5STARS CHRONICLE Book 3 VIXEEN

CHAPTER 25

by @xayyeesherthulhumaerath

asamu matsala ba In Sha Allah domin kuwa a lokacin suna da kwarewar kare kansu."

Karaf wata mata ta katse Deejerh da fadin, "kare kansu kamar ya? Mun aminta da batun training din amman batun a hada baki da su a koma wanda ke wannan lamarin babu shi Domin ko an kamasa babu abun da aka isa yi a karshe ma mu za a kara jefawa cikin wani bala'in kinga angudu ba a tsira ba kenan."

Tana shiru wata ma ta fara, "Gaskiya kam indai sai hakan yafaru gwanda mu hakura da training dinma gabadaya, tun ana illata yaranmu su kadai baza mu kai kanmu inda za a hada damu da mazajenmu ba."

Alamu dai ya nuna cewa suna shakka ds matukar tsoron duk mai aikata wannan badalar kuma akwai yiwuwar cewa wasu sun san shi, tsoro ne ya hanasu bayyanawa bare kuma akai ga tunanin daukan mataki.

Wajen ya kaure da hayaniya, Papi ya dakatar da su da fadin , "in dai kun yarda dani, kuma kun yarda da duk abun da zan kawo gareku bana cutarwa bane, to ina so ku bawa Deejerh hadin kai,sannan batun duk da muka yi anan ya zamana iya mu dinne kadai ke da alhakin jinsi kada ko harafi daya ya fita."

Duk da cewa tsoro ne fal ransu amman kuma sun yarda da papi kuma ba za su iya bijire ma shi ba.

Hakan yasa suka amince.

Deejerh tayi musu godiya sosai da kuma alkawarin cewa da ikon Allah komai zai tafi daidai kuma zasu gyara rayuwar al'ummar kauyen ba tare da kasancewa cikin fargabar zuwa ko ina ba.

Ta cire rana biyu da bata zuwa office suna yiwa yaran training ita da Ammar.

★★★★Deejerh Ganin cewa tana kara samun gaba da matsayi kuma rububin Designing dinta ake ako ina,sannan ogansu gabadaya ya fi ji da ita ta fara samun matsala a wajen aiki.

Har ya kai ga tana zuwa wajen duk zasu watse suna bata fuska sai dai Somir da ya zama mayenta,duk inda zata yi suna tare.

Ranar tana gama aiki daga office ta nufi wani police station babba da ke cikin garin domin kai shigar da karar batun fyaden da ke afkuwa a kauyensu.

Hamida shine babba a wajen gabadaya hakan yasa ta bukaci ganawa da shi kai tsaye.

Da har ya nuna ba zai iya ganawa da kowa ba ganin cewa lokacin tashinsa ya yi,ta window yana ganin Deejerh ya bada izinin ta shiga.

Tana shiga ya bata wajen zama.

Binta yake da kallo tana shiga,ta sanar masa da sunanta da kuma kauyen da take,sannan ta fara yi masa jawabin makasudin zuwanta da kuma abun da take so ayi.

Hamid ya ce, "Ehto Yan mata wannan matsalar babba ce amman kuma ba wacce ake damuwa da hukunci akanta ba, domin kuwa sai adau karamar matsala da bata kaita ba a girmama, yawanci irin cases dinnan baya kaiwa ko ina da an fara akan sa a dikilar domin mafi yawanci masu hannu da shuni ke aikatawa,yanzu kuwa da duniya ke kara tabarbarewa da an bada wani abu,ko anyi wata barazana Shikenan za a rufe abu duk girmansa, saboda ke,zan yi iya yina inyi kokarin ganin anyi abun da kikeso In sha Allah zaki karba numberta in kinje gida ki kirani ma karasa maganar a waya kinga yanzu lokacin tashi a aiki ya yi."

Ya fada fuskarshi sake.

Murmushi ita ma Deejerh ta yi tana yi masa Godiya ta karbi number sannan ta fita ta tafi.

An ci gaba da yiwa Yaran kauyen training a ɓoye kuma suna samun kwarewa sosai ko da Deejerh bata nan Ammar na kokari wajen gabatarwa.

★★★

Lokacin taron Fashion Designers na karshen shekara ya yi,kuma daman duk shekara kowanni kamfani suna tafiya ne da gwarzuwarsu wacce take tashe kuma mutane ke ji da ita domin samo masu kambun kasancewa Best Fashion Design Company.

Domin taro ne na gani a fada da manyan mutane,kasashe daban-daban suke halartar sannan ake tanadar wani kofi na musamman domin baiwa duk companyn da suka ci wasannin da ake tsarawa a wajen sannan kuma sukai shigar da ta birge ko ince babu kamarta.

Wanda suke yiwa lakabi da Coketail Party.

Tunda Mr Charles ya sanar kan cewa da ita kadai zai tafi ta kara fadawa wata matsalar kowa na jin haushinta da jin tsanarta.

Ita kuwa Deejerh aranta ma sam bata wani son zuwa Dubai din ta kudirta cewa zata sanar Mr Charles ya yi hakuri ya dauki wata.

Da ta fadawa Ammar da Ma'am sai suka nuna yin hakan bai kamata ba, ta yi wa ogansu biyayya ta amince ta bishi sannan ta yi addu'a.

Haka ta amince ba don taso ba, Mr Charles da kanshi ya yi mata bayanin irin kayan da zata yi Designing tasa a taron.

Yanayin kayan duk sai ya fitarwa da mutum sura a takaice ma duk kirjin ta zai kasance a wajene.

Bata ce masa komai ba ita dai ta yi Designing din amman ta rufe duk wata kofa da surarta zata fita.

A ka kammala komai suka bi jirgi.

★★DUBAI

Dare ne ranar taron, wanda ya kasance tamkar sallah ga fashion designers din duniya da ke ji da kansu hakan yasa kowa yake kokarinsa iya yi wajen ganin ya birge a wannan ranar.

Shaye-shaye babu irin wanda ba ayi wanda ya zamto masu ma gasa ne kowanni kamfani zasu sha aga wa inda suka fi kowa iya kokarin sha ba tare da sun fice a hayyacinsu duka ba.

Mr Charles na gani shigar da Deejerh ta yi ya bata rai cikin fushi yana jan hannunta tare da fadin, "mene ne hakan? Wannan wacce irin shiga ce kika yi? Kina so ki zubar mun da mutunci? Haka na ce kiyi?"

Deejerh ta ce, "Sir ba zan iya yin waccer shigar da ka umarta ba domin addinana ya haneni ga sanya kayan da zai fiddamun tsaraici waje matsayina na mace."

Cikin Fushi y daga hannu ya sake mata mari a fuska,zai kara sake mata wani tayi saurin dakatar da shi ta hanyar rike masa hannun.

Ya ce, "ki sani wallahi Allah na rantse muddin kika sa wannan damar ta yau ta subuce mana ki kuka da kanki da duk abun da ya biyo baya."

Yana gama fada ya shige dakin taron ita ma ta bi bayanshi.

Kasaƙe Deejerh ta tsaya ganin yadda ake rayuwar badala a wajen.

Wasu matanma kayan jikinsu tamkar babu ne.

Ga shi sai tikar rawa suke da shafe shafen jikin juna.

Jikinta a sanyaye ta karasa tebur da Mr Charles ya zauna ita ma ta zauna suna hada ido yana binta da wani mummunan kallo,duk da cewa a tsoro take amman a zahiri kuma murmushin karfin hali ta sake masa.

Ya kara kula a cikin ransa.

Ba bata lokaci suka fara wasanni taron ta hanyar gabatar da kai.

Deejerh na gabatar da kanta gabadaya binta da wani irin kallo suke na raini ko ince kallon rashin isa.

Daga nan aka fara kawo giya.

Aka ajewa kowa kwalba uku.

Daga mazan har matan kowa kokarin shanyewa yake amman Deejerh ko motsawa batai ba bare tayi kokariin sha.

Mr Charles ya bige kafarta ta kasan tebur.

Ta kalleshi kafin ta girgiza masa kai alamar ba zata sha ba.

Har suka gama sha Deejerh kam ko daga wa batai ba.

Mr Charles ya kara kula ranshi ya ɓaci.

Aka zo aka kawo masu kashi, kashi dai na mutane wanda yake a ka'idar partyn har kashi suke ci.

Nan ma haka sukai tururuwa suna ci tamkar nama, Deejerh kuwa harda toshe hanci ta ki tabawa bare tunanin ci.

A karshe ma tashi tayi ta bar wajen.

Suka bi ta kallo.

Duk wani abu da suke agun kin shiga tayi ta ja gefe.

Kafin a gama ta fice ta hau taxi ta koma hotel dinsu da suka sauka.

Idanun Mr Charles sun canja kala jajir takaici ya rasa inda zai sa kanshi da aka tashi shi ya bi bayanta kai tsaye dakin da take ya fara nufa cikin zafin rai yake nocking kofar......

Deejerh na budewa ta koma gefen gadon ta zauna.

Cikin fushi Mr Charles ya fara magana, "kin san asarar da kika janyo mun yau kuwa? Na ce kinsan koma bayan da kika jawa company a yau kuwa? Kin manta furuncin da na miki tun farko ko? Ina kara jaddada miki cewa duk abin da ya biyo baya kike kika janyo domin kuwa hukunci mai tsanani ya hau kanki babu tantama, kuma ki shirya gobe zamu bar kasar nan kuma kisa aranki sai kinyi mafiyin abubuwan da kika ki aikatawa a yau in mun koma." Yana gama fada ya fice tare da jan kofar da ƙarfi.

Deejerh kam bata ce komai ba,ta bishi da murmushi kawai.

A cikin ranta kuwa bata jin dadi ko kadan tunani take ta ya zata fuskanci wannan kazamiyar rayuwar tasu a haka.

Bata wani samu damar yin barci ba,har asuba tayi,ta tashi kenan zata yi sallah Mr Charles ya kara shiga dakin yana fadin , "ki fito mu tafi."

Deejerh ta kallesa cikin ladabi ta ce, "Sir bara inyi sallah to."

"What?" Ya fada cikin daga murya.

Deejerh ta ce, "Sallah zanyi sai inzo."

Ya girgiza kai tare da fadin, "Sallah ko? Karki fasa shugabar masu ibada, ni ba zan tsaya jiranki ba,kuma in jirgi ya riga ya tashi sai dai ki nemi yadda zaki yi." Ya fice abunsa.

Ita kuwa Deejerh toilet ta shiga ta dauro alwala ta yi sallarta.

Cikin ikon Allah kuwa har sai da ta isa airport din tana shiga jirgin ya tashi.

A tunanin Mr Charles bata zo ba don tun yana kallon hanya har ya gaji ya Kau da kai.

Yana kallon gefen sa kuwa ya ganta ya yi saurin kawar da kai kamar bai ganta ba.

Domin aransa jin tsantsar tsanarta yake ba don yana tunanin cewa a yanzu Designing dinta na daya daga cikin wa inda ke tashe a Company ba da kudirin da ke ransa gareta sai ya nininka yadda zata gagara komai.

Kwafa ya yi kawai ya ci gaba da karanta jaridar dake hannunsa.

Har suka isa paris Babu wanda ya yiwa wani magana.

Deejerh na shiga kauyensu ta ga Ammar gyara gidan Ma'am sosai ya yi kyau tamkar ba a kauyen.

Ta yi farinciki da sosai har tana tsokanar shi kodai aure yake so ya yi.

Tunda ta dawo taki zuwa gun aiki kuma Mr Charles har sawa ya yi a kirata amman taki zuwa,a karshe ma sai tafi mai da hankali akan yiwa yaran nan MMA TRAINING.

★★★Yamma ta yi yanayin garin ya yi duhu ga wata iska mai dadi dake karadewa, Deejerh ta kira officer kan cewa ko yau zasu gwanda aje yaransu a hanyar fita kauyen domin ganin ko za adace.

Ba musu kuwa ya amsa mata domin daman yana son ganinta har cikin ransa.

Hakan yasa ya dauki mota da kanshi ya ba wa yaran umarnin ta yadda zasu tsaya a zagaye kauyen shi kuma kai tsaye ya karasa gun Deejerhn ya tarar da ita da Ammar.

Daya daga cikin yan matan Deejerh ta tura wacce tafi yarda da kwarewarta a training din.

Tafiya take tamkar ba komai tana sauri mai nunin cewa akwai abun da takeso ta je cikin gari tayi.

Kamar yadda aka saba yiwa sauran matan ji ta yi kawai an rungumeta ta baya,da karfi ana kokarin janye mata wandon da ke jikinta.

Cikin ikon Allah ta juyar da hannunta tana riko fuskarsa.

Tare da buga masa hannunta amara.

Ya saki wata kara yana faduwa.

Takai yan sandan da suka buya suka fito wasu na video wasu kuma na kokarin cefeke shi.

Ganin yan sanda yasa Abdu rikicewa yana kokarin gudu.

Yana fara gudun kuwa suka cafkeshi daidai lokacin da Deejerh da officer suka iso wajen.

Da mamaki Ammar da Deejerh suke binshi da kallo.

Ammar ya ce, "Abdu? Daman kaine kake wannan aika-aikar?"

Fuska duk gumi yana haki ya ce, "wallahi sharrin shedan ne amman daga yau nayi alƙawari ba zan kara ba, na daina wallahi na tuba,ku rufa mun asiri."

Deejerh kam don takaici ma bata iya cewa komai ba.

Haka suka tafi dashi tana yiwa officer godiya.

Ya ce, "godiyar tukunna dai yanzu na baki kyauta amman nima akwai nawa lokacin zan kiraki a waya ko innazo'

Murmushi Deejerh ta yi ta ce, "to Shikenan Allah ya kaimu."

Yana tafiya Ammar ya bata rai, "wai wannan Murmushin fa? Ni fa ban gane miki ba da mutumin nan kamar son shi kike."

Deejerh ta ce, "to waya sani ne ma."

Tana fada ta tafi ta bar Ammar a gun.

Tana shiga daki taga wani sako ta Gmail dinta mai jaddada mata cewa lallai gobe ana nemanta a Company.

Ba yadda ta iya washegari haka taje.

Tana zuwa kai Tsaye office din Mr Charles ta nufa.

Bayan ta gaisheshi,yana amsawa mika mata magazine ya yi na tallen da za ayi da irin kayan da za asa wanda suka saba duk karshen shekara ake domin tallata kayan da suke Designing.

Sunanta ta gani kan wacce zata yi Designing din kuma tasa kayan ta yi tallen.

Ba Designing din bane ya tada mata hankali yanayin kayan ne ya tayar mata da hankali domin gabadaya yanayin kayan da fidda surar jiki ne gabadaya jikinta zai kasance a waje kuma duk kayan iya ka gwiwa ne, gashi babu damar rufe gashi hasali ma sai dai a kara wani gashin ma.

Take yanayinta ya sauya tana gama dubawa ya ce.

"Wannan shine hukuncinki na farko,na biyu kuma akwai wani babban Fashion Designer da ke buƙatar yin hulda dake na wata guda, zai kama muku hotel zaki koma can ku kasance tare."

Cike da mamaki Deejerh ta ce, "Hulda dani as how sir?"

Charles ya ce, "ki zama Girlfriend dinsa ta wani bangaren kuma ince tamkar matarsa domin hakan da zakiyi ne kawai zai iya kwato muna Wancen kambun da kika mana asara."

Ji tayi kanta ya fara yi mata wani azababben ciwo,ta yi saurin dafewa.

Charles ya kara fadin, "ki sani wa innan abubuwan biyu sun wajaba akanki kuma baki isa ki kaurace masu ba, in kuwa kikai attempting hakan tamkar kina yiwa rayuwar ki a kasar nan barazana ne."

Yana fada ya juya mata baya ci gaba da duba files din da ke gabansa.

Wani dishi dishi take gani, haka ta tashi jikinta ba kwari ta fita tana tafiya a hankali.

Kasa shiga office dinta tayi kai tsaye ta shige motar ta ta dafe kai.

Ganin disordern ta shirin motsawa yasa ta nutsu tare da tattalin hankalinta waje guda tana fidda numfashi a hankali.

Har sai da ta ji ta samu nutsuwar sannan ta dara driving ta dauki hanyar shiga kauyensu.

Har yanzu bata so ta fadawa Ma'am da Ammar domin tasan hankalinsu zai tashi Sosai.

Hakan yasa ta daure taki bari su gane.

Washegari da sasafe haka ta kara riskar wani sako mai razanarwa kan cewa lallai indai bata zo ta aiwatar da abun da aka umarceta ba za a kasheta.

Ta dawo kullum bata barci yadda ta ga rana haka take ganin dare.

Ranar ta rasa meke yi mata dadi kawai ta dauki wayarta ta yi posting a timeline dinta.

"I don't know how to explain what I'm feeling right now.

All i can say is that it hurts.

Everything hurts,my heart feels so heavy that all i want is to cry.

Ga shi kuma na gagara kukan.

Yana da matukar daci ya kasance duk kokarin mutum na wajen ganin komai ya tafi daidai ya gagara.

Ina kokarin maida raunani karfi, amman aduk sanda na yi kokarin tabbatar da hakan wani lamarin kan iya shigowa da raunani zai katse karfin.

Na gaji!

Some days really really hard to just move,

It's to hard to get out of the bed.

Its hard to even go outside.

Duk da cewa ni ba mutum ba ce da ke iya fidda abun da ke damunta ko yake ranta kai tsaye, Amman kuma ina bukata zababbun mutanen da zasu iya fahimtar yanayina ba tare da furta komai ba."

Kusan kullum ta kan yi rubutu mai yanayi da hakan a timeline dinta amman babu mai kulata wani lokacinma in tayi sa'a bai zarce ayi mata like a wuce.

Reply din da ta gani ne cikin sauri yasata gyara zama domin dubawa.

Ibrahim Khalil sunan shi.

Ya yi mata reply da fadin, "Yayin da kafa ta yi nauyi aka gaggara dagata daga inda ta kame,ba wai barinta ake da nufin anan za ata zama ba,aa kokarin Dagata ake komin zafi da radadin da za aji domin kuwa hakan na nufin maganin da zaiyi mata aiki yana gaba ne,sannan wannan ciwon kuma rubutaccene da Ubangiji ya kudurta cewa sai anyisa kafin aji sauki, don haka babu babu bukatar fidda tsammani komin tsananin rayuwa akwai sauki, da yawan lamura Ubangiji na jarabtar mu ne ba don baya sonmu ba illa don ya ga ya zamuyi kokarin rayuwa a yanayin da ya sanya mu? Shin zamu karbi kaddarar? Zamu jure? Kuma zamu tuna cewa komai tsanani yana tare da sauki? Ka da ki karaya,in a kwance kike ki tashi,in hawaye kike ,ki maida shi murmushi."

Tana kaiwa karshen ba ta san sanda ta fara goge hawayen da ke fuskarta tana sakin murmushi ba........

Ji tayi karfin gwiwarta na dawowa.

Ta yi masa reply da , "Thank you so much, har cikin raina na ji dadin jawabanka sai nake ji cewa tamkar ka san dafin dake cikin zuciyata."

Emojin Murmushi Khalil ya tura mata yana, "Kila kan na shiga cikin zuciyar ki na karanto ne ba tare da kin sani ba."

Ta tura masa emojin zare ido da mamaki tana, "kenan kai Aljanine ba mutum ba, domin ai mutum ba zai iya shiga cikin ran mutum ba."

Khalil ya kara yin dariya ya ce, "Aiko dai ni mutum ne."

Daga nan suka ci gaba da chatting karshe ma suka koma Dm tamkar wa inda suka jima da sanin juna.

Deejerh ji tayi ta aminta da khalil duk da cewa bata taba ganinsa,jin muryarsa ba, bare wani abu illa media da ta ci karo da shi.

Ranar neman damuwarta ta yi ta rasa