5STARS CHRONICLE Book 2 FREEYA
CHAPTER 7
ya dawo ya mata Reply da fadin, "That's Good,You Just tell your self,no matter how hard it is,or how hard it gets, I'm going to make it." Daga nan suka bige da hira ta Dm suna hirar duniya da yadda ta zama,abun mamaki cikin kankanin lokaci har sun fara sabawa da juna,nan zahra ke basa labarin case din su da Mr Alhassan, nan khaleel ya ba da shawarar yadda zasu bullowa lamarin sannan ya ce zai hadata da wani lawyer ɗan Indonesian yadda abun zai zo mata da sauki. Ba karamin dadi ta ji da hakan ba sosai. Hamdala tayi tana godewa Allah da ya kawo mata dauki a lokacin da take da bukata. Kamar daga sama kuwa ta jiyo
Madam ta turo a kirata. Fitanta kuwa sammaci ne wanda Mr Alhassan ya kai kararta kotu. Aranta ta ce, "Ina mamakin yadda marasa gaskiya suke fin masu gaskiya kwarin gwiwa,ina mamakin yadda masu kudi suke ganin za su iya komai don wulakanta talaka,ina mamaki yadda ake kokarin ingata abu mara inganci da kudi." Murmurshi kawai ta yi,ta karba takardar tana komawa ciki. ★★Dare na yi kuwa karfe tara daidai Zahra ta shirya za ta tafi Skul,ta bar Husnah gun suhana da su Anushka. Ta rasa dalili amman gaba-daya ranar cikin farinciki take. Yau seminar za su yi cewar Mr Imam Abdullah kan *HAKIN YARA GUN IYAYE* hakan yasa suna zuwa lokacin class na yi ya fara jawabi. Da sunan Allah
Rayayyen Sarki wanda gyangyaɗi bai taɓa riskar Sa ba balle barci. Tsira da AmincinSa su ƙara tabbata ga Fiyayyen Halitta Shugabanmu Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama tare da iyalen gidanSa. Kamar yadda muka sani ba IYAYE KADAI KE DA HAKKI KAN YARAN SU BA, YARAN MA NA DA HAKKI KAN IYAYENSU, bari in fara da ku mata,sam ba ku damu rayuwar 'Ya'yanku ba, a kullum damuwarku Namiji, Namiji,gudun kishiya wanda nasan duk shi ne gaba, ba kwa da aikin yi sai neman kudin da za a yi neman maganin mata a karewa namiji kuma duk da hakan in yaso sai tarwatsa miki tunani da duk wata walwalarki,ka da mu matan yaranmu tamkar amana ne a garemu, amanar ma ta Ubangiji,shin
wa zai so Allah ya tambayesa amanarsa kuma ya ga ba daidai ba? Bakwa tsoron tsayawa gaban Allah ku fada masa tarbiyar da kuka ba 'Ya'yanku? Kular da kuka basu? Damuwa da damuwar su kamar yadda kuke damuwa da mazajenku? Yawancin mata damuwarsu su haifa ne kawai,son kuma iya bakine,amman ba adamu da rayuwar 'ya'yan ba, Iyaye maza kuwa kuma kuna taka babbar rawan gani wajen rugujewar rayuwar 'Ya'yanku kuna da kudi ba za ku buda masu ba,son zuciya ya rufe maku ido, ba ku sauki hakkin da ke kanku ba, bare kuma ku kaisu wajen da suma za su iya dogara da kansu,a yanzu son zuciya ba sai bare ba,iyaye ma na da son zuciya kan yaransu,in dai muna
so mu gamu da rahamar Ubangiji, rayuwarmu data yaranmu ta inganta to mu kasance masu sauke nauyinsu a koyaushe kuma kan Lokaci,mu rike amanar da Allah ya bamu hannu bibbiyu cikin aminci da mutuntawa, zan tsaya anan ba don ban da abun cewa ba illa don lokaci ya yi kuma ina so mu dan tattauna Gaɓadaya, Allah yasa mu dace kuma ya ganar da dukkanin iyaye su fahimci sauki nauyin da ke kansu kan yaya na da matukar muhimmanci." Gabadaya zancen ya tsara iyayen da ke cikin ajin har ma da yaran ban da godiya ba abun da suke yi masa. Bayan sun gama komai ana shirin tashi ya ce, "To ga talla ban san ko da mai ra'ayi ba
Culinary school da ke west London sun bude admissions din su ga duk masu ra'ayi za ana karatu online, Culinary school dai makaranta ce ta girke-girke wacce ake horar da Mutane suyi degree kan girki kowanni iri na fadin duniya, za ku yi karatunku cikin nutsuwa a wayar da ke hannunku sannan in kun kammala za su aika ku internship sannan za abaku certificate dinku na kammalawa wanda za ku iya aiki ako ina kuma za ku iya bude naku bangaren aikin aduk inda kuka so domin kun riga kun zam kwararrun masu girki." Zahra na ji ta ce za ta yi tana so ta yi rigista. Aiko ana tashi taje gun Imam Abdullah Wayarta ya karba ya shiga website
din culinary school ya cika mata komai yana Tsokanar ta tana dariya. ★★★suna komawa gida Khaleel ya shiga kitchen sai masu girki, domin Noor ba wani iys cin takeaway yake ba. Ji yayi gidan shiru babu motsin Noor Ya kwalla masa kira amman shiru,kusan sau uku yaji bai amsa ba hakan yasa ya fito ya fara dubasa Kamar wasa Sai zagaya gidan yake amman babu Noor babu dalilinsa . "Noor ka fito, Kana wasa da Dady ko? Ka san bana son irin wannan wasan ka fito,oyaaa ka fito in baka chocolate dinka ka ji, ga shi nan,Norr." Ba motsinsa bare sautin muryarsa. Gabadaya hankalin khaleel ya tashi tun yana iya dubasa har ya kasa ya durkusa bakin get kawai ban
da hawaye ba abun da ke zuba a idununsa. Jin hannu ya yi a fuskarsa ana share masa hawaye. "Dad ka daina kuka,ka daina kuka,ke nan inna mutu kuka za ka yi? Ni ka daina bana so hawayen ka yana zuba, ina sonka Dad." Cikin Sauri Khaleel ya bude ido ya ga Noor a gabansa. Rugumesa ya yi,yana sauke numfashi. "Boo ina ka je? Ka san bana so ka yi nisa dani ina ka tafi?" Noor ya ce, "Lokacin da muke shigowa na ga wata tsohowa abakin get tana zaune,yunwa take ji,shi ne na dauko biscuit da cake dina na skul na kai mata, Dad ina kaine ka ce in naga mutane na son abu kuma basa da shi in
basu? Shi ne na je na kai mata, kullum kana ce mun, One of the most lesson in life,that you should know,is to remember that, to have an attitude of gratitude of humanity, understand where gifts comes from,is not mine its given to me by the grace of God use what i have,use what you have to help others, i used what i have and i help her right? kuma ta ce Allah ya mun albarka kamar yadda kake fada,na ji dadi sosai." Kissing dinsa Khaleel ya yi ya ce, "Good boy ina son hakan, nima naji dadi da ta sanya ma albarka yaron kirki, amman ka da ka kara fita ba tare da ka fada mun ba ka ji,
Mussamman dare kasan ba kyau yara suna fita waje ko?" "Yess Dad I'm Sorry ba zan kara ba By the grace of God, amman kullum zanna kai mata cake da biscuit ko? ." Khaleel ya ce, "Why Not, za kana kai mata, tare ma za muna zuwa, yanzu mu je ka ci food ko." Daukansa ya yi suka nufi cikin gidan. Noor yana, "Can't Love You Less Dad." "Love you too boo." Suna shiga Khaleel ya zaunar da Noor kan daining ya zuba masu abincin,kafin su fara ci a tare suka ce, "Bismillahir-Rahmanir-Rahim." Tukun suka fara ci. Suna kammalawa suka ce, "Alhamdulillah." Bayan sun gama sai da suka wuta kafin Khaleel ya dauki Noor suka je, suka canja kayan barci.
★★★lawyern da khaleel ya Turo ya zo gun Zahra kuma ta masa bayanin komai, har Husnah ma ta fada masa dukkanin abun da ke faruwa. Lamari ya kankama domin kuwa za a fara case din a kotu. Gaɓadaya Zahra ta faɗa duniyar tunani ko ya yau abun zai kasance ko suyi nasara ko kuma ayi nasara akansu. Addu'a take ta yi aranta, ta fito zasu tafi kenan sai ga Mrs Imam Abdullah ya zo wajen abincinsu. Bayani ta masa za su tafi kotu ne, ya Ce, "alright daman gunki na zo zan iya kaiku in ba matsala." Zahra ta girgiza kai alamar ehr Bude mata gaban motan ya yi ta zauna . Husna kuma ta shiga baya suka tafi. Suna
zuwa bayan kotu ta bada damar kowanni bangare su gabatar da kansu Lawyoyi suka fara aikinsu. Gaɓadaya Mr Alhassan da lawyernsa sun mai da zancen kan cewa ana son bata masa suna ne, wanda suna haɗa ido da husna yake mata barazanar kisa indai ta tona masa asiri, ta gama tsorata sam ta kasa amsa tambayoyin da ya dace. A haka aka tashi a kotun domin ba wani kwakwaran hujja da za a kama Mr Alhassan, tunda har kotu ta umarci da aje gidansa da company ayi abincike kuma ba asa mu komai ba, an basu kwana goma kafin su dawo wanda aranar in basu kawo hujja ba daga husna har zahra xa a kamasu da laifin yin kazafi domin
bata masa suna. Ganin yadda yanayin Zahra tayi Gaɓadaya jikinta ya muta yasa Imam ya ce, "Zahra adukkan lamarun duniya akwai faduwa kuma akwai nasara,kamar yadda wata nasarar ta ke da inganci haka ma faduwar,babban abun shi ne ka da ki fidda tsammani,ki sa aranki cewa Nasara ko faduwa dukkaninsu ba za su saki faduwa a kasa ba sai da karfin gwiwa ga dukkan lamuran da kika sa agaba, Don't Loss Yor Hope,ba a taɓa cin Nasara har sai an sha wuya,Hope is a such a marvelous thing,it bends,it twists,it sometimes hides,but rarely does it break, it sustains us when nothing else can,it gives us reason to to continue and courage to move ahead,when we tell ourselves we'd rather given
in, So kisa aranki cewa komai rintsi, tsanani,dadi da akasinsa komai zai tafi daidai" Murmurshi ta yi azahiri domin kalamansa ba karamin karfafa mata gwiwa suka yi ba a ta ce, "Thank You So Much." Sai da suka koma gida kafin Husnah take sanar da Zahra kashedin kisan da Mr Alhassan ya mata wanda har yasa ta kasa magana, nan take Zahra ta kira lawyern ta sanar da shi kuma, sannan suka tattauna kan yadda za ayi su nemo inda ya kai sauran yaran ya boye. ★★bincike suka shiga yi ta kowanni bangare domin nemo mafita kafin kwanakin da aka basu ya dauke. Zahra na chatting da khaleel suna tattauna Khaleel ya ce, "Yau ina son jin labarin rayuwarki ,
ba kowanne aboki ya cancanci sannin ainhin labaranmu ba,ban sani ba ko ni na cancanci sani." Murmurshi Zahra ta yi ta ce, "Why not? Zan fada ma rayuwata har ma da wacce nake ciki yanzu, domin har yanzu ina cikin Fuskantar kalubalen rayuwa amman kuma ina da labarin ba dawa ko da nayi kuka awani bangaren wani bangaren zan yi murmushi." Nan zahra ta dauko labarinta ta bashi gaba-daya, in masu karatu basu manta ba a farkon feji tarihin rayuwar Zahra ne, to wannan shi ne tarihin da ta bawa khaleel. Numfasawa ya yi kafin ya ce, "ta wani bangaren tamkar kalubalen mu na rayuwa ɗaya amman kuma da bambanci." Anan shi ma ya kwace dukkanin tarihinsa da ke fejin
farko ya sanar da ita. Anan Zahra ta fara fahimtar cewa ashe ba mata kadai ke fuskantar kalubale ba harda maza. Kamar yadda mata ke shan wahala wajen wasu mazajen. Haka wasu mazajen ke shan wahala wajen matansu. Zahra ta ce, "na kara jin tsoron duniyar nan tamkar ba zan iya ci gaba da rayuwa a haka ba." Murmurshi khaleel ya ce, "It's easy to be happy when everything is fine when you have a place to sleep When you have a place to eat your bills are paid there are people to talk to places to go Of course nothing can go wrong everyone can be happy when everything is alright But the true test of the self When
everything goes south You can't see to understand why You fall on your knees and you play the victim Why me? And why is this happening to me? You say life is unfair. But it has been And it always will be. So if we learn that,the real Question is when do you stop? When do you stop feeling Sorry for yourself,And when do you rise? What can you do, with what you have? Do that, Do that, Do that which makes you more then a person in a bad situation, rise above the pain, use the pain as fuel, and drive into the dark night, for only After driving, can you stop to heal, we might have lost,we might
have tired,we might have have failed, But No matter Do that which tranforms you,Do that which ignites ta fire in you, Do that which will light up the dark,for there's hope,and whers there's hope, there's Life." Zahra na ganin wannan rubutun na sa sai ta ji gaba-daya ta samu kwarin gwiwa fiye da baya,irin kwarin gwiwar da bata taɓa samu ba. Ta ce, "Wooo tabbas kai din na musamman ne,kuma samun aboki irinka alkairi, am so glad yo have you as my friend, Thank You So Much." Khaleel ya ce, "Never mind,You Need to help so that mu kai ga inda muke son kai wa, ki samo ko da mutum dayane a irin mutane masu yanayinmu and i will fight
for the others let makes the company work, we will work and we will help in sha Allah." Zahra ta ce, 'In sha Allah kuwa." Aranta sosai take jin farinciki mara misaltuwa wanda ita kanta bata san adadinsa ba. Suna cikin magana kawai ta hango wani posting na. Umar Farouk "Ba zan bari ba, in dai zan yi numfashi to zan yi amfani da baiwata wajen taimakon talakawa mussaman daga ɓangarorin shugabbani marasa imani, masu facaka da dokiyoyinmu wajen inganta rayuwarsu da ta yaranau kawai tare da wofantar da rayuwar talakawa Ba zai yiwu ba Ba zai yiwu ba Kuma ba zan bari ba Ba zan taba bari ba. Rayuwata domin al'umma ce kuma zan komai domin al'umma." Duba profile
dinsa tayi ta ga ya rubuta, "If You Love me Just talk to me, i will love you too, Kyakkyawan saurayi kamata sai an tona ake samu,amman ni ina free ina son duk mai sona." A karshe yasa emojin dariya. Sai da Zahra tayi dariya aranta ta cr daga gani wannan dan comedy ne. Screenshot page dinsa da posting din Zahra tayi ta turawa Khaleel. Yana gani ya ce, "Wooo wannan wane ne? Ya hada ɓangarori biyu da yake cikin lissafina zan yi magana da shi yanzu kuwa." Duba agogon wayarta Zahra ta yi ta ce, "Ok to kuyi magana lokacin tashin Anushka a skul ya yi zan je daukota byeebyee." Suka rabu. Zahra na zuwa skul din su Anushka
head teachernsu ta ce tana son ganinta. "Yarinyar nan sam bata da walwala kamar sauran yara,tana da tsoro, rashin magana da kuma rashin son shig a mutane, wanda kuma indai ta ci gaba a haka gaba za a iya samun matsala,kin fi kowa sanin ta da dalilin janyo hakan so You have to work for it, da gani tana da basira amman tsoro na hanata abubuwa da dama a Shawarce ki dunga mata abubuwan da za su sanya ta sakewa kamar sauran yara." Duniyar tunani Zahra ta fada domin ita ma kanta wannan lamarin Anushka na damunnta aranta ta kudira da ikon Allah yau za ta nemo mafita. Suna tafiya gida bayan Anushka ya ci abinci tunani Zahra ta fara
shin ta ina zata bollowa lamarin,nan take dabara tazo mata. Murmurshi ta yi ganin cewa ta gama aikinta lectures ma na Culinary school sun gama tun dazu yasa ta dauko Anitha ta zaunar da ita ta kira Anushka ma ta ce, "komai na fada kuna yi, kun ji,are you with me?" Anushka ta girgiza kai Zahra ta fara "What if it's too hard? I'm gonna push Through! What if it's too rough? I'm gonna push through! What if it's too tough? I'm gonna push through! What if you're just too young? That's Not True! What if you re not good enough? That's not true! Why? Because.. I can do anything that i put my mind to! I believe in you...
Chin up! Believe in yourself.. Head high! Tell me Why. We push through anything we put our minds to." Abun mamaki Anushka ta dage tana yi harda dariya tana tsalle da rawa. Abun da bata taba yi ba arayuwata. Ci gaba da masu ZAHRA tayi tana mamaki. ★★ Washegari da Anushka ta je skul sai da gaba-daya malaman suka yi mamakinta, ta zo a sake ga walwala fal ta bayyana a fuskarta. A karshe ma tara yan ajin tayi lokacin break tana koya masu I CAN DO ANYTHING THAT I PUT MY MIND TO. Su kansu dariya suke ta yi suna tsalle, maganar na ratsa su kuma suna jin dadin furtawa. ★★ Khaleel kuwa har sun tattauna da Farouk Sosai
kuma sun fahimci juna, ya basa dama 💯 Zahra na zaune aba yi masu lectures a Culinary school, Suhana ta zo sai sosa kanta take tana sambatu. "Wannan amosarin ya ishe ni wallahi ina ga aske kannan zan yi in huta kawai na gaji ni kam,in ta susa kamar wata tsohuwar mahaukaciya." Zahra na jin ta. Ta dauko almakashi za ta fara aske kan ta ce , "Aa ki bari." Ganin an gama lectures din yasa ta ajiye wayar ta taso tana. "Ba sai kin aske kanki ba, ki samu cocumber kiyi gretin dinsa sannan ki zuba kwai akai da gishiri dan daidai ki hada su waje daya ki kwaba,in kin kwaba sai ki raba gashinki gida biyu ko hudu
ma yadda kikasan zai ji ta ko ina, ki goga, sai ya yi kusan minti talatin ki wanke, ki yawaita yin hakan ko na sati biyune in sha Allah ke da amosari sai dai hange, har laushin kai da kyali zai kara miki, in ma ba amosarin za ki iya amfani da zallan kwai kina kwaba shi sai kisa abu kamar robar tirare mai hanyar fita sai ki dunga fesawa akanki zai gyara maki gashi sosai." Suhana ta ce, "Wooo sister, Thank you so much da yanzu nayi asaran gashi na, duk abun da kika fada mun nayi ina ganin aikin shi, Allah ya saka miki da Alkairi na gode sosai." Murmurshi kawai Zahra ta yi, ta ce, "Amin na