5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN

CHAPTER 7

by @xayyeesherthulhumaerath

ta daidaita ada ni drug addicted ne wanda har ya kai ba babu abun da bana yi na rashin ji, rayuwata ta samu tangarda tun ina karamin yaro na taso ba iyaye ,rayuwar maraici tasa ban da wani mai ja na a jiki bare ya san damuwata ko ya ban shawara sai kawai naji cewa ai kowa kan shi kadai ya sani a duniyar nan ba a damu da kowa ba,ba a tunanin ya rayuwar marasa iyaye ke kasancewa, na ji na tsani kowa kuma ina iya yin komai ga kowa aduk lokacin da na yi niya ,kwacen kudi, sata, kai babu abun da banyi ba, amman a karshe kuma kunsan wani abun mamaki?"

Dukansu suka ce, "aa." Cikin zakuwar jin me zai fada.

"Na hadu da wata wacce ta sauya mun tunanina ta nuna mun cewa akwai masu damuwa da damuwar al'umma akwai masu son ganin farincikin al'umma, ta sani a makaranta ta mun komai kuma ta nuna mun in tashi in nema arziki na da kaina kuma kada inyi ƙyashin taimakon duk wani mai bukata, ita ta fara bani kwarin gwiwar cewa zan iya canja kaina daga mutum mara kirki zuwa mutum mai kirki kuma agunta na ji cewa lallai zan rayu ne domin in taimakawa al'umma."

Noha ta ce, "kenan yanzu muma zamu iya taimakawa al'umma musamman masu bukata wa inda suka rasa iyaye?"

Maestro Ramon ya ce, "ai ba sai wa inda suka rasa iyaye ne kadai keda bukatar taimako ba,akwai wa inda suna da iyayen amman suna bukatar taimako sosai don haka zaku iya taimakon kowa ma da duk abun da kuke da shi komin kankartarsa ko da kuwa addua ce."

Deejerh na jin su bata ce komai illa abun da take sakawa aranta, "ni kam ban yarda da cewa mutane suna da kirki ba, duk mutane masu son zuciya ne kawai kowa burinsa da nufinsa ne kawai a gabansa."

Dukansu sunata hira ana wasa da dariya.

Maestro Ramon ya ga Deejerh ce kadai tayi shiru tana tunani.

Ya ce, "Deejerh...Deejerh sai da ya kirata sau uku kafin ta amsa arazane tana.

"Sorry Please Uncle....

Idanunta ya a rufe.

Maestro Ramon ya ce, "bude ido ni ne ki nutsu kinji."

A hankali ta bude ido tana kallonsa tukun ta saki wata irin ajiyar zuciya don duk azatonta gaban Zayd take.

★★★sun tashi a School da wuri saboda basu da lesson a ranar.

Hanya ta dunga bi kamar ba zata tafi ba, don batason ta isa gida su momynta ba su dawo daga office ba.

Shi ko Zayd ya gama shirya yadda hutawarshi zata kasance aranar.

Tun yana jiran ta har ya gaji ya tunzura ya fita nemanta bayan su Dadynta sun dawo daga office.

Aikuwa karo ya ci da ita tana tafiya da kyar ga gajiya ga yunwa duk ta galabaice.

Da saukar maruka ya fara tarar ta yana yi mata masifa, "Wato kin koyi mugun hali ko? Anya ma ba maza kika fara bi ba kuwa? To wallahi in kika je kika kwaso wata cuta sai na kasheki kafin ni ki illatani."

Ya fada yana janta.

Suna shiga get din gidan kuma ya rungumeta.

Momyn ta suka taso cikin sauri tare da tambayar me ya faru lafiya kuwa?

Zayd ya ce, "ba komai fa rigimar Little Princess ne ya motsa wai ta gaji shine ta zauna tana kuka."

A tare duka suka yi dariya suka koma ciki kawai ba tare da sun ko kalli idanunta ba.

Zayd na ganin sun tafi sun shige dakinsu janyeta ya yi a jikinsa cikin zafin rai yana, "Munafukar banza kawai, mu ma je ki cire wando inga tabbacin ko kin biya yawon iskancinkine."

Suna shige da kan shi ya janye uniform din da ke jikinta yana lekawa.

Yana sa mata hannu a ciki tayi kara, ya dago ya kara sake mata wani marin da tayi saurin sa hannu a baki tana toshewa.

Sai da ya dubata tas kamar mai karban haihuwa kafin ya ce, "maza ki zauna anan saura in ga kafarki a palourn gidan nan,ina nan dawowa."

A sanyaye ta ce, "Uncle Zayd, yunwa nake ji Help me please."

Har zai kulle kofar sai kuma ya kara budewa yana kallonta ya ce, "Yunwa ko? Yunwa kike ji ina? Zan zo in baki abinci ki jirani zaki ci abinci ina dai abinci?" Ya fada yana ficewa.

Haka ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido domin ta gagara komai jikinta har rawa yake tsabar yunwa ga wasu abubuwa da idanunta ke gane mata a dakin, ta takure tamkar sabon ɓarawo.

Bai koma dakin ba sai can dare.

Bayan ya daure mata baki, ya Daureta a jikin gadon dakin a tsaye kuma ya cire mata kayan jikinta kaf.

Ya dauki wata sanda ya dunga buga mata a bayanta har saida ya fara farfashewa jini na zuba.

Bayan ya gama jibgarta haka a tsayen ya sadu da ita ta karfi da ya tabbatar ya biyawa kansa bukata tukun ya fice ya barta.

Haka ta kwana a tsaye,ko ince a tsaye ta kasance har safiya domin barci ko na seconds guda bai kawo mata ziyara ba.

Asuba na yi ya lallaba ya kunceta sannan ya fice masallaci.

Haka ta rarrafa ta tashi ta shiga toilet ta yi alwala ta yi sallah.

Bayan ta idar ta zauna tayi adduo'i sosai kafin ta tashi ta je ta kara gasa jikinta ta sanya uniform.

A hankali take abubuwa domin jikinta kara macewa yake musamman yunwar da ta gama cinyeta.

Ban da kugi babu abun da cikinta ke yi,ga kirjin ta na ciwo kamar wacce aka famawa gyambo.

Kan gari ya yi haske ta lallaba ta shiga kitchen.

Tana shiga kuwa ta yi nasarar samun sauran kanzon abinci a tukunya.

Tukunyar ta dauka gabadaya ta zauna ta kankara zata sa a bakinta kenan kawai taji an tunkude.

Zayd ne yana dariyar ƙetar, ita kuwa a raunace tana binsa da kallo daga karshe ta sunkuyar da kai tana kokarin kara kankarar kanzon.

Kan ta ankare ya fisge tukunyar ya tuttufa yawu ciki yana, "Mayya kawai,ba abun da kika iya sai ci ko? Tun asuba kinzo kina bin tukune, ga shi nan in zaki iya sai ki ci." Ya kara tufa yawun harda kakin majina ya jefa mata.

Ganin duk da hakan dauka zata yi , ya kara daukewa da sauri.

Ya bude wandonsa.

Ya yi fitsari ciki kafin ya kara a jiyewa.

"Gashi nan in kinfi kowa mayinci sai ki ci ai muga."

Cikinta kara ƙugi yake hanjinta na zillo,bata sa wata mafita haka ta kara jan tukunyar tana cin kanzon ga fitsari da kakinsa amman duk bata su take ba,ci kawai take ta samu cikinta ya yi nauyi Domin tasan in ya kai gari ya gama wayewa ba za ta samu ko kamar hakan ba ma.

Tana ci amman shi ke ji mata kyankyamin yana ya mitsa fuska.

Sai da ta cinye kanzon nan tas kafin ta tashi zata diba ruwan.

Ruwan ma tana diba ya bigesa ya Zube.

Ya ce, "ai baki isa kisha wannan ruwan ba yarinya."

Ya dauki kofin ya tattare mata ruwan dattin wanke wanke ya mika mata.

Ruwa duk mai ƙo da kayan miya haka ta rufe idanunta ta sha tana ajiyar zuciya.

Tsaki ya yi ya fice.

Ita ma ta fita aranta tana jin ko ba komai dai yanzu jikinta ya dan yi karfi da gwaɓi.

Tana fita zata tafi school ya bita kan cewa zai kaita.

Maimakon school din kai tsaye gidan Mr Juan ya kaita.

Tun safe ake abu ɗaya da ita har yamma, taimakonta Ɗaya an bata lafiyayyen abincin da ta kara samun kuzahari, duk da cewa zuciyar ta cike take fal da ƙuna tare da ciwuka wanda ita kadai ta san radadinsu.

Ga babban abun da ya fi bata mamaki da kasancewar Mr Juan ba shi kadai ba yake hawa kanta harda Karuwansa wanda har fada suke da juna kan wannan ce zata fara.

Ya san school din zasu iya kiran waya kan Deejerh bata je ba, don haka tuni yaje ya sanar da su kan cewa bata da lafiya, lokacin fitowarsa kuwa suka ci karo da Maestro Ramon.

Dukanninsu kallon kallo suka yiwa juna.

★★★Saturday

Tun safe take neman hanyar da za ta samu ta fita HOPEFUL ENDEAVORS ORGANIZATION.

Amman Zayd ya ya kane-kane a gida kuma ya ki fita.

Deejerh na ta adduar Allah ya kawo abun da zaisa ya fita ta saci hanya ita ma, da kyar aka kira shi a waya ya tashi ya fita.

Yana fita kuwa data tabbatar ya yi nisa tayi sauri ta fice ita ma.

Tana zuwa daidai inda zata fita daga street dinsu sai ga Zayd kuwa.

Gabanta ne ya yi wani irin faduwa....

Gefe ta yi da sauri ta boye jikin wani gini, har ya wuce ta ya kara komawa baya kamar ya manta wani ba.

Ta kara buya ya wuce ya tafi.

Tana ganin ya tafi ta fito da sauri ta ci gaba da tafiya.

Kamar yadda Maestro Ramon ya masu kwatance haka ta dunga bi, har ta isa,ai kuwa tana zuwa bakin gun ta ci karo da su Maira duk sun zo suna kokarin shiga kenan.

Da sauri Noha ta rugumeta tana , "har mun cire rai da zuwanki, yanzu nan muke cewa ko mu kira wayar gidanku ne, ashe zaki zo, welcome friend."

Murmushi ta yi kawai ta ce, "Thank you."

Dukansu suka rungumeta kafin suka shiga tare.

Babban waje ne wanda ya hada da mutane kala kala, wasu gasu nan a nutse amman yanayin damuwa ya bayyana a fuskarsu,wasu kuwa kayan jikinsu ma kadai ya wadatar wajen bayyanar da halin da suke ciki, sa'anninsu da ma wa inda basu kai su ba, wasu kuwa sun girme masu ma.

Da murmushi maestro Ramon ya karbesu yana basu wajen Zama, Ajeef ma ya karasa garesu yana fadin, "Welcome Friends." Ya mika masu hannu duka suka gaisa fuska a sake.

Suka gabatar mi shi da kansu.

Lokaci guda duk suka ji ya birgesu yadda yake wasa da dariya da kowa agun.

Abinci aka fara rarraba masu sai da suka ci suka koshi sannan Ajeef ya sanar cewa suna da babban bako da zaiyi masu wani takaitaccen jawabi kafin su fara wasanninsu na nishadi kamar yadda suka saba.

Mr Ameen ne, Babban counsellor ne dake aiki a Universidad Nacional Autonoma de Mexico.

Yana tashi suka fara tafa masa yana daga masu hannu kafin ya fara jawabinsa.

"Ina matukar farincikin kasancewata anan kuma a wannan rana musamman yadda nake ganin dukaninku kowa dauke da fuska mai bayyananniyar farinciki, hakan ba karamin faranta mun rai ya yi ba, kuma zuciyata ta kara jin cewa lallai akwai bukatar kasancewata anan din ko da bazan fada kalmomi masu yawa ba, in dai zan furta kadan da zata iya amfanin wanin ku hakan zai kara faranta mun rai matuka, dukannin mu yan Adam ne kuma yan uwan juna ne muna kaunar juna don haka babu mara gata anan domin Ubangiji shine gatan kowa, kada kuyi tunanin rasa wani bari na rayuwarku hakan ya zam silar tabarbarewarku aa, wani rashin Allah na jarantarmu ne domin ya zame mana karfin da zamu iya tsayawa kanmu ba tare da fidda tsammani ba komai tsananin wahalar da zamu sha arayuwa, don na rasa wanda zai bani kafadarsa in kwanta inyi kuka ba shi ke nufin in bar hawaye na yana zuba kan titi ba, duk lokacin da yazo zanyi gaggawan gogewa ne da hannuna sannan in sake murmushi tare da jin cewa lallai watarana wannan hawayen shine karfina, Let me tell you this

If you've made it through addiction or mental illness

You have something cause alot of people don't

If you're still kicking today

Battling those demons

You have something cause alot of people didn't wake up today

Because they couldn't make it.

They couldn't cut it

And you fucking did.

(Bari in fada muku wani abu, shi sabo da yin wani abu misali chating, danna waya, game, da duk wani abu koda shan Coke ne idan ya zamar maka jiki za a iya kiran sa shaye shaye ko kuma abinda ya shafi lafiyar kwakwalwa, idan har ka iya kokari kabar wannan abun to ba karamin kokari kayi ba saboda mutane da yawa masu wannan halin suna fada da zuciyoyin su da kuma kawunan su saboda su yi kokari su rabu da wannan abu wanda bai zamar musu tilas ba, ko kuma abin da ya shafi lafiyar kwakwalwar su, Amman kai ka yi.)

Duk wani abu da muke yi,mai kyau ko mara kyau kafin wani ya sanar da mu,mu muna fara sani da kanmu don haka yaƙi da zuciyar mu ya wajaba ga duk wani abu da zai iya kawo mana illa ga rayuwarmu, And daga yau,kuma yanzu ina so ku mun alƙawari zaku fara yaki da zuciyarku ga duk wani abu da kuke yi da zai iya kawo maku illa arayuwa, PROMISE?"

Ya fada yana daga hannunsa.

Dukansu suma daga hannun suka yi suna fadin, "YES Promise Sir."

Ajeef da Roman suka fara tafa masu Gabadaya dakin taron ya kaure da tafi.

Bayan sun gama Ajeef ya ce, " Guys Get Ready ko wanni bangare su shirya, masu son yin ball, masu jump, What Ever let me bring the materials."

Shi da Roman ne suka fito da kayan wasan , yawancin matan igiyar jomba suka karba, matan kuma ball.

Wasa suka fara ta ko ina ban da dariya babu abun da suke, kowa ya manta da damuwarsa ta lokacin, sun dauki 30 minute suna wasa kafin daga karshe suka koma Ciki,

Haka ranar suka tashi cikin farinciki.

Musamman Deejerh ji take tamkar ta dauwama a cikin wajen domin bata taba zuwa wajen da ta ji cewa ita ma kamar kowa bace irin yau , ta yi farinciki kuma ta manta duk wasu damuwoyinta.

Suna rabuwa da Su Abiel yanayinta ya canja hankalin ta ya fara tashi domin ta fara hasaso tashin hankalin da zata fuskanta inta je gida.

Sambatu ta fara tana tafiya kawai ba tare da ta ankare ba.

Tana zuwa get din gidansu ta fara labe laɓe da leke leƙen yadda za ayi ta shige.

Juyawan da zata yi kawai ji tayi Zayd ya damketa.

Tana kallonsa tsabar tsoro take jijiyoyin wuyanta suka tattashi ta yi wata ajiyar zuciya.

Ko kulata bai ba ya rike hannunta kawai ya jata cikin gidan.

Suna shiga ya ce, "Ga mu nan mun dawo ashe wai da nace ta fara gaba ina zuwa bata gane gidan bane mai taxi din ya batar da ita."

Momynta ta kalleta ta na, "Wato ke yanzu komai saidai ki fadawa Uncle dinki saboda ya shagwabar da ke,shiyasa da sassafe kika wuce biki gidan kawarki ba sanarwa ko?"

Kallon Zayd tayi da mamaki tana tunanin ta ya za ayi ace ya shirya karya don kawai ya kareta, anya kuwa shine? Inma kuwa shine din to babu shakka akwai wani abu na musamman da yake shirin haɗawa.

Murmushi ya yi yana, "ai ni nace kar ta tadaku kuna barci ba matsala amman ayi hakuri Little Princess ba zata kara ba."

Ya fada yana rungumeta tare da fadin, "Ko?

Kau da kai tayi, aiko ya danna mata mintsini a jiki, cikin sauri ta yi murmushin dole tana girgiza kai alamar eh.

Zayd ya ce, "Yawwa My Little Princess yanzu ki tashi kije kiyi wanka sai kizo in baki food ko?"

Tuni ta tashi domin daman jinta take kamar tana zaune kan ƙaya.

Ta shige dakinta.

Tana shiga ta daura hannu tana danne kanta don gabadaya juya mata yake,dakin ma juya mata yake yi addu'a ta fara , " Rabbie Inniy Lima Anzalta ilayya min khairin Faqir."

Haka ta dunga maimaitawa har saida ta ji ta fara dawowa daidai kafin ta dakata.

(Wanda daman wannan addua ce mai tasiri sosai tare da kubutar da bawa cikin yanayi mara kyau da kuma biyan bukatu na Alkairi ga duk wanda ya jibanci yinta)

Kwanta ta yi ta dan huta na mintuna sannan ta ta shi zumbur kamar an tsikareta tayi toilet wanke hannu ta yi kamar yadda ta saba, har sai tazo ta zauna kan gadon ta sai ta kara komawa a karshe ma ta je ta yi wanka gabadaya ta canja kaya, tana gama sa kaya taji an kira sallah ta koma ta dauro alwala ta yi da ta idar ma ta kara karanta Rabbie Inniy Lima Anzalta ilayya min khairin Faqir sannan ta tashi ta fara gyaran dakin duk da cewa a gyara yake babu wani datti amman ita gabadaya a tsarge take tana jin kamar tana zaune cikin datti shara tayi ba adadi haka ma gadonta ta kade ta kara gyarawa yafi a irga.

Daga karshe kuma kawai ta tsaya tana irga tiles din dakinta.

Zayd ne ya hankada kofar yana, "Kina ina Little Princess? Azo aci abinci don na sanki da kin son abinci yanzu sai ki kama barcin karya."

Ya rike mata hannu yana janta suka fita.

Ji take kamar ta fisge hannunta ta koma dakinta amman ba dama haka ta bisa yana janta.

Dadynta ya ce, "ta bata rai wai bazata ci ba ko?"

Zayd ya yi dariya yana, "eh fa wai ita ta koshi bata jin yunwa,bata so ta kara girma ta kamoni ne, don haka ni bazan yarda ba da kaina zan bata abincin ma."

Dukan su suka yi dariya.

Dauke abincin ya yi daga kan Dining ya kai kasa ya zauna ita ma ya zaunar da ita.

Ya diba yaji ya cika acikin abincin har saida ya canja kala,kuma yasan kwatakwata bata cin yaji arayuwarta saboda ita ne ma basa sa yaji a abinci sai dai a aje duk mai so yasa.

Zai bata a baki ta kau da kai, ya zare mata ido daidai kunnenta yana fadin, "in baki ci abincin nan ba sai kin jawa kanki bala'in da bakya zato ba ke Yar gantali ba? Har kin iya tafiya gantali ko?"

Sannan ya bude muryarsa yana matsar da kansa daga kunnen ta ya ce, "Haba My Little Princess My Beautiful Daughter, Oya take."

Bude bakin ta yi don dole tana jin abincin ya sauka akan harshen ta rufe idanu tsabar azabar yaji.

Zungureta ya