5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN

CHAPTER 14

by @xayyeesherthulhumaerath

gaji Momynta da Dadynta sun sadakar sun koma gida tsawon kwana shida dan takaici ko aiki basa iya zuwa Momynta ma na kwance kullum cikin jinya.

★★Nawar ya gama hurda hurdar sa saidai ya tabbatar ya sama mata Visa zuwa Paris

Ta Cruise ship su zai tashi karfe shida na Yamma shi kuma lokacin Zayd yaje bakin ruwan yana ci gaba da nemanta.

Suna fitowa a mota yana juyawa daidai saitinsu.

Idanunsa idon Deejerh.

Tayi saurin razana tana komawa bayan Nawar.

Daga kan da zaiyi ko shi ma yaga Zayd amman kuma ga dukkan alamu idanunsa ne kawai ke kallon wajen amman zuciyarsa na wani bangaren.

Hakan yasa Nawar ya yi saurin shigar da ita ship ya mika mata wani bargo ya rufe ta da shi sannan ya tsaya agefen.

A dube dubensa ya je ya tsaya gaban nawar inda ya tsaya yana kallon Deejerhn

Zayd zai juya kenan Nawar ya yi saurin sunkuyar da kai kasa.

Har ya wuce nan yaje ya ci gaba da lalubensu bai ga ko alamar ƙeyar Deejerh ba.

Ajiyar zuciya Nawar ya yi ya daga kai yana yi mata magana, "Duk inda zaki kasance ina fatan ki yi kokarin inganta rayuwarki kada ki dubi bayan ki,ki duba gaba da tunanin haskaka ta Kinji wayar dake gunki kuna sauka ki kira sona zata zo ta dauke ki, in kin huta muma ki kira mu kinji Allah tsare hanya."

Yana tafiya kuwa suka tashi.

PARIS

★★sai da suka isa Ta fito daga ship din kenan ta laluba jakarta don daukan wayar da Nawar ya bata ta kira Sona,waya ta ce daukeni a hankali babu ita babu dalilinta.

Ta daga kai

Ga mutane kowa na harkar gabansa ba wanda ke yi da wani kawai kowa damuwarsa yake, suna neman hanyar shiga cikin gari kawai.

Bata san lokacin da hawaye ya fara zuban mata daga idanu ba ganin cewa ta rasa makafa da hanyar bi.

Tafiya ta fara yi kawai ba tare da tasan hanyar da take bi ba.

Har ta fita cikin jama'a ta fara shiga gun da ba mutane sosai.

Can gaba kuma ta ci karo da wani team din maza kallo daya za a masu a fahimci cewa tantirai ne na karshe.

Suna ganinta kuwa suka yo kanta suna kokarin bin jikinta

Duk kokarinsu na sai sun aiwatar mata da abun da bai dace ba sai kara kaucewa take ganin hakan suka hadu duka tare suna so su jata na karfi.

Da kyar ta samu ta bigesu gefe ta fara gudu,tana yi suna binta tana yi suna binta har jini ya fara kwaranya daga jikinta.

Haka ta ci gaba da gudun duk da cewa ta jima da ficewa a hayyacinta haka ta ci gaba da gudun a karshe har suka gaji suka daina binta ba tare da ta sani ba ita dai gudu take har ya kai ga ta shiga cikin wani karamin kauye.

Jirine ya dibeta yayin da wani gudun halita ke fita daga jikinta take ta fadi,jini sai babbala yake kamar ruwa ga wani irin guda kuma shi ba na jini ba.

Haka ta baje yashe agefen wani karamin rafi tamkar gawa.

Kusan awa guda tana haka.

Wata tsohuwa dake kauyen ta fito diban ruwa a rafin kawai ta ci karo da ita.

Da farko sai da ta razana har tana komawa baya kafin tayi jarumtar zuwa ta tsaya tana kallon Deejerhn.

A hankali ta kai hannunta ga hancinta ta ji tana numfashi kadan kadan , hakan yasa ta ajiye tulin ruwan nata a gefe ta fara kokarin daga Deejerh da taga baza ta iya ba,da dabarata ta jata zuwa karamin dakinta na jinka, ko daga wajen dakin kadai mutum ya gani zai fahimci cewa akwai tsantsar talauci anan bare kuma a shiga ciki ita kanta katifar ta kara ce kuma duk ta cinye ta gama sakewa.

Haka ta kwantar da Deejerh kan shimfidar ta fita cikin kauyen ta tsinto wasu ita ce , sannan ta kara komawa cen inda ta dauko Deejerhn ta rufe gudaji da jin da kasa.

Bayan ta koma dafasu tayi kan huta, ta dan diba ruwan kadan tasawa Deejerh a goshi.

Cikin minti biyar ta farfaɗo idanunta sun bude amman bata cikin hayyacinta.

Tsohuwar ta dagata ta dura mata ruwan maganin.

Take ta fara wata irin zufa gabadaya ta jiƙe, ga jini na kara zuba ta sankare take ta kara sumewa.

Da gudu tsohuwar ta fita ba inda ta nufa sai gidan Dr Ali

★★Dr Ali Tsohon babban likitane a birnin Paris da ya yi ritaya hakan yasa ya dawo kauye da zama domin taimakon mutanan karkara da ke shan wahala.

Tana zuwa ta sanar da shi cewa tayi bakuwa kuma bakuwar bata da lafiya tana bukatar taimakon Gaggawa da saurin sa kuwa ya bi bayanta suka je gidan.

Bayan sun shiga ya fara duba Deejerh kuma ya tambayeta yadda akayi ta samota da yanayin da take ciki.

Ta fada masa komai.

Ya kara dubata kafin ya ce, "a yanzu gaskiya bazan iya gane meke damunta ba sai anyi scanning tukunna."

"Ehto Don Allah ayi aceci rayuwar baiwar Allah."

Kai tsaye ya tashi yaje ya kira sauran yaran da ke tayasa aiki suka kaita karamin dakin da tanada domin yin duk wani abu da ya shafi kiwon lafiya.

Ba bata lokaci ya mata scanning bayan ya yi yake sanar da tsohuwar cewa

."Ectopic pregnancy ne."

Tsohuwar ta ce, "kamar ya kenan?"

Dr Ali ya ce, "Ciki a bayan mahaifa ke nan, shi ne pregnancy outside the uterus.Ciki ne da ake samun shi a bayan mahaifa a maimakon a samu ciki a cikin mahaifa wannan shi kuma a bayan mahaifa yake zama.

Amma mafi akasari idan ya fashe ne ko mu ce idan ya yi rupturing shi ne ake samun ciwon ciki mai tsanani da kuma zubar jini sosai.Ana yin theater a cire shi wanda ake cewa Ex-lap, aiki ne da za a buɗe cikin gabadaya sannan a fito da abin da ake son fitowa, saɓanin Cs da mafi akasari an san a inda yaro yake kwance ana buɗe cikin direct za a tafi cikin uterus ne a ciro ɗan.Amma shi na Ectopic yawanci sai an buɗe cikin ake lalube a gano a inda cikin ya maƙale dama ne ko hagu, sama ne ko ƙasa. Shi ya sa ake cewa aikin Ex lap So yanzu akwai bukatar yi mata aiki cikin gaggawa domin tseratar da rayuwarta in hakan bai samu kan lokaci ba zata iya rasa rayuwarta duk da cewa yin aikin ma ban da tabbacin samun lafiyarta a yanzu amman adai gwada fiye da cewa an zauna."

Rawa jikin tsohuwar ya fara tausayin Deejerh ya gama mamaye zuciyarta.

Gadan-gadan ya fara yi mata aikin yana kokarin cetonta duk da cewa ya mata allura amman sai wani irin numfashi take sama-sama yana ta sauri har ya kammalawa kenan numfashinta ya tsaya cak.....

Jiki a sanyaye ya fita ya tarar da wannan tsohuwar na kai kawo ta gagara samun nutsuwa ya ce, "Ma'am Am Sorry to say wannan da mai rayuwa ba ce,ga dukan alamu ta sha wahala sosai kuma ta zubar da jini Sosai."

Gabanta ne ya yi mummunan faduwa ji ta ke tamkar jinin ta ce Deejerh.

Za ta yi magana kenan wani ya fito yana fadin, "Papi tana motsi numfashin ya dawo."

Da sauri dukan su suka shiga ciki.

Cike da mamaki kuwa Deejerh ta dawo numfashi.

Dr Ali ya ce, "Alhmdu Lillah an tsalleke rijiya da baya tabbas Ubangiji shi kadai ya barwa kansa sanin da yasa Numfashin wannan baiwar tasa ya dawo."

Gyarata ya yi, ya duba jinin jikinta sannan yasa yaransa su bincika ko suna da irin jinin.

Cikin sa'a aka samu jinin ba bata lokaci kuwa aka sa mata, wani irin barcin wahala take.

Sai da Deejerh ta kwana uku cir tana barci.

Kullum sai Ma'am ta je ta dubata ta yi mata Adduo'i kafin in dare ya yi ta koma gidanta.

Karfe tara na safiya Ma'am na zaune ta kurawa Deejerh idanu

Kamar wasa ta fara motsawa tana kokarin bude ido.

A hankali ta bude idanunta babu abun da ta fara cin karo da shi sai hangen kanta tayi lokacin da mazan nan suke binta.

Zubura tayi tana rike kai tare da kokarin gudu.

Da hanzari ta tashi ta riƙeta tana fadin, "Aa zauna ki nutsu ki nutsu kinji."

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta idanunta kan ma'am kafin tayi ajiyar zuciya ta koma.

Ma'am ta gyara mata kwanciyar tana, "karki tashi kinji babu abun da zai sameki ina zuwa ko."

Tana fita gun Dr Ali papi ta nufa ta sanar da shi Deejerh ta farka, ba bata lokaci kuwa yazo ya dubata sai da ya tabbatar jikinta ya yi kyau kafin ya ce, "za ku iya tafiya gida yanzu amman ga magungunanta nan wa inda zatana sha saboda cikinta zaina dan mata ciwo kafin a hankali ya daidaita."

Deejerh kam bata cewa komai binsu kawai take da kallo.

Godiya sosai ma'am ta yi masa sannan ta kama Deejerh tare suka tafi .

Suna zuwa ta gyara mata waje ta shingida sannan ta haɗa mata ruwan tea mai zafi ta bata ta sha.

Deejerh ta ce, "nan ina ne ? Waya kawo ni?"

Ma'am ta ce, "Tsintarki nayi bakin rafi shine na kawoki nan ina zakije?"

Deejerh ta ce, "na rasa wayata da jakata bayan na sauka daga jirgin kasa kuma anan ne zan kira wacce nazo gunta."

Murmushi Ma'am ta yi kafin ta ce, "karki damu zaki ci gaba da zama anan har ki samu wacce kika zo gunta, ni daya ce anan ban taba haihuwa ban da 'Ya kuma mijina Allah ya yi masa rasuwa zaki zama kamar 'Ya gareni?.

Deejerh ta yi shiru batare da ta ce komai ba, ganin cewa tana cikin yanayi na damuwa yasa Ma'am ta yi shiru ba tare da ta kara tada mata zancen ba.

Haka Deejerh ta ci gaba da zama anan su biyu Ma'am na bata kulawa sosai sannan shi ma papi Dr Ali ya kan zo da kan shi ya dubata har ya kai ga ta fara sakin jiki da su.

Amman lokaci zuwa lokaci yanayinta na sauyawa hakan yasa ya cire mata lokaci a kullum ta kan je gunsa domin ya yi mata Therapy kuma ya tabbatar mata da cewa tana dauke da OCD kuma ta amince da hakan tare da ɗaukan dukannin shawarwarin da yake bata.

Har ya kai ga ya sata a Therapy group dinsa domin kara samun horar yadda zata kula da lafiyarta bisa ga lalurar da take dauke da shi.

Ranarta ta farko ga zuwa group din ya gabatar da ita ga sauran group members dinsa sannan ya ce, "Kasancewar maza da mata duk an tattara anan dalilin wannan bakuwar akwai wani sako da nake son sanarwa mai mahimmanci garemu gabadaya, wanda rashin kiyayewa babbar illace ga rayuwarmu da ta matanmu, magana zanyi akan lura da duk wata mace mai juna biyu ko ince ciki kai tsaye, wasu mazan na da kyashin bawa mace kulawa tare amince mata kan cewa tana zuwa asibiti domin duba lafiyarta har yanzu wannan jahilcin na yawo aranmu na cewa ai da kakanninmu basu san asibiti ba kuma babu mai duba su har suke haihuwa lafiya, yanzu fa daban abincinmu ma da yanayin rayuwar mu ya canja dole duk sanda kida ya canja ya wajaba rawa ma ya sauya salo, a daure a dunga zuwa asibiti domin yin awu a tabbatar da cewa ciki da abun da ke ciki na cikin koshin lafiya rashin yin hakan kan iya sawa in wata matsala ta taso a karshe a gagara magancewa musamman yanzu da ake yawan samun matsalar zaman ciki a bayan mahaifa in wannan abun ya afku da yawa mata rasa rayuwarsu suke kai tsaye in ma ko sun rayu su kan sha bakar wahala sosai kafin komai ya daidaita kamar dai Deejerh har na fidda rai da numfashinta sai kuma ya dawo bayan ya dawo dinma saida ta yi kwana uku cir sume kafin ta farfaɗo mu daure mu cire son zuciya, ƙyashi da jahilci mu nemi lafiya domin gujewa afkawa kogin nadama."

Wata matashiyar mata ce ta daga hannu da alamun tana so tayi magana, papi ya bata dama ta ce ,"Na gode sosai,kuma na ji dadin wannan tunasarwan taka domin hakan ya faru ga 'Yata 'Yar cikina har ya kai ga ta rasa ranta wanda kuwa babban abun shine ba mu yarda da batun zuwa awu ko lafiyar mai ciki ba, duk da cewa komai Allah ne mai yi amman wani lokacin sakacinmu ne sanadi, da haka nima ina kara shawartarmu duka yan uwa mata da maza kada ayi wasa da lafiyar duk wata mace mai juna biyu."

Tana gama jawabin suka tafa mata dukanin su sun nuna jin dadinsu da kuma amincewa da maganar papi kafin suka tsunduman cikin Therapy dinsu.

Bayan sun tashi kai tsaye Deejerh ta koma gidan Ma'am.

Tana zaune tayi tagumi ganin cewa kayan abincinsu ya kare kuma gashi inda take aiki sunyi tafiya bare tasa ran samun albashi.

Har ta shiga ta zauna Ma'am bata sani ba tsabar ta shiga duniyar tunani ga babban tashin hankalinma ko gawayi da icen da zasuyi girkin ma in an samu hatsin babu.

Ta zauna shiru tsawon minti guda Ma'am bata lura da ita ba.

Deejerh ta tashi ta dafata tana fadin, "Ma'am lafiya,m baki ganni ba? Ko da ba kya jin dadi ne?"

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta ta kalli Deejerh ta ce, "Ayyah har kin dawo? Kuma kina jin yunwa ko? Tunani nake yadda zan samo miki abincin da zaki ci komai namu ya kare gashi ban da kudi."

Deejerh ta ce, "aa karki damu nikam ma bana jin yunwa Bakin da Allah ya tsaga ai bazai hana shi abinci ba."

Ita dai Ma'am bata gamsu ba damuwar ta ta inda zata samowa Deejerh abinci ne.

Deejerh ta tashi ta fita kofar dakin nasu tana kallon waje dake kusa suke da bola ana zubda kayayyaki da yawa.

Sai da ta tsaya tayi tunani na tsawon mintina kafin ta je ta dauko wani bawun ta diba irin diddigar gawayi wanda yake zuwa a karshen buhu da aka zubar a sharar ta zuba ciki, sannan taje can gefe ta diba kashin shanu ma dan daidai ta zuba, can gaba kuma inda kafintoci suke ma taje ta diba dos irin sauran sharar da ake cirewa jikin katako.

Ta hada su waje guda sannan ta koma.

Tana komawa ta diba ruwa ta zauna zata zuba kenan ma'am ta fito tana fadin, "Aa wannan kuma fa?"

Deejerh ta ce, "zan gwada yin gawayine in ya yi sai muna saidawa muns cin abinci kuma muma muna girki da shi kinga mun huta da siyan abun girki ko?"

Ma'am ta girgiza kai, "To fa zan ga ikon Allah, Allah Ya tabbatar da Alkairi amman wa innan duk sharace ai abun da ake zubdawa kika dauko."

Deejerh ta yi Murmushii, "wani abun sai an gwada za aga amfaninsa."

Ta kwaba da ruwa da dan kaurinsa yadda zai iya hade jiki, sannan taje kan wani dutse tana mulmulawa kananan tana sawa har ta kammala.

★★★dake garin da rana sosai ba jimawa ya bushe bayan ya bushe Deejerh ta kulla a ledoji ta daura a Faranti sannan ta diba wani ta zuba cikin murhunsu tana kunnawa kuwa ya kamu Ma'am na ta kallo cike da mamaki aranta ta ce, "Ikon Allah ka ga yar baiwa."

Deejerh ta zuba ruwa a tukunya ta daura sannan ta kalli Ma'am ta ce, "Ma'am kin ga ya kama zanje in saida wannan in an samu masu saya sai mu samu kayan abinci."

Ma'am ta kalleta cike da tausayawa ta ce, "Shikenan Allah ya tsare mun ke,ya dawo da ke lafiya."

Deejerh ta amsa da "Ameen." Kafin ta fita.

Haka ta dunga zagaya kauyen tana neman su siya amman fir suka ki har wasu na bige farantin suna xubar mata,haka ta kwashe ta ci gaba da tafiya suna zaginta da fadin cutar su zata yi taya ma za ayi wannan abun ya yi girki ban da rainin hankali.

Tana cikin tafiya ta hadu da Dr Ali Papi ya tambayeta mene ne wannan

Ta sheda masa cewa gawayi ne tayi take talla ko za asamu mai siya .

Ya ce, "kin tabbatar kuma yana kamawa?"

Deejerh ta ce , "E ko kafin in fito ma na kunna kuma ya yi yana ci ma."

Papi ya ce, "ok shikenan nawa nawa ne?"

Deejerh ta ce, "€5 ne."

Ciri €50 ya yi ya mika mata.

Godiya sosai Deejerh ta mai har tana durkusawa

Papi yasa mata albarka sannan ya ce, "In sha Allah zaki samu masu siya in an gano kinji karki damu."

Aiko yana tafiya ta jura aguje kasuwa ta yi masu siyayyan kayan abinci ta koma ta kaiwa Ma'am.

Ma'am na ganin ta rike da kayan abinci batasan lokacin da ta fashe da kuka ba tana kokarin faduwa, Deejerh tai saurin......

Rungumeta.

Hawayen da ke sauka daga idanun Ma'am tai saurin gogewa tana fadin, "Allah ya miki Albarka Deejerhtou na, Allah ya kara haskaka rayuwarki da hasken sa, Allah ya tsaremun ke gaba da baya,zahiri da badini, tabbas ban yi rashin haihuwa ba, Ubangiji kadai ya san dalilin Kasancewarmu tare anan,kuma ina fatan hakan ya dauwama cikin Alkairi."

Deejerh ta ce , "ki daina kuka ni bana so kina kuka bana so hawayenki yana zuba."

Murmushi Ma'am ta yi ta ce, "Ai indai dake ba zan yi kuka ba,sai dariya inma na yi kukan sai dai na farinciki domin ke haske ce mai haskaka duhu, kuma inuwace mai dauke rana,sannan ruwa ce mai maganin kishi,ina sonki kinji Deejerhtou na."

Abinci Deejerh ta daura masa, har saida ya yi,ta zuba masu ita da Ma'am suka ci suka koshi sannan ta gyara komai tas tamkar babu abun da aka taba kamar yadda ta saba.

★★★

Kamar wasa a kwana a tashi har yan kauyen sun gane inganci da saukin dake tattare da gawayin Deejerh,hakan yasa har tururuwan siya ake sosai da tayi yake karewa ,wasu har kamawa suke su bada kudi kan tana yi a aje masu.

Saidai kuma ta fara