5STARS CHRONICLE Book 2 FREEYA
CHAPTER 10
ta shi Anitha ta ce, "Noor do you no what?" "Nop." Ya fada. "Mom munyi shuka a garden din sabon gidanmu harda su flowers, And abun mamakin ko? Kowanne na fitowa da kyau, Mom ta koya mana wani abu, Bawon banana (ayaba) muke yayyankawa in mun cinye mu zuba a ruwa in ya jiƙu sai muje muna zubawa a shukokin just like magic abu suta fitowa da kyau Sosai." Anushka ta ce, "Yes kuma Mom ma ta ce ana iya goga Bawon banana din Afuska yana gyarawa ya cire wasu datti da kananun gashi." Noor ya ce, "Wooo daman shukokinmu sunata mutuwa na rasa dalili i will use the process,Thank You So Much,anuna mun videon garden you know I really
like vegetables." Daukan wayan Anuska tayi Anitha na binta a baya suka je garden din suna nunawa Noor. Anitha ta ce, 'You see Cabbage, pepper, tomatoes, carrots,they are meny oh Oh ." Noor ya ce, "Awn i just love dis small garden." Anushka ta ce, "Umm ni fa yau kai da Anitha kun dameni ina so in ma addu'ar da na ji Mom na yi har na iya bata sani ba mu koma cikin gida." Ta karfe wayar gun Anitha ta shiga. Tana zama ta ce, "Eheen Bismillahir-Rahmanir-Rahim *Allahu Litifun bi ibadihi yarzuqu man yasha'u wa.....* Ta kakare agun. Noor ya yi dariya . "Nasan addu'ar nima Dad dina yana yi kuma ya koya mun adduar samun budine wajen Ubangiji
bari ki ji, *Allahu Litifun bi ibadihi yarzuqu man yasha'u wa huwa I'-Qawiyyu 1'-azizi*." Anushka ta ce, "Yes ita ce." Hirarsu suka dunga yi suna wasa da dariya. Tun Noor na gudun Theraa har sai da ya fara sakewa da ita,suka saba saboda yadda take son yara, tana nuna masa so Sosai tamkar yadda take yi wa mahaifinsa,hatta barci ba ya yi sai acinyarta,ta goyasa ta mai wasa sun shaku sosai ita da za ta yi kwana daya akan Noor sai da tayi sati ranar da zata tafi kuwa ya dunga kuka da kyar Khaleel ya rarrashe shi kan cewa xai kaisa gunta shi ma in anyi hutun skul. ★★Zarah nata sauri zata tafi night School Study Center Suna da
taron daukan sabin dalibai da aka yi, kasancewar dare ya yi har lokacin ya kure a yadda akasa za a fara taron, fitowarta kenan sai ga Brrst.Danish yazo. Suna gaisawa ta ce, "ai da ka fadamun zan shiga skul ne yanzu kuma." Danish ya ce, "Oh oh no problem zan wuce ne daman kawai na ce bari inzo in ga gida kafin in wuce,yanzu sai kizo in rage miki hanya in ba damuwa." Zarah ta ce, "Ok to na gode." Suna zuwa daidai da zuwan Mr Imam. Da sauri ya fito amota yana mamaki da takaicin ganin Zarah da Danish. Tana ta murmurshi tare da yi masa godiya. Mr Imam ya kasa hakuri karasowa inda suke ya yi yana, "Madam
kin san ke nake jira ko? Kuma an riga an fara taron nan tun dazu?." Ya karasa maganar yana yi wa Danish wani kallo shi ma ya mai. Zahra ta ce, "Ok, Byee Danish Thank You So Much za mu yi magana awaya." Sai da ya tabbatar Zarah ta tafi kafin shima ya bar wajen. Cikin sauri yaje ya sha gabanta kafin ta shiga cikin class yana, "ya isa! Duk wannan abubuwan sun isa haka,kin fi kowa sanin ina sonki amman kike kula wasu,kin jima da fahimta na sani amman kike kaucewa maganar,bana so in ganki da wani domin ba zan jurewa hakan ba, daga yau ka da in kara ganinki da shi a makarantar nan in ba haka ba
kuma zamu samu matsala." Murmurshi zahra ta yi a bayyane tana, "Shi din ya furta ma cewa sona yake? Ko ni nace ina son shi? Kowa na rayuwa da tsarinsa ne ba wanda ya isa ya shiga tsarin wani." Karasa maganar ta yi tana wucewa ciki ta bar shi Tsaye. ★★washegari. Weekend ne kuma ranar zarah zata fara aiki a karamin restaurant dinta da ta bude. Tun safe take aiki da su Anushka. Gaɓadaya su Madam Zuby, sun zo. Sawa tayi aka yi mata sauka sannan kuma ta ce abincin ranar free ne ga kowa ma ya zo ya ci. Haka kuwa aka yi, Gaɓadaya duk wanda ya ci abincin nan da Snacks sai ya yaba. Video call suke su
khaleel na ganin komai suma suna tayata murna. Haiydar ya ce, "ni kam babbar damuwata abincin nan ba zan jure kallon mutane na cin abinci ni bana ci ba fa." Dariya suka yi Deejerh na, "eheen food Master ba." Farouk ya hango suhana ya ce, "Woo Madam ya za a ayi mun hanyar yarinyar nan ne? Zan iya gyarata fa kalata." Dariya suka yi dukansu khaleel na, "kowa da damuwarsa ni barci na ke ji um." Tamkar suna wajen haka aka yi taron tun farkonsa har watsewarsa,kowa na farinciki. Mussamman shigar da suka yi dukanninsu rigace deejerh tai designing da sunan zarah da tambarin 5stars har Noor da su Anushka sai da suka sa. *FREYA* ★★ ★★Khaleel ya dauko Noor
ke nan daga skul sai ga kiran Theraa Amsawa ya yi, yana, "Madam." "Yes Naji kawai ina son jin muryarka da Noor Mussamman ma shi oh oh nayi kewarsa sosai." Murmurshi Khaleel ya yi kawai ya ce, "Alright kawai ki ce kina son jin muryan Ɗanki, Oya Noor Antynka magana." Karba Noor ya yi yana, "Assalamualaikum Anty Goodafternon." "Afternoon Noor yaka ke ya skul?" "Alhamdu Lillah Anty , yaushe za ki dawo? I really Miss You." "Miss You too Noor,Soon In sha Allah zanzo ko dan in ganka ka ji." Noor ya ce, "Thank You So Much." Kiss ta mai ta wayar yana dariya kafin ya mikawa Khaleel. ★★Zahra kuwa karshen wata ya yi, zata je kauyen su Husnah ta
duba yadda tsarin masu lura da su yake,da kuma su kansu rayuwar yaran. Mr Imam ne ya dauketa suka tafi. Suna zuwa ƙauyen da gudu Husnah da Aleesha suka tawo gareta suna rungumeta. Kallon Aleesha tai da mamaki domin ta wartsake da kuzaharinta illa wari dake fita ajikinta. Zahra bata nuna mata hakan ba murmurshi kawai tayi Mussamman yadda taga suna ta aiki, wa inda ake koyawa girki nayi,masu kwalliya nayi, masu dinki da masu koyan yadda ake su sabulu duk sunyi Busy. Bi tayi tana ta kallonsu tana matukar jin dadi aranta,fannin masu girki taje ta tayasu, lokacin tashin su karfe 4 daidai suka hadu duka waje daya suna gaisawa da Zahra,bayan sun gama gaisawa ta tashi tana yi
masu jawabi. "Ba zan iya misalta farincikin da na tsinci kaina aciki ba ganinku da nai haka yau, bakina ya yi kadan wajen furtawa sai dai fuskata tai kokarin bayyanawa,ba zan gaza ba,kullum shawarata a gareku shine ku ci gaba da jajircewa,ku manta da baya ku kalli gaba, You Know what i truly believe? That every single person has to go through something,that absolutely destroys them, so they can figure out, WHO they really are and let me tell you, until you are BROKEN . you don't know what you're really made of and it gives you the ability To build yourself all over again,but STRONGER then Ever , And one day,you will tell your story of you over come
what you just went through,and the crazy thing is ,is that to you,it will just be a story in your life,but to someone else,it will be guide to help them survive their own life, watarana za ku iya zama taurarin da labaranku zai haskaka rayuwar wasu har ma ya inganta su,kuyi aiki tuƙuru ku zam na musamman abun Alfahari ga kanku har ma da sauran al'umma, sannan ga wani abu da ya kamata muna yi duka ba matan auren ba,kuma ba yan matan kadai ba, kuna amfani da lemun tsami da gishiri ku hada su waje ɗaya kuna goge jikinku kafin shiga wanka da wajen minti goma, zai rabaku da warin jiki sannan zai sa jikinku ya kasance cikin kamshi
na musamman ko da baku kasance masu sanya turare ba,hakan tamkar assignment ne,kafin dawowata kowa ya gwada hakan na wata guda,kar amanta fa mussaman hammata,da duk wani lungu da sako na jiki,ya sa kamshin jiki kuma ya gyara ma mutum fata tai kyau tana sheƙi, nayi alƙawarin kyauta ta musamman ga duk wacce jikinta yafi kyau da kamshi." Tafa mata suka shiga yi suna murna duka, aranar da farinciki Zahra ta bar kauyen nan,Mr Imam ya lura fuskatar ta kasa daina bayyanar da Murmurshi bayan ta shiga mota sun kama hanya ya ce, "wannan Farincikin fa?" Murmurshi tayi ta ce, "ya za ka ji, alokacin da ka ga al'umma na Murmushi ta dalilinka? Ya za ka tsinci kanka ya yin
da kai nasarar daidaita rayuwar wasu? Umm kasan miye? Ko da ace a yau zan kara komawa baya ga rayuwa hakan ba zai taba sa naji cewa na karaya ba,saboda ko ba komai rayuwata ta tada wasu,kaddarata na karamin kwarin gwiwa ne maimakon nukusar dani, na tabbaata a duniya babu nakasasshe sai wanda bai da zuciyar taimako, adalci da kuma jin kan al'umma, yau ina farinciki matuka fiye da tunanin mai tunani, ko da ace wa innan zasu taka mataki arayuwa fiye dani ko ya ninkani ba zan taba jin takaici ko kyashi ba, murna zanyi,farinciki zanyi domin na tabbaatar da cewa na sanya masu kudiri da kwadayin taimakon wasu,zasu taso da zuciya mai kyau,mai albarka da kuma inganci,kullum darasi
nake kara samu a rayuwa kuma nake kara jin cewa Allah ne kadai abun godiya ,domin ba zai taba bari rayuwarka ta baci ba sai in har kai kaso." Kallonta ya yi , alokaci guda tana kuka kuma tana Murmushi. Mr Imam ya ce, "ba iya jawabanki ba,fuskarki ma kadai ta kara sanar dani wani darasin na rayuwa, baki bari hawaye ya zam silar canjin fuskarki murmurshi ya daina bayyana ba, lokacin da hawayen ke zuwa a lokacin kike kara wani Murmushi na musamman mai tare da ma'anoni da dama , bana da fata agareki a kullum da ya wuce na alkairy ,ba zan gaza ba zan ci gaba da bibiya har ya kai ga ranar da zaki bani damar
shiga rayuwarki aranar ban san irin farincikin da zan shiga ba, na tabbaata ranar ta musamman ce kamar yadda kike ta musamman." Murmurshi kawai Zahra ta kara yi ba tare da ta ce komai ba. Yana kaita gida ta ce, "Thank You So Much,amman ba zaka shiga ko abinci ka ci ba?" "Oh a koshe nake And ina da aiki a office ki gaida Anitha da Anushka sai munyi waya." "Okay Thanks byee byee ." Ta fada dauke da Murmurshi a fuskarta. Tana shiga Anitha ta tawo da gudu tana. "Mom ki rufe ido." Zarah ta ce, "Rufe ido akan me?" Shagwabe baki Anitha tai tana, "Mom i said you should close eyes please." Zahra na rufewa Anuska ta tawo
da sauri tana, "Surprise." Zahra na budewa ta ga chocolate irin wanda take so sosai. Bude baki tayi tana, "awwwn ina kuka samo wannan." Anuska ta ce, "mu muka yi miki da kanmu da bornvita , we just serch the process a Google,mom are you happy?" Tsabar farinciki Zahra bata san sanda hawaye ya fara zubowa daga idanunta ba,ta kowanni fanni farinciki,ta bar wani gashi ta kara riskar wani. Rungumesu tayi tana, "ina farinciki,ina farinciki sosai Yarana, taya ma ba xan yi farin ciki ba Allah ya bani ku? Ina sonku ina sonku,thank you so much." Chocolate din ta fara sha ,yayi dadi Sosai fiye da zatonta, albarka ta dunga sanya masu tana jin dadi. Sai da tayi sallah kafin
ta dauki wayarta ta kunna data,domin basu gaisa da 5stars ba yau kwatakwata. Farouk na ganinta Online ya ce, "saura kiris in haye jirgi in tawo Indonesia cikiya na zata ai an sace ki ne,kin san yan gajerun nan suna kasuwa fa tuni za a yi ciniki." Dariya Zahra tayi ta ce, "Su kuma dogayen mutane farare masu kama da aljanu fa? Ai an fi saurin kasuwarsu ka ga kafin a saidani sai an fara siyar da kai." Farouk ya ce, "Never ni mai iya siyata ai sai ya shirya inada tsada fa duk bina kuke ina gudu." "Sai dai wasu su bika fa ban da ni, ka ga bari inje mu gaisa da Friend." Khalil ta je ta ma
magana suna gaisawa, gani tayi ya yi tagging dinta wani waje. Tana dubawq taga Cooking challenge ne. Ta dawo Private ta ce, "Wannan fa na manya ne,ina ni ina shiga watakila ko ta karshe ba zan zo ba,kuma kaga Bamu gani kan lokaci ba gobe ne za ayi fa,ina ga duk masu yi ai yanzu sun gama shirya komai da komai." Dariya Khaleel ya yi ya ce, "ni nasan zaki iya kisa aranki kawai, nina faɗa miki,fatan nasara,zamu tayaki da addu'a kiyi duk abun da ya dace kawai yanzu kije ki bada sunanki a list tunda a Indonesian ne ba wata kasa ba komai yazo da sauki in kin bada suna sai kizo kiyi tunanin abun yi,in kina da bukatar
taimako ki mun magana, lokaci bai kure ba har yanzu akwai dama tunda basu rufe daukan participant ba, Oyaa kije." Haka Zahra taje ta bada sunanta sannan ta shiga nazarin shin me za ta yi daidai nata wanda ba zai fi karfi ba kuma ya yiwu zuwa goben? Zama tai tayi tagumi. Anuska ta ce, "me ya faru Mom?" Zahra ta ce, "na shiga cook challenge ne gobe za ayi kuma na rasa me zanyi , ba lokaci." Anushka ta tsaya jim tana tunani. Sai can ta ce, "Potatoes salad Mom." Tuni zarah ta mike tana" yesss Good Idea let me see ,mu je garden ina tunanin muna da komai acen." Zuwa suka yi ta diba duk wani kayan bukatan
da za ta yi amfani da shi agun, su Attahiru, dankali,albasa, allayawo da tattasai, adaren sai da ta tabbatar da komai ya yi ready tukun ta kwanta barci. Da safe kuwa tana tashi bayan ta shirya su Anitha ta kaisu skul,kasuwa ta wuce ta siyo kifi da duk wasu abubuwan da babu agidan. Camern da Khalil ya Turo mata da shi ta kunna kafin ta fara tare da gabatar da kanta da fadin sunan abun da zata fara Potatoes salad Dankalinta ta fara daurawa a wuta, sannan ta kare dauraye duka kayan miyanta da vegetable. Attahiru, Tattasai ja green, albasa mai kayan da allayawo dukkaninsu ta yanka kanakanana. Dubawa tayi ta ga dankalinta yayi daidai dahuwa baiyi danye ba,kuma bai
dahu duka ba. Saukewa tayi ta tsame shi sannan ta juye a bowl. Sannan ta ajiye agefe. Wani bowl din ta dauko ta zuba Olive oil, da mayonise wanda ta hada kanta, sannan ta sa gishiri sannan ta juye dankalin ,ta dauko vegetable da kayan miyan duka ta zuba ta juya. A zahiri ta ce, "Alhamdu Lillah Potatoes salad ya kammala." Tana gamawa ta koma hada CHICKEN BREAST Naman kaza ta yanka falele, tasa avocado oil, gishiri dan daidai tasa yaji ma dan daidai. Butter ta zuba a wani bowl sannan tasa Garlic da parsley ta hada su waje daya ta juya. Naman ta fara daurawa kan abun Gashi sai da ya ya fara gasuwa sannan ta dauko wannan hadin
butter din ta shafa ajikin naman ya karasa gasuwa ta zuba a plate. Sannan kuma ta dauko strawBerry ta wanki shi tas tasa a blander ta zuba madara, zuma da ganyen na'a na'a sannan tayi blanding, tana gama blanding tasa a jug. Hamdala tayi aranta tana mai godewa Allah sannan ta kashe cameran,ta zauna ta gyara videon tukun tayi masu sending. Tana sending ta hau online domin sanar da khaleel . Ta ce, "DONE na tura amun fatan Alkairi." "Eheen Good Ma sha Allah All the Best Fatan alkairi na yana tare da ke a kullum a ko ina ai." "Thank you so much." Tashi tayi ta jera masu komai a daining. Ganin lokacin zuwa dauko su Anushka a Skul
ya yi,yasata fita ta dauko, dake Madam Zuby ta bar mata suhana tana lura da restaurant. Suna dawowa sallah su Anushka da Anitha suka yi,kafin Anitha ta ce, "Mom am so hungry." Ta fada kamar za ta yi kuka. Anushka ma ta ce, "me too Mom zan je restaurant Anty Suhana ta ban food." Zahra ta ce, "umm Oya dukanku kuje daining kuga surprise." Suna zuwa Anushka ce ta fara budew tana , "Awwn Potatoes salad." Nan take fuskarta ta canja sai dariya tana washe baki. Anitha ma tana duba dayan ta ce, "Mom chicken breast, potatoes salad and Strawberry juice Wooo." Zama tayi tana kokarin diɓa. Zahra ta zuba masu duka. Suna cikin ci Anitha ta ce, "Thank You
So Much Mom Allah miki albarka yadda muma kike ce mana ko?" Murmurshi tayi tana girgiza kai, "Yes Amin." Anushka ma ta juyo ta ce, "Thank You So Much Mom Allah kara miki iya girki da kudi mai albarka Allah yasa kita farinciki,Kuma Allah sa ki samo mana Dad mu ma ko?" Jikin Zarah ya yi sanyi da maganar Anushka, cikin yanayin tausayi take kallonsu yadda suke kwadaituwa da son ganin ance wannan mahaifinsu ne, ba musu yaran suna cike da kewar mahaifi Mussamman da suka shiga makarantar kowa ya kan bada labarin iyayensa maza da mata,amman su in anzo fannin uba sai dai suyi shiru. Anitha ce ta katsewa zarah tunani da fadin, "Mom ance kafin mu canja aji
speech and prize giving day dinmu kowa sai mom and Dad dinsu sunzo ,mu kam na san ke kadai za ki ko?" Hawayen da ke kokarin zuba a idanunta tai saurin sharewa kar su gane tare da fadin, "Bana son wannan surutan naku so maza ku ci food ku gama malamin islamiyanku ya zo And kun san Noor zai kiraku zuwa anjima ku yi sauri ko." Ta fada tare da ficewa afalon. Dakinta, ta shiga ta kwanta ban da hawaye ba abun da ke zubo mata, Anitha ce ta shigo dauke da kayan lesson jikinta. Da sauri Zahra ta goge fuska. Anitha ta ce, "Mom mene ne? Kamar kinyi kuka? Mom kiyi hakuri koma wane ne ya dakeki Ki fada