansu ai."
Ta ce, "Yara naka fa,ko har yanzu ba a samu karuwa bane?"
"Eh." Haiydar ya fada yana kawar da kai.
Girgiza kai tayi kawai tayi shiru.
Baba ya ce, "Kuma Lafiya? Anje asibiti an duba ko da mai matsala cikin ku?"
Haiydar ya ce, "Eh munyi Babba kuma duka muna lafiya lokacine dai ina ga har yanzu baiyi ba."
Deedarth ne ya katse maganar da fadin, "Ai gwanda ma Amaryata karta tsufa da wuri."
Dukansu dariya suka yi ban da Antou da Unaisa da ke bin kowa da ido kawai.
Sai da suka fita sallah kafin baba Haiydar suka tsaya suna zantawa,baba ya bashi labarin wahalar da suka sha wajen shekara uku suna nemansa basu samu.
"Haiydar ka yafe mun,mahaifiyarka ta bar duniya bare in nemi yafiyarta, don Allah ku yafe mun ko ba komai nikeda alhakin lura da ku amman na banzantar da ku a kullum inna tuna hakan ina jin zafi araina." Baba ya karasa maganar yana kuka.
Haiydar ya ce, "Baba kar ka damu ba wanda ya zarce wa kaddara, yanzu zanzo in kaiku gida anjima sannan zan nema maku wani gidan nan da sati ku koma sai ka zaɓa mota in canja ma taka, dawainiyar su Deedarth da Unaisa kuma in sha Allah yanzu ta dawo kaina."
Godiya baba ya yi Sosai yana shi ma haiydar albarka.
★★
Sai bayan sallar magriba ya maida su gida.
Deedarth kam ma bai tafi ba agidan ya zauna.
Washegari da sassafe Haiydar ya sa aje anemo masu sabon gida.
Deedarth da Zeeyter na kitchen suna haɗa kayan break.
Haiydar ya shigo yana, "Wato kazo kana son kwace mun mata karfi da yaji ko?"
Dariya Deedarth yi yi yana, "To ai daman tawa ce ba taka ba aro na baka ko ba haka ba Anty?"
Cikin dariya Zeeyter ta ce, "Eh mana ina ganin fine guy kamarka ai shi yanzu ya mun tsufa."
"Iyee ni ko? Dukanku zan rama, yanzu dai ba wannan ba,wani aikin zan yi abani nawa inyi." Cewar Haiydar.
Deedarth ya ce, "Anty kin san Yaya zaiyi kyau da dakan sakwara kawai mu ba shi dakan."
Dariya Zeeyter tayi tana kallon haiydar, "Yoo wannan ina zai iya? Kace dai ya fasa mana doya kawai."
Dukansu suka yi dariya
Haiydar na nannaɗe hannun riga ya ce, "Eheen aiko zan baku mamaki duka,ina doyar,dakun sakwarar Saudiya za ku ci agidannan, ba dai ni kuka raina ba."
Dariya suka yi Zeeyter na fadin, "We shall See Oh Oh."
Nan da nan Haiydar ya dage ya fara dakun sakwara yana zufa yana kara dagewa har sai da ya dakata lugwi ya kalli Zeeyter da Deedarth, "Kun ga bambamci ko? Na ce za ku iya daku irin wannan? Yara kuna wasa,baku san ni wane ne fa."
"Laaa Yaya daman ka iya? Anty ki ga yadda ya dakata sosai fa." Deedarth ya fada yana duba sakwarar.
Zeeyter ta ce, "Inhin Daz My Sunshine, mene ne ma ba zai iya ba da yardar Allah,Really Proud Of You." Ta fada tana rungume Haiydar.
Kissing dinta ya yi ya ce, "Thank you, Proud Of You More Bright Eye."
Zuwa tayi ta dauko Yam pounder tana nuna masa tana dariya, "Boyewa nayi daman in ga ko zaka iya."
Ta fice a kitchen din da gudu yana binta, "wato da yam pounder agidannan amman shi ne sai da kika bani wahala wannan yarinyar in kika shiga hannuna baza kiji da dadi."
Ya karasa maganar yana damkota.
Tsugunawa tayi tana riko ciki, "Wash cikina."
Da sauri ya durkusa shima "mene ne?"
Saki shi tayi ta tafi tana masa gwalo da dariya.
Shima dariyar ya yi.
Karasa hada kayan a break din suka yi kan suka shirya kan daining, tare suka ci,cikin wasa da dariya.
Shiryawa Haiydar ya yi tafi Office, Deedarth kuma gidan mai yaje kasancewar bai da lectures ranar.
Zeeyter agida ta wuni suna wasa da su Miemie.
Sai yamma ta koma bangarenta,har tayi girki ta gama,ta yi wanka, Sleeping dress tasa wanda ya yi matukar mata kyau Sosai.
Zama tayi afalo tana chatting da Farouk, wanda har yanzu bata san cewa shine ba.
"Hi Friend yakike? Ya kwana biyu? Ya Oga kuma?"
Zeeyter ta ce, "Alhamdu Lillah ya kake ya aiki? Oga na Lafiya oh oh ya tafi Office shi kadai nake jira."
Dariya ya yi, "Alhamdu Lillah nima,umm wato yanzu ba wasa har ana fada mun shi kadai ake jira, Amman in tambaye ki mana."
"Eheen ina jinka." Zeeyter ta fada.
"Wasu dabi'u ne na mijinki da yake birgeki kika ji cewa zaki iya rayuwa da shi har karshen numfashi?"
Zeeyter ta numfasa kafin ta ce, "Mijina, shine asalin misali kan miji na gari kuma mijin kwarai,yana da duk wani abu da 'Ya mace zata so kasancewa da shi,sai dai azanci na dan adam wanda ba arasa ba,in zan ce zan fada ma wanene Sunshine sai mu kwana mu hini ban gama ba ai,amman ga kadan daga ciki,Yana da tausayi, Fara'a, Rashin girman kai, girmama da gaba da shi, kyauta da kuma son kyautatawa duk wani mukusancinshi har ma da sauran al'umma, Mijine mai goyon bayan matarshi a kullum kuma ako ina, har sai ga ta kai ga cin Nasara,mijine mai son matarshi don zuciyarta ba don siffa ko yanayi ba,mijine na rufin asiri,rayuwarmu ba boye-boye muna gudun bacin ran juna fiye da tunaninka, yanzu zan yi mai abu ya ce zai rama, kuma sai ya raman Amman ba hakan ke nufin zamu kullaci juna ba, na kanyi fushi mara dalili ko da nice da laifi amman zai aje girmansa ya ban hakuri, kasan meyasa duk yake hakan? Ba wai na fi kowacce mace ba ne aa, ya san darajar mace ne,yana mutunta mace,yana girmamata da kimarta, bai son ganin mace tayi ƙasa arayuwarta sam, burin sa a kullum mu dagu mu gyara komai ya tafi daidai, ban ya zan misalta maka ba amman a yanzu yadda muke Companyna ya fi na shi daguwa da daukaka ,harma da samun kudi wanda kuma duk asanadinsa ne amman bai damu ba ko kadan duk da hakan a kullum ci gaba na yake burin gani ,baya jin assara, hassada ko kyashi kuma baya tsoron matar shi ta fi shi,yasan zan iya bijere ma shi amman bai damu da hakan ba,saboda so kuma saboda Allah kawai yake komai,akomai nawa sai yadda karfinsa ya kare he is one in the Million ba ba kowanni namiji yake da wannan jarumtar ba na sha wuya arayuwa amman haduwata da shi alhamdu Lillah,duk da cewa yana da tashi Matsalar kamar yadda nima nake da tawa tun da bazaka taba samun mutum 💯 Amman Allah na tare da bayaninsa,duk zabin da Allah ya ma kamata ya yi ka gode masa ba kokarin nuna damuwa ko bijirewa ba Sunshine na daban ne aduniya ma gabadaya ba zan yi shakka ko jin tsoron nuna shi ako ina ba, ina alfahari da shi."
Farouk ya ce, "Umm gaskiya ne kun birgeni sosai da Sosai ina ma ace zan Kasance da tawa matar haka da nayi farinciki sosai, kasancewar ki cikin farinciki na sani Farinciki fiye da zatonki, ina miki fatan alkairy a kullum akuma kodayaushe sannan ina kara baki shawarar da ki rike mijinki tsakani da Allah kada ki bi rudin duniya."
"Hakane In sha Allah na gode sosai my abokin Dole watarana dai zamu hadu har ma in nuna ma Sunshine ko?"
Farouk ya yi dariya yana, "Eheen very Soon In sha Allah,byee Bara inyi wani aiki."
Zeeyter ta ce, "Owk Byee."
Kallon agogon wayarta tayi ta ga har 11 na dare babu Haiydar ba Deedarth.
Ga shi harta fara jin barci.
Kiran wayoyinsu tayi duka yaƙi shiga.
Hakan yasa ta tashi ta nufi gidan mai,ba kowa aciki sai mai gadi ko da ta tambayesa ya sanar mata cewa tun rana Deedarth ya bar compaynin.
Hakan yasa ta koma gida cikin damuwa.
Tana shiga falon wuta ta dauke.
Ji tayi an makure mata wuya ta kasa Numfashi bare magana .
Kokawa suke sosai amman sam anƙi saketa.
Jin alamun shigowar mutum yasa aka yi saurin saketa.
Haiydar da Deedarth suka shigo .
"Ya haka gidan ba wuta? Lafiya? Ina kike?"Cewar Haiydar.
Haska wayarsa da zaiyi sai ga Zeeyter agigice ta fita hayyacinta ban da kuka ba abun da take.
Da sauri ya ce Deedarth ya je ya duba wutar shi kuma ya karasa inda take.
Kankamesa tayi tana kuka.
"Mene ne ya faru? Ki fada mun Mene ne ya faru? Meyasa kike kuka?"
Cikin shashsheƙar ta ce , "wuyana,wuyana aka rike mun ina zaune kawai aka kashe wuta aka rike mun wuyana." Ta karasa maganar tana nuna wuyanta.
Dai-dai lokacin Deedarth ya kunna wutar yana, "cirewa aka yi kuwa."
Haiydar ya ce, "Kira mun mai gadi da sauran yaran gidannan dole akwai wanda ya shigo."
Dukansu suka ce su basu ga kowa ba,kuma basu san lokacin da aka shigo ba.
Cikin fushi Haiydar yake magana, "Kenan baku da amfani in har za a iya shigowa ba tare da kun sani ba,har a kashe wuta azo ana sheƙe mata wuya,da bamu zo yanzu ba da Shikenan ko? To Wallahi ba zan lamunci hakan ba,koma waye nasan yanzu yana cikin gidannan ku duba ko ina, lungu da sako a tabbatar an binciko mun shi in ba so kuke ranku ya ɓaci ba."
Ya karasa maganar yana sharewa Zeeyter hawaye tare da rike mata hannu su shiga daki.
Nan Gaɓadaya suka bazama bincika gidan amman abun mamaki an rasa gane ko waye babu kowa har suka gama bincikawa.
Kwantar da ita ya yi yana shafa mata baya , "ki yi hakuri kin ji.koma mene ne kuma koma wane ne zan nemo shi, ba zan taba bari wani abu ya sameki ba in dai ina numfashi kin ji."
Zeeyter ta ce, "nikam wana tarewa gani? Wa na hana rayuwa ake son kashe ni? Na san da kyar za abar ni, kullum da abun da ake bullowa da shi fa, Shikenan rayuwata cikin hatsari zata kare? Ba zan iya ba,na gaji wallahi."
Haiydar ya ce, "ba ina tare da ke ba? Koma me zai faru sai dai ya faru dani dake mu biyu bare ma in sha Allah indai ina raye ba wanda ya isa ya taɓaki, zan kira akaro mana securities cikin gidannan da ma company kuma za a kara zurfafa wannan binciken mu gano ko wane ne, kiyi hakuri harda dadewarmu ne silan faruwan hakan wanda an samu gida ne,muka je nida Deedarth muka kai su Baba kawai a wuce gun, kiyi hakuri kin ji,ina tare da ke har karshen numfashi na."
Gaba-daya Zeeyter a tsorace take da kyar Haiydar ya lallaɓata tayi barci.
Washegari
Da sassafe Haiydar yaje har office ya samu Dpo.
A fusace ya shiga ya ce, "Wato dai ba za ka fita harkarmu ba ko? Na ce ba za ka fita harkarmu ba ko? To Wallahi daga yanzu duk abun da ya sameta kaine na fada ma kuma za ka yi danasanin hakan,don haka tun farko ina kara tunatar da kai cewa ka fita a sabgarta domin in dai nina shigo rayuwarka za ka sha mamaki fiye da zatonka." Ya ƙarasa maganar yana ficewa.
Kallon fitar sa Dpo ya tsaya yi kawai yana dariya tare da fadin, "ga dukkan alamu matarshi ta manna masa haukar shi ma."
Haiydar na komawa gida Zeeyter ta ce, "Ina kaje ne da sassafen nan?."
Murmurshi ya yi kawai yana, "kinyi break?"
Zeeyter ta ce, "Aa amman ga Deedarth can a kitchen din ban san koyi yake ba."
Haiydar ya ce, "Ok zauna bara inje in taya shi, yau agida zamuyi aiki duka,in da abun da kike bukata a dauko ki aika tun yanzu."
"Ok."Zeeyter ta amsa.
Suna gama breakfast kowa ya fara aikinsa.
Zeeyter ta dafa kai tana tsaki.
Da sauri Haiydar ya juyo yana, "mene ne ya faru kuma?"
Zeeyter ta nuna masa system din tana, "na rasa yadda zanyi in fidda lissafin komai ya tafi a tsari tun shekaran jiya nake a company amman na kasa."
Haiydar ya karbi system din yana, "muga."
Sai da ya duba Sosai kafin ya ce, "tun farko ke kika yi mistake a lissafin ga yadda ya kamata ya kasance."
Sai da ya gyara mata komai kafin ya bata.
Murmurshi ta yi ta ce, "Sunshine."
Ya ce, "Yessss."
"Thank you,You are indeed a husband who has helped me in need. I Love you,I really really Love You."
Rumeta yana, "U are welcome My Baby."
Dagowa tayi tana cino baki, "am not ur baby oh oh am ur anty eheen."
Dariya Deedarth da Haiydar suka yi.
"Umm my Anty son girma." Deedarth ya fada.
Zeeyter ta kalli agogon hannunta , "Eheen rana ta kusa yi tunda Oga yace zaman gida za ayi kuxo mu je free food muyi girki,kowa ya sako kayansa yau mu barsu su huta."
"Owk Madame." Duka suka fada a tare.
Dariya tayi ta shige daki tare da dauko rigunan da hulunan ta ba kowa yasa suka fita.
Suna zuwa ma'aikatan suka fara yi masu barka da
Zeeyter ta ce, "CHICKEN BIRYANI za mu yi, yau ku huta duka kitchen din namune."
ASHIRIN DA SHIDA
Deedarth ya ce, "Yesss Ant ina son cin abincinki da dadi Sosaii,
Attaruhu,gree pepper,Albasa ta ba Deedarth ya yanka.
Haiydar kuma ta bashi nama ya wanke sannan kuma ya tafasa.
Tukunya ta daura akan gas din ta zuba mangyada da albasa mai yawa wanda Deedarth ya yanka sai da yan fara soyuwa kafin.
Ta zuba Tafarnuwa da attaruhu suma ta juya su sosai.
Tukun ta dauko naman kazan da Haiydar ya tafasa ta zuba, kayan kamshinta ,kori,kurkur da sauran abubuwan duk ta zuba sannan magi tana juyawa sai da komai ya kama jikin kazar sosai ta fara soyuwa kafin ta zuba tumatur nikakke.
Shima da ya kama jikin kazar sannan ta zuba ruwa.
Kafin ya tafasa ta wanke shinkafar ta.
Yana tafasa ta juye shinkafar cikin ruwan.