5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN

CHAPTER 17

by @xayyeesherthulhumaerath

daya za a mata a fahimci halin da take ciki na tsantsan jin dadi.

Sai da ta kammala komai kafin ta fito cikin shigar ta, kayan ba karamin kyau sukai mata ba,tamkar a jikinta aka tsara su, kyan su da nata sai ya haɗe waje guda ya bada wani salo.

Ta yi wa Ma'am sallama, ta fita fuskarta dauke da murmushi tana tafiya cikin nutsuwa zata je gun Ammar su tafi dake papi ya ce Ammar ne zai kaita.

Tana cikin tafiya kamar daga sama taji an zubo mata abu ta baya, daga kan da zata yi gabadaya kasan wandonta ya baci da ruwan laka har ya fara taba rigar ma.

Abdu tsaye da bikiti yana yi mata dariya cikin issa da izza.

Ji tayi zuciyarta ta fara daukan zafi,kamar zata durkusa sai kuma ta tashi ta karasa gabansa yana ci gaba da dariya tare da fadin, "Haba mana karkiyi kuka mai gawayi ai ba gawayi aka rasa masu siya ba ko? Ki je ki canja wasu kayan kar ki makara don wa innan kam sun gama." Ya fada yana taba mata kasan riga.

A fusace tayi wani juyi ta sake masa mari a fuska, ta kara daga hannu ta sake masa biyu zafafa a jere.

Ya ma gagara motsawa kawai yana kallonta hannunsa dauke kan kumatu.

Daidai lokacin Ammar ya fito kenan sai da gabansa ya yi mummunan faduwa.

Zuciyar ta a tsorace take tana bugu amman a zahirance ta dage wajen bayyanar da jarumtarta.

Da sauri Ammar yaje yana janyeta gefe, "ke baki da hankali ne? Lafiyar ki? Me yasa zaki maresa? ke baki san halin shi ba ko?"

Deejerh ba ta ce masa komai ba, Abdu ya kalleta ya yi kwafa ya tafi.

Yana tafiya ta kalli Ammar ta ce, "mu koma gidan Ma'am in gyara kayana.

Ammar ya kalleta sama da kasa kamar dariya zata subuce masa sai kuma ya make ya ce, "gyara? Mu je, wannan kayan ai saidai a cire sa kuma ya gama aiki."

Bata ce masa komai ba har suka koma,suna shiga Ma'am ta tashi da sauri cike da mamaki tana tambayar me ya faru.

Atakaice Deejerh ta ce, "Abdu ne ya bata mun kaya."

Daga nan bata ce komai ba ta shige.

Sai da Ammar ya ga ta shige kafin ya bawa Ma'am labarin abun da ya faru yana.

Har lokacin mamakinta yake ta yadda akai ta mari Abdu ba tare da nuna shakka ba kuma ta ci gaba da harkar da ke gabanta.

Tana shiga ta cire wandon ta dauki almakashi ta yanke gabadaya wajen da ya bata mata, sannan ta kara bi ta fidda kasan ya zama kamar star kananu ta dauki golden din zare tasa a jikin allura ta dunga bin bakin stars tana dinkewa da zaren kan kace miye ta kammala wando ya fita da wani style din.

Rigar ma dake iya bayane ya taba kuma kadan nan ma yankewq ta yi ta maida stars din ta bi.

Da sauri sauri ta yi cikin minti 20 ta kammala, tana fita Ammar da Ma'am suka kura mata idanu cike da zillimun ina ta samo wasu kayan.

"Wa innan kayan fa? Daman kina da wasu ne?"

Cikin Murmushi Deejerh ta ce, "Sune fa na gyara." Ta fada tana juyawa.

Sannan ta kara fadin, "Ammar mu tafi ka ji mun makara fa."

Kafin ma'am tayi magana ta mata kiss ta na kara rataya jaka ta fice, Ammar ya bita shi ma da gudu suka tafi.

Suna tafiya yana mata surutan da ya saba.

"Amman ko kinga yadda kika yi kyau? Har ma fa kin fi dazun nan wallahi, da Abdu zai ganki yanzu ina ga suma zaiyi,ni na fara ma tunanin fa sonki yake ysn kish....

Idanunta da ta sauke kan nashi yasa ya yi saurin dakatar da karasa maganar ba don ya so ba, ya wayance da in-ina yana, "Umm ba wani kyau ma kika yi ba ai kawai kayan ne ya sa miki kyau,kayan ne masu kyau ba ke din ba."

Har suka isa shi kadai yake kidansa yake rawansa.

Tun daga Gate din Stylish Wordplay fashion School za ka fara hango yan kwalisa maza da mata , isassu kuma yaran isassu masu jini a jika, daga zafafan motoci sai irin mashin dinnan kananu irin na matan da suka amsa sunansu mata.

Kallo Daya Deejerh ta yiwa Get din da mutanen da ke shigar sa gabanta ya yi wani mummunan faduwa.

Ammar ya fahimci hakan ya kalleta kafin ya ce, "Kisa aranki zaki iya abun da kikazo yi,ba ruwanki da mutanen wajen, ba ruwanki da yanayinsu,ba ruwanki da sun fiki gata ko wani abu dukkanin mu daidai muke wajen Ubangiji, na san ba za ki karaya ba,ke jaruma ce, amman kara jaddada miki cewa kisa aranki za ki iya, zaki iya da rayuwarki, zaki gina rayuwarki da tafin hannunki, zaki kunnawa rayuwarki haske da fitilar zuciyarki, ka da kisa tsoron kowa aranki, kinji."

Maganganun da Ammar ya mata sun matukar shiga jikinta hakan yasa ta sake masa murmushi tana ajiyar dogon numfashi.

Shi ma ya maida mata da martanin murmushiin kafin ya ce, "mu je ko."

Ta girgiza masa kai.

Suna zuwa gun Gate din suka nuna pass din da papi ya basu sannan aka barsu suka shiga.

Dake Ammar yasan gurin kai tsaye yaje ya nufi office din Mr Jacques.

Bayan an basu izini sun shiga har sun zauna ma kafin Mr Jacques ya shiga kasancewar ya fita.

Idanunsa akan Deejerh ya fara sauka, ya tsaya yana kallonta magana Ammar ke masa amman ina, hankalin sa na kan Deejerh.

Ita kuma ganin yadda yake bin surarta da kallo yasa ta tsorata jikinta ya fara rawa.

Ammar ya ce, "Barkanmu dai Yallabai , Yallabai, Yallabai."

har sai da ya fada sau uku kafin ya kalli Ammar yana murmushi, "amman dai Design din kayan yarinyar nan ya yi matukar kyau ya ƙayatar dani,da gani za a so shi sosai a kasuwa."

Sai a lokacin Deejerh ta yi ajiyar zuciya aranta tana hamdalar godewa Allah da ya kasance kayan jikinta ne ya birge shi ba,surarta ba.

"Kodayake ba ma kayan ba har mai kayan za aso da alama." Mr Jacques ya fada cikin sigar tsokana yana dariya kafin ya kara fadin , "na ga duk kin tsorata nan ba ma cin naman mutane sai na dabbobi kinji, Welcome to stylish Wordplay fashion School Girl."

Ya fada yana mika mata hannu.

Hada hannunta biyu tayi ta sunkuya ta gaisheshi.

Cikin fara'a ya amsa tare da fadin, "Allah ya yi albarka yasa anzo asa'a."

Ammar ma ya gaida shi, kafin ya ce, "Ya Dr Ali ina fatan yana lafiya?"

Ammar ya ce, "lafiya lau ya ma ce agaidaka."

"Ma sha Allah. Hakan ya yi kyau." Ya kalli Deejerh ya ce, "Girl Da gaske design din kayan ki sunyi matukar kyau Dr Ali ya ban labarinki ina fatan mu ga mafiyin hakan a tattare da ke."

Kanta na kasa ta ce,"In sha Allah Sir."

Mr Jacques ya ce, "Alright Ammar yanzu kai zaka iya tafiya, ke kuma muje ki shiga Class don yanzu ma na an fara."

Tare suka fita Ammar ya tafi su kuma suka nufi Class din.

Jiki na dari dari Deejerh ta shiga ganin yadda duk suka jura mata idanu ana yi mata kallon tara saura kwata.

Class din irin seat mai mutane bibbiyu ne,ya kasance wata a gaba ita kadai Mr Jacques ya ce Deejerh ta je nan ta zauna.

Tana zama suka hada ido da dayar yarinyar ta sake mata wani kasurgumin tsaki tana janye jikinta tare da nuna ƙyama.

Haka Deejerh ta zauna a takure gam da jikinta.

Ita kuwa ta gefen nata Esme sai tsaki take tana kananun mita, har saida ta dauko turare a jakarta ta ta fesa, sannan kuma ta dauki facemasks tasa ta toshe hancinta.

Deejerh na lure da ita amman ta kau da kai tana bin karatun da ake yi masu kawai.

Ana cikin yi malamin nasu ya yi bayanin yadda yake fidda shape din wando jeans na mata, bayan ya gama ya ce ko da wacce zata iya kwatantawa kafin shi ya yi?

Dukkaninsu shiru suka yi har zai wuce Deejerh ta daga hannu jiki a sanyaye.

Ya ce ta tashi taje gaban Whiteboard dinsu ta gwada, kamar wacce akama duka haka take jan kafa har ta karasa.

Cikin zuciyarta na son yi amman a zahiri a tsorace take.

Ko da ta dauki maker dinma hannunta rawa ya fara, tana fara zanen ya karkace yaki tafiya daidai.

Ji tayi kawai gabadaya class din sun kwashe mata da dariya.

Ta daga kai ta kalli zanen, rufe idanunta ta bude, kafin ta ci gaba kan wanda ya karkace din.

Maganganun da Ammar ya fada mata ne kawai ke mata yawo a zuciya tana zanen.

Sabanin dariya da suke yi mata sai kuma ta ji an bige da tafi.

Ita kanta mamakin yadda akai ta zana take bare su kuma.

Malamin ya karba maker hannunta yana, "yau dai kam an bana mamaki rana ta farko da students dina ta yi Designing ba tare da na koya mata ba,kuma design mai wahala domin da dama har maimaicin aji ake samu akan wannan bangaren, can't believe this."

Ya kalli Deejerh kafin ya ce, "Mene ne Sunanki? Daga ina kike?"

Take idanunta suka cicciko hawaye na shirin fara yi mata ambaliya.....

Laurent ya ce, "Oh Kukan na mene ne? Alright Sorry, Sorry ,sannu kinji , je ki zauna."

Ya fada yana lallashinta da hannu.

Share hawayen da ke fuskarta ta yi, ta saki murmushi ta daga kai ta kalleshi tare da fadin , "Sunana Khadeeja-Deejerh."

Tana fada ta juya ta je ta zauna a seat dinta.

"Nice Name, Weldone Deejerh,ina fatan wannan ya zama shine mataki na farkon ci gabanki ba tare da kinsa wasa ba."

"In sha Allah." Ta furta a zuciyarta.

Laurent ya ce, "Gaskiya yau ina farinciki matuka,infact ma I'm Speechless, sai nake ji a jikina cewa wannan set din naku zai kasance na musamman da ba a taba yin masu hazaka irinsa ba, na ji cewa zan so ku fiye da yan baya, ina fata addu'ar cewa Allah yasa kar ku bani kunya."

Esme ce karaf ta ce, "Oh Sir ba za mu taba baka kunya ba, wannan 'Yar talakawan ma ta yi abun arziki bare mu."

Ta fada tana yiwa Deejerh kallon tara saura kwata.

Shi ko Laurent cewa ya yi, "Za dai mu gani ai."

Daga nan ya yi masu design din da kansa ya nuna masu, sannan ya cirewa Deejerh inda ya kamata ta dan gyara domin daidaiton tsayuwar wandon.

Bayan sun gama ya basu Assignment kan kowa ya je gida ya yi ya tawo da shi next Class.

Duk da cewa Deejerh a takure take,amman ta ji Dadin karatun matuka kasancewar abun da takeso ne,kuma muradinta take cikawa.

Ana tashi ma haka ta fito zata fita kenan daga Class din Esme ta bangajeta har sai da ta kusan wuntsilawa, ta kalleta tana tauna cingum tare da daga keyn mota a hannu, ta kara sake mata wani kallon banza dauke da tsaki tana, "Poor Girl." Ta wuce cikin takunta na kasaita.

Deejerh ta kau da kai kawai ,ta tashi ta na karkade jikinta ta fita daga School din.

Ta kama hanyar komawa gida, ta yi nisa sosai har ta fara shiga cikin Dajin da zai sadata ga kauyensu, ba kowa shiru ban da kukan tsuntsaye da sautin iska bishiya babu abun da ke tashi.

Tana cikin tafiya ta bayanta kawai taji an zungureta, a zabure ta juya, bata ga kowa ba, ta ci gaba da tafiya cikin sauri,aka kara tabata,

Na ukun tana juyowa ta saki ihu idanunta rufe shima Ammar ya firgita kawai ya saki ihu.

Duka su biyu suka gauraye wajen da ihu.

Sai ita ce ta fara rage sautin nata a hankali ta bude ido kawai ta gan shi ya zake sai ihu yake.

Ajiyar zuciya ta yi tana tsaki,ta duba gefenta ta ga wani icce ta dauka ta maka masa a jiki.

A hargitse ya bude ido ya na waige-waige.

Deejerh ta kara yin wani gajaren tsaki kafin ta ce, "Jarumin jarumai anji jiki, wato madadin ka ban tsoro sai tsoro ya koma kanka?"

Hannu yasa yana sosa keya cikin wayancewa ya ce, "ba wani nan, nima na tayaki ne kawai amman akan me zan tsorata ma."

Kallon shi tayi kawai ta yarda iccen hannunta ta ci gaba da tafiya, ya bi bayanta yana fadin, "ke kin ma gode ai da nazo da yanzu wani dodo ne zai kamaki ya cinye gani na yasa ya gudu."

. Deejerh ta ce, "Umm."

Ya kara fadin, "Fatan komai dai lafiya? An yi karatu lafiya an kammala lafiya?"

"Alhmdu Lillah." Ta furta a gajarce.

Suka ci gaba da tafiya har suka shiga cikin kauyensu.

★★★★Mexico.

Zaune take tana danna Wayar da ke hannunta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,ga dukkan alamu ta ji dadin zaman da tayi,domin ban da murmushi babu abun da ke sauka daga fuskarta.

Nocking kofar da aka yi ne yasa ta daga kai nan da nan fara'ar da ke fuskarta ta dauke tana sakin karamin tsaki tare da fadin, "Yes Shigo."

Zayd ne yana zuwa ya rungumeta ta yi saurin janye jikinta.

Ya kalleta yana, "Mon Cherie ya haka? Kamar baki ji dadin zuwa na ba."

Tabe baki ta yi kafin ta ce, "Umm hutawa nake,kuma kasan in ina hutawa bana son takura sam." Ta karasa maganar tana kara shingidewa jikin kujerar.

Fuskarsa a raunane ya ce, "Me yasa kike mun haka ne Mon Cherie? Kin san bana jure zama ba tare da na ji motsinki kusa dani ba , ban san me na miki ba kike azabtar dani, Please ki fadamin in gyara, ina son farincikinki ina son ganin farinciki a fuskarki ina son kasancewa da ke."

Ya fada yana durkusawa gabanta tare da rike mata hannu.

Hannunta ta janye a hankali tana kara yatsina fuska.

"Nothing fa, ni kawai na fada ma hutu nake so Shiyasa bana son takura,kai kuma ka cika takura da naci wallahi."

Zayd ya ce, "shikenan zan yi kokarin ganin ina baki tazara in har zakiyi farinciki,amman ki sani ni zan cutu a cikin zuciyata,ban da burin da ya zarce ace na malleki, a yanzu kullum cikin fargaba da zillimun rasaki nake, ni dai fatana Don Allah karki barni......

Zata yi magana kenan sai ga wani ya shigo dakin.

Da sauri ta tashi ta rugume shi tana kai masa kiss

"Welcome baby, ina ta jiranka kasa na shirya tuntuni kaki zuwa ko?"

Ta fada cikin shagwaba.

Shi ma kissing din nata ya shiga yi na Tsawon minti guda kafin ya ce, "Sorry Beb sai da na biya office na aje wasu document ne, yanzu dai zamu iya tafiya ko?"

Ta ce, "Yes."

Sannan ta kalli Zayd da ya yi mutuwar tsaye ko ince suman tsaye ban da zufar takaici babu abun da yake , yana huci.

Ta ce, "Zayd zamu fita da Beb in mun dawo da dare zan kiraka ko? And please in ba abun da zaka yi,kadan gyara mun dakin kafin ka fita ko kuma ka kira cleaner."

Tana fada Wancen din ya dauketa cak tana dariya suna wasa suka fice.

Ji Zayd ya yi kamar zuciyarsa zata fashe tsabar zafi da kishi, idanunsa suka kada suka yi jajir , Gabadaya jikinsa ya fara rawa.

Bai san lokacin da ya fara buga kansa da bango ba har sai da jini ya fara bulbula daga goshin shi, ya kwashe kusan minti biyar a gidan yana fama duk ya hargitsa kansa ya ciwo kuma ya hargitsa gidan, daga karshe haka ya bar gidan a galabaice, kai tsaye gidan giya ya nufa ya sha ya yi tatul ya fito yana maye zai tsallaka titi kenan...........

★★★

Paris

Deejerh ta kammala Assignment dinta kuma ta shirya tsaf zata tafi stylish Wordplay fashion School.

Ma'am da kanta ta tashi ta mata Panisses snacks ta sa mata cikin karamin kularsu domin ta tafi dashi, ta zuba mata ruwa a gora, da Apple ganin cewa sai yamma suke tashi dole sai dai mutum yaje da abinci ko ya siya acen bare siya acen din ma sai masu kudi domin restaurant din school din babu kananun abinci na talakawa.

Karba tayi ta rataya jakar ta na yiwa Ma'am sannu da aiki.

Ma'am ta ce, "Adawo lafiya, Allah ya tsare hanya ya bada abun da aka je nema, kisa aranki Ubangiji na tare da ke a duk inda zaki kasance kuma kada ki manta kiyi addu'a kafin ki fita *bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala*

*kuwatan illa billahi* sannan in kina tafiya har ki isa ki lizimci fadin Astagfirullah tare da karato *Rabbie Inniy Lima Anzalta ilayya min khairin* kinji fatan Alkairi Diyar kirki Deejerhtouna."

Suka rungume Juna kafin Deejerh ta yi mata Bye-bye.

Kai tsaye ta kama hanya tun kan gari ya waye kasancewar tafiyar kafa zata yi kafin ta fita daga kauyen ta hau Bus kuma ita kadai ne, Ammar na da aiki agun papi.

Suna zuwa Kuwa kafin kowa ya shiga lecture room sai ya yi submitting assignment.

Hakan yasa ita ma tana zuwa tayi submitting kafin ta shiga.

Yau ma dai kam Esme bata fasa yi mata kallon banzan ba, harda sa abun raba masu zama yadda jikin wani ba zai taba na wani ba, kuma duk bayan mintuna ta dauko turare ta fesa tana kara goge hanci.

2:30 suke fita Break kowa ya tafi Restaurant ita kam Deejerh ta zauna cikin class din ta bude jakarta ta fara cin abinci.

Sautin dariyar da taji yasa ta daga kanta,wasu mata da maza ne tsaye suna nunata suna dariya.

Ta kallesu maimakon taji Haushi kawai ita ma sai ta bi su da murmushiin da ita kanta bata san dalilin fitar sa ba.

Gabadaya sai suka yi dif suna kallon juna yadda ta maida su sune abun Dariyar hakan yasa Dukansu a sulale suka watse.

Ita kam ta gyara zama ta ci abincinta ta koshi ta kora da ruwa sannan ta tashi ta shiga school toilet din tayi alwala ta dawo class din ta keɓe gefe guda fara sallah.

Ta fara kenan suka fara dawowa