5STARS CHRONICLE Book 2 FREEYA

CHAPTER 3

by @xayyeesherthulhumaerath

asibiti, shi kuma aka kullesa da zargin cewa yana cin zarafin matarshi ta hanyar duka. Farkawa ta yi ta ga Noor gefenta ga ta kuma a asibiti. Da mamaki ta tambayi Doctor ina Khaleel. Ya sanar da ita yana police station. Noor ta dauka kawai ta fice. Tana fita ta shiga taxi. Ko da taje office din ta samu anata fama da Khaleel kan cewa me ta masa yake dukanta ya kasa bada amsa kuma ya kasa karyata hakan. Aransa ya san cewa karyatawan ba ta da amfani domin in zai bude baki ya ce Sarah ce ke dukansa ba shi ya duketa ba,kallon makaryaci za amai,wasu ma su mai kallon mahaukaci. Ya zaɓa yin shiru saboda rashin karfin gwiwar

bayyanar da gaskiya,duk da cewa yana jin zafi aransa. Tana shiga ta nemi belinsa sannan ta sanar da su cewa ba laifinsa bane,laifinta ne, duk da cewa basu yarda da hakan ba kawai sun bata shi, domin gani suke kawai tana son kwatar mijinta ne. Mika masa Noor tayi suka shige mota. Ta ce, "Meyasa ba ka fada masu gaskiya kan cewa ni ce da laifi ba?" Tsaki Khaleel ya yi ya ce, "wa zai yarda? Wa zai aminta da abun da zan ce,karki yi tunanin Cewa sun yarda da abun da kika fada masu, sun aminta da hakan ne kawai don abu biyu,na farko kudi na biyu kuma kan cewa ni mijinki ne." Matsowa tai daf da shi tana

kokarin rungumarsa ta ce, "na ma alkawari zan canja,ka yi hakuri ka ji, ka san dai ina son ka ko?" Janye jikinsa ya yi,ya ce, "hakan ba sabon abu bane da kunnuwa na suka fara ji, canjawarki sai dai awata rayuwar amman ba a wannan rayuwar ba Sarah." Tsaki ta yi tana, "eh ba zan canja ba,ba zan canja ba,ka yi abun da ka ga dama in za ka iya." Ta fada tana daga murya. Murmurshi Khaleel ya yi, a zuciyarsa yana fadin, "ni na sani, ko da kowa na duniyar nan zai canja ban da ke, na san kina sona, canjinki na lokaci kalilan ya canja mana rayuwa dagani har kai,ban san wacce irin kaddara ce ke bibiyar rayuwata

haka ba, amman ba komai ,mahakurci mawadaci komai zai daidaita da ikon Allah." Suna isa gida tunda Khaleel ya ga sarah ta karbi Noor kan cewa shi yaje ya yi wanka,ita ma ta yi ta ma Noor ya fahimci inda ta dosa. Domin Sarah bata da hakuri sam aduk sanda ta so kasancewa da shi, amman shi in bukatar shi ta tashi a lokacin da bata ra ayi dolensa ya yi hakuri domin ba za ta taba amincewa ba ko zai mutu. Shi kuwa ya zaɓi hakuri tare da mikawa Ubangiji kukansa a kullum hakan kuma baya hanasa biya mata bukata aduk lokacin da ta so. Aransa yake fadin, "ba zan rayu da hakkinki ba Sarah, zan biya miki duk

wata bukata ta duniya indai ina da hali ko da ni ba za ki dubeni ba." Da kanta ta sanya Noor cikin abin wasa sannan nufi Khaleel tare da fara janye masa kayan jikinsa. Addu'ar da ya saba yi ya yin kasancewar hakan ya fara *Allahumma Jannibnash-shaiɗana Wajannibshi Shaiɗana Ma Raxaƙtana* Sai da ya tabbatar ta gamsu da biyan buƙatar ta kafin ya barta. Ta shi tayi abunta tamkar wacce ta je shago siyan abu,an bata ta tafi. tashi ya yi shi ma,ya je ya kara yin wanka ya yi sallah raka'a biyu bayan ya idar ya yi addu'ar Neman Tsari Da Kasala da kuma mummunan tsufa اللهم إني أعوذ بك من العجز والكسل والجبن والحرم والبخل, وأعوءبك من عذاب

القبر ,وأعوذ من فتنة المحيا والممات Sai da ya shafa kafin ya je ya yi shirin office. Sarah har ta kammala breakfast ya ci ya ba Noor ma. Zai fita ya ce,"Byee." Kallon shi tayi ta sake Murmurshi , "Byee." Ya fice. ★★★★zaune Adams yake da Sofiya suna hira. Zahra ta kammala abinci ta kawo masu. Da sauri Sofiya ta dauki abincin tana fadin, "Bo Yarinyar nan ta iya girki sosai,tun daga kamshin abincin ta zaka ji bambanci ina so inxo nan gidan inci abincinta, wannan dama gidan abinci ka bude mata." Tsaki Adams ya yi yana, "Tir wannan me ta iya,ki ma daina wannan batun." "Amman ina fada ma da Gaske za a samu kudi da girkin yarinyar nan

,ta iya fiye da zatonka,na tabbaata ko da bani ba,duk wanda zai shigo ya ci abincinta dole ya yaba." Adams ya numfasa,"ki bar batun nan Please bana so zai fi kyau ki ci abincin nan muyi mu gama mu fice." Dariys sofy tayi tana kai masa kiss. Zahra na jinsu ta koma kitchen din ta zauna abunta. Har aranta ta san cewa ta iya girki amman bata daukan hakan wani abun jin dadi domin baya da wani cikakken amfani gareta, sai dai ta girka wa wasu su ci su sammata, wani zubin ma sai dai hange. Jiyo Kukan Anitha tayi tana wani irin numfashi zazzaɓi ya kamata. A razane ta karasa ta dauketa. Gaɓadaya numfashinta ma na shirin daukewa. Kuka

Zahra ta fara cikin firgice tana yi wa Adams magana. "Don Allah ka taimakeni Anitha ba lafiya zata mutu,ta kasa Numfashi, Don Allah." Gaɓadaya daga shi har sofy sun shiga duniyar baɗalarsu , suna ganinta Amman ko ta ita basa yi bare su fahimci me take fada. Jikin Anitha sai ya kara zafi yake tana gurnani. Tunawa tayi da wannan kudin da mutumin ya bata, ta dauko su ta kara daurewa a jikinta. Kallon waje tayi,ruwa ake kamar da bakin kwarya ga shi ba bu lemar da zata sa ta fita. Tunani tayi cikin sauri ta goya Anushka a baya, ita kuma Anitha ta riketa a hannu tare da lullubeta da bargo. Haka ta shiga cikin ruwan nan ba takalmi

tana gudu, tana kuka tare da tambayar Mutane chemist ko wani a asibiti da ke kusa ta kaita. Da kyar ta samu wani asibiti da ke cikin jakartan ta kaita. Tana kaita aka karbeta taimakon gaggawa. Da kyar likitocin suka yi nasarar ceto rayuwar Anitha. Zahra kuwa Gaɓadaya ta fice a hayyacinta... ★★Uk Dare ne sosai Noor da Khaleel suna karatu kamar yadda ya saba duk dare sai koya masa karat mussamman addu'o'i Khaleel ya ce, "Oya karanta mun Addu'ar tashi daga barci." Noor ya fara, " *Alhamdu Lillahil lazi Ahyana ba'adama amatana wa'illaihin nushur*." Cikin muryar yara gwanin sha awa yake karatun. Khaleel ya ce, "Ma sha Allah Barakallahu fikha,yanzu yi mun adduar cire kaya." *"Alhamdu Lillahil lazi kasani

ma asturu bihi aurati wa'atahammalu bihi."* Ya fada. Murmurshi Khaleel ya yi ya ce , "Ma sha Allah bara mu yi ta yau to Addu'ar juyawa cikin barci, "La'ilaha ilallahu wahidul kahhar Rabbis Samati wal ardi wama bainahuml azizul gaffar." Sai da ya masa yana maimaitawa sau uku kafin ya ce ya yi shu daya. Noor ya ce, " *La'ilaha ilallahu wahidul kahhar Rabbis Samati wal ardi wama bainahuml azizul gaffar."* Khaleel ya shafa kansa yana, "Maddalla Allah ya yi albarka ka da ka manta kullum da safe da yamma me ake yi?" Noor ya ce, " *Hasbiyallah La'ilaha ilallah,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim*, sau bakwai da safe kuma sau bakwai da dare,Allah zai dauke mana dukkanin gajiyarmu

kuma ya gafarta mana." "Good boy yanzu sai barci ko?" Khaleel ya fada. Cikin tsamin bakin Noor ne ya ce, "Dad." Khaleel ya amsa da, "Yes." "Me yasa Mom bata sona? Bata kula dani? Amman grandma da kai kuna sona,kuma kuna kula dani,Ni bana sonta,kuma bana son ganinta,na tsaneta." Cikin sauri khaleel ya rufewa Noor baki, domin yasan Noor zai iya fadin mafiyin hakan yarone karami amman sai shegen Suratu da wayo, shekara hudu kacal amman yana lure da kowa. Khaleel ya ce, "Kar in kara jin haka ka ji,Mom dinka ce,kuma tana sonka SOSAI, kai ma na san kana sonta ko." Girgiza kai ya yi, alamar Aa. Khaleel ya rike masa hannu, "kana sonta Noor, ba a kin uwa

ko ya take ka ji,ita ce tai sanadin zuwanka duniya,kuma tun kana ciki take dawainiya da kai." Noor ya ce, "Dad amman meyasa take mana haka ni da kai?" "Me take mana? Bata mana komai ai, kowa da yanayinsa ka dauka cewa wannan shi ne yanayinta ita ai." Cewar Khaleel. Noor ya fara girgiza kai yana, "Aa aa Dad kai ne,kai ne za ka gyara." Daga nan Noor bai kara cewa komai ba,har ya yi barci. Khaleel kuwa tunanin maganganun Noor yake gabadaya ya kasa runtsawa mussamman in da ya ce, "Kai ne za ka gyara." Ganin cewa ya kasa barci yasa shi tashi ya dauro alwala da niyar yin Salatul-Tasbihi. *Salatul-Tasbihi* Raka Hudu ake kamar la'asar, Azahar ko Isha.

In kaso za ka yi karatu a sirrin ko a bayyane. Ko ka raba biyu a sirince biyu a bayyane. Ita ana karanta mata fatiha da sura ne acikin kowacce raka'a bambamcin kenan. In ka gama karatun fatiha da sura ba ruku'u za ka yi ba sai ka yi tasbihi. *Subhannallahi Wal-hamdulillahi wa la ilaha illallahu wal lahu akbar* sau goma a tsaye. Bayan ka yi ruku'u ma ka yi zikirorin da ake a ruku'u sai ka kara Yi *Subhannallahi Wal-hamdulillahi wa la ilaha illallahu wal lahu akbar* sau goma. In ka taso ma ka kara sau goma kafin kayi sujuda, in kayi sujuda ma kayi zikirorin da ake cikin sujuda ka kara tasbihi goma. *Subhannallahi Wal-hamdulillahi wa la ilaha

illallahu wal lahu akbar* Sanda ka dago daga sujuda ta biyu kar ka mike tsaye sai ka kara tasbihin sau goma. Sannan mutum ya tashi ya ci gaba har ya idar. Manzon Allah S.a.w ya ce , "za ka iya yi da rana kuma za ka iya yi da dare, in da hali kayi duk sati, in bai samu ba duk wata,in hakan ma duka bai samu ba ko sau dayane kayi kafin Allah ya dauki ranka, tana da falala mai dama da inganci. Wannan ita ce Salatul-Tasbihi sallah mai daraja, wanda Annabi S.A.W ya bawa kawunsa. Tare da albashirin Allah zai yafe masa kurakurensa kananu da manya, sannan ya biya masa bukatunsa da ikonSa. Haka Khaleel ya yi,yana idarwa

tun daga lokacin ya fara jin sanyi aransa tare da jin tsammanin da ya rasa ya dawo. Barcinsa ya yi cikin kwanciyar hankali nan take. ★★Indonesia Zahra kuwa tana zaune dauke da Anushka a hannunta tana feeding dinta. Kallonta take ita kanta ta san cewa babu maraba tsakanin kammaninta da na su Anushka, tamkar anyi kofin ta ne. Duk cikin kunci da take shiga indai ta kalli Anitha da Anushka ta kan ji dadi aranta zuciyarta tai sanyi. Ta lula duniyar tunanin hanyar da za ta bi ta koma gidan Adams kamar daga sama ta jiyo sauti a Tv,daga idonta tai cikin sauri ta ga wani matashin saurayi na jawabi. "Daga karshe, kuma a karshe A wani yanayi na rayuwar

mutum ya kamata ya yankewa kansa cewa ya isa haka, wannan ba rayuwar da zan ci gaba da yi ba ce, na hango rayuwa ta daban wa kaina, a yanzu kuma zai zamto yanayi mara dadi, kuma zai zamto yanayi mai ban tsoro, sannan yanayi na daban,kuma yanzu ne ya kamata na fuskanci abubuwan da zan canza game da kaina da rayuwata, kuma dole na girma, dole kuma na shiryawa wa kaina kuma na tsarawa kaina, na nemi taimako, amman wannan abar da ake kira rayuwa, lallai ya zo karshe yanzu, dole na canzata zuwa wani abu daban, Kuma dukan dan Adam din da ya ke jina ko sauraron muryata a yanzu, yanada karfi da damar da zai iya canza

rayuwarsa. Ba a fidda tsammani,ka da mu fidda ko na second dayane sanya tsammanin wani ci gaba na rayuwarka." Maganar Doctor ne ya katseta yana mika mata Anitha tare da bata Bill din kudin da ta biya harda sauran canji. Dare ya yi sosai ga shi tana jin yunwa karban canjin tayi tana kallo, tare da goya Anushka kafin ta rike Anitha suka fice. Tana cikin tafiya ta ga wajen sai da abinci, karasawa tayi ta bada kudi aka zubo mata da mamaki kudin nata kadan ne amman an zubo mata abinci da yawa,aranta ta ke rayawa lallai nan gurin suna da arhan abinci. Tana cikin ci jawabin mutumin tvn nan na yawo aranta nan take ta ji cewa ba

za ta koma gidan Adams ba, ta yarda da cewa ta fuskanci rayuwarta da duk wani ƙalubale har ta kai ga cin Nasara da kuma samun ma'ana fiye da ta koma rayuwa irinta baya. Ta ci abinci ta koshi sannan ta bawa Anitha ma ta ci. Duka sunyi barci Har kowa ya watse agun sai ita kadai da mai gun abincin. Karasowa matar ta yi gareta tana, "Madam ya dai? Dare ya yi gashi har yaranki sunyi barci,ya kamata ki koma gida kar mijinki ya nemeki." Dagowa Zahra tayi cikin sanyayar muryarta ta furta, "Don Allah ko za ki iya taimaka mun da aiki da gurin kwana anan? Ko me ki ke so zan miki." Tsayawa matar tayi tana kallonta

kafin ta ce, "ina da wadatattun ma'aikata anan, amman kuma in zaki iya aikin wanke-wanke da Shara sai abaki,gaki kuma da yara anya zaki iya?" Zahra ta ce, "xan iya,na miki alƙawari zan iya indai xaki daukeni." tausayin zahra ne ya kama matar duk da cewa bata san asalin dalilin zuwanta ba,amman Mussamman domin yaran taji cewa lallai zata taimaka mata. Hakan yasa ta karbi Anitha suka shiga ciki tare da nuna mata wani dan gefe ta dunga kwana da yaran. Ta dauko mata wani dan bargo mai kauri da za su kwanta akai. Ba karamin dadi Zahra ta ji ba hakan yasa ta fara gode mata. Washegari Safiya na yi kuwa Zahra ce ta fara tashi ta share wajen

tas ta yi moping tayi wanke-wanke . Madam Zuby na zuwa da mamaki ta tarar har Zahra ta gama komai, gun ya yi kyau fiye da zatonta tamkar mutane goma sunyi kwalimarsa. Ba karamin farinciki ta ji ba da ta tarar da wajen haka. Hakan ya kara sawa taji zahra ta shiga ranta Sosai. Su kansu sauran ma'aikatan da suka zo cikin mamaki suka kasance,sai da Madam Zuby ta gabatar masu da Zahra tare da nuna cewa ita tayi dukkanin wannan aikin. Faran faran sun amsheta hannu bibbiyu sai mutum daya Sumy da kallon banza ne kawai ya haɗata da Zahra,tana gaisheta ma ko Amsawa ba ta yi ba. Nan da nan suka shiga girki, ganin cewa Zahra bata aikin

komai taje ta fara kama masu tana taya su. Da sun hada ido da Sumy sai ta harareta. Ita ko sunkuyar da kanta take kawai. Anitha na gun Madame zuby har sun fara sabawa da ke tana son yara. Anushka kuwa na bayan Zahra. ★★★Uk Khaleel na Tashi da safe kawai zuciyarsa ta yara masa cewa komai ya zo karshe. Bayan sun shirya shi da Noor ko Sarah ba su jira ta fito ba ya fice. Driect kotu ya nufa tare da karbo takardar saki. Ya nufi gidan Ammuh. Bayan yaje ya kira sarah kan cewa ta zo ta same shi acen. Sarah ta ce, "Mene ne ya faru da ba zaka zo gida ba,ko kuma ka bari sai ka

dawo?" "Aa wannan lokacin shi ya dace kuma anan gidan, ba zan bari tsammanin da nake da shi ya kau ba,ya zam dole a yau in canja rayuwata, taki,har ma da ta Noor.". Bai ce ma Ammuh komai ba har sai da sarah ta zo ya ciro takardan saki ya karasa gareta yana, "komai ya zo karshe komai ya zo karshe daga yanzu bazan kara lamunta ba,ba zan kara barin komai ba,ci gaba za a samu ba ci baya ba, dole in gyara ya zam dole in gyara." Ammuh ce ta karaso tana fadin, "meya faru? Wai mene ne kake haka ne Ibrahim Khalil? Me ka ke nufi." Khaleel ya ce, "Ammuh cutarwar da nake fuskanta a rayuwar aure bana

da muryar furta, tsoro,gudun magana da kawa zuci sun hanani aikata komai uwa uba jawabanki da na rike araina sukan kara karya mun zuciya a kullum ki kan ce (mace Abar tausayi ce,abar a girmama ce kumq abar a tarairaya, ka da in musgunawa kowacce 'Ya mace domin mata taurari ne,a tafiyar dasu tamkar sarakai) a kullum wannan batutuwan suna yawo acikin zuciyata ,suna kara sanya mun cewa mace ba zata iya cutar da kowa ba, na kan manta cewa ni ana cutar dani, rayuwar shekara ɗaya na yi kacal na jin dadin rayuwar aure daga nan Sarah ta fara fidda mun Dabi'un da suke kokarin nukusar dani na tsawon shekaru hudu,ban taba furtawa ba,kuma ban taba nunawa ba,a yau

yazo karshe komai ya zo karshe." Ammuh ta ce, "duk da haka ka bata dama,na tabbaata zata gyara da ikon Allah ." Khaleel ya ce, "Aa na tabbaatar ba zata gyara ba Ammuh ba zata taba sauya wa ba wannan jta ce rayuwarta ,na gaji zan matsa ga wata rayuwar haka.". Ammuh zata kara magana sarah ta dakatar da ita cikin kuka tana fadin. "Aa Ammuh zan sanya hannu komai da ya fada gaskiya ne,babu karya aciki ko da wasa na aikata mafiyin zato ma Amma kafin nan zan tabbatar maka da cewa hakan ba son raina bane,a tunani hakan ne kawai mafitar da zan bi don kubutar da rayuwa daga kuncin rayuwar da Mahaifiyata ta fuskanta,na dauki hakanne tamkar

daukan fansa,munyi auren soyayya kamar yadda mahaifina suka yi da mamana, amman abun mamakin shine daga shekara biyu bayan auren su ya fara juya mata baya,na taso da kiyayya, tsana da rashin son mahaifina sam. Mahaifiyata ta zam tamkar baiwa ga ubana,ta zam shara mara amfani, baya darajarata bare darajara ra ayinta,bata da karfin furta damuwarta, tunda na taso aduniya ban taba ganin mahaifina yana yiwa mahaifiyata magana cikin lumana da nuna kauna ba, kullum hawaye ne dak ke mamaye fuskar mahaifiyata maimakon dariya, inko zata yi murmushi sai dai ni takewa wasa gudun kada in sanya damuwa araina, hatta kai ta kawo duka ne yake mahaifina da Mahaifiyata, kullum cikin duka da zagi ga, cin fuska ba wanda bata