5STARS CHRONICLE Book 2 FREEYA

CHAPTER 4

by @xayyeesherthulhumaerath

fuskanta, agaban idanunmu zai shigo da 'Ya'Ya mata,yaje ya kwanta da su, Mahaifiyata bata isa ta ce komai ba,to ina ma take da karfin maganar? Ya yi amfani da rauninta ya tozartata har ta mutu sanadin bakin cikinsa, na taso da zuciyar daukan fansa, da kallon cewa dukkanin maxa haka suke mugaye da alhakin cutar da mata, na sa araina ba zan taba lamuntar hakan ba, kuma ba zan jure ba, sai na fito na gwada mace ma za ta iya,amman haduwata Khaleel ya sauya mun tunani tun farkon kasancewar mu , shekara guda da muka yi na yarda cewa ba duka aka tura aka zama daya ba,abu dayane sanadin komawa ga wannan mummunan kudirin nawa." Cikin kuka Ta numfasa

ka fin ta ci gaba da fadin. _"ba zan taba mantawa ba akwai ranar da naje office na bi Khaleel domin ba shi wasu takaddu da ya manta da su, office din dad na fara bi, kamar a kunnena na ji yana sanar da wani abokin huldarsa kan cewa shi ne yasa Khaleel ya nemeni har ya aure ni, ba tare da na jira jin mai zai ce agaba ba kawai na tafi tare da wata fasarar araina, na dauka cewa kawai ya aura mun Khaleel ne don nima inyi rayuwa tamkar yadda Mahaifiyata ta yi,hakan kuma yasa na canja akalar rayuwarmu tare da niyar daukan fansa tunkan a aikata mun ni na aikata._ Gabadaya jikinsu ya yi sanyi karfan

takardar tayi da bairo tayi signing. Ammuh na kuka ita ma na kuka. Ta ce, "Na sa hannu, amman ina buƙatar alfarma daya,ba don ni ba ko Don Noor mu ci gaba da rayuwa tare ba tare da kowa ya sani ba, sannan na je asibiti bayan wannan abun ya faru likita ya kirani ya sanar da ni cewa ina dauke da Leukemia ma ana blood concer,ya riga ya yi karfi tun kafin in sani ba abun da za a iya a yanzu, na san sauran rayuwata aduniya kalilan ne ya rage,ka yafe mun kuma ka gafarta mun." Rungumeta Khaleel ya yi yana share mata hawaye tare da fadin, "In sha Allah ba zan taba fidda miki sirrinki ba, ina

sonki ba wai hadani da ke dad ya yi ba,har cikin raina ina kaunarki." A lokacin Khaleel ya tafi tunanin farkon haduwar su da sarah. _ranata ta farko da kasancewa a company, ke ce wacce na fara toxali da ita in ban manta ba,kina sauri kin fito na bige ki takardun hannunki suka fadi kasa,na baki hakuri sannan ya kwashe miki,baki ce dani komai ba,inata kallonki ko ince muna kallon juna, a lokacin dad dinki na lure da mu ba tare da mun sani ba,bai mun magana awannan ranar ba har sai da ya gama aminta da ni kuma ya lura da cewa a kullum in kikaxo company bana da muradi sai kallonki.ya bani amarnki tare da fadin indai ina

sonki inje mu daidai ,na kuma amshi hakan ne da son raina domin cika muradi na har muka fara soyayya,sannan abun da yake fadawa mutumin nan ba komai bane illa nuna cewa yarda da kuma yana neman hanyar da zaki yafe mai ne yasa shi jin sha'awar hadani da ke ba komai ba."_ A lokacin sarah ta fara wani irin tari Da aman jini...... A kwana a tashi rayuwa ta sauyawa Khaleel da Noor tamkar an ciro su daga keji. Dadyn Sarah kuwa ya ce wa Khaleel zai iya ci gaba da aiki in yanada ra ayi ko ya bude nasa companin. Kullum yana tunanin tsare tsaren da zaiyi tare da gina abun da zai taimake sa kuma ya taimaki

al'umma, hakan yasa ya ci gaba da zuwa Officen din kafin ya kammala komai. Da safe yana shiri zasu fita har sun je kofa Noor ya ce, "Wait Dad, *Hasbiyallah La'ilaha ilallahuwa alaihi takwalna wa huwa rabbul arshil azim* 7× In The Morning Also In The Evening, You forgot it right?" Murmurshi Khaleel ya yi,ya rike hannun Noor suka zauna yana, "Eheen good boy,Na Gode da tunatarwa yaron kirki." Sai da suka yi sau bakwai din a tare kafin suka tashi ya fara mika Noor Skul kan in lokacin tashi ya yi za a kaisa gidan Ammuh,sannan ya wuce office. Yana isa office ya tarar an kafa dandalin gulmarsa ana yi ba tare da sun san ya zo ba banda

zagi ba abun da suke. Dayansu ya ce, "ni fa daman tun farkon zuwan sa Compaynin nanin na fahimci yana da son duniya amman a munafurci yake abunsa yoo ba dole ya jure wulakanci ba tunda daman yasan dole zai samu kudi, na tabbata don kudi ya zauna da ita har ta mutu ga shi yanzu ya kwashi garabasa amman tsabar son duniya ya kasa barin Compaynin nan muma mu sarara kowa ya zo fa sai ya ce ya fi so ya jagoranci zanensa na tsanesa wallahi." Karaf dayan ya ce, "burinsa ya cika ya kwashi kudin ai yanzu ko da bai bar Office dinnan ba,mu zamu kora shi, haba ace namiji mace na juyasa kamar waina kai ma kasan

ai ba a banza ba,kudi ne ke aiki kawai." Murmurshi Khaleel ya yi ya karaso inda suke yana, "Most people won't ever know your full story They will know a version of it. Don't live your life chasing people to understand you. When you ware made to be different And Anybody who blieves lies about you, before even hearing your side of the story,was Already looking for way to be against you." Dukan su kasa dogawa su kalleshi suka yi, gaba-daya jikin su ya yi sanyi tamkar an dauke ruwan sama. Yana karasa maganar ya yi Murmurshi ya wuce. ★★Zahra na sauri Zata mikawa Madam Zuby kayan abincin da tasa ta ta dauko fitowan da za ta yi Sumy ta

sa mata kafa,ta kifa da baya ga Anushka na goye. Wata irin kara Anushka ta..... ★★ Sake wani gigitaccen kukan Cikin dimaucewa Zahra ta tashi tana Ciro Anushka a baya, Gaɓadaya ta kwarjane ta ji ciwo, ga hancinta ban da jini ba abun da ke zuba. Da sauri Madam Zuby ta karaso tana karban Anushka suka yi asibiti. Gaɓadaya Zahra ta dimauce ta rasa meke yi mata dadi, Sumy kuwa ko ajikinta tafiya ta yi ta ci gaba da aikinta,yayin da sauran ma'aikatan suka tsaya jimami wasu kuma suka bisu asibitin. Cikin ikon Allah ake yi ma Anushka Treatment jini ya daina zuba,aka mata allura sannan suka dawo. Madam Zuby ta cewa sumy, " Shin ke bazaki je ki duba

yarinyar bane? Ke kika bigeta amman ko kalmar hakuri banji kin furta ba,bare duba ta." Bata rai tayi ta ce, "Madam zan je ina so ne in gama aikin da nake." Madame zuby na tafiya, sumy tayi tsaki ta ci gaba da aikinta. Tana fadin, "A son raina ma da yarinyar mutuwa tayi har ma uwar duk sun zo sun takura mu." Zaune suke duka suna aiki wata kawar madam Zuby ta zo gunta . Ta ce, "Daga asibiti nake wallahi, maganar jan da hokorannan nawa suka yi yana damuna,na kasa hakura ko za a dace ,har kunyar shiga cikin mutane nake." Kafin Madam Zuby ta yi magana karaf Zahra ta ce, "In ba damuwa zan iya taimakonki?" Murmurshi ta

yi,ta ce, "Why Not." Zahra ta je ta tsinko mata aloevera ta ce, "Wannan ruwan nasa zaki matsa ki sanya akan toothBrush dinki sai ki wanke bakin ,ka da ki damu da batun jini, domin ba zaiyi ba, kuma ko da ma ya yi ba wata matsala,in sha Allah hakorinki zai yi fari tas." Nan take Anty Asma'u ta ce, "Ah wannan ai ba sai anjima ko gobe ba, anan tun yanzu zan gwada gogewa daman da toothBrush din da na siya a asibiti bara in gwada da shi." Kamar wasa kuwa ta shiga toilet din wajen abincin, ta wanke bakinta tas da ruwan aloevera, kamar a Mafarki har tun ayi na farko har yanayin bakin ya fara sauyawa ya

dan yi kyau. Tsabar farinciki aguje ta fito tana rungume Zahra, ta kasa rufe bakin tsabar murna ta ce, "ku san shekara biyar ina faman neman mafita amman yau cikin kankanin lokaci kin kawo mun hanyar warware matsalata, , tun a yi daya na ga canji,ina ga inna ci gaba da yi a kullum kuma?Allah ya rayaki ya raya yaranki, ya biya miki dukkanin bukatunki na alkairi,na yi matukar farincikin zuwa wajen nan yau fiye da kullum." Madame zuby ta yi Murmurshi ta ce, "tabbas Zahra ta ci sunanta ,haske ce ako ina domin zuwanta ban da haske ba abun da ke karuwa a wajenan, yanzu dai in sha Allah case close madam Asmy hankali ya kwanta na tabbata kika

daurewa yin hakan sai an sha mamakin yadda haƙoranki za su yi haske,ba ma ke ba,ni kaina zan fara domin kogi bai ƙi dadi ba." Dariya ta yi ta ce, "Sosai ma wallahi kamar anmun wata babbar kyau,ke sai na miki kyauta ma in sha Allah zuwa gobe,yanzu zan yi sauri in karasa gida saboda yan night School Study Center yau zan fara daukan sabin dalibai kuma nasan tun yanzu za a fara zuwa cika Form,byee oll see you tomorrow." Har ta tafi ta kara dawowa ta ce wa Zahra, "Thank you so much Daughter." Bayan ta tafi Zahra ta ce wa Madam zuby, "Madam makaranta ce take da ita?" "Eh Makaranta ce amman ba norml school jami'a ko secondry

ba, makaranta ce ta koyarda wa inda suka girma ba tare da sunyi karatu ba, basu san komai, Madam Asmy bata son ta ga mutum ba karatu Mussamman mata, bata so ta ga ana tozarta su don basu yi karatu ba,hakan yasa ta yanke shawarar bude Makarantar yaƙi da jahilci (Night School Study Center) Amman da dare ake yi from 9 to 12 , ana koyarda maza da mata karatu sosai wanda in mutum ya kammala ma zai iya ci gaba driect saboda government Approved ce,mutane da yawa suna zuwa nan Sumba Island zama don Makarantar kawai." Zahra ta ce, "Nima zan iya shiga? Ina so nayi karatu ko ba don kaina ba, domin su Anitha da kuma taimakon Al'umma

in hakan zai yiwu." Madame zuby ta ce, "me zai hana? Zaki iya ni da ke ma gobe za mu je sai kiyi registration daman goben zaki fara karban albashi, karfe 9 lokacin ba ki da wani aiki daman sai kije school dinku su Anitha za ana lura da su in sha Allah." Ba karamin dadi Zahra ta ji ba, domin duk da kasancewar sunan school kawai take ji abaki ba ta san ya take ba,ba karamin so da kaunar kasancewa cikinta take ba. Washegari kuwa bayan sun gama aiki Madam Zuby ta dauki Zahra suka nufi gidan Anty Asmy wanda anan school din take. Suna zuwa kuwa suka tarar mutane sosai anata registration. Anty Asmy taji dadin ganinsu Sosai

Mussamman da taji batun cewa Zahra ce ta zo registration. Ko biyar bata karba nan take aka mata. Ko da aka zo mata interview ta fannin Turanci ba a sha wuya sosai ba, saboda tana dauka lokuta da dama in Adams nayi, Shiyasa hakan yazo mata da sauki. Littafan da za'a koyar da su Anty Asmy ta haɗa mata tare da sanar da ita bayan sati biyu za su fara ɗaukar darasi, godiya suka yi suka tafi zuciyar Zahra cike da farin ciki, tana son karatu sosai, don haka ta ƙudirta a zuciyar ta zata jajirce sosai tunda ta samu dama dole zata yi amfani da ita. ★★Khaleel zaune yana aiki a system, Noor kuma yana kallo A tablet dinsa.

Wayarsa ce ta fara kara ya na dubawa ya ga number Xavier . Murmurshi ya yi a zahiri kafin ya daga yana, "Hello Friend yau wacce sa'a na taka ne?" Xavier ya ce, "Kai dai ko, ba wani batun sa'a amman afwa ban kira gaisuwar madam ba sai yau aiki ya yi yawa,ya karin hakuri? Allah ya jikanta ya gafarta mata." "Alhamdu Lillah, mun gode Allah."khaleel ya fada Xavier ya ce, "Ma sha Allah ana nan ana shan barcin fama ko? ya Yarona kuma?" Dariya Khaleel ya yi ya ce, "barci ka san ba fashi ai,yanzu ma yaronka ne ya hanani wai muna Lesson." Noor ya ce, "Dady abani Uncle mana." Mika masa wayar khaleel ya yi, Noor na karba

ya ce, "Uncle na yi kewanka yaushe za ka zo? Ka tawo mun da irin uniform dinka ka ji, da takalmi,da agogo da turare fa." Dariya Xavier ya yi yana, "Oh Yarona kullum surutu karuwa yake,to shikenan zan kawo ka ji in sha Allah, ka kula da kanka kuma ana karatu sosai da kyau, Gudnyt byeebyee." Noor ya ce, "Ok Byeebyee unlce kar ka manta da addu'a in zaka kwanta barci dady ya fada mun ba kyau barci ba addu'a kuma ba hali bane mai kyau hakan zai sa mutum ya yi mafarkin Dodo, Byeebyee." Har cikin ran Xavier yana matukar kaunar Noor, Mussamman dabi'unsa da suka kasance na daban cikin yara. Khaleel ne ya karbi wayar Xavier ya ce,

"Friend yau ba wani guzirin da za abani ne ko da yake kace ka yayeni." Dariya Khaleel ya yi ya ce, "Eh mana yanzu kam ai sai dai ka koyar dani ba dai in koyar da kai ba,amman kar ka ce nama rowa ,ka wata addu'a da zaka karanta in wani abu ya faru da kai, *Allahumma La Sahla Illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alul hazna iza shi'ita Sahlan*." Murmurshi Xavier ya yi ya ce, "Barakallahu fikha Abokina, Maddallah da kai,ina farincikin kasancewa da kai a kullum domin kai din alkairi ne gare ni." "Umm baka da dama Friend ,na san ba abun da yafi sadaukarwa a duniyar nan cire komai arai,ya yin da duhu yazo yi sauri ka kawar

da idanunka tare da hango haske mafi inganci, Allah zaba mana rayuwa mai albarka,ni dai ina fada ma na kusa maka aure kowa ma ya huta,don yanzu ka wuce gauro ka zam tuzuru." Khalil ya fada Dariya Xavier ya yi yana, "Ey aure ko? Da saura fa,har yanzu ban ga wacce ta dace da tsalelen saurayi kamata ba, sai na zaɓa na dirje eheen amman ka ce za ka mun aure ai za ayi abun kunya don guduwa zan yi in barka da matar." A tare duka suka yi dariya. Khaleel ya ce, "ka tsaya wasa ka ga, serious aure zan ma kuma dole ka zauna." Da haka suka rabu ana wasa da dariya. _Xavier abokin Khaleel ne, tare suka

tashi har suka yi karatu shi ya karanci Law, Khaleel kuma Art suna kammala ya fara aikin MI6 (Military Interligent service) Christian ne Xavier amman kasancewar sa da khaleel ya sanya masa sha'awa da muradin musulunci, khaleel ya yi amfani da wannan damar wajen kara kwadaita masa dadi da inganciin musulunci amman har yanzu Allah baiyi ya musulunta ba, Duk da cewa sanadin Khaleel ya san abubuwa da dama da suka shafi Addinin Musulunci Sosai,Sallah har ma da addu'a, wanda hakan yana masa amfani sosai wajen aikinsa, lokuta da dama ba a iya bambamce cewa shi musulmi ne ko akasin hakan domin ya kan yi amfani da kowacce siffa so,a kullum buri da fatan Khaleel ya ga ya musulunta, Mussamman

yadda ya kasance da kyawawan dabi'u_ ★★Ruwa ake sosai tamkar da bakin kwarya, Noor ya ce, "Gud....... Kafin ya karasa aka yi wata tsawa mai hargitsa kwakwala. Ya ce, " *Subhana Man Yusabbihu Ra'adu Bihamdihi,wal mala'ikatu min khifatihi*." (Wannan ita ce addu'ar da ake yi ya yin da aka yi tsawa cikin ruwan sama) Khaleel ya kalli Noor Ya ce, "Ma sha Allah daz my boy,Gudnyt ayi addu'a kar amanta ama Mom addu'a Allah ya haskaka kabarinta ko?" Noor ya ce, "In sha Allah Dad,Ina sonka ka ji,u are d best papa in the world." Ya karasa gaban Khaleel ya masa yana yi masa kiss Kan ya tafi yana, "Byeebyee,Gudnyt." ★★ ★★a kwana a tashi yau sati biyu cir tayi

,adaren ranar Zahra za ta fara attempting class. Da safe bayan ta gama aikinta ta yi ma su Anitha wanka, ta shirya su tsaf da kayan da madam Zuby ta basu. Sumy ce ta fito daga kitchen jiki ba laka ta karaso gaban Madam ta ce, "Ma... Sai kuma ta kasa karasa maganar ga alamun tsoro fal fuskarta. Madam Zuby ta ce, "Ya dai? Lafiya kuwa? Kiyi magana mana Sumayyah." Cikin in ina Sumy ta ce, "Maaa...dam wallahi Allah ba da sani na bane Allah ku..wa..." "Ki fada mun mai ya faru mana mene ne wai?" Madame Zuby ta fada Sumy ta ce, "Ruwan Shinkafar da nasa ya yi yawa ta fara caɓewa, kuma,kumaa Soup din ma gishiri ya zarce

mun." Hanu aka Madame zuby tasa tana furta, "Innallillahi wa inna illar raji'un, yanzu kina nufin Shikennan na yi asarar abincin yau? Shikennan sai dai a kara komai sabo? Allahumma ajirni fi musibatiy." Zarah ta ce, "Aa Madam muje in gani watakila za a iya gyarawa ba tare da anyi asara ba." Kitchen din suka je duka, Zahra ta duba Shinkafar ta ga ta fara caɓewa. Biredi ta dauko irin mai yanka yanka dinnan ta jera guda hudu a saman tukunyar da ke abincin da yawa kan ta rufe. Ta duba miyar ta dandana gishiri sosai ya fito,ta dauko dankali ta fare guda biyu ta jefa cikin miyar ta barsa ya ci gaba da tafasa. Gun Shinkafar ta dawo cikin

minti biyar har ruwan ya kafe duk ya koma jikin biredin ta ware kamar ba ita ba. Miyar ma aka cire dankalin tana dandanawa duk babu gishirin ya koma ya tattare cikin dankalin. Rungumeta Madame Zuby ta yi tana fadin, "Thank you, thank you so much, da yanzu ban san yadda zanyi ba, da na tafka babban asara wanda kafin in dawo daidai sai anji jiki na gode sosai Zahra,kina da baiwa matuka, Allah ya kara haskaka rayuwarki da hasken sa, Allah ya biya miki dukkan bukatunki na alkairi duniya da lahira, baki ya yi kadan wajen nuna farin ciki na,mamaki nake wai biredi ne ya gyara mun Shinkafar da ta fara jiƙewa ko kyan gani babu, dankali kuma ya