5STARS CHRONICLE Book 2 FREEYA
CHAPTER 8
gode." Komawa tayi Instagram ta duba Khaleel da Farouk ko suna On. Aiko ta na hawa ta ci karo da Farouk. "Hey Bro." "Hello my gurl." Da haka ya amsa mata Dariya Zahra ta yi ta ce, "am not ur girl oh oh." "Kar dai ki bari acikinki ki mutu da sona,kawai ki fada kiji dadi." Dariya Zahra ta kara yi. "Za dai mu gani." Shi ma ya yi dariya Kafin suka fara gaisawa, suna kara tattaunawa kan yadda Khaleel ya masu bayani duka. Khaleel na hawa on kuwa ya sanar da Zahra kan cewa ya hada Xavier da lawyern Husnah domin fadada bincikensu yadda ya dace. Can kuwa sai ga lawyern yazo har restaurant gun Zahra. Ya kara mata
bayanin cewa ana daf da samun nasara domin Xavier ya taimaka masu matuka yadda ya dace. Zahra ta ce, "Ma sha Allah ba abun da zance da ku kam sai dai Allah saka da alkairi na gode sosai matuka." Barista Danish ya ce, "Kar ki ji komai, kasancewa da ke ma ai wani babban lamari ne,da ace za ki bani dama dana kyautata miki fiye da tunanin zatonki,kin hadu ta kowanni ɓangare." Murmurshi kawai Zahra ta yi kafin ta kara da, "Na gode sosai." Tashi ya yi,ya tafi zuciyarsa fal na sake-saken yadda za ayi ya mallaki Zahra, "tun aranar farkon ganinta ta mun,kuma raina ya aminta da ita, ina matukar kaunarta.". Ya furta aransa ya yin da yake kokarin
shiga mota. Suna haɗa ido ta kara sake masa murmurshi tare da daga hannu alamun byeebyee. Chat suka ci gaba da yi da Khaleel ya ce, "Ga Noor nan yau ya dameni sai na hadasa da Su Anushka sunyi video call, tunda na nuna masa hotonsu ya dage ai kawayensa ne." Murmurshi Zahra ta yi ta ce, "Why not ka kira ko in kira mu hadasu mana?" Khalil ya ce, "Ok to Amman bare in connecting ta Tablet dinsa don yanzu Noor ya fara magana ba sauki tamkar famfo." Dariya Zahra ta yi ta ce, "ai Gwanda haka." Nan Khaleel ya yi connecting, yana mikawa Noor. Zahra kuma ta kira Anushka da Anitha suma. "Hello Anushka, Hello Anitha how are
all?" Noor ya fada. "We are Fine, And You?" Anuska ta fada tana washe baki, Anitha kuwa tsayawa kallon sa kawai ta yi. Noor ya ce, "I'm fine Alhamdu Lillah,yaushe za ku zo Uk mu yi wasa tare?" Kallon zahra Dukansu suka yi donin basu san amsar da za su bada ba. Zahra ta ce, "Soon In sha Allah." "Owk Mom in ma baku zo ba zan ce Dad ya kawo ni, ko ni inzo da kaina,ina da wayo zan iya zuwa ko ina har Dad nake ma wayo fa in shanye chocolate in hanasa." Dariya Zahra ta yi , khaleel ya ce, "Allahumma Yahadikha Son." Noor ya amsa da, "Ameen." Anushka ta dauko cake zata sa abaki kenan Noor
ya ce, "Stop." Dukansu suka tsaya kallonsa, ya ci gaba da magana, "Say Bismillahir-Rahmanir-Rahim before eating Everything." Anushka ta ce, "Bismillahir-Rahmanir-Rahim ." Tukun ta ci. Dariya ya yi yana tafi ya ce, "Oyaa Anitha mu tafa mata good girl ce." Tamkar ba ranar suka fara ganin juna ba, hira suka dunga sha, Zahra da khaleel kuwa sai dai su kalli juna suyi murmurshi. Lokacin sallah nayi Noor ya ce, "Time For Prayer,byee bye Anitha,bye Anuska , don't forget to say Allahumma Antas-salam wa minkas-salam Tabarakhta Ya Zaljalalu Wal-Ikram after each pray And kuna ma Mom da dadynku addu'a nima ina yiwa mom da Dad dina,byeeebyeee, love you all see you letter." "Thank you,thank you so much, byeebyee." Anuska ta fada
Anitha kuma ta ce, "byeebyee." Tun daga Ranar Kullum sai Noor da su Anushka sunyi video call, suna kara samun shakuwa sosai kuma yana kara koya masu karatu,daga Anitha har Anushka bakinsu ya kara budewa sosai da magana da nishaɗi, duk da kasancewar su yara amman sam basa wasa da sallah, lokaci nayi ko Zahra bata nan Anuska za ta yi alwala ta yiwa Anitha ma suyi sallah, in suna waya da Noor kuwa Rabi ne hira rabi wasa ne,har khaleel ya turo masu da tablet irinta Noor yadda ba sai sun takurawa Zahra ba, wani lokacin ma har su gama wayarsu ba tare da iyayen sun sani ba. Gwanin ban sha'awa tamkar suna tare suna ganin juna tun da.
★★Khaleel na zaune a office ba aiki ya kunna data ya bincike, kamar wasa ya ga wani comment na ALIYU HAIYDAR "The Beautiful realization that every living being has a life as complex as your own,they experience,pain, suffering, happiness And life just as vivid as you do." Liking comments din ya yi, azahiri ya ce, "Yes wannan ya yi ." Nan take ya yi following dinsa , tare da nuna bayanai akansa. Bayanan Haiydar khaleel ya duba tas kafin ya fara yi masa magana har suka fara fahimtar juna. ★★Yau ne ranar da su Zahra zasu koma kotu domin a yanke Shari'a Brss Danish ya zo domin tafiya da su tare, lokacin kuma Mr Imam har ya daukesu ya kai
su kotun Sam bai ji dadin hakan aransa ba,ya cije yatsa kawai ya shiga mota ya mai jin takaici. Suna zuwa kotu kafin su shiga Zahra ta ce,"Husnah, domin mu rayu dole sai mun taka siratsi, domin mu yi nasara dole sai mun sha wuya, haka kuma domin fadan gaskiya dole sai mun cire tsoro, ki kwantar da hankalinki, ki furta dukkanin abubuwan da ke yawo a cikin ranki, ki sa aranki cewa ba rayuwarki za ki ceto ba,rayuwar yan uwanki mata ne,na yanzu dama wasu masu zuwa nan gaba,ya yin da kike furta duk wani abu da ya fito aranki ki maida idonki tamkar cikin duhu kike, babu mai ganinki kuma babu wanda kike gani,har sai kin kai ga
matsaya, a lokacin da kika samu matsaya tabbas za ki fuskanci wani haske wanda bakya zaton cewa fitowar ki cikin duhu za ki iya arba da shi, haka kuma kar ki manta babu bawan da ya isa yi miki abun da Allah bai miki ba,kin jure rayuwa cikin wannan kuncin a baya yanzu da kike kokarin fitowa ne ba za ki jure ƙalubalen da ke bakin kofa ba,ki sa a zuciyarki za ki iya kin ji? Duk abun da kika sa arai za ki iya ka da ki karaya za ki iya kina tare da ni?" Husnah ta girgiza kai, "In sha Allah zan iya, na sa araina Mah kuma zan iya indai ina tare da ke ba zan gagara
komai ba da ikon Allah." "Alright, Allah zaba mana mafi Alkairi." Zahra ta fada tana rike hanun Husnah suka shiga ciki. Ko da aka fara shari'a babban buri da kudirin Mr Alhassan shi ne a kama Zahra da Husnah a kulle gidan yari,kamar yadda ya saba ada duk wanda ya nemi tona masa asiri sai yasa a kamasa da laifin cewa ya yi masa kazafi. Husnah za ta fara jawabi kenan ta haɗa ido da shi, ji ta yi gabanta ya fadi nan take a zuciyarta ta furta , " *La'ilaha illa anta subhannakha inni kuntu minal zalimin* Tsintar ta yi da yi masa murmurshi ya yin da jawaban Zahra ke yawo a kunnenta. Cikin kwarin gwiwa ta furta dukkanin
abubuwan da ke faruwa har ma wanda bata fadawa Zahra ba kan cewa akwai abokanensa da suke zuwa yana sa su kwanta da su. Nan take shi da lawyern sa suka musanta kan cewa sharri ne da kahe kawai suna son samu kudine agunsa kawai suka ga ba hanya shiyasa za su bata masa suna. Nan take Brrst. Danish ya gabatar da hujjar sakamakon asibitin da aka bayar da Husnah da kuma dan sandan da ya sa hannu kafin adubata. Sannan kuma ya gabatar da sauran yan matan da Mr Alhassan ya boye har ma da iyayensu. (Xavier ya sa abokinsa na Indonesia ys yi zurfaffen bincike har sai da ya gano inda aka boye yaran ya fiddo da su
ba tare da sanin Mr Alhassan ) Gaɓadaya Mr Alhassan da lawyernsa har ma da mutanensa sun shiga cikin rudu domin tunda suke ba a taba sanin sirrinsu kamar haka har a fitar ba. Nan take Alkali ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari tsawon shekara ashirin bisa cutar da rayuwar yara kanana mata ya yi da zambo cikin Aminci. Kamar xaiyi karamar hauka Gaɓadaya ya fita a haiyacinsa ya birkice, su ko yara suna ganin iyayensu suka je suna rungumesu ,dukansu kuka suka fara ba ga iyayenba, ba ga yaran ba. Don farinciki Zahra ma sai da tayi kwalla. Karasowa gareta suka yi, suka durkusa suna godiya tare da fatan alkairi. Murmurshi ta yi ta share hawayen da ke
idanunta ta ce, "ni dai kumun alkawari kawai za ku lura da yaranku wannan shi ne babban burina,kuma ku sanya suyi karatu,ku inganta masu rayuwa yadda za ku yi Alfahari da juna nan gaba duka." Wata babbar cikinsu ce ta ce, "In sha Allah Yar nan mun yi miki wannan alƙawarin ,ina ma ace su kasance kamarki ai da munii dadi." Murmurshi Zahra ta kara yi, "bana so su zam kamar ni,sai dai su zama maifiyina,ko ninkina wanda kasa Gaɓadaya za su Alfahari da su, na Gode sosai,sannan na san za a iya samun matsala Mussamman stage din da suke a yanzu yaki ce masu dabi'ar da ya fara daurasu za ta iya masu wahala ko ta zam barazana a
gare su,In sha Allah zan forming mana group da zanna zuwa duk karshen wata muna tattaunawa yadda komai zai tafi daidai,amman da taimakon ku iyayensu,kuna nuna masu cewa hakan baya nufin rayuwar farincikin su ta kare ko babu abun da za su iya,aa an rufe babin waccer rayuwar yanzu sabuwa za abude a ginata su rayu kamar kowa, zan kasance da ku in sha Allah aduk lokacin da ake bukata ina tare da ku ." Albarka suka dunga sa mata kafin suka tafi, har Husnah ta tafi ta dawo ta ce."Na gode sosai Mah Allah kara haskaka rayuwarki, zan yi kewarki sosai ina sonki." Rungumeta Zahra ta yi ta ce, "Nima ina sonki Husna ba mu rabu ba in sha
Allah ana tare ai,babban alkawarin da nake so ki mun shine ku kula da kanki kuma ka da ki kara tunanin cewa rayuwarki ta lalace ki karfi kaddararki a hska kuma kiyi farinciki da ita komai zai yi dai-dai da ikon Allah." Husnah ta ce, "nayi alkawari Mah In sha Allah na gode sosai." Da haka suka rabu cikin kewar juna. Brrst. Danish na zuwa ya ce, "Congratulations Mss Zahra ina fatan ba dai daga yau an bar gaisawa za a manta damu ba ko?" Zahra ta ce, "Ah haba dai Aboki ai an fara zumunci kenan in sha Allah, words can't express how Happy am I wallah, ka taimakeni fiye da zatona ban da abun fada gareka sai fatan
alkairi Allah biya ma dukkanin bukatunka na alkairi duniya da lahira." "Ana tare In sha Allah,Amin nima na gode sosai,za mu yi waya akwai maganar da nake so mu yi." Brss Danish ya fada yana Murmurshi,suna hada ido da Mr Imam kuma ya bata rai tare da kawarma ya tafi cikin sauri. Murmurshi Mr Imam ya bisa da shi kawai. Yana tafiya Mr Imam ya budewa Zahra mota ta shiga tana, "Thank Sir." Suna cikin tafiya ya ce, "Ma Sha Allah nima yanzu let me say congratulations Allah kara dimbin nasarori arayuwa , kin taimake su kuma kin ceci rayuwar wasu yaran masu tasowa nan gaba, na san kina da kokari wajen azkar amman ya kamata ki kara da abu
guda,wato sadaka,komin kankantar abu ki ba da,,in yau nasara ce gobe ba mu san mene ne ba, ki kasance mai ba da sadaka,in kina da hali ki dunga sadakar dabino ki sai kamar mudu ko rabin mudu,ko kulla guda uku uku a leda kije wajen da akwai yara sosai ki ajiye kowa cikinsu yazo ya dauka da kansa,in sha Allah za ki ci gaba da ganin haske rayuwarki ta fanninkan da bakya zato bare tunani." Zahra ta ce, "In sha Allah zan kokarta hakan na gode sosai Allah saka da alkairi kuma in sha Allah zan yi ." Har sai da ya kaita restaurant ya ajeta kafin ya wuce. Tana shiga Anushka da Anitha suka rungumeta Anushka na ,"welcome Momy."
Tsayawa kallonta Zahra tayi tana mamaki domin tunda take bata taba fita ta dawo Anushka ta zo ta rungumeta da gudu haka ba Murmurshi ta yi ta ce, "Thank You, How Are you doing all?" Cikin fara'a Anushka ta ce, "We Are Fine Momy." "That's Good,Oya Mu je agaida Madam ko?" Zahra ta fada tana daukan Anitha tare da rike hannun Anushka. ★★Washegari Noor na zuwa skul yanata Tsokanar Anjali amman sam ko juyowa ba ta yi ba Har lokacin break ya yi, kowa ya fice ita bata fita ba. Dask dinta ya karasa ya dago fuskarta yaga tana kuka Goge mata hawayen ya fara yana, "What's Wrong Anjali? Stop crying please." Cikin sheshshekar kuka ta ce, "I Forgot my
chocolate,cake, biscuits with my drinks at home, i don't have anything for break,and am feeling hungry." Ta karasa maganar tana kara fashewa da kuka. Share mata hawayen ya yi harda runguma yana shafa mata baya. "Sorry Anjali, i will give you my own ,stop crying, alright?" Ya karasa maganar yana dauko jakarsa. Gaɓadaya kayan break dinsa ya dire mata agaba,ya fara bata abaki tana dariya yana dariya. Mika masa ita ta yi zata ba shi abaki. Ya girgiza kai, "Aa ki ci kinji." Ita ma ta girgiza kai. Har sai da ya bude baki ta sa mai kafin ita ma ta ci gaba da ci. Suka yi wasan su Sosai suna dariya. Yana komawa gida bayan ya yi sallah ya
kira Anushka. Ta ce, "Assalamualaikum." "Wassalam alaikum good Evening Anushka." Cewar Noor. "Good Evening,How i are you?" "Alhamdu Lillah And You?" Anuska ta ce, "Nima Alhamdu Lillah." "Yau wani wasa za mu yi kafin mu yi karatu?" Noor ya fada. Anuska "Umm i have no idea." Noor ya ce, "Oyaa close our eyes." Nan suka yi wasan su Sosai tukun Noor ya ce yess na tuna yau addu'ar hawa abun hawa za mu karanta bari kiji yadda Dad ya koya mun. " *Bismillahi Mujraha wamursaha inni Rabbi lagafurun rahim*, Kullum in zamu fita kan mu hau mota sai mun karanta ni da Dad ko ma dawowa za mu yi, ranar ma na kara koyawa Ammah (Granny) And you know what
Anuskha?" Ta girgiza kai. Noor ya ce, "Ina son granny sosai, Dadyn Mom suna sona suma suna goyani suna mun wasa da yawa inna girma dukansu nima zan na goyasu, in basu abinci a baki kuma ina masu addu'a kullum inna yi sallah,ke da Anitha ma zan ce su soku ina kuma kuna sonsu." "Eh mana sosai ma,muma muna sonsu,ina so ana goyani, kuma ni ban da Dad momy kadai ce dani, za ka bani aron dadyn ka?"Anuska ta fada cikin yanayin tausayi kamar za ta yi kuka. Cikin sauri Noor ya ce, "Aa kar kiyi kuka,e ai dad dinmune harda ku.". Ya kara sa wajen Khaleel yana, "Dad ka cewa Anuska kai Dadyn su ne kaima ko?" Murmurshi khaleel
ya yi ya ce, "daman waya ce ni ba dad dinku ne ba? Am all urs oh oh, ina sonku yaran kirki." Zahra na zaune tana jin Anushka ta ce bata da dady ta tsunduma duniyar tunani. _(Aiki ya birkice mata ta kowanni ɓangare ga Anitha nata kuka,Adams ya shigo a fusace yana daukan Anushka tare da fadin, "ki dauko ta ita ma yanzu muje hospital akwai abun da zan yi, haka ta saba Anitha a baya suka nufi asibiti,suna zuwa aka ce abada yara, ba yadda ta iya dukanninsu suna kuka haka aka shiga dasu wani daki a asibitin, can kusan awanni uku sai ga shi an dawo da su likita na yiwa Adams da abokinsa Anash bayani, tsarin
jini da kwayoyin halittar sa sam basu yi daidai dana su Anushka ba, atakaice komai na su na Adams ne,don haka ba za a iya amfani da komai nasu ba wajen cutar da ke domin Anash wato LUEKEMIA,Saboda bincike ya tabbatar da cewa yaran ba na Anash bane,na Adams ne, ba karamin takaici Adams ya yi ba, domin yasan bayan shi a wa inda suka fi kwanciya da Zahra Anash ne na biyu amman kuma yaran sun zama duka nasa,ason ransa ya so ace komai ya yi daidai abada yaran ko da zasu rasa Rayuwar su ne, shi dai ya samu kudi"_ Hawayen da Zahra taji Anitha na goge mata ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta fada.
Aranta ta ce, "Kuna da uba,tabbas kuna da uba,kuma ubanku na raye amman baya da zuciyar rikeku bare ya ja ku ajiki har ya kai ga ya goyaku,mahaifinku azzalumi ne mai zuciyar dalma, baya da tausayi kuma baya da adalci ban san yadda za ku ji aranar da zaku kasance gabansa.. Anushka ta ce, "What Wrong Mom?" Murmurshi Zahra ta yi azahiri ta ce, "Nothing Oh oh kun gama hira da Dad da Noor dinne?" Anuska ta ce, "Yes Mom Dad ya ce zai zo ya daukemu,muyi wasa, ina son shi sosai Mom." "Eheen good girl hakan ya mun,yanzu ki je ki aje tab din a huta ko?" Zahra ta fada. Tashi Anuska ta yi tana, "Okay Mom." Ci gaba
da danna wayarta ta yi tana dube dube wannan posting ne ya ja mata hankali sosai. KHADIJA (DEEJERH) Rayuwa ta kan yi tsanani, Mussamman in ka ce za ka dauki komai a lokaci ɗaya,bi komai a sannu tare da sanyawa arai zan kai ga cin Nasara shine kawai haka kuma A women can be in the worst position possible,And Only words you will hear from her is "I'll figure it out." and i promise you she wil find a way,she might have a trillion breakdown,but she will get through it,To All the women's your hard work does not go unnoticed keep striving. Watarana mune masu ba da labarin da za aji har ma ayi mamakin ya muka kasance ? Ya