5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN

CHAPTER 9

by @xayyeesherthulhumaerath

a dangerous situation"

Ana gamawa Deejerh tai gida da sauri kasancewar ranar basu wani dade ba, har ta shige dakinta ba wanda ya ganta kuma bata tunanin ma an nemata.

Tana shiga ta sake yin wanka.

Ta zauna kenan zata huta training da aka masu ya fara dawo mata arai.

Tashi tayi ta dunga bi tana kara maimaitawa.

Ji tayi kawai an hankado kofa tana durkushe.

Dagowan da zata yi ta ga Zayd ne tsaye yana kallonta.

"Wannan kuma wani irin iskancine kike?"

Kallon shi tayi ta kawar da kai gefe.

Ya yi tsaki har zai fita ya koma ya ce, "kiyi wanka ki tsaftace jikin ki nan zuwa anjima da dare zamu fita." Yana fada ya fita.

Yana fita,Ci gaba da MMA dinta tayi ta ma manta da wani batunsa.

Ta riga ta ci ta ƙoshi gun training dinsu hakan yasa ko tunanin fita palourn ma bata yi ba.

Bayan ta gama zuciyarta ta raya mata kan cewa ta dauki Qur'ani ta karanta.

Haka kuwa ya kasance da ta karanta ta kara jin wani sanyi aranta hankalinta ya kwanta kuma ta samu nutsuwa har barci ya dauketa ba tare da ta ankare ba.

Har wajen karfe hudu tana barci bata farka ba, shiganshi dakin ya ganta tana barci cikin nutsuwa wani takaici ne ya turnukesa a zuciya, cikin fushi ya ja kafafunta daga kan gadon ya dire ƙasa.

Ta farka arazane tana waige-waige.

"Sannu ko! Wato har ni zance ki shirya ki jirani ina zuwa zamu fita ki kwanta kina wani barcin banza ko? Kina son wasa dani cikin kwanakin nan fa."

Ya wurga mata wasu kaya yana, gashi nan ki tashi ki je ki wanke fuska kisa kuma ki gyara jikinki minti Uku na baki.

Deejerh ta tashi ta shiga toilet tana zuwa alwala ta fara, bayan ta idar ta fito yana tsaye ta dauki hijabi zata shinfida sallaya tai sallah kenan ya daka mata tsawa.

"Ke! Me zakiyi wai? Me kike nufi?"

Deejerh ta ce, "Sallah zanyi sai insa kayan mu tafi."

Bugawa zuciyarsa ta fara tsabar takaici ya fisge sallayar, hijabinma ya janye mata saida ya kusan sheƙeta kafin ya kara wurga mata kayan da yazo mata dasu.

"In baki sa kayan nan yanzu mun fita kafin iyayenki su dawo daga anguwar da suka je ba sai na babbalaki cikin gidan nan."

Ta dauka zata sa ya kara fisgewa ganin tana yi kamar baza ta yi ba.

Da kanshi ya cire mata kayan da sauri yana zungureta yasa mata ya dauko turare ya kurma mata sannan ya jata suka fice.

A sit din baya ya ajiyeta duk da cewa ba a ganin mutum in yana cikin motar.

Kai tsaye gidan Nawar ya wuce da ita.

Gida ne da kana shiga zaka fahimce lallai ba abun Alkairi ake aikatawa ciki ba, musamman yanayin mutanen ciki, yawancin su duk bugaggune wa inda basa bigen kuwa suna cen suna wata tabarar ne,ko ca-ca ko dambe.

Duk da kasancewar gidan karami ba wani babba ba,amman haka suke lalatacciyar harkallarsu tsakanin maza da mata,har ma maza da mazan.

Deejerh na fita daga mota gabadaya idanunsu da hankulansu ya koma kanta, musamman matan da suke binta da kallon banza domin a tunaninsu tazo ne ta tuge su daga kan kujerar mulkinsu.

Zasu shige cikin dakin Nawar kenan wata na fitowa ta takewa Deejerh kafa da gangan sai da ta saki kara,kallonta tayi tana galla mata harara kafin ta ce, "Oh Sorry."

Ta wuce abinta.

Zayd kuwa ya fisgeta suka shige.

Suna shiga Nawar ya mika mata hannu,taki mika nata, Zayd ya mata kallon azabar da ya saba mata, haka ta mika masa hannun ya rungumeta.

Zayd ya fita ya bar su adakin.

Nawar ya kankameta kenan Deejerh ta janye jikinta.

"Mene ne lafiyanki kuwa? Kin san ni ba amun rashin daraja kuwa?"

Kan Deejerh na kasa ta ce, "Ranka Ya Dade Sallah nake son yi Don Allah ka barni inyi sai kayi duk abun da kake son yi ma."

Nawar ya ce, "Okay shikenan koma mene ne kiyi ina jiranki."

Tashi tayi ta yi Rolling din gyalenta, tana da wani agogo a hannunta dake iya nuna mata gabas hakan ta duba, ta kalla sannan ta fara sallah.

Idon shi na kanta yana kallonta har ta idar.

Tana idarwa ya ce, "Amman ita wannan sallar tana da mahimmanci ne? Na ga a prison wasu da yawa nayi kuma basa wasa da ita,yadda na ga kinyin nan suma haka suke."

Ganin yadda yake mata magana cikin nutsuwa yasa ta zauna kafin ta ce, "Is the ritual prayer of Muslims, performed five times daily in a set form, one of the Five Pillars of Islam. duk musulmin da ya yi wasa da sallah tamkar ya yi wasa da addini ne gabadaya ko ince ya fita ma daga addinin ne ma gabadaya."

Nawar ya ce, "Umm ni ba damuwana ne wannan ba yanzu tashi muyi abun da ke gabanmu."

Cikin nutsuwa ta bashi kanta domin bai mata kamar yadda sauran ke yi ba.

Kuma ta sake masa Sosai.

Har ya kai ga sun gama abun da suke ma sun zauna suna hira tare.

Tana tambayarsa to meyasa shi baya sallah.

Nawar ya ce, "mu addinimu babu wannan ba ace muyi ba church kawai muke zuwa addua."

Deejerh ta ce, "aiko in baka fara sallah ba za a ƙonaka a huta."

Dariya ya yi yana mamakin furucin nata ya ce, "Da gaske?"

Deejerh ta ce , "Eh mana."

"To shikenan zaki koyamun yadda ake sallah nima kar in shiga huta."

Har saida Zayd ya gaji da jira ya nocking masu kofa.

Koda Nawar ya bashi damar shiga dakin yadda yaga Deejerh cikin sakewa da walwala abun ya matukar bashi mamaki kawai tsayawa binta da kallo ya yi....

Nawar ya ce, "Ah ya ka tsaya kana mana wani irin kallone ni da Amaryar tawa?"

Binta ya yi da harara yana fadin, "Oh No na ga lokaci zai kure ne,ina so mu koma gida yanzu."

Nawar ya kalli Deejerh ya ce, "Girl,kina so ki tafi ki barni?"

Kallon Zayd ta yi,yana zare mata ido,kafin ta maida kallonta ga Nawar da ke sake mata murmushi ta girgiza masa kai alamar aa.

Nawar ya ce, "You see? bata son tafiya anan tare zamu kwana ko?"

Ya fada yana kallonta tare da mika mata hannu.

Ita ma mika masa tayi, tana kara girgiza kai a karo na biyu kan cewa ta eh.

Wani irin takaici da mamaki ne ya kubulu a zuciyar Zayd kamar ya janyota ya buga da ƙasa.

Murya na rawa Zayd ya ce, "O...o...Oga amman hakan zai zai...je mun matsala za a nemeta akwai matsala in aka fahimta."

Nawar ya ce, "Common, duk iya shirya zancen naka akan kankanin abu don na ce kawai ta kwana shine zaka rude,ka je cen ka shirya abun da zaka fada ni bai dameni ba,matsalarka ce."

Zayd ya kara cewa, "Oga Serious akwai matsala kasan da ace babu ban da damuwar hakan ni zan fi so ma."

Ya karasa maganaar yana rike hannun Deejerh.

Ita kuwa da sauri ta kara damke hannun Nawar yana janta kamar batasan yana yi ba tayi mirsisi da ido.

Tana kara janye jikinta.

Nawar ya yi murmushi ya kalleta yana fadin, "Sorry Kinji, karki damu ki bishi ku tafi gobe sai mu ci gaba da hirar mu ko?"

Deejerh dai bata so ba ta sunkuyar da kai kasa.

Nawar Ya kalli Zayd ya ce, "Saura kuma goben karka dawo mun da ita kasan sauran."

"Ah haba Oga kasan bama hakan zai faru ba ai dole na." Zayd ya fada ya riko hannun Deejerh da yi mata murmushiin karya.

Bye-bye Nawar ya fara mata cikin sakin fuska,ita ma ta yi masa har suka fice daga dakin.

Ban da kwafa da tsaki babu abun da zayd yake yana driving har suka isa gida, Deejerh kuwa abun da ya matukar bata mamaki da tsoro da ya gagara dukanta tabbas dole akwai wani abu da ya shirya a ranshi da zai mata.

Dakinta ta wuce da sauri kawai tayi sallar magrib da isha har ta kwanta a gado kamar an mintsineta da ta fara ganin abubuwa na dawo mata tuni ta tashi fara practice din MMA training dinsu neman barci ta yi a idanun ta ta rasa.

Karshe kawai ta ciro Tablet dinta tana dubawa, cikin sa'a kuwa kamar kullum Maestro Ramon ya tura mata da wa'azuzzuka da azkar, shiga tayi ta fara bin azkar din ana karantawa ita ma tana bi tana karantawa, bayan ta gama ta shiga wani video da ya turo mata Islamic words of encouragement da Sheik Umar Sulaiman ya gabatar yana fadin, "Allah Knows you're tired, He Knows You're trying ,He Knows it's difficult for you,But know that Allah will never put you in a situation you can't handle."

Tana saurara sai ta ke ji tamkar Don ita yake furucin nan take taji wani sanyi a zuciyarta yana ratsata.

Murmushi ta yi azahiri tana fadin, "Na sani daman Ubangiji na bai manta dani ba,kuma duk rintsi,duk daren da dadewa bazan taba dauwama cikin wannan halin ba, hakan shine jarabawata kuma ina fatan inci ta da kyakkyawan sakamako."

Ta kara bi ta karanta adduo'in kwanciya barci ma da ya saba turo mata sannan ta kwanta cikin ikon Allah kuwa barci ya yi awun gaba da ita.

Monday

Da wurwuri ta tashi ta shirya taje ta diba abinci a kitchen ba tare da sanin kowa ba , ta dunga sauri kar Zayd ya ganta aiko ta ci Sa'a har ta fice a gidan basu hadu ba.

6;00 ta kama hanyar skul

Ko da taje babu kowa cikin School din sai ita kadai hakan yasa ta zauna a stairs dinsu.

Tana zaune jigum cikinta ya fara yi mata ciwo,zufa take ta ko ina,cikin lokaci kadan ta fara ficewa a hayyacinta,gashi ita kadai babu kowa Students basu fara zuwa ba, karshe da tayi wani numfashi take ta sume.

Students na fara zuwa duk suka taru akanta anata cecekuce hayaniya ta gauraye School, Su Noha na zuwa suka je suna jijjigata duk sun gama razana a tunaninsu ta mutu,jin hayaniyar bata kare bane yasa Shugaban makarantar ya fito, aiko yana fitowa daidai da zuwan Maestro Ramon tare suka karasa,suna ganin Deejerh kwance haka cikin sauri suka kira waya clinic din school sukazo suka dauketa.

Su Maira kasa shiga class suka yi suka je suka tsaya kofar Clinic din suna ta zarya,sun kasa zaune sun kasa tsaye hankali a tashe.

Maestro Ramon ma hankalinsa ya tashi matuka.

Taimakon Gaggawa suka bata cikin sa'a ta farka,tana farkawa kuwa ta koma barci kasancewar allurar hutu da suka yi mata.

Dakyar Maestro Ramon ya kora su Daeej class kan cewa lallai da ta farka zai sanar da su.

Bata farka ba sai da lokacin tashi ya yi,ana ringing belt din tashi tana farkawa.

Clinic din suka nufa kai tsaye, suna shiga Noha ta ce, "Da kin mutu da munyi fushi da ke, kuma yanzunma ba ruwanmu dake tunda har munata jiranki kinki farkawa."

"Ai rabu da ita,tana kara yi mana irin wannan shikenan ba ruwanmu da ita kawai tasa mutane cikin damuwa,ni Allah class din yau kaf babu abun da na fahimta ciki fa." Daeej ya fada.

Abiel ya ce, "Yoo ba gwara ku ba,ni wani juyi kaina ya dunga yi kamar zai tsaye gashi babu harka bare mutum ya sha ya dan samu sauki."

Sai a lokacin Maira ta yi magana, "Duk naku mai saukine,ni har yanzu jina nake wata iri ban dawo daidai ba."

Deejerh binsu da kallo kawai take, sai da taga sunyi shiru sannan ta yi Murmushii tana mika masu hannunta.

Noha ce ta fara daura nata kai,Daeej ya daura, Hakama Abiel,sannan Maira karshe.

Deejerh ta ce, "Kawancenmu na nan, kun yafe mun ko sai na kama kunne?" Ta fada a shagwabe.

Dariya suka yi duka suna daga hannun sannan suka rugume juna.

Maestro Ramon ya shigo yana dariya, "Ma Sha Allah jiki ya yi sauki hankali ya kwanta ko?"

Daeej ya ce, "Yes Sir yanzu kam hankali ya kwanta."

"Maddallah haka nakeson ji kuma nake son gani,yanzu zan kaita gida a motata zaku iya tafiya."

Rikota suka yi duka kamar wata jaririya suna lallabata har suka rakata motar Roman sannan suka tafi suna yi mata Bye-bye.

Suna cikin tafiya ya tsaya ya siya mata kayan fruits da cake da drinks, sai da ya tabbatar ta cinye cake din ta sha drinks din sannan ya ta motar suka ci gaba da tafiya.

Suna isa gidan kuwa lokacin su Dadynta suka dawo daga wajen aiki, Zayd kuwa ya tafi wajen Nawar.

Da Mamaki suka tsaya kallon Maestro Ramon, ya mikawa Dadynta hannu suka gaisa.

Sannan ya ba shi damar binsu shiga gidan.

Momynta ta ce , "Daughter ya na ganki Somehow? What's going on? Fatan dai ba wani laifi kika yi ba."

Shiru Deejerh ta yi bata ce komai ba.

Saida suka shiga bayan sun gaisa Maestro Ramon yake fadin, "Kuyi hakuri na kara zuwa a karo na biyu ba tare da sanarwa ba."

"No problem ." Dadyn Deejerh ya fada cikin sakin fuska.

Maestro Ramon ya gyara zama kafin ya ce, "Yau Deejerh bata ji dadi ba School wanda har ya kai ga sai da muka danganata ga school Clinic sakamakon ciwon ciki mai tsanani da ya taso mata wanda har ya kai ga ta suma."

Da sauri Momynta ta kalleta tana taba jikinta. Tare da fadin, "Oh Sorry Daughter,sannu kinji yanzu da kwai abun da ke miki ciwo?"

Ta girgiza mata alamar aa ba tare da cewa komai ba.

Ya ci gaba da fadin, "Alhmdu Lillah yanzu kam ta dawo daidai amman akwai matsalar da zata iya afkuwa nan gaba muddin ba a nema mata mafita ba, yan gwaje-gwajen da aka mata a School clinic ya tabbatar da cewa Ulcer ce ta rike mata ciki wanda hakan ke bayyanar da cewa bata cin abinci yadda ya kamata hakan ya yi kasa sosai da har ya fara taba lafiyar cikinta sannan akwai yiwuwar ma tana yawan tunani wanda shi ma yana kara taso da ciwon sosai."

Dadynta ya ce, "aikuwa batun cin abinci kam hakan zai iya faruwa ba makawa domin sam bata son cin abinci in kaga ta danci abinci ma to Uncle dinta ne ya tursasata dole ta ci,tana da matsala ta wannan bangaren tunani kuma banjin gaskiya da kwai abun da har zai dameta ta zauna tunani akai tunda babu abun da ta rasa."

Roman ya ce, "amman ranka ya dade mai zai sa ku dunga tursasata da kanku ba sai Uncle din nata ba,na tabbata da cewa Zata fi sakewa kuma ta ci cikin nutsuwa sannan batun tunani ai ba sai mutum nada damuwa ba kila bata samun masu debe mata kewa ne."

Karaf Momynta ta ce, "to ai tafi sabawa da Uncle dinta kuma shi yake yi mata Komai sannan mu bamu cika zama da ita a gida ba,shine yake zama domin ita muna gun aiki kuma bamu da wata matsala yana debe mata kewa dama duk abun da ya kamata."

Roman ya ce, "Amman Madam bai kamata ace aiki zaisa baza ku damu da rayuwar Yarku ba,ko da kuwa Uncle dinta na dawainiya da ita dole tana bukatar iyayenta ma su jata a jiki sosai sannan su samar mata da lokacin su, 'Ya'ya mata rayuwar su na dauke da kalubale kala kala daban daban wanda kuskure kankani kan iya ruguza komai na cikinta."

Ta ce, "hakane Amman Deejerh bata da wata matsala da Uncle dinta kuma na tabbatar da cewa yana yi mata abubuwan da suka dace mafiyin yadda mu muke."

Dadynta ya ce, "Karka Damu Ranka Ya Dade za a kula in sha Allah mun gode sosai."

Maestro Ramon ya ce, "Nike da godiya na barku lafiya."

Yana fada ya fita daga gidan.

Motar sa na fita ta Zayd na shiga.

Sai lakewa Zayd yake yaga wanene amman ina har Roman ya wuce.

Zayd na shiga ciki Momyn Deejerh na mita, "wannan mutumin ya cika shishshigi wallahi nufinsa kenan Dan uwans baya kula da ita ko ya? Tsabar gulma da munafurci."

Dadyn Deejerh ya ce, "ke ko kiyo shiru ki bar maganar mana ba dai na amsa masa ba ai Shikenan."

Zayd ya katse su da fadin, "mene ne yake faruwa ne? Naga wani ya fita yanzu gashi kuma kuna ta hayaniya."

Momyn Deejerh ta ce, "wannan Maestro Ramon dinne yazo wai ba a kula da Deejerh yunwa ya sa mata Ulcer, naga ma ai mutum na iya ciwon ciki kawai yanzu haka munafurcinsa ne kawai ke cinsa."

Zayd ya zauna yana kallon Deejerh da ta tashi ta shige dakinta ya ce, "wannan mutumin ai kasurgumin munafuki ne,ni tun zuwansa na farko bai mun ba,shiyasa na je nayi bincike a kasansa, Da ya yi rashin ji sosai baya jin magana kuma yana da kudi sosai tsabar munafurci da son sawa 'ya'yan mutane idone yasa shi fara koyarwa a makarantar nan,tunda ance albashinsa na makarantar shine na mai gadin gidansa fa."

Momyn Deejerh ta ce, "No wonder, aiko Deejerh na kammala high school dinta bazata ci gaba Anan ba sai yaje can ya ta munafurincinsa."

Zayd ya ce, "nima abun da nake tunani kenan."

Ya fada yana tashi ya shiga Dakin Deejerh.

Yana tura kofar......

Zaune take rike da Tablet dinta tana danna karatu yana yi tana bi.

Wayar ya fisge ya jefar gefe, sannan ya ce, "kin dage sai kin sanar da wancen munafukin malamin naki sirrinmu ko? Ko ince atakaice kina son numfashi ya bar jikinki dana iyayenki ko?"

Ta girgiza kai kafin ta ce,"Na rantse ni ban fada masa komai ba,na je School dinne ban da lafiya shine daga Clinic ya kawo ni gida,kuma ni bance masa komai ba."

Wani kallon banza ya mata yana daga kai tare da fadin, "Really? kenan haka kawai yake kokarin sa mana ido da bin diddigi ba tare da kin bashi kofar yin hakan ba? U are very stupid taya ma zan yarda da hakan? U think am idiot as u?"

Ya karasa maganar cikin daga murya yana daga hannu zai mareta.

Kafin hannunsa ya kai fuskarta ta kauce.

Hannun ya sauka kan karfen gefen gado.

Wata