5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUAR
CHAPTER 5
aikin barin duniya ba za ka kwanta ka huta ka samu ishasshen barci ba?"
"Umm Allah na ji ni kamar wani abu bai same ni ba,gaskiya ban ga laifin mai martaba ba da yake riƙo da al'adu sosai ka ga maganin gargajiyan nan ko kaɗan ban yi tunanin zai yi mun aiki ba, amman gashi cikin mamakina ina ji na tamkar wani abu bai sameni ba, kai ba ma wannan ba ashe kuma kuna da kasurgumin barawo a gari." Farouq ya faɗa.
Da sauri Javed ya ƙarasa inda yake yana,"Kamar ya ? A ta ina kuma?"
Farouq ya ce,"Anan Niger State mana mai kwamushe kudaden mutane amman ba halin ganin address Location ɗin ma da ya bari aka ga Nigern ina ga akwi dalili kuma ban san wani tsari yake bi ba amman dai zan san yadda za ayi mu kulla alaƙa da shi ta yadda zamuji bayanai duk da hakan zai yi wuya."
Javed ya ce,"Ikon Allah yoo ni wannan abun naku ai na kusa in sare ace mutum ba hutu ba lafiya ma bazai huta ba."
Farouq ya yi dariya,"Kai dai ai ragon namijine ne je ka yi barcinka."
Aiko tashi Javed ya yi yana,"Sai da safe ma karasa magana."
Farouq ya daga masa hannu yana ci gaba da danna System dinsa.
Washegari
Karfe Bakwai na safe ya gama shiryawa zasu bangaren Hajiya Kaka shi da Javed ya ji alamar sako ya shigo wayarsa.
Yana dubawa ya ga.
,"Ya dai? Ya Kashin? Ya tsaya ko dai sai an kawo taimako, yau kam na san da kyar ai a iya motswa,KAƊAN KA GANI asha jinya lafiya."
Da number aka turo sakon amman dake yana amfani da tracker yana dubawa ya bayyana masa da details din Jinanah.
Murmushi ya yi yana karanta saƙon.
Javed ya ce,"Lafiya ? Mu tafi ka tsaya kanata kallon waya kana murmushi."
Farouq ya ce,"Oh Sorry mu je ko."
Suna zuwa bangaren Hajiya Kaka kuwa da Janinah suka fara cin karo.
Da mamaki ta kallesa tamkar wanda ba wani abu da ya sameshi.
Karshe ma kallonta ya yi yana sake mata matsakaicin murmushi ya wuce ya shige ciki ya barta da suman Tsaye.
Hajiya Kaka na ganinsa tai rau da fuska,"Ayyah mijin yanzu nake cewa Janinah ta zo ta rakani mu duboka ashe kana tafe,jikin yi sauki ke nan."
Zama ya yi daidai da lokacin da Janinah ta karaso cikin falon ya na kallonta ya ce,"Kin san ba a taba jinin sarauta cikin ruwan sanyi ko da ace wanda ya taɓa shin kuwa shi ma yana dauke da jinin ne."
Hajiya Kaka ta ce,"Kar dai kace mun kuma acen kasar wajen akwai sarauta."
Farouq ya yi dariya kafin ya ce,"Sosai ma ai ako ina akwai jinin sarauta bare ma ni tunda nake da mata sarauniya kuma gimbiya ai dole jinin sarauta ya zagaye jikina."
Dariya Kaka ta yi ta ce,"Lallai kam mijin ba ka da dama yanzu dai na ji dadin ganinka haka don ni ban shirya takaba ba ga lokacin shagali na karatowa ina so in dau wanka in kashe kala ai nace muje ka sakeni kawai kafin ka mutu."
Suka yi dariya Farouq ya ce,"Wato ma ta ado da kwalliya kike ba lafiyata ba."
Hajiya Kaka ta ce,"Aa fa tunda dai ka ji sauki ka fasa mutuwar to aurenmu na nan gam gam ba motsin komai yawwa."
Dariya suka yi duka.
Farouq ya tashi yana fadin,"Tom mun tafi ayi mana addua."
"Allah ya bada sa'a,aje lafiya adawo lafiya kuma ubangiji yasa muku albarka a dukkanin lamuranku."
Hajiya Kaka ta fada.
Da Amin duka suka amsa Farouq ya ce,"Amman yau ba ke ba iskirim."
Hajiya Kaka ta ce,"Haba Masoyi na har a bada,bari in maku irin na yarenku ma na yan gayu Elubuyu haka ake cewa ko Janinah."
Ta karasa maganar tana kallon Janinah.
Tintsirewa da dariya duka suka yi ba tare da sun bata amsa ba.
Ɓata rai kaka ta yi ta ce,"Dadin abun ma nima ina da yarena ai sai in fada da shi Na mi ve eko (Ina sonka)."
"Na mi ve eko kwo (nima ina sonki) dole a siyo miki iskirim yau kam harda shawarma ma." Farouq ya fada yana dariya suna fita.
DigitalCraft suka nufa,suna zuwa Farouq ya yi Lectures Room.
Karatu suka kutsa kai tsaye.
Bayan kowacce ta kunna system dinta.
"Yau za mu magana ne akan HACKERS
Hackers mutane ne da ke da kwarewa a fannin kwamfuta da tsare-tsarenta suna bincika salo da tsarin kwamfuta,hanyoyon sadarwa da kuma software don fahimtar yadda suke aiki,suna gano rauninsu da kuma yiwuwar canzasu,sarrafasu ko ma tarwatsasu.
(Hackers: Individuals who use technical skills to gain access, manipulate, or exploit computer systems, networks, or data, often with varying motivations (malicious, ethical, or neutral).)
Sannan sun rabu kashi kashi kamar su:
White Hat Hackers
Sune masu amfani da kwarewarsu dom kare tsarin kwamfuta suna taimakawa kungiyoyi da ma'aikata wajen sanya tsaro mai karfi a kwamfuta da kuma gano rauninta kuma suna bada shawarwarin hanyoyin da za abi domin inganta tsaro da izinin masu na'ura.
Black hat hackers
Waddannan sune masu gudanar da aiyukan cutarwa ta hanyar bin raunin tsaron kwamfuta domin sato bayanai don wata manufa na cutarwa ko kuma tarwatsa tsari da shirin na'ura ba tare da izinin masu shi ba.
Gray hat Hackers
Su kuma wa innan suna tsakanin white hackers da black Hackers sukan iya yin kutse ga na'ura ba tare da izini ba amman kuma ba da niyar cutarwa ba sai dai don duba raunin tsaro kuma su kan yi kokarin sanar da kungiyoyin ko ma'aikatan domin suyi gaggawar Gyara a wasu lokutan kuma sukan iya neman kudi bayan sun gano wasu bayanai.
Wa innan ukun sune jiga-jigai da kan iya aikata komai amman bayan su kuma akwai.
Script Kiddie
Wa innan masu harin basu da kwarewa sosai suna amfani da rubutun da wasu suka kirkira ne don gudanar da hare-harensu.
Hacktivist
Su kuma wa innan suna amfani da hari ne matsayin nuna ra ayi na siyasa yawanci suna kai hari ne kan shafukan yanar gizo na gwamnati ko kamfanoni don nuna adawa da manufofin ayyukan da basu yarda da su ba.
State Sponsored Hackers
Su kuma wa innan gwamnati ne suke daukan nauyinsu suna cikin harkokin leken asiri na yanar gizo,kuma su kan iya sato bayanai masu mahimmanci daga wasu kasashen ko kuma katse muhimman hanyoyin sadarwa.
Phreakers
Su kuma suna maida hankali wajen harin tsarin sadarwa a tarihi suna yin amfani da tsarin waya don yin kira kyauta ko kuma amfani da hanyoyin sadarwa na waya.
Amman karku manta The three main types of hackers to consider are:
White Hat Hackers: Ethical hackers who help organizations improve security.
Black Hat Hackers: Malicious hackers who exploit vulnerabilities for personal gain or harm.
Gray Hat Hackers: Hackers who operate in between, often without malicious intent but without permission.
Dukkanin wa innan guda ukun zamu gudanar da practical kan yadda kowannensu ke gudunar da aiki In sha Allah.
Ina fatan kun gane?"
"Yes Sir." Suka amsa cike da kwarin gwiwa.
Farouq ya ce,"Ko da kwai mai tambaya?"
Kamar kullum Meemah ce dai ta fara daga hannu ta ce,"Sir Ke nan mu mata zamu iya zama white hackers ko black Hackers dinnan nan?"
Farouq ya ce,"Eheen me zai hana? Ka da kiyi tunanin akwai wani abu da ba za ki iya ba don kasancewarki mace muddin ba addini bane ya haramta miki,mata sun fi maza naci da dagiya ma indai suna son abu har sukan zarce namiji kwarewa ka da al'ada tana ruɗarku kuna tauyewa kanku hakki indai abu ba ubangiji bane ya haneku ga aikatawa mussamman bangaren neman ilimi ko dogoro da kai ka da kuyi wasa da shi sam sam kuma In sha Allah kafin in bar kasar nan sai kun zama kwararrun mata na farko da a bangaren na ura kaf nigeria ba iya Niger state ba babban burina shi ne kusa aranku za ku iya."
Tafa masa suka fara yi cike da jin dadi.
Farouq yana komawa office ya tarar da Javed zaune suka shiga hira yake bashi labarin yadda yake jin dadin tambayoyi da nutsuwar da Meemah ta ke yi "Ga dukkan alamu yarinyar na da basira sosai ba laifi."
Javed ya ce,"Gaskiya nima na lura da hakan,ni fa ba don kar ace na cika azarɓabi bama sai ince ni tamun kamar in shiga daga ciki amman kuma inna tuna yanayin gidanmu sai inji ban da kwarin gwiwa hakan yasa ma ni ko tunanin aure ban sa a gaba ba domin ina gudun kada inje in faɗa kogin da zan azabtu kuma in azabtar da 'Yar da mutane."
Farouq ya ce,"Ban gane ba, Ke nan hatta matar aure ma ba ku da hurumin zaɓa sai dai a zaɓa maku?"
Javed ya ce,"Kwarai kuma Mai martaba ne da kanshi yake shedawa mutum ya je ya ga 'Yar wane kaza su sasanta kuma dole sai jinin sarauta,kuma ni sam lamarin sarautar nan bai taɓa birgeni ba shiyasa na ke jin dadin kasancewa da Abba Malik rayuwarsa ba tsanani sam."
Farouq ya numfasa kafin ya ce,"Lallai abun babba ne shawarar da zan baka kawai shi ne ka dage da addu'a domin babu abun da yafi karfin ubangiji in yaso sai ka ga ka auri yarinyar da kakeso take sonka cikin aminci ba tare da takura ba."
Javed ya ce,"Hakane kam In sha Allah mussamman yarinyar tun farkon ganina da ita nake kwana nake tashi ina daurewa ne kawai."
Farouq ya yi dariya,"Ka bayyana a gareta kawai sannan ka mikawa ubangiji yakinin cewa indai ita alkairi ce a gareka zaka sameta."
Javed ya gyara zama,"Ko?"
Girgiza masa kai Farouq ya yi yana murmushi.
Javed ya ce,"Yess ban taba samun kwarin gwiwa irin ta yau ba,na gode sosai Oga ashe kai fa ka shahara ta ko wanni fanni daga yau za a fara wasan In sha Allah. "
Farouq ya ce,"Yawwa wai Janinah bata School ne na kullum tana gida."
Javed ya ce,"Eheen ai a ƙa'idar gidan Maza ne kadai ke da ikon yin karatun jami'a mace na gama sakandari aure ake yi mata kawai ita ma yanzu Arham kawai take jira ya kammala digirinsa sai ayi masu aure amman ta samu ta yi School dinnan ta samu training akan computer shi ma hakan sai da Abba Malik yasa baki da kyar Mai martaba ya amince shi ma na wata uku kacal ta yi acewarsa karatun ba wani amfani zai mata ba domin a gida zata zauna ta haihu ta kula da yaranta."
Farouq ya ce,"Huh Abubuwan da yawa ashe amman kuma shekararta nawa ne ma wai?"
Javed ya ce,"wannan shekarar zata cika 17."
"Ikon Allah baya karewa,amman ko da an bari ita ma ta dan kara karatun zai fi ko da bangaren computer dinne anan ko shekara ta yi."
Farouq ya fada.
Murmushi Javed ya yi ya ce,"Hmm ba ka san gidanmu bane har yanzu."
Alamar shigowar kira Farouq ya gani.
Yana dubawa ya ga Zoe ce murmushi ya sake a zahiri kafin ya dauki wayar.
"Our Own pilot yau an tuna dani ke nan."
Gajeran tsaki Zoe ta yi kafin ta ce,"Ba wani nan,wato kana Nigeria ba labari sai da mu ka yi magana da Khalil ya ke shedamun kana Nigeria ."
Farouq ya ce,"Eh wallahi a lokacin i try to reach you but bana samun ki seems you're off and ban san wani da zan iya tuntuɓa ba."
Zoe ta ce,"Oh Yeah I have been bedridden for two weeks So wayoyina duk suna kashe."
"Subhanallah yanzu ya jikin to? Fatan dai ya yi sauki."
Cewar Farouq.
Zoe ta ce,"Eh har ma na koma kan aiki."
Farouq ya ce,"Ma sha Allah yanzu yaushe zamu hadu? Zaki shigo ta Nigeria ne?"
Zoe ta ce,"E to bana ce ba amman zan duba jadawalina daman ina so ka dan seta mun wani abu a system dina amman dai za muyi magana zuwa dare ma I will chat u."
Farouq ya ce,"Okay Byee."
Javed na kallonsa tunda ya fara wayar har ya gama.
"Oga ko dai Madam ce wannan irin shauki tunda ka ga kiran fa kaketa murmushi har yanzu."
Farouq na dariya ya ce,"Nop wannan kawatace fa ai ni ban da Madam duk wacce ta nuna tana yina kawai binta na ke."
Javed ya ce,"Kowa darling kenan amman ni dai duk da haka wannan fa kila ta dabance."
Murmushi kawai Farouq ya yi ba tare da ya ce masa komai ba.
Suna tashi zasu tafi gida kamar yadda Farouq ya faɗa bai fasa ba sai da ya yi wa Hajiya Kaka siyayyar ta, har da shawarman kuwa sannan suka tafi.
Suna zuwa ya bata, sosai ta ji daɗi ta karɓa tare da saka masa albarka har ma da ɗan taka rawar ta daga zaune.
Sun sha hira sosai don a part ɗin nata ma suka ci abinci, suna cikin cin abincin ta ke cewa. "Bikin Sallar Gani fa ya zo, muna daf da tafiya Bida, don an fara shirye-shiryen tafiyar, ka ga idan na tafi zan yi kewar ka domin muna yin kusan sati a can. "
Da mamaki ya ce. "Mene kuma bikin sallar gan
Hajiya Kaka ta ce. "Biki ne na Al'ada da ake shiryawa kowacce shekara acn gidan Baban Mai martaba da ke Bida, dukkanin mu za mu tafi can har sai an kammala shagalin kafin mu dawo nan mu yi namu."
Farouq ya ce. "Ai ko nima zan je don ina son ganin al'adunku na gargajiya sosai abubuwan suna birge ni."
Haɗa ido Javed da Hajiya kaka suka yi domin sun tuna cewa Mai Martaba ya haramta masa kasancewa a cikin su a koma mene ne.
Gudun ka da maganar ta ja Javed ya yi saurin katsewa tare da faɗin. "Oga dare fa ya yi maganarku kai da matar nan taka ba karewa za ta yi ba, kawai ka zo mu tafi Please. "
Dariya Hajiya Kaka ta yi ta ce. "Kai dai ka faɗi gaskiya kishi kake ya zo ya ƙwace maka mata, yo kai ma da za ka riƙa shigowa da baƙar leda ai da mun sasanta ko da rabin igiya ɗaya ne in barma."
Dariya suka yi Farouq ya tashi yana. "Na jima da fahimtar sa ai, karki damu 'yan matana ni kaɗai ma na ishe ki."
Dariya suka yi duka kafin nan suka yi mata sallama suka fice.
Suna zuwa ɓangaren Javed suka baje a falo.
Farouq ya ce. "Yawwa gobe Sunday za mu fita yawo dai in ga gari ko? Mussamman river niger, ina so na gane wa idona, na ji an ce Mungo Park ne ya fara gano rafin ko?'
"A'a Gaskiya, asalin waɗanda suka fara gano rafin Richard Leander ce da kuma John Leander kwai dai..."
Kafin Javed ya ƙarasa magana wayarsa ta yi ƙara, yana dubawa ya ga kiran mai Martaba ne ke kiransa.
Tashi ya yi da sauri ya na. "Mai Martaba ne ya ke kira na, bari na je na ji."
Ya ƙarasa maganar yana amsa wayar tare da ficewa.
Numfasawa Farouq ya yi a zahiri ya ce. "Bikin Sallar Gani, tabbas duk yadda za a yi sai na kasance a wannan shagalin, zan iya samun wani bayanin na san."
Ya kai ƙarshen maganar yana ɗaga kai sama.
Kamar wanda aka tsikara ya miƙe tare da shigewa bedroom, waya ya fara yi wanda ba mai jiyo abin da ya ke fadi daga shi sai wa inda yake wayar da su, ya kwashe kusan awa guda yana wayar kafin ya katse ya koma kan System.
♡♡♡♡♡
Ƙarfe huɗu na yamma dukkanin su sun yi wanka sun shirya, sun yi kyau matuƙa.
Farouq sanye yake da ƙananun kaya kamar yadda ya saba saka wa, yayin da Javed ya shirya cikin manyan kaya domin ba sosai mai martaba ya ke son ganinsu sun yi shigar ƙananun kaya ba.
Kai tsaye River Niger suka nufa.
Javed ne ke driving din su suna tafe suna hira har suka isa.
Cike da mamaki Farouq da ya ga wasu manyan motoci na tafiya ya ce. "To su kuma waɗannan manyan motocin fa?"
Ya yi magana tare da kallon Javed.
"Suna dawowa daga gabas da kuma kudu ne, don nan din shi ya zama kamar meeting point ɗin su, don ko lokacin da ka turo taimakon nan da na baka labari, ai a nan aka yi hatsarin.
Da yake yawanci 'yan cirani suna ƙyashin biyan kuɗin mota, shi ne suke raɓuwa gefen manyan motocin da ke ɗauko mai (petrol) wanda ƙarshe duk kusan a nan suke rasa rayukansu, babban abun takaicin kuma 'yan road safety ɗin maimakon su kula su riƙa hanawa, to da an basu ɗan cin hanci shikenan bakinsu ya yi shiru."
"Lallai suna wasa da rayukansu sosai, Allah ya kyauta! Gashi kuma hanyar na bukatar gyara sosai." Farooq ya faɗa cikin sassanyar muryar jimami.
Kallon sa Javed ya yi kafin ya ce. "Sauƙin ta ma yanzu an dawo da tollgate, ka san shi yana taimakawa sosai da kuɗin harajin da suke bayarwa, ana amfani da shi wajen gyaran titin da tabbatuwar hanya bisa tsari har ma da tattalin arziki."
Kasancewar babu nisa sosai ba su jima ba suka isa.
Suna zuwa wajen kuwa Farouq ya ce. "Ya Subhanallahi! Ai kogin ya fi kyau ma a zahiri fiye da yadda ake Misalta shi da kuma hotunansa da ake ɗauka."
Javed ya ce. "Haka ne kam to ka ga wannan shine kogin Nijar yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dukkanin al'ummar Jihar Niger da Nigeria da ma tarihin yankin, a matsayin jigo. Kogin yana da tasiri sosai a cikin al'adunmu, yana bayar da gudummawa wajen ci gaban tattalin arziki ta fannin noman hatsi da kuma kamun kifaye. Wannan yana nuna cewa kogin ba kawai wani jigon ruwa ba ne, har ma yana da tasiri a cikin rayuwar yau da kullum na al'ummomin da ke zaune a gefensa.
Batun Mungo Park kuma yana daga cikin muhimman abubuwan da suka shafi binciken Kogin Nijar. Mungo Park ya kasance ɗaya daga cikin masu bincike da suka bayar da gudummawa wajen gano ingancin kogin da alfanunsa, amman ba shi ne farkon wanda ya fara ganowa ba Richard Leander da John Leander suna daga cikin waɗanda suka yi fice wajen bincike