CHAPTER 41
Numfasawa Baba ya yi sai da ya yi dogon tunani kafin ya ce, "Tabbas kinyi tunani mai kyau kuma hanyar nan mai bullewa ce,amman tukun shin ita saudatoun za ta so shi? Sannan shi ma haiydar din zai so ta? Ina ganin mu ba shi dama kawai ya samu zabinsa."
Antou ta fara kame-kame, "umm yhum uhum saudatou ai yarinyar kirki ce ko da ni na tsara abu ba Mahaifiyar ta ba zata amince bare kuma Mahaifiyarta ,sannan shi ma haiydar kai ba ubansa bane da zaka fada ya ki amincewa ko da baya so? Ko kuwa ka taba sa Deedarth abu yaƙi yi sai shi Haiydar don yana da kudi? Bare kuma saudatou ba ta da mukusa arayuwa cikakkiyar mace ce ba irin matar shi ba ina da tabbacin zai sota don wannan matar ta shi ma in an bincika asirce shi tayi ta aure shi."
Ta karasa maganar tana kwalawa Unaisa kira.
"Ke Unaisa zo ki nunawa babanku hotunan da Deedarth yasa astatus."
Unaisa na zuwa ta fara nuna mai tana, "Baba kalli Yaya Haiydar fa ta mai da shi mai dakan sakwara shi kuma Yaya Deedarth harda yanka kayan miya,baba wallahii ta raina su,nikam na tsaneta wallahi gata munanniya ga jiki,kuma gata baƙa fa Allah sa ma Yaya Haiydar ya sake ta karta cinye masa kudi."
Antou ta teɓe baki, "umm to ka ga yarinya ma kenan bare kuma mu masu hankali."
Girgiza kai Baba ya yi yana, "ku shirya gobe za mu je can bobiel din."
Ya karasa maganar yana fita.
Tafi da shewa Unaisa da Antou suka yi.
Unaisa na fadin, "Antou kin fada masa ko? Ai gwanda nikam ma Allah sa in ya auri Sadatoun ya saki wacce zeeyten ni ko ganinta bana son yi."
Antou tayi wata irin dariyar mugunta, "kar ki ji komai ɗiyata indai ina nan komai ma mai sauki ne ai,na iya kora Mahaifiyar sa bare kuma matar sa? A dai juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, zamu dawo mune da komai shi kuma sai yadda muka yi da shi,na ji dadin yadda Deedarth ke shige mata jiki ko ba komai zan bi hanyar sako zargi a tsakanin su."
"Shi yasa ina sonki Antounmu ai gwanda wallahi muyi maganinta sai ta rasa wannan Murmurshin da ke fuskarta a kullum."
★★★
Su Zeeyter na kammala cin abinci masu aiki suka fara wanke wanke bangarensu suka koma ita da Haiydar Deedarth kuma ya shige bangaren su Madame Ayshe yana yiwa su Baby Lesson.
Sallah suka yi duka tana ganin Haiydar ya zauna a kujera yana danna waya tayi saurin kwanciya acinyar shi tare da fisge wayar ta ce, "Sunshine."
"Uhumm bani wayata mana sako zan duba fa ko an turo mun." Cewar Haiydar.
Zeeyter ta ce, "Yanzu ai ba lokacin duba sako bane ka ce yau free muke ba wanda zaiyi aiki, Don haka ka ta shi muyi rawa ka ji."
Haiydar ya bude baki, "Rawa ana zaune kalau? Ke dai je ki yi zanna miki video."
Dukan cinyarsa tayi cikin Shagwaba ta ce, "ni ba zan yi ni kadai ba, tare za mu yi."
"To ki daga ni sai muyi ko? Amman koya mun za ki yi." Haiydar ya fada.
Dariya Zeeyter ta yi tana, "eh mana daman kai mai ka iya ban da juya kai." Ta karasa maganar tana tashi tare da kunna kidan.
Yi take tana nuna masa suna yi tare Haiydar ya kyalkyale da dariya, "ke wallahi na gaji,wai ke bakyajin nauyin jikinki ne ma har kike iya abunnan? Bar ni in huta wallahi." Ya karasa yana dariya.
Ita ma dariyar tayi tana, "Yoo kai ba acici Mala'ikun tauna ba ai dole jiki ya ma nauyi ga shi ba wata kibar azo agani ba,zan fara tsara ma abubuwan da za ka ci yasin in kuma kayi wasa ka tsufa nikam ina yar cafes dina."
Haiydar ya rike mata kwankwaso yana, "ina yar cafes din anan?"
"Gani nan ko kana musu ne in nuna ma? ." Ta karasa maganar tana kokarin cire kaya.
Dariya ya yi yana rike mata hannu tare da fadin, "ba zai dai ki girma ba, kin fiso kullum kina birkitani,kin san yanzu indai na shiga wannan yanayin ba mai gane kaina So ki taimaka mun ki bari sai dare don gidan naki baya rabo da jama'a." Ya karasa maganar yana kissing dinta.
Ita ma din kiss din ta maida masa tana dariya, "Matsoraci kawai."
Ta karasa tana tafiya cikin kitchen.
Youghourt ta dauko tana sha, shi kuma yana duba wayarsa suna hira sama sama .
Zeeyter ta ce, "Sunshine wai ina Ammie ne? Kwana biyu ta manta damu tana can Saudia abinta."
Haiydar ya dafa kai, "Oh kin tuna mun fa,bara in kira ta ta Sykpee jiya mun gaisa a office ta ce tayi missing ɗinki ba ku yi hira ba."
Matsowa daf da shi Zeeyter ta yi ,yana kira kuwa Ammie ta dauko.
Tare suka mata sallama da gaisuwa.
Da Murmurshi ta amsa tana, "Allah ya maku Albarka 'Ya'yan kirki."
Dukansu suka amsa da "Ameen."
Ammie ta ce, "Yarinyar Kirki yakike ya kwana biyu? Ince yaron kirki baya bata miki rai ko? In yana yi ki fada mun inzo in zane shi ai bai wuce duka ba ko?" Ta fada tana dan dariya
Murmurshi Zeeyter ta yi ta ce, "Ammie ai in yamun tuni zan kiraki,tunda Ammie na ce ke ba tashi ba tashi ba,ina lafiya lau."
Haiydar ya ce, "nikam ina ganin kwace kiri-kiri."
Dariya Ammie ta yi tana, "kai na yayeka ai."
Zeeyter ta ce, "Ammie kinki zuwa Don Allah yaushe za ki zo?"
"Na kusa kadan in sha Allah kawai ku kasance cikin shirya mun abubuwan tarba , jiya munyi magana da Haiydar ya fada mun zuwan babansa da komai ,abun da nake so da ku shine ku rike junanku da amana sannan ku kawar da kai kan komai dole nasan akwai wasu sabun lamura da zasu bullo Mussamman gareki Zeeyter zai zo miki cikin bazata gwanda shi zsn iya cewa akusan cikin hakan ya taso, Amman duk wuya duk rintsi ina rokonku da ku rike junanku ka da kuyi abun da zai iya sanya ku dana sani daga baya,ku rungumi duk wata kaddara kamar yadda kuka rungumi na baya to na gaban ma masu zuwa ko wa inda suke zuwa ku rungumesu hannu bibbiyu Allah yana tare da ku aduk inda zaku kasance adduata da fatan nasara na na gareku har karshen numfashi na, ku rayu tamkar hanta d jini shine burina kuna ji ko? Allah ya yi maku albarka agaida su Madame Ayshe da Baby."
"In sha Allah Ammie don ma bata ji yarinyar taki." Haiydar ya fada.
Murmurshi Zeeyter kawai ta yi tana, "Mun gode sosai Ammie Allah saka da alkairi za su ji in sha Allah."
Da haka suka katse kiran.
WAIWAYE
Wannan Ammie ke nan Yayar Mahaifiyar Haiydar.wacce suka koma gunta alokacin da Antou tai sanadiyar barin mahaifiyar sa daga gidan babansa wanda bayan rasuwar maman ta sa ita ta ci gaba da kula da shi har ya girma ya tsaya da kafafunsa kafin daga bisani ta koma Saudiya da zama.
★★★ci gaban labari
Sun gama waya da Ammie kenan Zeeyter ta ji wayarta ta yi ƙara kamar yadda aka saba alert ne na kudi wanda tamkar albashi yake duk karshen wata sai an turo kuma har yanzu ta rasa gane wane ne.
Ta ce, "Sunshine koma wane ne mai turo kudinnan nikam kullum ina mai addu'a da fatan alkairi na wancen watan ma cikawa nayi na bada ayi masallaci a ƙauyen ƙaura wannan kuwa ina ga makaranta za mu gina masu domin yan ƙauyen na fama da zahilci ba arabi na boko wannan ai babbar masiba ce."
Murmurshi ya yi, "duk mai badawan ma yafi bukatar aikata alkairi ne fiye da asan shi, Allah ya mai albarka,kuma ya biyasa da Alkairansa,ke kuma Allah baki nasara adukkan aiyukanki na alkairi da kika sa agaba, sai ki samu Khaleel ku tattauna yadda ya kamata Makarantar ta kasance tun da kin ga kauye ne."
"Ameen Ameen ya Allah, can't love you less my Dan Lukuti acici, karfafa mun gwiwa da kake ya fi komai faranta mun ayanzu kam cikin rayuwata, bari dai in zama Hajiya zan yi maka rumbun abinci acikinka yadda ba sai ka ci ba za ka ji ka koshi."
Dariya ya yi yana, "Allah ya shirya mun ke Bright Eye."
Shigowar Deedarth ne ya dakatar da su kasancewar dare ya yi.
Alwala suka yi shi da Haiydar suka fita zuwa masallacin da ke gidan.
Suna fita Zeeyter ta shiga daki kenan aka kashe wutar gidan ga shi ta bar wayarta afalo.
Dibirbircewa tayi tana neman hanyar fita sai aka kunna.
A kunna a kashe a kunna a kashe ga wani irin taku da take ji tamkar ba mutum ba.
Daura hannu tayi aka da tayi wata kara daidai lokacin da suka idar da salla karaf Haiydar yaji a kunnesa.
Ko takalmi bai sa ba ganin yadda ya hango gidan ba wuta ya nufa.
Deedarth ma ya bi bayansa tare da tsayawa wajen inda wutar gidan take ya kunna.
A gigice Haiydar ya shiga gidan Zeeyter ta make agefen daki ban da rawa ba abun da jikinta ke yi ga hawaye da kwararowa daga fuskarta,tana ganinsa ta rungemsa tana, "ba za abar ni ba, wallahii kashe ni za suyi Shikenan."
Share mata hawayen ya yi ya zaunar da ita kan gado sannan ya dibo ruwa ya bata ta sha.
"Ba komai in sha Allah ki kwantar da hankalinki, ina tare d ke kinji."
A lokacin ta tashi tayi sallah tukun ta dawo ta kwanta a jikinsa ba tare da ta ce komai ba.
Deedarth kuwa dudduba gidan ya yi bai ga komai ba, ya dawo ya zauna yana jin takaicin wani azzalumine ke son ganin bayan zeeyter.
Washegari
Da sassafe sun dawo daga training.
Suna hutawa kenan Deedarth ya ce, "Anty me za ayi na break ne?"
Kafin Zeeyter ta bada amsa an fara nocking kofa.
Zuwa ya yi ya bude da Mamaki,Baba ne da Antou da kuma Unaisa.
Cike da mamaki Deedarth ya ce, "Baba Lafiya?"
"Lafiya lau Deedarth batu ne kawai muka zo da shi."
Ya ƙarasa Maganar suna shigewa falon.
Suna shiga shiga kowa ya zauna da sauri Zeeyter ta tashi tana gaida Antou kai ya kauce ta amsa Unaisa ko ban da kallon banza ba abun da ba abun da take yi ma Zeeyter, ko da ta gaida Baba ba yabo ba fallasa ya amsa.
Haiydar na gaida Antou kuwa cikin fara'ar kissa ta amsa, Unaisa taje ta rungume shi tana Murmurshi.
Gyaran Murya Baba ya yi yana, "To kun ganmu da sanyin safiyar nan, to batu ne ya tada mu batu wanda bana sanya bane, game da kai Haiydar mun yanke hukuncin da muke ganin yafi dacewa da kai da mu ma gaba-daya,domin zama da mata ɗaya ba naka ba ne,akwai yarinya ta wajen kawar Antounku Sadatou Mun zaɓa maka a matsayin wacce za ka ƙara a mata ta aure."
Wani irin mugun faduwar gaba Zeeyter ta ji, zuciyarta na bugawa cikin sauri a zaune take amman sai da jiri ya ɗibeta.
★★
Ganin ba za ta iya jure sauraren batun ba yasa ta saurin tashi ta nufi daki.
Tsaki Antou tayi.
Haiydar da Deedarth kuwa bin da ido suka yi.
Cikin zaƙuwa Deedarth ya ce, "Baba meyasa haka? Meyasa za ku ce haka? Me Anty ta rage Yaya da shi." Ya karasa maganar yana kokarin bin bayanta.
Cikin tsawa Antou ta dakatar da shi da fadin, "Kul na ce ma kul, Alhaji ka ga abun da nake fada ko? Ko baka gani ba? Rawar kafa yake zai bi biyanta me aka mata? Ince kishiya aka ce ba komai ba wanda Allah ya hallita ayi uku ma bayan ita? To dawo ka zauna ba za ta saɓu ba,baza amaidani uwar gantallu ba." Ta karasa maganar tana wuci kamar bijimin sa.
Deedarth ya koma ya zauna , "Antou Amman hakan bai dace ba sam ko da za a nemi ya kara auren bai kamata a fada gabanta ba,wannan ai kamar cin fuska ne, Gaskiya bai dace ba."
Baba ya ce, "ka ci gidanku na ce ungo nan ka ci gidan ku,kana nufin ka fi mu sannanin abun da ya dace kenan?mune muke ba daidai ba amman kai kana daidai ko? Hakan ya yi kyau,ko shi dan uwan naka bai musa zancen mu ba sai kai uban yan kaudi ka shiga tuggun mata zan yi maganin ka ne."
"Ahto ai ruwa ba ya tsami banza an gama da dan uwansa ne aka dawo kansa kuma wallahi ba za ta sabu ba zan dau tsattsauran mataki."
Haiydar kuwa kan shi a ƙasa ya ce, "Baba na san duk batunnan ba zai wuce kan haihuwa ba, kuma kamar yadda na sanar ma munje asibiti an duba mu lafiyarmu kalau sannan na yarda da wannan gwajin dari bisa dari,lokaci ne kawai baiyi ba ko ince Allah bai bada ba, bare ni bana daukan kaina a matsayin wanda bai da 'Ya'Ya yara birjik ne cikin giddanan wanda Zainab take raino komai ita take daukar dawainiyarsu tun suna jarirai har yanzu da suka fara girma, na dauke su tamkar 'Ya'Yan cikina domin kuwa Allah kadai yasan dalilinsa na yin hakan, watakila suna mafi Alkairi gare mu a yanzu ko da ace nan gaba za mu iya samun haihuwar. Ita kanta Marainiya ce amman hakan bai hanata walwala da inganta rayuwar yan uwanta marayu ba, ba abun da na nema na rasa gareta farinciki daidai gwargwado Alhamdu Lillah muna samu ina ga ko da 'Ya'yan cikin da zamu haifa ne baza su kasance mana yadda muke so ba kamar marayun cen,ta kasance dani lokacin da nake cikin kadaici, ta haskaka mun rayuwata babu amfani ace za a wulakanta mace wai don bata haihu ba, Gwanda in ya kasance ra ayine ga mijin ya kara ba laifi, Amman muna tunawa duk zafi da raɗaɗi bamu san irin wanda take ji azuciyarta ba take dannewa ba tare da ta nuna ba, amun wannan alfarmar a bar maganar kara aure ina son matata aduk yadda take kuma Aduk yadda za ta kasance."
Baba na kallon Antou ta kyafta masa ido tare da girgiza kai.
Gyaran Murya Baba ya yi kafin ya ce, "Na ji kuma na yarda da batunka amman maganar kara aure ba fashi, domin rashin haihuwarta bai dameni ba, a yadda kake ya kamata ace qn samu mata biyune a giddanan ba ɗaya ba, abun kunya ne a gareka ma ace mata ɗaya kake da sam hakan baiyi ba kuma ba tsari bane, na riga na yanke hukunci sannan yarinya za su zo da Unaisa har gida ku fahimci juna ba sai kaje can ba mun yanke wannan hukuncin da Antounku,bana son jayayya ko wani batu magana ta kare."
Deedarth ya bude baki zaiyi magana Antou tai saurin dakatar da shi, "To shugaban marasa kunya za ka kara ja da maganar ko? To Ahir dinka maganar aure anyi an gama kai kanka aurar da kai zan yi kwanan nan don ba zan bari a lalatamun kai abar ni da salati ba."
A lokacin Baba ya tashi yana fadin, "ni dai na gama magana,ku tashi mu nufi gida in samu inje gun aiki."
Haiydar ne ya rakasu har inda suka yi parking mota sai da ya ga fitar su agidan kafin ya dawo
Deedarth kuwa na falo ya yi tagumi ya rasa meke yi masa dadi domin yasan wannan tuggun duk na mahaifiyar sa ne.
Cikin daki Haiydar ya nufa ya samu Zeeyter kwance tana kuka.
"Bright Eye,mene ne na kuka? Ki daina kuka kada kan ki ya yi ciwo mana." Ya fada yana zama akusa da ita.
Matsawa tayi tana share hawayen dake fuskarta.
Ya kara matsowa inda take yana rike hannunta.
Ta fisge .
A karshe ma tashi tayi ta fita adakin ta koma ɗayan tare da kulle kanta.
Buga kofar duniyar nan Zeeyter taki budewa ranar ko office ba ta je ba adaki ta wuni ba ci ba sha.
Tun daga ranar Haiydar ya kasa gane kan zeeyter domin in dai yana guri to bata zuwa inko zuwa inda take ya yi nan take zata bar gun.
Ta kai ga kullum baya sanin tafiyarta da dawowarta daga Office.
Tana dawowa zata shiga daki ta kulle kofa
In dai ka ganta tana magana da dariya sai dai in Deedarth ne ko su Miemie sunzo suna hira, suma din tana ganin Haiydar duk dariyar da take zata bari ta bar wajen.
Ko ya mata magana bata kulawa in ma abun da ya shafi companyne sai dai ta tura Deedarth ko Halliru koma miye.
Dukkaninsu kowa ya shiga damuwa da ka gansu zaka tabbatar da cewa akwai matsala ko da Madame Ayshe ta ma Zeeyter magana ba ta ce komai ba.
Hatta daki sun raba kowa a na shi yake kwana.
★★★Wata Safiyar Lahadi.
Zeeyter na zaune a falo tana break Sallamar Unaisa da Saudatou ne ya dago da ita.
Daidai da fitowar Haiydar daga dakinsa.
Unaisa suna haɗa ido da Zeeyter ta galla mata harara, Sadatou kuwa karasa wa tayi gaban Zeeyter ta na gaidata, "Ina kwana ANTY?"
Wani gigitaccen kallo ta mata ba tare da ta amsa ba ta kawar da kai tana sakin tsaki.
Murmurshi kawai Sadatou tayi taje ta zauna afalon tana wasa da ya tsunta.
Unaisa kuwa zuwa tayi ta rungumi Haiydar tana, "Yaya Ga Anty Saudatoun Baba ne ya ce in rakota.
Ka ganta a falo kyakkyawaa Wallahi Yaya,Ina sonta."
Dago kai Zeeyter ta yi suka hada ido da haiydar
Murmurshi kawai ya sake tare da fadin, "Nima kuwa ta mun kyau tun kafin in karasa gare ta."
Rike masa hannu Unaisa ta yi tana, "Yawwa Yayana na san za ka sota ai, kyakkyawaa ce sosai fa muje."