5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN
CHAPTER 13
tura abincin tana cikin ci sai ga shi ya kara fitowa yana fadin, "inna karaso wajen nan baki fice mun da gani ba sai na ballaki."
Kallonsa tayi kawai ta dauki jakar ta fice ba tare da ta ce masa komai ba.
School dinsu ta nufa kai tsaye ta fara zuwa office din Roman.
Yana ganinta kuwa ya tashi yana fadin, "lafiya kuwa?"
Bata ce komai ba kawai ta bude jakarta tana nuna masa.
Roman ya ce, "na mene ne?"
"Cewa ya yi saina saida na bashi kudin." Tana fadan hakan ta yi shiru.
Roman ya ce, "shi wa? Me yasa zai baki ya ce sai kin saida?"
Shiru tayi ta sunkuyar da kanta.
Ya kada kansa kawai ya dauki jakar yaje ya zuba duka drugs din a kwalbet sannan ya dawo ya ce mata, "ki tafi class in an tashi zan baki kudin, amman karki kara gigin karban wannan abun koma agun waye, ki san matakin da za ki iya karw kanki a ko ina cikin sauki ba tare da samun nasara ba."
Ta girgiza masa kai sannan ta wuce aji.
Lokacin tashi na yi Roman ya bata kudin kamar yadda ya fada sannan ta dauki hanyar gida.
Tana cikin tafiya kamar ance ta daga idonta kawai ta ga kamar an dire mata mutum gaba.
Ta.....
Tana daga kanta ta ga Zayd tsaye yana zare mata idanu tare da mika mata hannu.
"Bani kudadena."
Yana fada ta sa hannu cikin jaka ta mika masa kudin.
Har ransa bai so ba,domin hasashensa ta ce babu ne ya yi mata abun da ya ga dama.
Ya ce, "to wuce mu tafi guzumar munafuka daman nazo ne in tabbatar da cewa kinzo School din ko kuwa naki yawon barikin kika tafi,ban ma yarda dake da wannan Teachern naki ba, dole akwai wata kullalliya tsakaninku, ke da ma kika ce ba a siyan drugs din taya kika samu kudi in ba wai bashi kanki kika yi ba? Zan yi maganinku kuwa daga ke har shi tunda ku kananun yan iska ne."
Deejerh kam bata ce masa komai ba ya hankada keyarta gaba yana binta a baya da kafa har suka isa gidan.
Suna isa kafin ya ankare,da gudu ta shige dakinta tasa key ta kulle kofar windownta ma ta kulle.
Cikin bacin rai ya dunga jijjiga mata kofar yana kiran sunanta.
Tun tana jin karar sautinsa har ta gaji ta dau earphone dinta tana sauraren karatu ta daina jiyo sautin sa.
Ganin bata da alamar budewa dole ya hakura ya tafi dakinsa cike da takaici don aranshi ya gama shirya irin muguntar da zaiyi mata kenan.
Tunda ta shiga dakin bata bude ha har safiya.
★★★
Tana tashi ta fice sim sim ba tare da sanin kowa ba , Hopeful Endeavors ta wuce kasancewar yaune ranar da za a kaddaramar da taron su na gargajiya.
Tana zuwa aka bata rigar da tayi Designing nata,tayi matukar yin kyau fiye da hasashenta har ma ta fi kyau a zahiri fiye da a zanen.
Dukanin su sai yabon kayan suke.
Wani babban bako da Roman ya gayyata ya bukaci da abashi damar fidda design din a kamfanin sa.
Sun yi taro anci an sha kuma an nishadantu sosai da sosai kowa ya ji dadi, tun safe sai karfe hudu aka gama ana gamawa Deejerh taji ba inda take buƙatar zuwa sai gida domin ta yi wanka jikinta na yi mata wani iri duk ta tsargu.
Hakan yasa tayiwq su Daeej sallama ta kama hanyar gida.
Tunaninta ba kowa gidan hakan yasa ta shiga hankali kwance da karfin gwiwarta.
Tana shiga dakinta ta tube kenan zata shiga toilet taji an hankadata ta fada kasa, kafin ta yi wani yunkuri zayd ya fara taka mata ruwan ciki yana dukanta da belt, duk kokarinta na ganin ta janye jiki ta gagara tamkar wanda aka turo dukanta yake da hannu da bulala da kafa kawai, tsabar azaba aman jini ta fara,tana sa hannu ta ga jini ts kara firgicewa tana kuka , "Uncle Please.... please.... Uncle...." Abun da take iya furtawa kenan.
Ya dagata kamar tsumma yana tsayar da ita sannan ya fara tusa hannunsa gabanta.
Yana fara hakan ta rufe idanunta babu abun da take gani sai training din su na MMA ita kanta batasan ya akayi ba sai ji tayi kawai ta saki wata kara ta daidaici daidai marar Zayd din ta dunkule hannunta ta dunga buga masa.
Yana kokarin kare kansa amman kamar ingizata ake ko ince wacce aka sakewa famfom karfi.
Wani bugu da tayi masa a karshe ya yi wani gajeren nishi take numfashinsa ya tsaya caj ya fadi a wajen.
Ta tabashi ta ga baya motsi kuma baya numfashi hakan yasa ta birkicewa da tunanin cewa ya mutu, rigarta guntuwa kawai tasa ta fice da gudu, haka ta dunga tafiya tana haki akafa har gari yayi duhu dare ya yi a kafa har ta isa gidan Nawar.
Tana zuwa masu gadin suka hanata shiga tana ta kuka da shashsheka.
Hanayaniyar da tayi yawa yasa shi fitowa aiko ya ganta yaji mamaki matuka ganin ta cikin dare, kai tsaye ya bada umarnin abarta ta shiga.
Ban da nishi da ajiyar kuka tare da hawayen da ke ambaliya daga fuskarta babu abun da take.
Ya dibo ruwa ya bata tasha sannan ya ce, 'Mene ne? Me ya faru ne?"
Deejerh ta saki ajiyar zuciya ta ce, "Uncle, Uncle Zayd...."
Sai kuma ta yi shiru.
Nawar ya ce, "Zayd? Me ya faru ya miki wani abu ne ko wani abune ya same shi?"
Ta girgiza kai a tsorace.
Rike mata hannu Nawar ya yi,ya na shafa mata kai a hankali ya ce, "ki nutsu ki fadamun gaskiya kinji, ba zan taba bari wani ya cutar dake ba, ni ai abokinki ne ko? Kuma aboki na sadaukar da rayuwar sa ga aboki."
Murya na rawa ta ce, "na...na...na... kashe...shi."
Sai da mamaki ya bayyana a fuskar Nawar ya kalleta ya ce, "kashe shi kuma? Akan me? Garin yaya?"
Da ya ga Deejerh na shirin firgicewa sai ya yi shiru ya ce, "shikenan yanzu ki nutsu ki kwanta kinji gobe da safe za mu yi magana.
★★tana fita ba jimawa sai ga momynta da Daddynta sun dawo gidan, basu yi tunanin komai ba kowa ya fara harkar gabansa sai wajen karfe goma Dadyn Deejerh ya ga wayar zayd a palourn su kuma ya tabbatar baya taba barin waya a gida, da mamaki ya dauka yana nunawa momyn Deejerh ta yi Murmushii ta karba tana, "yanzu haka yana nan gaban Daughter tana ta masa rigima shiyasa muka ji su tsit bara in kai masa wayar." Ta nufi dakinsa bata gansa ba sai ta koma na Deejerh.
Tana zuwa ta ganshi kwance warwas batasan lokacin da ta saki wata gigitacciyar kara ba.
Da gudu Dadyn Deejerh ya karasa dakin shima dukan ninsu suka birkice, cikin gaggawa Dadyn Deejerh ya yi jarumtar kiran motar asibiti.
Cikin 10minute suka zo suka daukesu Ban da kuka babu abun da Momyn Deejerh ke yi.
Suna shiga aka fara yi masa taimakon gaggawa.
★★
A takure ta kwanta, idanunta biyu har safiya,
Nawar na hankalce da hakan ya ce mata, "kin gani ki nutsu ki ci abinci yanzu in kika gama sai muyi magana ko? Ki tashi kiyi wanka." Ta girgiza masa kai ta tashi taje tayi wankan sannan ta kara zama a takure.
Abincin ma kasa ci tayi da kyar ta iya shan tea.
Nawar ya ce, "akwai wani da kike son gani ? Zaki yi magana da shi?"
Deejerh ta girgiza kai alamar eh.
Nawar ya ce, "Ok wane ne? Ko in baki waya ki kirashi?"
Ta kara girgiza masa kai.
Mika mata wayar ya yi ta danna number meastro Roman.
Sai kuma ta mika masa.
Bayan sun gaisa Nawar ke sheda masa cewa in babu matsala yazo dalibarsa na da bukatarsa a yanzu.
Babu musu kuwa duk da cewa Roman yasan hadarin da ke tattare da Nawar haka ya amsa da fadin gashi nan zuwa.
Take ya fice daga School ya nufi gidan Nawar.
Yana zuwa ya kurawa Deejerh idanu yana mamakin yadda akai tazo nan din.
Nawar ya ce, "ka kwantar da hankalinka,ka fahimceni, ba cutar da ita zan yi ba hasalima ita ta zabawa kanta wajena a matsayin mafaka,ni abokinta ne kawai kuma aboki mai son taimakon abokiyarsa jiya da yamma tazo nan cikin wani hali wanda kalmar cewa tayi kisa kadai ta iya fadamun daga nan ta gagara kara fadin komai shiyasa na bukaci da ta kira wani makusancinta wanda zata iya sake jiki tayi bayanin meke faruwa?"
Da sauri Roman ya durkusa gabanta murya a sanyaye ya ce, "ki fadamin kinji mene ne ya faru?"
Ta ce, "Uncle Zayd ne yaketa dukana yake mun irin abun da yake mun ni kuma na bigesa a mararsa shine ya mutu." Tana karasa fada hawaye na zuba daga idanunta.
Roman ya kalli Nawar ya ce, "tabbas hakam ta aikata tunda ta fada kuma abun ya kai mata makura ne,iyaye marasa daukan rayuwar yara da mahimmanci da Uncle mai son zuciya."
Roman ya ce, "gaskiya dan zamana da ita na fahimci cewa tana da matsala a tunanina zan iya kareta daga wani abun amman Zayd ya wuce tunanina yanzu dai mene ne mafita?"
"Sai dai afitar da ita daga cikin Kasar nan shine kawai mafitar ko da kuwa zuwa paris ne akwai wata friend dita na aiki acen zan iya hada su don anan innace zan ajiye akwai matsala muddin ya kasance Zayd na raye to zai yi duk abun da zaiyi wajen ganin ya illata ko ince ya hallaka yarinyar nan duk da kasancewar sa karami cikin mu amman kuma tsaf zai iya bawa Kasuwancina ma matsala don babban abun da nake gudu kenan ya iya dadin baki da shirya zance cikin kankanin lokaci." Cewar Nawar
Zayd ya ce, "Tabbas nima na fahimci hakan,amman yanzu ya za ayi a fitar da itan?"
Nawar ya ce, "fitar da ita cikin sauri sai dai mu bi ta gurbatacciyar hanya kasani."
Rowan girgiza kai, "ehwen zanyi kokarin hakan In Sha Allah."
Murmushi Nawar ya yi kafin ya ce, "aa zan yi abun da ya dace karka damu domin kai ba irin da ba bane tunda ka zubda makamanka nasan yin jagaliyanci zai ma wahala a yanzu."
Roman ya yi dariya, "ai da sai in tada sabon liki indai Deejerh zata fita cikin kangin nan burina ya cika."
Suka yi dariya duka.
A wajen Nawar ya kira waya kan ayi ciku-cikun yiwa Deejerh Visa ta samu ta bar kasan."
Nawar ya dafa shi ya ce, "karka damu zanyi bakin kokarina,kasan 15days ne Amman ni zanyi yadda za ayi cikin 5days a kammala komai and kuma kasan in tana gidan nan bata da wata matsala she is save."
Roman ya ce, "hakane kam Allah saka da Alkairi zanna tabaka ta waya kuma kila ma in dawo kafin ta tafin, yanzu zan koma school kar aneme ni."
Daga nan ya tashi ya tafi yawa Deejerh sallama tare da fadin ta kwantar da hankalinta ta zauna gidan babu abun da zai faru.
Su momynta kuwa a asibiti suka kwana har safiya likitoci na kan Zayd kuma basu fada masu cewa yana raye ko akasin hakan ba koda suka yi magana ce masu suka yi kawai suta addu'a don ba lallai ya tashi ba.
Da safe duka suka koma gida, sai a lokacin tunaninsu duka ya koma kan Deejerh suka duba babu alamarta a gidan.
Dadyn ta ya kira school aka tabbatar masa da cewa bata je ba.
Nan hankalin su ya tashi suka fara bincike gidan.
Momynta na kan bincika dakin tana daga pilonta tayi karo da diary book dinta,wanda take rubuta abun da ya shafi rayuwarta ciki.
Da sauri ta dauka ta zauna ta fara bude shafin farko.