5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUAR

CHAPTER 4

by @xayyeesherthulhumaerath

cike da sakin fuska.

Abba Malik ya ce,"Nace bakon Malaysia yazo mu ci abinci tare mu yi hira ."

"Ya kamata dai kam yanzu bara insa akawo maku abincin in kun gama dole nima in zo in zauna ayi hirar nan dani."

Ta fada cike da zolaya ta fice.

Bayan an kawo masu abinci sun ci sun koshi Abba Malik ya kalli Farouq ya ce,"Malam Umar ya ka ga dan garin namu ne ko ince kauyen namu?"

Farouq ya ce,"Abba ai nan ya zarce kauye banyi tunanin zan ga hakan ba gaskiya garin ya birge ni har ina cewa Javed na ji sha'awar gini anan sannan kuma yadda na ga ana ruruta matsalar rashin tsaro a Nigeria nidai tunda na shigo ban alamar hakan anan ba."

Abba Malik ya ce,"mu kam gaskiya ba mu da matsalar rashin tsaro sam sam Shugaban dake jan ragamar garin nan a tsaye yake ba a yadda da batun sace-sace ko hare-hare duk abubuwan nan da ake a sauran garuruwan dake kewaye da Nigeria mu bama fuskanta domin a kwanaki ma yan Ta'addan sun turo da takadda mai dauke da sakon suna son shigowa su karya tarihi da ya kafa ya ce da su ba matsala yana jiransu su shigo,to karshe ma dai koda suka zo garin basu ga Mokwa ba cikin garin nan din suka bi amman daji ya zame masu sai da suka yi nisa har sun fada kanji tukun suka hango mokwa,Babban matsafi ne na karshe amman yana taimakon al'ummarsa kuma yana karesu da tsafinsa a yanzu haka shekara biyu ke nan ba yana fama da lalura bai da ishasshiyar lafiya magauta sun sanya masa hannu an hana shi zuwa sallar idi a yadda aka sheda mana lallai muddin yaje zai iya rasa ransa kuma gaskiya ana matukar kaunarsa al'umma na kukan rasashi domin duk ranar da ya bar duniya mun rasa adilin shugaba a mokwa.

"Ikon Allah ke nan lallai yana da karfi sosai wannan shi ake kira shugaba mai sadaukarwa kuma na lura yanayin garin nan sam babu yunwa ga dukkan alamu babu tsawallawa a kan kayan hatsi."

Abba Malik ya yi murmushi,"Ai Mai Martaba bai yadda da batun rashin abinci ba ga al'ummarsa ka ga ko boye kayan hatsin da ake a wasu jihohin? Mu nan ba a isa ba domin in ma kunyi za a karba a rabawa al'umma shiyasa kowa yake taka tsantsan mussamman ma dake muna da albarkar noma sosai."

Javed ne ya kalli agogon wayarsa ya ce,"Abba dare ya yi karfe sha ɗaya da rabi gashi baku gama ba."

Abba Malik ya ce,"Subhanallah lokaci na sauri kuje ku kwanta kam."

Farouq ya ce,"Gaskiya ban so a katse wannan tarihi ba amman dole watarana inzo in zauna a ci gaba mun daga inda muka tsaya."

Murmushi Abba Malik ya yi ya ce,"Baka da matsala In sha Allah akwai shagali ma da za ayi na al'ada kana nan ai zaka gani . "

Sallama suka yi masa kafin suka tafi.

♡♡♡Barci ya gama cin idanun Javed sallama shima yama Farouq ya wuce ya kwanta.

Shi ko Farouq Nafila ya yi kafin ya dauki system dinsa ya fara aiki,sai wajen karfe uku kafin ya kwanta.

Asuba na yi kuwa da ya tashi yin sallah bai kwanta ba.

System din ya dauka ya shiga bincike....

Jin alamar motsin mutum yasa Javed shiga dakin.

Yana shiga Farouq ya yi saurin kashe System din kafin ya karasa gabansa.

Ya daga kai yana binsa da kallo,Javed ya ce,"kai dai kam baka hutu inaga a kullum da kyar in kana samun barcin awa uku zuwa huɗu."

Farouq ya yi murmushi,"Hutu ai ba nawa bane,akwai abubuwa masu mahimmanci da yawa da nake kan gudanarwa kuma hankalina ba zai taɓa kwanciya ba har sai na ga tabbatuwarsu na cimma nasara."

Javed ya yi dariya,"Ai kai kwaro ne Ga ka barawo ga ka adili kodayake ba ace da kai barawo ba tunda kana kwamusowa al'umma hakkinsu ne da manya ƙasa suka danne, nima fa da zan iya lamarin nan naka da na fara anan Nigeria wallahi don muma muna da azzaluman shugabbanni da attajirai da suka danne dukiyoyin talakawa suna gina rayuwarsu da ta iyalansu."

Farouq ya ce,"Mai zai hana? Tsab zaka iya kuma zan baka gudunmawa wajen tabbatuwar hakan,Duk da cewa ba hanyar kwarai nake bi ba wajen diban dokiyoyinsu ba amman kuma hanyar kwarai nake bi da ita wajen tallafawa mabukata kuma na tabbatar da cewa Ubangiji zai dubi zuciyata don haka ban taba jin dana-sani ko fatan dainawa ba,muddin numfashi bai bar karakaina a jikina ba zan taba dainawa ba duk wani arzikin da bai taimakon al'umma ko yake danne al'umma idona na zuwa kanshi sai na kwatar masu rabonsu sun amfana suma sun gina rayuwarsu cikin aminci hakan ba karamin tallafawa yake ba wajen kawar da talauci a kasa ba sai iya ka gwamnati ke da alhakin kula da al'umma ma muma muna da wannan nauyin muddin ana son ci gaba a kowacce kasa."

Javed ya numfasa ya ce,"Gaskiya ne dukkanin bayanka kuma na gamsu da su sannan nima ina bukatar ka daura ni akan hanya amman dai kasan nan ba malaysia ba ne abubuwanmu da bambamci."

Farouq ya ce,"Yeah kuma ka ga ni kowanni mutum indai na taɓa masa dukiya ina tura masa takaddar gargadi kan dalilin da yasa na diba tare da hujojjojina kuma ina basu tsari da dokoki yadda zasuna tallafawa al'umma yadda na tsara ina biye da duk wani motsinsu ta yadda duk wanda yaƙi aiwatar da abun da na bukata ina iya kara aikata masa mafiyin abun da na yi a farko,to hakan yasa suke shakka suna kokarin bin tsarina ko iya hakanma babbar nasara da galabace a gareni ìna sanya su yin alkairi ga al'umma ko da basu yi niya ni in samu lada suma su samu kuma ubangiji ya kara buɗa musu to amman kuma kamar yadda ka fada Nigeria da kamar malaysia zan danyi bincike mu ga yadda abun zai iya kasancewa."

Javed ya ce,"Yes My Boss da ana iya hallarta sata da nace wannan satar hallartacciya ce tunda da nufin alkairi ake yinta."

Farouq ya yi murmushi.

Javed ya kara faɗin,"yanzu bara in barka ka ci gaba da aikinka kar in dameka."

Ya fada yana dariya ya fice.

Yana fita da sauri Farouq ya dago system dinsa ya kunna.

Wani page ya shiga wanda aka yi rubuta NIGER STATE/MOKWA

a kasa kuma GIDAN SARKIN AL'ADU.

Sauran rubutun da ya yi a kasan duk da programming language wanda sai cikakken Computer scientist ne kadai zai iya fahimta.

Shiga ya dunga yi yana ta duba wasu abubuwa kafin daga karshe ya kulle wajen karfe bakwa na safiya.

Cikin sauri ya karya domin 8 daidai zasu fara Lectures kuma Farouq ne farko.

Kafin ya gama Javed ya fito,yana gamawa suka fice ko Hajiya Kaka basu je sun gaida ba.

Kai tsaye lecture room Farouq ya nufa inda student duk sun hallara shi kadai ake jira.

Da tambayoyi ya fara masu kan binciken da yace su fara kan cybersecurity.

"Ko akwai wacce zata iya fadamun mene ne Cybersecurity atakaice?"

Kusan mutane biyar ne suka daga hannu ya tashi ta farkon ta ce,"Hanyoyin sanya tsaro ga na'ura."

Sanyawa ya yi atafa mata kafin ya kara tada wata ma ta ce,"Yadda ake kula da kwamfuta gudun samun hari."

Ita ma sawa ya yi aka tafa mata bayan sun zauna duka ya ce,"Ehto duk kunyi kokari yanzu amman akwai bukatar cikakken bayani kowacce ta kunna system dinta ta login PDF dinmu na Cybersecurity daman ai jiya ance an koya muku ko?"

Suka amsa da ,"Yes Sir."

Cike da zumudi dukkaninsu suka bude systems din suka shiga PDF din gwanin sha'awa.

Farouq ya ce,"Are we ready?"

Nan ma suka kara amsawa da ,"Yes Sir."

Cikin kwarewa Farouq ya fara jawabinsa.

Da farko shin mene ne CYBER SECURITY?

Cybersecurity shine tsaro na yanar gizo yana da alaƙa da kare kwamfutoci,hanyoyin sadarwa,kiyaye bayanai ta hanyar shiga ba bisa ka'ida ba ko ba da izini ba,kawar da hare-hare,lalacewa ko sata,kunshi fasahohi da hanyoyi tare da ƙa'idoji da aka tsara don kare bayanai tare da tabbatar da ingancinsu,sirrinsu da samuwarsu.

Wannan shi ne cikakken bayani dangane da Cybersecurity ina fatan kowa ya fahimta?

Sai da ya tabbatar da duk sun fahimta kafin ya ci gaba.

"Yanzu za mu wuce gaba,Akwai muhimman abubuwa na tsaro a yanar gizo da ya kamata ku sani kamar su.

Network Security

Kare hanyoyin sadarwa.

Application Security

Sanya tsaro ga aikace-aikace da kubutar da su daga rauni.

Information Security

Kare ingancin da sirrin bayanai a dukkan na urori da hanyoyin sadarwa.

Endpoint Security

Tsaron na'ura guda dake samun damar shiga hanyoyin sadarwa na kamfani.

Cloud Security

Shi kuma shi ne tsaron gajimare wanda ake kare bayanai da aka ajje cikin yanayi na gajimare.

Sannan akwai

Disaster recovery

Incident response

Regulatory compliance wa innan kenan

Sannan ina so ku sani cewa tsaro na yanar gizo yana da matukar muhimmici a wannan rayuwar yayin fa barazana ke ci gaba da wanzuwa yana da kyau ga murane da duk wasu kamfani ko kungiyoyi da su kasance masu tsaurara tsaro da ka idoji masu karfi ga dukkan wani abu da ke mallakinsu a yanar gizo." yana ka karasa wannan maganar ya ce,"ko akwai masu tambaya ko abun da baku gane ba?"

Caraf wata ta daga hannu.

Ya bata damar tashi kafin ta ce,"Sir Amman a binciken dana fara na ga akwai yadda mutum ke koyan yadda zai kai kutse ko hari ga wani shin ba za a koya mana bane."

Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Ke ko Meemah wa kikeson kaiwa hari tun yanzu? Za a koya maku amman hakan ba wai yana nufin ku koya ku dunga cutar da mutane bane,za a koya muke domin karin tsaurara tsaro tare da fahimtar tsaron da hanyoyin da ake iya bi don ruguzawa amman ba don cutar da kowa ba,kuma ba mu zo bangaren ba tukunna muna tafe zamu zo In Sha Allah amman a yau dai zamu tsaya anan."

Godiya Meemah ta yi masa cike da gamsuwa da bayanansa ta zauna.

Cikin jin dadi Farouq ya kammala masu lectures dinsa na ranar kafin ya fita.

Can yamma suna zaune da Javed ya kalli wayarsa ya ce,"Oga na manta fa in sheda ma yau muna da zaman babban falo da dare duk ranar Friday haduwa ake aci abincin dare dukka family a babban falon mai martaba sannan muna sanya kayan gargajiya a daren za aci abinci tare ayi wasa da dariya in mutum na da matsala ko wata magana da yake son yi yana iya yi duk a gun."

Farouq ya ce,"Ma sha Allah hakan ba karamin kara dankon zumunci zaiyi ba to yanzu har ni zan iya shiga? Zanso in ganni cikinku ko zanji kwatankwacin yadda mutane suke jin yayin da suka gansu cikin danginsu."

Javed ya ce,"Haba dai,ai ba kwatankwaci za ka ji komai zaka ji duk yadda kowa ke ji na sha fada ma always feel like home please. "

Da hirar suka yi sallama da sauran Staffs din kafin suka tafi gidan.

Sai da akayi sallar isha suka nufi babban falo.

Suna zuwa kuwa kowa ya hallara hatta hajiya Kaka.

Tana ganin Farouq ta fara washe baki tana,"Mijin aiko yau inata nemanka."

Karasawa gabanta Farouq ya yi ya zauna yana,"aiko gani nan yan mata kaina kasa."

Duka suka fara dariya.

Mai Martaba ne ya yi gyaran murya da yasa dukkaninsu yin shiru.

Janinah da Kilishi suna ganin shigar Farouq suka fara kuskus.

Karshe dai Janinah ta tashi ta fita kafin ta dawo suna kallon juna suna sakin murmushi.

Abinci aka fara kawowa a ƙa ida jikoki maza faranti ɗaya ake masu su ma yara matan da matan jikokin ɗaya,na iyaye ma ɗaya.

Mai martaba kuma shi da Abba Malik da Hajiya Kaka.

Hakan kuwa ya kasance.

Sannan a ƙa ida ba a surutu lokacin da ake cin abincin hakan yasa gabadaya falon ya yi shiru.

Suka yi bismillahi aka fara ci.

Tuwon shinkafa ne miyar wake wanda yana daya daga cikin abincinsu na gargajiya da suke ji dashi.

Falo ya yi tsit

Kowa yana cin abincinsa cikin nutsuwa karaf cikin Farouq ya fara kugi.

Kallon kallo suka fara.

Ya make ya ci gaba da cin abincinsa.

Can da cikin ya yi masa wata irin murɗawa da kuka bai san lokacin da aguje ya tashi ba yana.....

Yana gudu ba, kai tsaye ya faɗa bayi.

Cikinsa ya riga ya burga kafin ya ƙarasa toilet ɗin har wandonsa ya fara ɓaci.

Janinah da ta kalli kowa anyi tsuru-tsuru ta haɗa ido da kilishi tuntsirewa da dariya suka yi har da riƙe ciki.

Cike da ɓacin rai da fushi mai martaba ya yi gyaran murya.

Ba shiri suka guntse dariyar suka yi nutsuwar dole.

Cike da izza ya fara magana.

"Javed garin ya ya ka kawo mana mashirmaci irin haka? Me hakan da ya yi yake nufi? Ni fa ba wani son alaƙa da turawan nan nake ba."

Ya yi shiru ya na jan numfashi kafin ya ce. "Ni ban gama yarda ma yana sallah ba, domin yawanci duk 'yan ƙasashen wajen nan ko sun ce su musulmai ne, a baki ne kawai ba su cika yin addinin ba."

Kan Javed na ƙasa ya ce. "Ranka ya daɗe a yi mana afuwa, amman ga dukkan alamu cikinsa ne ya ɓaci, tunda ba saba cin irin cimarmu ya yi ba, sannan kuma batun ibada gaskiya ba ya wasa da ita sam."

Mai martaba ya ce. "Maddalla! Amman ba hakan ne zai bashi damar zuwa yana karya mana dokoki da ka'idoji ba, daga yau ba na buƙatar sake ganin sa a duk wani taro ko zama da za a yi har ya tafi, hasali ma ban so ya shiga duk wasu lamura da suka shafi sarautar gidan nan."

Ta ido Janinah da Kilishi suka kalli juna cikin jin daɗi.

Ba wanda ya yi magana sai can Abba Malik ya ce. "Kar ka manta wannan bako ne kuma ya nuna yana sha'awar kasancewa cikinmu aka ce bakonka annabinka, ko ba komai in muka masa halacci zai ji daɗin bayyanawa yayin da ya bar ƙasar nan, kuma ga dukkan alamu ba da son ransa ko da gangan ya yi ba."

Mai Martaba ya ce. "Na riga na gama magana kuma ka san ba na magana biyu."

Hajiya Kaka ta ce, "Da dai an yi masa lamuni yaron na da hankali. "

"Ko da a ce jinin gidan nan ne zan iya dakatar da shi balle kuma wani bare, kun wani dage kuna son kare shi kun manta cewa maganata ba mai canjuwa ba ce."

Mai martaba ya faɗa cikin fushi yana miƙewa.

Cikin sauri dakaransa suka rufesa har zai fita sai kuma ya tsaya ya ce. "Ba ma shi kaɗai ba, daga yau ba na buƙatar wani bare cikin zaman da ya shafi al'ada." yana gama faɗa ya fice.

Ba abin da Abba Malik ya iya furtawa sai. "Allah ya kyauta."

Shi ko Farouq yana nan zufa ta jiƙe shi shakaf kamar wanda aka kwara wa ruwa.

Da ƙyar ya rarrafo ya kwanta a kan gado domin ƙarfin jikinsa kaf ya tafi.

Mai martaba na fita da Sauri Javed ma ya bisa ya je gun Farouq.

Yashe a kan gado ya gan shi yana ta murƙususu.

Ƙarasawa ya yi ya riƙe shi yana. "Ya dai cikinka ke ciwo?"

Farouq ya girgiza masa kai alamar eh.

Javed ya rasa ta ina zai fara daga kan da zaiyi sai ga Abba Malik ya shigo.

"Subhanallah ya kamata asamu abashi magani gashi ba ma kusa da asibiti kuma kar abashi maganin gargajiya ya zame masa matsala tunda ba saba sha ya yi ba."

Javed ya ce,"Abba ko dai za a gwada domin jinkirin zai iya zama wata matsalar kuma."

Abba Malik ya ce. "Eh to haka ne kuma, yi sauri ka kira Baban ganye mu ga ko da taimakon da zai iya yi masa."

A hanzarce Javed ya fita ya kira Baban ganye, yana zuwa kuwa wani ruwa ya fara ba wa Farouq ya sha cikin mintuna kaɗan ya fara dawowa hayyacinsa.

Tambayoyi ya fara yi masa me ya faru.

Farouq ya ce,"Ehto na fara cin abinci sai na ji yaji ya yi yawa ba irin wanda na sababa daga nan kawai sai na ji cikina ya fara murɗawa kuma cikin ya yi zafi sosai kamar wuta na ci."

Numfasawa Baban ganye ya yi ya ce. "Ba matsala In sha Allah, wannan ruwan ma da na baka kawai ya wadatar, zan ajiye maka sauran zuwa anjima sai ka ƙara sha, da izinin Allah cikin zai wanku ko ma miye a ciki zai fita, yanzu ka samu ka huta ka ɗan yi bacci ko da zaka farka zuwa anjima."

Abba Malik ya kallesa ya ce. "Sannu ko Malam Umar, Allah ya ƙara sauƙi, ka kwanta ka huta ɗin."

Cikin muryar rashin lafiya Farouq ya amsa "Amin Abba, na gode Allah ya saka da alkairi. "

Ya kalli Baban ganye ma ya ce,"Na gode Baba Allah ya saka da alkairi. "

"Ba komai sannu ko."

BabanGanyen ya fada yana haɗa kayansa kafin ya fita.

Abba Malik ya kalli Javed ya ce,"Sai ka zauna da shi Incase ko zai buƙaci wani abu."

Javed Ya ce,"Okay tom In sha Allah Abba."

Sallama ya yi masu ya fice.

Farouq kuwa wani barcin wahala ne ya yi awun gaba da shi.

Javed ya hau kujerar da ke gefen gadon shi ma ya fara barci.

Karfe biyun dare na yi tsilif kamar an tsikari Farouq ya tashi.

Da sauri ya dauki System dinsa cikin Foldern Gidan Sarkin Al'adu ya fara shiga.

Wasu abubuwa ya yi tickin sannan ya yi kansil ɗin wasu ya yi saving kafin ya shiga Yanar gizo bincike.

Jin motsin da Javed ya yi ya saka shi farkawa.

Yana farkawa ya ga Farouq ya duƙufa kan System sai shiga da fita yake.

Cike da mamaki ya ce,"Ah mara lafiyan ke nan?"

Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Na dameka da mutsu-mutsu ka farka ko? Sorry ko zaka koma dakinka to na ji sauki fa."

Javed ya ce,"Ba wani damu wallahi,amman dai wannan ƙarfin hali ne sai ka ce