5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN

CHAPTER 21

by @xayyeesherthulhumaerath

zaki, ki tsaya mana,ki rufe Idonka Don Allah."

Deejerh ta bisa da wani kallo zata wuce, ya rike mata hannu ta kara daga idanunta sama.

Araunane ya ce, "Please."

Tsayawa tayi tana kallon gefe har lokacin bata sake fuskarta ba.

Ammar ya ce, "to ki sake fuskarki mana,kuma ki rufe ido abu zan nuna miki."

Deejerh ta ce, "Ka ga na dawo na gaji ni fa hutuwa nake so inyi."

Ammar ya ce, "yanzu zaki huta nidai Don Allah ki rufe idon to."

Ta rufe idon duk da haka dai fuska babu walwala.

Tana rufewa ya ciro kwalin wayar da ya boye a bayansa ya mika mata yana, "bude to."

Tana budewa ya ce, "surprise,ban sani ba ko ta miki na dai siyo mana kala daya kuma na san zata taimaka miki wajen binciken wasu abubuwan na School."

Tsabar farinciki Deejerh ta gagara rufe bakinta.

Karban wayar tayi tana budewa cikin rawar murya ta ce, "Subhannallah!

Ya Allah ya akayi ka san target dina? Oh , Thank you so much."

Ta dago ta kallesa shi kafin ta ci gaba da magana, "kalmomin bakina baza su iya misalta farincikin da nake ji a yanzu ba, I'm out of words wallah, na gode sosai Allah ya saka ma da Alkairi da dai fushi nake da kai amman yanzu na sauko."

Dariya Ammar ya yi ya ce, "Amin, kuma Alhmdu Lillah tunda dai kin sauko da kin kumbura kamar sabon bread."

Deejerh ta watsa ma shi harara tana, "kai ne bread din ai."

Kiran sallah aka fara.

Ammar ya ce, "kinga har an fara kiran sallah na tafi masallaci."

Deejerh ta ce, "Adawo lafiya." Tana shigewa ciki.

Tana shiga ta nunawa Ma'am wayar.

Ma'am ta ce, "Ammar ai yaron kirki ne yana da hankali da tunani sosai Allah ya kara inganta maku rayuwa duka."

Deejerh ta amsa da. , "Ameen."

Mexico

★★★

Zayd warewan dole ya yi, damuwarsa Kada huda ta ce zata tafi hakan yasa tun safe ya tashi yake nan nan da ita, hatta abinci cewa tayi ba za ta ci na restaurant ba sai dai shi ya girka mata.

Haka kuwa ya shiga kitchen ya girka.

Tana kwance a jikinsa cikin yanayin kissa ta langwabe a dole har lokacin wai bata gama dawowa daidai ba, jiya ta tsorata sosai.

Zayd ya ce, "Mon Cherie please ki bani dama yanzu, na gaji,na kasa daurewa ,kin fi kowa sanin cewa ban da burin da ya wuce ace na mallake ki."

Huda ta taɓe baki ta ce, "Amman ai gamu tare yanzu ko? So what do you want after this?"

Zayd ya ce, "ki zama tawa,Mine ni kadai,ki daina kula kowa ki dawo rayuwa dani, kullum mu kasance tare shine abun da nake so."

Ta numfasa kafin ta ce, "To da wani kudin? Kasan nidai kuma ba zan zauna a wannan gidan ba."

Zayd ya kalli dakin da suke ciki kafin ya ce, "mene ne aibun nan gidan? Alright shikenan za a nemi wani, wanda kikeso, maganar kudi kuma zan saida mota ta."

Wani kallo ta masa tana mikewa tsam tare da furta, "Allah ya sawake ba ma zai yiwu ba harkar tsiya da karanta kasan bana gun, Saboda mu muka fi kowa son aure ko? Kuma ana yawo dani na auri matsiyaci ko....?

Zayd ya ce, "Matsiyaci kamar ya? Yanzu duk wadatar da nake da bai miki ba,har zakiyi tunanin za a min kallon matsiyaci? Ko da ace yau zan saida duk abun da na mallaka na tabbatar da cewa zan maida su babu haufi, yanzu ma abar batun saida mota ko wani abu, na ji na yarda zan fita in kara neman kudi inyi abubuwan da kikeso har ma da wanda ba kya zato amman da sharadin kin yarda kin amince zamu yi aure babu fashi."

Huda ta ce, "Eheen ni dai kasan ba zan iya rayuwar talauci ba,kuma hakan na daya daga cikin abun da yasa na ki amincewa inyi aure,amman indai zaka yi abun da ya dace ai Shikenan ban da matsala."

Zayd ya ce, "alright ni kuma na miki alƙawari zaki sha mamaki."

Dariya ta yi, "nima zan so sha ai har in koshi ma."

Daukan key din motarsa ya yi,zai fita.

Huda ta ce, "Ah Ina zaka kuma?"

Ya amsa da , "Neman arziki." Yana karasa fada ya fita ba tare da ya jira amsarta ba.

Dariya Huda ta yi tana tashi daga kan gadon tare da fadin, "Wahala bata isheka ba."

Wayarta ta ciro ta gyara zama tare da fadawa duniyar chatting da samarinta harda video call.

★★★Paris.

Ba karamin Jin dadin wayar nan Deejerh ta yi ba domin har ta fara bincike kan design tana kara duba abubuwa sosai musamman wa inda bata fahimta ba.

Wasa wasa Ammar ya fara kwarewa MMA training duk abun da Deejerh ta ce ya yi , ya kan yi kokarin yi ba tare da haufi ko tsoro ba, acewarta yanzu ne ya ke kokarin zama Namiji amman ada muna namiji ne.

Kamar kullum yau ma training din suke Deejerh ta gaji cikin Nishi ta ce, "ka ga ni kam na gaji ga wani barci da nake ji na dawo School ban wani huta ba zan je in kwanta."

Ammar ya daga kai yana kallonta, "ki tsaya wasa in fi ki karfi wallahi naga alamar so kike ki zama raguwa."

Gajeran murmushi Deejerh ta yi ta ce, "yoo ni ko da ace zan yi wata guda ban yi training din nan ba,ai ban jin cewa akwai abin da zai iya shan gabana in gagara, kawai dai stress ne ya mun yawa, so ina bukatar hutu Don haka jarumi kuma mazaje masu ji da karfi sai a kwana anayi." Ta fada tana kokarin tafiya.

Tashi ya yi da gudu ya sha gabanta yana, "cab yaushe zan ci gaba ni daya ba ke,ni ma na hakura hakan , Allah ya kaimu gobe."

Deejerh tai dariya, "mazaje to kar dai amanta da addua,na ma tuna bara in baka wannan,ka daure kana yi kullum kafin ka kwanta, "Subhanaka Allahumma rabbiy bika wada'atu

janbiy wa bika arfa'uhu, in-amsakta nafsiy

fagfir laha, wa-in arsaltaha fahfaz'ha

bima-tahfazu bihi ibadas-saliheena"

Ma'anar Addu'ar ita ce

(Tsarki ya tabbata gareka ya Allah, da sunanka na

kwantar da hakarkarina kuma da sunanka nake

tashinsa, idan ka karbi rayuwata, to kayi mata

gafara, idan kuma ka saketa, to ka kiyayeta da

abinda kake kiyaye bayinka salihai) ka ga kenan Addua ce mai mahimmaci da kuma tasiri sannan ka da ka manta da yin alwala ma kafin ka kwantan."

Ammar ya yi murmushi ya kalleta ya ce, "Na gode sosai , In kina fada mun wasu kalmomin sai inji tamkar mahaifiyata ce gabana, aduk wani abu da zaki nusar na Alkairi ba kya shayin fadi, zan yi su In sha Allah kuma ina godiya matuka."

Suka yi sallama ya tafi ita ma ta tafi.

★★★ Stylish Wordplay fashion School.

Tun abun da ya faru ranar jikin Esme ya yi sanyi akan Deejerh ,ko sakewa ba ta iya yi bare mata wani mummunan kallo.

Ita kuwa camellia suna hada ido da Deejerh ban da gira babu abun da take daga mata,har sai da ya Deejerh ta gaji ta daina daga kai.

Students sun cika class din da surutai tamkar kasuwa kowa da abun da yake,sabanin Desk din su Deejerh da Esme da dukaninnsu biyu suka mika hankalin su ga waya.

Ranar basu da lecture da Mr Laurent sai Mr Anthony.

Yana shiga Class din ya danna wani ball yana fadin, "Oya One Class Please."

Take suka tsagaita da hayaniyar da suke tare da mika Gabadaya hankalinsu gareshi.

"VINTAGE" Ya rubuta a White Board din nasu kafin ya ce, "Who can Define Vintage for us."

Duk shiru suka yi.

Ya kara fadin, "Nobody?"

Nan ma suka yi shiru.

Ya ce, "Alrigh....

Kafin ya karasa ya ga Deejerh ta daga hannu a hankali.

Team din su Deal da ke gefe suka fara nunata suna magana kasa-kasa.

Mr Anthony ya ce, "Yes,Go On."

Tashi ta yi ta ce, "Definitions. "Vintage" is a colloquialism commonly used to refer to all old styles of clothing. A generally accepted industry standard is that items made between 20 and 100 years ago are considered "vintage" if they clearly reflect the styles and trends of the era they represent."

Tafa mata ya fara yi yana fadin, "Very Good, That's the real Definition of vintage, na san yanzu kowa ya fahimci cewa Vintage na nufin tsofin kaya na da wa inda kakanni ko ince kakannin kakanninmu suka yi amfani da shi kuma har yanzu ana iya kara kirkirarsu har ma ayi amfani da su, yau kuma yanzu ina bukatar kowa ya yi Designing VINTAGE LOOKS Yes ina nufin a zana mun samfuri na tsofin kaya yanzu,kuna da ishashshan lokaci Zan ma fita in barku ku sha iska All I Want Shine in dawo in tarar da Vintage Looks, All The Best." Ya fada yana daga masu hannu tare da murmushi ya fice.

Yana fita kuwa, kowa ya fara ciku-cikun ciro Design Materials dinsa, suka fara, kowa ya fara amman ban da Esme ta ma rasa ta ina zata fara,sai dai ta kalli can,ta kalli nan.

Can Deejerh ta kalleta tayi kasaƙe kawai zaune.

Ta ce, "mene ne ya faru?"

A raunane Esme ta ce, "ban iya ba,ban san ya zan yi ba , na kasa."

Deejerh ta ce, "Alright zan goge nawa, yanzu zanna yi ina miki bayani kina kallo sai kema kiyi, kin gane?"

Esme ta girgiza kai.

Haka Deejerh ta goge nata da take ta fara yi tana yiwa Esme bayani ita ma tana yi har sai da ta tabbatar ta kammala kafin ta kara gogewa ta yi nata ita ma.

Tana gamawa Mr Anthony ya dawo ya na fadin Pen Off.

Suka yi submitting.

An tashi kenan Deejerh zata fita Esme ta taɓata ta baya.

Da sauri ta juyo tana daga hannu a tunaninta Camellia ce.

Sai da Esme ta razana , ta ce, "Sorry, I just wanna Say Thank You."

Murmushi Deejerh ta mata ba ce komai ba kawai ta gyara jakarta a baya ta tafi.

Da sauri ta ke kokarin fita daga Makarantar gudun kar camellia ta biyota.

Tana fita daidai wata karamar kofa bayan an fita a get kawai ta ci karo da team din Mael.

Ga dukkan alamu sun shahu tatil.

Su Bakwai uku sun tsaya gabanta, hudu sun tsaya a bayanta.

Jikinta ne ya fara rawa, kafafunta na kokarin gagara daukarta, ta kalli gabanta, ta kalli bayanta wani Numfashi ta sake tana ajiyar zuciya.

Dariya suka fara yi suna karasawa inda take,tana matsawa suna kara binta har sai da sukai daf da ita.

Daya a cikinsu ne ya fara rike mata fuska yana kissing.

Sauran kuma suka fara shafa mata jiki.

Wasu na lashewa.

Gabadaya tsigar jikinta ya tashi, kwakwalwarta ta fara birkicewa.

Kusan second biyar suna yin abun da suka ga dama ba tare da ta yi kokarin hanna su ba bare tanka masu.

Rufe idonta tayi Sosai, sai ji tayi suna kokarin zare mata kaya, dayan kuma yasa mata hannunshi a mara.

Kara kankame idon tayi ta ja hannunta daidai kan wanda yasa mata a mara ta murda hannun sai da ya yi kara.

Wanda yake mata kiss kuma ta buga goshinshi da nata.

Wanda yake kokarin ja mata sket kafarta ta buga masa a mara.

Sauran ma ta hankada su gabadaya ban da ihu babu abun da suke sakewa musamman wanda yaji bugu a mara da gudu ya bar wajen.

Karkade jikinta tayi ta gyara ta dauki jakarta ta maida baya sannan ta ci gaba da tafiyarta har ta fita wajen taran boss.

Tana zuwa kuwa cikin sa'a ta samu ta hau.

★★Dare kamar kullum zaune suke suna cin Dinner Ammar,Ma'am da Deejerh.

Ma'am ta yi masu Syrian Fatteh.

Ammar sai ci yake yana girgiza kai ya ce, "Ma'am yau kin tuna mun da kasata sai nake ji tamkar acen nake, wannan shine abincin da nafi so, lokacin Mamana tana yawan mun shi sosai musamman da nake karamin yaro kowanni dare shi nake ci a dinner in ba amun shi ba to ba zan ci komai ba."

Ma'am ta ce, "nima ina so sosai gaskiya shiyasa nake yi,wata kawata ce Yar kasarku nima ta koyamun And tunda ta koyamun na yi naji dadinsa."

Ammar ya ce, "Sosai fa ,Sai nake ji kamar yau a syria nake,idanuna na tuna mun da abubuwa sosai na jin dadi da kuma na rashin jin dadi da suka faru, ina fata ace watarana in koma inga kasata ko da sau ɗayane a rayuwa kafin in bar duniya."

Sai a lokacin Deejerh ta daga kai ta kalle shi ta ce, "amman ko yau ba MMA training gaskiya ni labarin Syria zaka ban na ga yadda kaketa kurantata kamar tafi kasata kyau."

Dariya Ammar ya yi, "aiko zan baki labari sosai ma duk abun da kike son sani mu dai gama cin syrian Fatteh."

Sai da suka gama tas, Deejerh ta kwashe kwanukan kafin suka fita tare suka zauna waje.

Ammar ya ce, "Oyaa to me da me kike son sani dangane da syria?"

Deejerh ta ce, "Abubuwa da yawa,amman dai da farko me yasa ka bar Syria din? Sannan Ina Iyayenka da yan uwanka?"

Ammar ya gyara zama ya ce, "to da farko dai ni kadai iyayena suka haifa,na taso cikin rayuwar jin dadi da gata duk da cewa mu ba wasu masu arziki bane,amman muna da rufin da asirin da muka fi karfin bukatunmu domin daga mahaifiyata har mahaifiyana ma'aikatan gomnati ne, silar rashin samun zaman lafiya da tashin hankali aka kashe iyayena da mutane da dama a kasar wanda har saida ya kai ga mu da muka saura wasunmu muka zaɓa yin hijira musamman ga wa inda suka rasa ahalinsu kamar ni dai kinji abun da ya faru."

Jikin Deejerh ya yi sanyi tausayinsa ne ya kamata har cikin ranta wanda sai da yanayinta ya sauya .

Da Ammar ya lura da hakan da ya kalleta sai ya ce, "Amman yanzu gani da wani ahalin ai Ubangiji ya maida mun har ma da 'Yar Uwa duk da dai mummunace amman haka zan lallaba."

Dariya Deejerh ta yi ta ce, "ka ji da shi dai to yanzu fadamun ya Kasar Syria take."

Ammar ya ce, "Syria Kasa ce mai a yanayi,amman tana da yawan mutanen da basa da aikin yi,sannan akwai cin hanci da rashawa sosai tamkar kasuwanci ko ince sun maida hakan ma kasuwanci, sannan mutanen kasar basa da kwanciyar hankali domin Yaƙin da ke kasancewa a ƙasar."

Deejerh ta ce, "Amman dai yanzu an rage Samun tashin hankalin Yaƙin ko?"

"Ehto haka na ji ana fada dai da sauki ba kamar da ba ko za mu je ne?"

Ammar ya fada.

Deejerh ta zaro ido tana.....

"Cab ni ba inda zani ina nan ai."

Ammar ya ce, "kin ga yanzu ina turawa da kaya gun wani cousin Brother na dake can yana saidawa ana turomin da kudin ina so sai na tsaya da kafafuna na san me na taka ya dai kasance komin kankatar abu zan iya yi wanda zai amfani kasar musamman bangaren marasa karfi da ke buƙatar tallafi."

Deejerh ta ce, "Great abun na birgeni in naga ana taimakon mutane nima ina fatan Watarana Allah ya bani ikon sanya murmushi, Farinciki da walwala a rayuwar wasu,in hakan ya kasance zan ji dadi matuka araina."

Ammar ya ce, "Addu'a ita muke,kuma ita zamu ci gaba da sannu burika na Alkairi wanda muke tsammani da ma wanda ba ma tsammanin zasu tabbata."

Deejerh ta ce, "Hakane In sha Allah nikam, companyny da kake aiki na mene ne wai ma?"

Ammar ya ce, "COLORFUL CREATIONS, shine sunan kamfanin kuma karamin paint company ne, muna hada paint da kanmu sannan mu sayar a kasuwa kinga yanzu sauran kudina bayan na siya mana waya paint din na karba a Company na turawa cousin Brother na a syria."

Deejerh ta ce, "Ma Sha Allah, Allah kara arziki mai albarka, amman dai zaka gyara motarka ko?"

Ammar ya ce, "For Sure,har ma na bada an fara aikin."

"Ya yi kyau,Yau mun sha hira,ya kamata yanzu inje inyi browsing ka da in fara jin barci in gagara katabus." Deejerh ta fada.

Ammar ya ce, "Gaskiya kam, amman watarana nima zaki bani Labarin ki ."

Murmushi Deejerh ta yi,ta ce, "In sha Allah, Good Night have a nice Dream."

★★★★

Stylish Wordplay fashion School sun hada party na zuwansu makarantar kamar yadda kowasu dalibai ke yi.

Gabadaya matan sai suka sa Jeans din da aka basu wanda Deejerh tayi Designing.

Riga kowa ra ayinsa yasa da yawansu wata rigar da suka sa ma tamkar babune domin duk girjinsu a waje yake, musamman camellia.

Ita kuwa Deejerh rigarta blue mai kyau tasa ta kwanta ajikinta kuma ta rufe mata ko ina.

Babban hall din dake School din suka tare.

Ta ko ina sauti ne kawai ke tashi.

Kowa na harkar gabansa.

Masu shaye-shaye na yi masu romance na yi.

Daga mazan har matan.

Deejerh na shiga hall din kanta ya fara bugawa tana kokarin fita a hayyacinta kamar na Free Day.

Har ta ja kafarta zata koma, sai kuma wata zuciyar ta ce ta koma.

"Dolene in yi rayuwa cikinsu,kuma dole ne in jure,in daure ko da cikin raina bana so,abu ɗaya na sani,ba zan taba komawa rayuwar da nayi a baya ba,koma mene ne zai faru zan daure,zan jure,in danne zuciyata da duk abun da kwakwalwata zata ayyana mun." Abun da ta saka kenan a cikin ranta kafin ta shiga.

Jan numfashi ta yi ta duba gurin da ta ga ba kowa ta nufa ta zauna.

Ji tayi kawai ana tabata da fadin, "Hello."

Camille ce tana sake mata. Wani munafukin murmushi.

Tare da ƙoƙarin rungumarta.

Cikin sauri Deejerh ta dakatar da ita da hannunta.

Ta ce, "kin gani,bana son wannan rayuwar,ban sonta kuma bana sha'awar kasancewarta wannan bangaren naku ba tsarina bane, za mu iya zama friends kamar yadda kika bukata a farko amman kada wani lamari haramtacce ya kara shiga tsakanina dake, Addinina da al'adata bata hallata mun cudayan tsakanin jinsi ba,hasali ma hakan haramtaccen abune mai girma,ki tsaya iya