5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN
PAGE3
"Wanda kuke kira da jigo gareni shine ya tarwatsa mun rayuwa,wanda kuke kallon shine farinciki gare ni shine babban bakin ciki gareni, ku yarda da cewa Uncle zayd zai kula dani zai kaunaceni baku taba damuwa da sanin shin cewa ina jin dadin rayuwa da shi ba, ban san meke faruwa ba amman ina ji a jikina cewa dole akwai wata rana da zata zo, kuma zakuyi nadamar barin rayuwata a tarwatse kuna nufin ban da amfani ga rayuwa kenan? "
Gagara karasa karantawa tayi tana kuka na fitar hayyaci ta tashi ta fice aguje....
Tana fita Dadyn Deejerh ya rike ta yana fadin, "Mene ne ya faru? Ina take? Kin ganta ne?"
Cikin muryar kuka ta ce, "Aa ,aa Zayd ya cuceni,ya cutar mun da rayuwar 'Ya ban san inda take ba, shikenan,muje gunsa ya nemo mana ita, muje ya nemota."
Take suka tari taxi suka nufi asibitin.
Suna shiga Zayd na farkawa kenan.
Dakin Momyn Deejerh ta kutsa kawai taje ta cakume Zayd tana fadin, "Ina Deejerh? Ina ka kai mun 'Yata? Ka fitomin da 'Yata, na ce ka fitomin da 'Yataaaa." Ta karasa tana kara fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
Tsaki Zayd ya yi duk da cewa jikinsa ba wani karfi amman haka ya hankadata gefe saida dadyn Deejerh ya riketa
"Kun bani ajiyarta ne? Ko ina take ma ku zaku fito da ita kuma Na rantse da girman Ubangiji idona idonta sai na kasheta ba ma ita ba hatta ku sai na kasheku."
Wani kallon mamaki Momyn Deejerh ta yiwa Zayd ta ma kasa cewa komai kawai abubuwa ne kawai ke mata yawo cikin zuciyarta arai tana sakawa, "Tabbas ni ce na cutar da 'Yata da kaina,ni na nuna mata cewa shine bangon da zai tallafi rayuwarta, ashe shine makamin da zai rusata?"
Karamin suman tsaye ta yi.
Ganin ta kame kam Dadyn Deejerh ya riketa .
Kara rugumesa ta yi cikin muryar kuka tana fadin, "Kana gani? Kana gani ko? Wai Dan Uwana ne zai tarwatsa mun rayuwar 'Ya? Ashe ba son mu yake ba? Ashe duk abun da take nunawa da gaske ne? Har abun da ta fadamin ranar?" Ta kara fashewa da kuka.
Jan hannunta ya yi suna fita daga dakin, "Duk ki bar batun nan,ki nutsu mu nemeta yanzu,ba komai ya ja mana hakan ba illa sakaci da son zuciya ganin cewa yana da arzikin da muke mora."
Cikin muryar kuka tana kara daga sauti ta ce, "Wallahi in banga Deejerh ba sai na kashe Zayd sai na kashe shi kafin ya kashe mu zan kashe shi gwanda duk mu mutu."
Tana maganar yana janta.
Kai tsaye police station suka je shigar da cikiyarta.
Suna Fita Dr yazo kan Zayd da takaddar sallama.
Zama ya yi gefensa yana fadin, "To aboki jiki ya yi sauki Alhmdu Lillah kuma mun sallameka yanzu ruwan nan na karewa Shikenan,amman kafin nan ina so muyi wata 'Yar magana,fatana dai ka fahimceni kuma ka karbi kaddara mai kyau ko mara kyau."
Zayd ya kalle shi ya ce, " kaddara kuma? Wacce kaddara? Ni ai banjin akwai abun da ya sameni lafiyata lau nake jina."
Murmushi Dr din ya yi ya dafa kafadarsa yana fadin, "ba abun da ya sameka kam Alhmdu Lillah amman an samu yar tangarda kadan kuma...
Kafin ya karasa Zayd ya katse shi,"wacce irin tangarda? Kamar ya? Zaifi kyau kamun magana kai tsaye Dalla Malam."
Dr Ya sunkuyar da kai kafin ya ce, "Ahto gaskiya ka samu matsala a testicle dinka ma'ana 'Ya'yan maraina wanda in aka samu matsala abu ya dokesu har ya kai duka akan samu matsala wacce hakan kai haifar da rashin haihuwa ma'ana atakaice baza ka taba samun haihuwa ba a rayuwa....
Fincike abun ruwan zayd ya yi yana kafawa Dr din mari a kumatu ya ce, "banza matsiyaci makaryacin karya, sai dai ka ga rashin haihuwa a kwaryarka ba dai tawa ba,ita kuma wacce Annamimiyar yarinyar duk inda take sai na nemo ta na kasheta na yi sanadin." Ya fice.
★★★Anyi neman Deejerh har an