5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN

CHAPTER 10

by @xayyeesherthulhumaerath

azaɓa ce ta ratsa hannun take ya canja kala abun ka da farin mutum.

Cikin takaici ya daga hannun na rawa yana kallonta.

Radadin da yaji ya sanya shi gagara yin wani kwakkwaran motsi bare tunanin daukan wani mataki.

Ita kuwa saurin sunkuyar da kanta ta yi,ta yi tsuru jikinta na rawa.

Kara binta ya yi da razanannen kallo yana cizon yatsa ya fice cikin sauri.

Tana jin fitarsa ta dago kai sai da ta tabbatar ya fita kafin ta fara zanga uban dariya harda rike ciki don mugunta,bata ankare ba har ana jiyo sautin dariyarta, taba kofarta alamar shigowar da za ayi yasata saurin gimtse dariyarta ta koma tamkar ba ita ke yi ba.

Dadynta ne ya shiga yana fadin, "Daughter kina lafiya? Na ji kamar wani sauti daga nan dakin?"

Deejerh ta ce, "Dad ba komai ni banji wani sauti ba, oh inaga karar Tablet din cen ne da ta fadi a hannuna." Ta tashi tana dauko wayarta.

Murmushii ya yi mata ita ma ta maida masa sannan ya fice ba tare da ya ce komai ba.

Ci gaba da bin karatunta ta yi,har ta gama,ta ajiye wayar kenan kamar an zabureta ta tashi ta fira zuwa kitchen,a hancinta ji take kamar an bar gas a kunne,taje ta duba taga a kashene,ba ta yarda da hakan ba ta danna ta kunna sannan ta kara kashewa.

Har ta fita zata koma dakinta ta kara juyawa zuwa kitchen din kwakwalwarta na tiriyomata cewa ai yanzu ba ta kashe gas din ba ta na zuwa ta gani a kashe dafe kanta tayi kawai ta koma dakinta.

Tana shiga ta kulle kofarta.

Can koma zuciyarta ta fara rayo mata in kuma gobara tazo fa ta kulle kofa babu mai iya shiga bare ataimaketa,da sauri ta tashi ta bude, tana budewa ta ci gaba da jiyo warin gas a hancinta.

Wani karamin gyalenta tasa ta rufe hanci da shi.

Ta daina jin wari amman kuma da kyar take numfashi,yana yi sama-sama kamar wacce zata bar duniya.

Tuni gumi ya rufe ta, da sauri ta janye gyalen sannan ta shige Toilet ta wanke fuskarta.

Magungunan da maestro Ramon ya bata tasha,ta dan kara shan sauran kayan fruits din kafin ta kwanta.

★★★ HOPEFUL ENDEAVORS ORGANIZATION

Yau dai kam Deejerh sai da ta nemi izinin gun Momynta kan cewa zata gidan su Maira akwai Assignment din da zasu hadu suyi, kasancewar Zayd baya gida ta barta ba tare da ko tsananta bincike kan lallai can din zata ko akasin hakan ba.

Ko da suka je Ranar ba ayi masu wani lectures ba, wassanni suka yi sosai suka samu nishadi da karsashi kafin Ajeef ya sanar da su cewa zasu hada karamin shagalin nuna fasaha na gargajiya.

Sunji Dadi sosai kowa sai murna da dariya suna nuna farincikin su.

Roman ya kalli Deejerh yana fadin, "akwai bukatar a zana mana yanayin kayan da ya kamata asa kuma Deejerh kece zaki jagoranci wannan bangaren ina fatan babu matsala."

Da sauri Deejerh ta amsa, "Yes Sir." Dadi taje aranta Sosai an tabo bangaren da tafi so da kwadayi arayuwarta.

Daga lokacin suka fara shirye-shirye fannin drama wacce Ajeef ya hada masu kan fito da illar shaye-shaye kan iya harfarwa ga kwakwalwa wanda ya kasance Su Daeej da Abiel ne kan gaba wajen jagorantar dramar.

Tun daga farkon yadda aka fara masu bayani kan matsalolin da shaye-shaye kan iya haifarwa ya shafi kwakwalwar Dan Adam jikin su gabadaya ya yi sanyi dukaninsu sai kallon kallo ji suke aransu tamkar donsu aka shirya hakan.

Wanda kuwa kusan hakanne Domin Maestro Ramon ne ya tsara domin nusar da su cikin sauki ba tare da jin cewa antakura masu ba.

Kowanni bangare sunyi rehearsal sosai kan abun da aka basu na cewa zasu gabatar akai hadda kalubalen da 'Ya'ya mata suke fuskanta in sunyi ciki ba tare da Aure ba, wasu koda ace ba da son ransu aka masu ciki ba,indai cikin ya bayyana Shikenan sun fara fuskantar tsangwama wajen al'umma wanda har hakan yakan iya haifar da babbar matsalar da zuciya ke iya ingizasu su fada ga babbar halaka.

Bayan sun gama suka hadu duka wajen cin abinci ranar traditional food dinsu aka yi, Nacho and tacos,sai da suka ci suka koshi Kowa ya fito Deejerh da su Daeej suka tsaya kamar yadda suka saba sai sunyiwa juna sallama kafin su rabu.

Jiki a sanyaye Maira ta ce, "Guys wai anya kuwa zamu iya ci gaba da shan harkar cen? Kanmu muke wa illa fa tunda dadin na dan lokaci ne."

"Gaskiya nima yau abun ya sake mun jiki matuka,kinga mu muke abun amman sai nke ji araina kamar muna hasaso abun da zai iya faruwa damu a nan gaba ne." Abiel ya fada.

Dafe kai Daeej ya yi kafin ya ce, "Duk yadda za ayi ma kawai ayi mu daure mu hana kanmu shan wannan abun inaga shine mafita ni kaina jikina a mace yake Gaskiya in mukace zamu ci gaba ba karamar illa zamuyi wa rayuwarmu ba, zaifi kyau in muka danne,kila muma watarana mu iya hana wasu."

Sai a lokacin Noha ta yi Magana, "ni yanzu kullum addu'a ta Allah ya ban zuciya irinta maestro Ramon in zama mai son taimako da gyara al'umma, kunga kenan dai dole sai mun fara gyara kanmu kafin mu iya gyara wasu."

Deejerh na binsu da kallo bata ce komai ba.

Maira ta ce, "Oyaa to daga yau muyiwa juna Alƙawari Duk rintsi duk bacin rai kuma duk tsanani ba za mu kara attempting shan kowanni drugs ba sai dai wanda aka bamu daga hospital in ya zama ba ma da lafiya." Dukan su suka hada baki wajen fadin Yes harda Deejerh.

Hannunta tasa suma suka sa sannan suka daga tare suna dariya yadda suka saba,kafin suka rabu suna Kewar juna.

Tana shiga gida kuwa ta ga Zayd zaune da Momynta a palour suna hira.

Ya bita da harara sannan kuma ya fara murmushin gulma yana mika mata hannu, "Oyoyo Daughter an gama Assignment din kenan? Na yi kewarki fa tun tuni nake jiranki baki dawo ba."

Kin mika masa hannun ta yi Momynta ta kalleta rai ɓace ta ce, "Miye haka? Baki ga ana miki magana bane?"

Zayd ya cafko hannunta yana zaunar da ita gefensa ya ce , "Am so sorry Daughter kina fushi dani? Chocolate dinki jiya da ban siyo ba, kiyi hakuri ko sai na kama kunne ne?"

Ya fada ta gefe yana sa hannunsa yana murɗa mata fatar cinya.tare da harara.

Haka dan dole ta saki fuska tana girgiza masa kai.

Momynta tayi guntun tsaki tana, "ku dai ai ba a shiga tsakanin ku, za ma ku shirya ne." Ta karasa maganar tana tashi daga palourn.

Yana tabbatarwa ta tafi ya dakawa Deejerh tsawa yana fadin, "Wawiya kazamiya kawai tashi min da gani anan."

Sai da ta zabura ta tashi ta shige dakinta abun ta.

Tana shiga tayi wanka,tayi alwala sannan ta yi sallah,tana idarwa drawing book dinta ta dauko da colours tana fara tsara irin customs din ya kamata su sa maza da mata.

Tun bayan magrib har aka kira isha taje tayi ta ci gaba da yi gabadaya duka biyun sai da ta zana daga na maza har mata ko rintsawa ba yi ba har asuba tana kai, sai da tayi sallar asuba din kafin ta kwanta agun.

Rigace guntuwa iya gwiwa wacce za a iya sawa da wando ta yi matukar kyau sosai ta tsarata yadda kowacce mace zata iya sawa kuma ya yi mata kyau sannan ya hau kan al'adarsu.

Na maza ma rigace mara hannu amman wacce za asata da gajeren wando.

Gabadaya design din sun yi kyau sosai matukar kyau.

Ruwan da taji kamar daga sama na sauka a jikinta ne yasata saurin farkawa.

Zayd ne tsaye da bucket din ruwa yana tsiyaya mata.

Arazane ta farka hankalinta na kan drawing book dinta da shima ruwa ya fara taɓawa ta janye.

Zayd ya bisge ya kara tsunduma shi cikin ruwan sannan ya tattare shi waje guda ya tura mata cikin baki.

Tsabar takaici batasan sanda hawaye ya fara ambaliya a fuskarta ba.

"Ki cinye shi tas tunda ke baki da wani aiki sai zama ki na zane zanen shirme da haukar na hanaki amman bazaki hanu ba,yanzu ma na lura kamar wani mugun hali da raini kikeson bullo mun da shi, kuma saura yau ma ki shirya ki tafi School ba tare da kin dauki drugs kin saida mun ba,sai na canja miki kammanni," ya karasa maganaar yana taka mata hannu da kafarsa.

Sannan ya yi tsaki ya fice.

Yana fita ta tashi da sauri taje toilet ta zubar da takaddun da ya tura mata a baki,ta amayar tas, ta wanke fuskarta da hawaye ya gama kwaranya, idanunta sunyi jajur sun shige ciki tsabar barcin da take ji, amman kuma aranta tunanin dole ta kammala Designing dinnan a yau domin zata yi submitting ga maestro ya duba a School kafin a fidda kayan.

Wani zazzafan hawayene ya kara zuɓo mata a karo na biyu,tuɓe kaya kawai ta yi ta fara kwanta tana tunanin yadda za ayi ta iya kara sabon wani Designing din kafin ta tafi School din ba.

A wannan tunanin ta yi wankan ta gama,ta shirya cikin uniform dinta.

Kallon agogon hannunta tayi ta ga 6:50 kuma 7:30 ya kamata ya yi mata cikin group ne.

Da sauri ta dauko wani drawing book din da colours ta durkusa ta fara sabon Designing, tamkar wacce aka bawa kwafin abu haka ta dungayi domin duk abun da take zanawa ta gama tsara shi a kwakwalwarta cikin kankanin lokaci.

7:20 daidai ta kammala Designing wanda har ya fi na farkon da tayi ma fita da kyau sosai tana kallon agogo ta numfasa tana kokarin maida Drawing book din jaka kenan Zayd ya turo kofa yana bambami, "Wato kedai bakya jin dadi in ba na taba lafiyarki ba ko?"

Kafin ya ankare da sauri tasa a jakar ta rufe.

Ta tashi tana sanyawa a baya.

Wurga mata wata karamar jaka ya yi yana, "Gashi nan kisa cikin jakarki kuma muddin Basu kare ba,kada ki kuskure ki dawo mun gida babu kudi , ko da kuwa ɗaya ne bai kare ba, ki san yadda zakiyi."

Bata ce masa komai ba,ta dauka tasa a jaka kawai ta fice, ko tunanin breakfast bata yi,haka ta dunga sauri,tana gudu har ta isa School din.

Ta ci sa'a saura 1 minute a rufe get kenan ta je ta shige.

Office din Maestro Ramon ta fara zuwa ta yi mika masa drawing book din kan ya duba.

Ajiyewa ya yi gefe ya kalleta kafin ya ce, "zan duba anjima."

Zata fita kenan ya dakatar da ita.

"Aa ki dawo ki zauna,anan tukunna,gudu kika yi?"

Ta girgiza masa kai alamar e.

Ya ce, "me yasa to? Ke da baki da lafiya."

Ta yi shiru bata ce komai ba.

Ya kara fadin, "kinyi breakfast?"

Nan ma ta yi masa shiru kanta na kasa.

Daukan Takeaway din BURRITO da ya yi Order zai ci ya yi,ya mika mata yana, "Oya Take this,ki zauna kici anan har ki gama tukun."

Idanunta na kaiwa kan abincin yawunta har yana zuba jikinta na rawa ta karɓe.

Tsabar sauri ta gagara budewa sai shi ya karɓa ya bude mata, sannan ya sa aka kawo mata coffee ma.

Ci ta dunga yi ba ji ba gani saida ta cinye tas,sannan ma ta koma kan coffe din,shima tunda ta kafa kai saida takai karshen sa kafin ta dire.

Binta yake kawai da kallo har a zuciyarsa yana matukar jin tausayinta.

Da ya ga ta gama duka ya ce, "kin koshi?"

Ta girgiza masa kai wanda hakan ya zame mata jiki fiye da iya furta wata kalma.

Ya ce, "Okay to in kin tawo da magungunanki ki ciro ki sha ko." Ya mika mata.

Ta ciro duka ta sha.

Abincin da taci har ta danyi kyan gani fiye da yadda ta baro gida.

Tsabar koshi tuni ta fara gyangyadin barci tana razana.

Maestro Ramon ya kalleta ya ce ,"ki je can ki kwanta in kin huta zuwa anjima sai ki shiga class."

Ba tare da ta ce masa komai ba ta tashi taje ta kwanta,tana kwanciyar kuwa barci ya yi awun gaba da ita.

Ya kalleta yana girgiza kai a zuciyarsa yana fadin, "Ya Rabbie ka bamu matan da suke da lokacin kula da 'Ya'yanmu, sannan muma ka ba mu zuciyar damuwa da tarbiyar 'Ya'yanmu, Rabbie ka rabamu da sakaci,son zuciya da kwadayi,yanzu Don Allah taya za ace wai wannan yarinyar tana zaune gaban iyayenta? Suna raye kuma suna ganinta, wa zai gasgata hakan? Wasu iyayen kam ma da su da babu duk ɗaya ne domin basa da maraba da fanko, indai bazamu damu da rayuwar wa inda zamu haifa ba,bai kamata ace muyi tunanin shi kan shi auren ma ba,bare kuma ya kai ga batun haihuwar. an shiga rayuwar da rudin duniya take rufewa iyaye idanu,rayuwar da iyaye ke son kansu fiye da yaransu,rayuwar da iyaye ke fifita farincikinsu fiye da farincikin 'ya'yansu."

Drawing book din ta bashi ya dauko yana dubawa, da mamakin sa ya ga zanen ya fito fiye da hasashensa,a tunaninsa dai zata iya mai kyau amman ba yi tunanin zai fita har haka ba.

Kallon ta ya yi tana sharbar barci hankali kwance ya numfasa kafin a zahiri ya ce, "Ubangiji ya yi masu kyautar 'Ya mai baiwa amman rashin tunani da hangen nesa yasa sun gaza fahimta bare su yi nasarar cin albarkacinta."

Maidawa ya yi,ya ajiye sannan ya tashi ya nufi class din su Deejerh lokacin shigarsa ya yi.

Yana zuwa ya ga Su Daeej jingum-jingum yanayin damuwa ya bayyana a fuskarsu karara duk sun takure waje guda.

Bayan sun gaisheshi duka class din ya kalle su ya na, "ku kuma lafiya yau? Kalau kuwa?"

Maira ta ce , "Sir Deejerh bata zo ba,ba mu sani ba ko jikinne ."

Murmushii ya yi kafin ya ce, "au duk shine wannan damuwar kuka takure? Ta zo fa."

Dukansu har suna hada baki a tare suka ce, "Ina take?"

Roman ya ce, "tana office jikinta ba kwari Sosai ne nace ta dan kwanta amman nasan tana tashi zaku gan.....

Kafin ya karasa maganaar taking excuse dinta da tayine ya katsar da shi.

Take duka suka saki fuska ganinta, Maira ta karasa ta rike mata hannu suka zauna.

Maestro Ramon Ya ce, "Shikenan ma,yanzu hankali ya kwanta,amman fa gaskiya nima zan shiga wannan team din naku,nuna soyayya da damuwa haka kamar za a hadiye juna? Daga yau nima na zama abokinku."

Duka class din dariya suka yi a tare kafin ya fara yi masu karatu.

Lokacin Break dinsu na yi suka fice tare , School Compound din suka zauna rana ta farko da basu shiga ajin duhun da suke shaye-shaye ba.

Kudin da sukazo da su, haɗawa suka yi suka siyo snacks da drinks suka zauna suka ci tare.

Abiel ya ce, "ni yanzu da bama shan harkar cen sai nake jin kaina wayam kamar babu komai amman wallahi da lokaci zuwa lokaci sai injini wani dim kaina na juyamun fa,duk da dai ina jin matsanancin ciwon kai amman gwanda mun yanzu akan da."

Noha ta ce, "hakane daman ai duk rintsi gwanda mu daure jiya fa da dare dana kasa barci har na daga gorar zan sha kawai na tuna da alkawarin mu tuni na jefar, haka nata fama da ciwon kan,da kyar na samu barcin ma ya sace ni."

"Ya za muyi dole haka zamuyi tayi har mu saba Ina zuwa komai zai wuce." Daeej ya fada.

Maira ta ce, "kwarai kuwa komai ma sai an daure."

Maestro Ramon yana kallon su daga Office din shi,ba karamin farinciki ya ji ba ganinsu yau kamar kowa sun zauna cikin students ba tare da sun ware kansu ba,wanda hakan na nu ga an samu ci gaba sosai kenan a garesu.

Bayan sun koma Class Roman yake fadawa Deejerh cewa tayi matukar kokari sosai sannan Designing din da tayi bai da wata matsala komai ya yi daidai musamman tsarin yadda ta bambamta tsakanin na mata da mazan wajen yawaita ado ana mata fiye da maza tamkar wata babbar fashion designer da ta kware ne ta yi.

Jin Hakan ya faranta mata rai Sosai wanda ta kasa boye farinciki har sai da ya bayyana a fili.

★★★

Tana zuwa zata shiga gida gabanta ya fadi zuciyarta na bugun tara tara ta tuna cewa yau bata saida wa Zayd drugs dinsa ba gashi sai da ya mata kashedin cewa kada ta dawo masa da ko ɗaya wanda yanzu kuwa ko dayan ma ba ta saida ba bare saura.

Aiko tana sa kafa zata shiga ciki,ganinsa tayi kicibis agabanta yana mika mata hannu alamar ta bashi hannu.

Take hawaye suka cika idannunta tama rasa abun cewa,ya yi tsaki yana fisge jakar ta ta, ya bude.

Yana ganin komai yadda ya bata a fusace ya dago yana kallonta.

Tuni ta matsa gefe da gudu.

Binta ya yi ya cafkota yana, "maza ki cire kayan jikinkin nan tas gabadaya yanzun nan tun kafin in kasheki in kashe banza,wato ke kin shahara kin kai mizanin yin abun da kika ga dama da har zaki dawo mun da Abu Yadda na baki? Har ni zaki dawo mun da kayana? Komin dare kuwa sai kin fita kinje kin nemo mun kudi kin kawo mun in ba haka ba kuwa saidai iyayenki suzo su dauki gawarki, wawiya,jaka kawai maza tuɓe."

Ya karasa maganaar cikin tsawa yana zare Belt din jikinsa.

Haka yasa ta tayi tsirara tunbur haihuwar uwarta ya daga Belt din kenan zai sauke mata wayarsa ta fara ringing.

Dubawan da zaiyi yaga Nawar ne.

Tsaki ya yi ya amsa.

"Barkanmu da yamma Ranka Ya Dade."

Nawar ya ce, "ba wannan ba,yanzu ina jira ka kawo mun Deejerh , wai kai baka da hankali ne,jiya kaki kawota yau ma me kake nufi? Na baka 10 minutes ko ka kawo mun ita ko kuma ka shigar da kanka trouble."

Nawar ya fada yana katse wayar.

Buga kafarsa ya yi da jikin kujera ya hankada ta na bacin rai, sannan ya kalli Deejerh yana, "ki tashi