5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUAR

CHAPTER 6

by @xayyeesherthulhumaerath

da nazarin kogin, suna bayar da muhimman bayanai game da tasirin kogin a cikin al'umma kuma sune wa inda suka fara gano kogin.

Dukansu, Richard da John Leander, an binne su a kusa da kogin don nuna girmamawa da ƙoƙarin su wajen tabbatar da ingancin kogin da kuma alfanunsa ga al'umma. Wannan yana nuna yadda kogin ya zama wani muhimmin ɓangare na tarihin al'ummar Niger, tare da bayar da gudummawa ga al'adun gargajiya da zamantakewar al'umma.

Sarakuna da Al'ummomi baya ga Richard da John Leander, akwai sarakuna da sauran al'ummomi da suka yi fice a cikin tarihin kogin. Waɗannan mutane sun taka rawa wajen tabbatar da cewa kogin yana ci gaba da zama jigon rayuwa da al'adu a yankin. Kogin Nijar yana da matukar tasiri a cikin al'ummomin da ke kewaye da shi, yana zama tushen rayuwa da ci gaban al'umma.

A taƙaice, Kogin Nijar yana da matukar muhimmanci ga al'ummar Jihar Niger , yana bayar da gudummawa ga al'adunmu da ci gaban tattalin arziki, tare da kasancewa jigo a cikin tarihinmu."

Farouq ya ce,"Maddalla! Amman ya nake ganin kamar electric power Station?" ya faɗa yana ƙarasawa ta wajen.

Dariya Javed ya yi kafin ya ce.

"Ah lallai kana wasa da mu ,ba ka san cewa mu ke da tushen wutar lantarki ba? Mu ke bawa Nigeria kaf wutar lantarki, mu ke da electricity Hydro Electric power station kenan yana samar da wurar lantarki da ya kai 760 megawatts (MW) wanda ya taimaka wajen samar da wutar a ƙasar nan tun cikin shekarun da aka gina ta a 1960s sannan tana da matakai biyu na bada wuta da kuma tasiri wajen rage katsewar wutar a Nigeria."

Farouq ya ce,"Ni na isa inyi wasa da ku ni fa son garin nan na ku kara shigata yake a kullum wallahi."

Suka ci gaba da magana suna tafiya.

Wasu mata suka gani sunata wanke ƙasa akan carpet.

Farouq ya ƙarasa gabansu da sauri yana,"Wannan fa me suke yi?"

Kafin Javed ya yi magana ɗaya daga cikin matan ne ta ɗaga kai ta kalli Farouq ta ce. "Zinare muke cirewa." Ta karasa maganar tana nuna masa yadda suke amfani da chemical suna cirewa.

Bude baki Farouq ya yi yama rasa abun cewa sai.

"Wow!"

Muryarta ta katse masa mamakin nasa ya ji ta na faɗin. "Ka ga yadda a ke gasawa ma."

Ta faɗa tana sakawa a abun gashin kafin ta ce. "A can sama kuma akwai inda ake narkawa in kana so za mu je in nuna maka."

Javed ya katse su da fadin,"Aa ba mu da ishasshen lokacin yammata, ya kamata mu koma gida ai dai ka ga wannan ka kara yarda mu ɗin mu ne."

Farouq ya ce. "Gaskiya kam wannan lamuran naku ko ƙasashen waje albarka."

Godiya suka yiwa matan Farouq ya yi masu kyautar kudi kafin suka juya Javed ya ce. "Ai ko gonar Mai Martaba akwai wa inda suka zo suka ce sunga zinare amman ya hana su sam har cewa suka yi ko nawa ne zai saida zasu iya siya amma ya ƙi amincewa wai gonar gadonsu ce."

"Amman ko da Mai Martaba ya sa ana yi masa aikin ya buɗe ƙaramin kamfani karkashinsa da za a samu alfanu sosai, don wannan babbar dama ce domin haɓaka arziƙin gidan." Farouq ya faɗa

Javed ya ce.

"To ka san shi da kafiya da tsayawa a kan batunsa, 'yan uwansa ma basu isa su ce ba bare kuma mu, lamarin mai martaba sai dai kallo."

Da wannan hirar suka shiga mota, suna cikin tafiya motar ta samu matsala ta tsaya ga dare ya yi gashi gari ya haɗe da hadari kan kace miye ruwa ya kece kamar da bakin ƙwarya.

Ganin ruwan bai da shirin tsayawa ga shi dare ya yi haka dukkaninsu suka fita a motar domin nemo bakanike,

sunyi neman duniya sun rasa saboda ruwa kowa ya tafi gida kuma dama dare ya yi gashi ba a wajen da mutane su ke wulgawa sosai suke ba.

Can tunanin Zeeyter ne yazowa Farouq ya kirata ya faɗa mata abun da ke faruwa.

Ta kirashi video call ita da Haiydar suka ga yanayin motar, da yake Allah ya taimaka Javed na dauke da box ɗin kayan gyara a motar, nan Zeeyter ta saka yi ɗauko tana faɗa masa abun da zai yi shi ma Haiydar na taimaka masu har suka samu suka gyara motar da ƙyar.

Sai wajen ƙarfe ɗayan dare kafin suka koma Gidan Sarkin Al'adu, suna shiga Javed ya kalli agogon hannunsa zuciyarsa ta yi wani irin mummunan faduwa domin ya san a ƙa'idar gidan ba a wuce karfe goma a waje gashi yau shine har ƙarfe ɗaya, sosai jikinsa ya yi sanyi mussamman da ya hango wuta a falon Mai Martaba.

Yana gama Parking suka fitowa gabaɗaya a jiƙe ruwa na bin jikinsu.

Ɗaya daga cikin dogaran Mai Martaba ne ya ƙaraso garesu da sauri yana faɗin.

"Ranka Ya Dade Mai Martaba da Jama'ar gida suna jiranku a babban falo."

Kallon Farouq ya yi cikin dauriya da ƙarfin hali ya ce. "Oga kai ka tafi ɗaki sai na...

Kafin ya karasa dogarin ya katse shi da faɗin. "A'a ai ance dukkaninku ake son gani Ranka yaɗaɗe."

Nan fa zuciyar Javed ta fara bugawa cikin sauri.

Muryarsa na rawa ya amsa da ,"Okay." Kallon Farouq ya yi yana ,"Mu je Oga."

Suna shiga suka ga Mai Martaba tsaye,Hajiya Kaka,Mammah,Kilishi,Abba Malik,Janinah da kowa.

Kafin Javed ya ankare sai jin saukar mari ya yi a kumatunsa.

Zai kara masa wani da sauri Abba Malik ya tare gaban Javed yana,"Ayi masa afwa Yaya."

Dakatar da shi ya yi da hannu alamun ya matsa ba ruwansa.

Matsawa gefe Abba Malik ya yi yana kallon ikon Allah.

Mai Martaba ya kalli Javed cike da tuhuwa ya fara jera masa tambayoyi,"Ba ka da hankali ne? na ce ba ka da hankali ne? ko kuwa ka samu taɓuwar hankalin da ya mantar da kai cewa kai ahalin wannan gidan ne?"

Javed bai iya cewa komai kansa na ƙasa.

Cikin dagun Murya Mai Martaba ya ce,"Za ka bani amsa ko kuwa?"

Cike da firgici Javed ya durkusar da gwiwarsa ƙasa yana,"Ayi mini afwa Mai Martaba akasi aka samu motata ta lalace a hanya." Ya faɗa muryarsa na rawa.

Mai Martaba ya ce,"Amman ka fi kowa sanin doka da tsarin wannan masarautar ko? Daga Yan Uwana har Yayunka da na haifa babu wanda ya taba gigin karya mun doka sai kai? Kana jin ka isa kenan ko kuma zama da wancen ne ya janyo?"

Ya karasa maganar yana nuna Farouq dake tsaye yana bin kowa da kallo yana ganin ikon Allah.

Caraf Kilishi ta ce,"Yoo shi ne ma mana shi ne zai ja shi yawon ma kuma ni ina zarginma gidan rawa ya kai shi domin yanayin yaron nan sam ba na kirki bane kila ma ba wani dan kasar waje bane yafi kama da sadakayalla,kana ganinsa ka ga munafu....

Tsawar da Abba Malik ya yi mata ne yasa ta shirun dole.

Cikin ɓacin rai ya ce,"Wato ke dai babu alkairi a bakinki ko? Sam ke ba kya nufin kowa da alkairi ne sai sharri? Ki rabani da wannan mummunan dabi'ar taki Kilishi."

Kau da kai ta yi tana faɗin,"Ai daman kai baka son gaskiya ni kuma wallahi ko za a mutu sai na faɗi gaskiya ehee."

Shi dai Farouq yana ta binsu da ido.

Gyaran muryan da Mai Martaba ya yi ne yasa dukkaninsu yin shiru.

Jan numfashi ya yi, cikin isa da izza ya ce,"Bakonka na da zaɓi biyu, ko ya bi dokokin wannan masarautar ya zauna ko akasin hakan ya barta,sannan daga yau ba za ku kara fita daga kai sai shi ba za a hadaku da ɗaya cikin dogarai yana lura da motsinku in aka kamaku da aikata wani abun da ba daidai ba babu shakka kowannenku ya karbi hukuncin bulala ashirin sannan kuma in an kammala hukuncin bakonka tafiya zai yi ba zai kara zama ba ya tabbata dai kenan muddin yana son zama sai ya bi tsari da dokokinmu."

Yana gama faɗa ya fice.

Tsaki Kilishi ta yi azahiri wanda ya bayyanar da ɓacin ranta ta fice,ita ma Janinah ta bi bayanta.

Sauran matan da mazan ma duk suka fice sai Hajiya Kaka,Abba Malik,Farouq da Javed.

Abba Malik ya kalli Farouq ya ce,"Malam Umar sai dai ana hakuri fa nan ba kamar can ba mussamman wannan masarautar ana riko da al'ada sosai tamkar addini. "

Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Hakan ma yana da kyau ai."

Hajiya Kaka ta ce,"Gashi duk kun jike,ku je kuyi wanka ku canja kaya ku samu ku kwanta in kuma ba za ku iya ba ko mu je in muku?"

Dukkaninsu basu san lokacin da dariya ta subuce musu ba da jin maganar Hajiya Kaka duk da cewa basa cikin yanayi mai daɗi.

Abba Malik ya ce,"Hajiya ke ina ke ina yiwa garadan nan wanka,mu je dai ki kwanta."

Ya karasa maganar yana riko hannunta.

Taɓe baki ta yi ta ce,"Yo miye a ciki dukkannsu mazajena ne ai in sun gagara sai in saɓesu tas ba don jikin tsufa ba ma har goyasu zan da majanyi."

Abba Malik ya ce,"Ah lallai wa innan Mazaje ana ji dasu."

Farouq ya ce,"Yanzu dai mun yafe ki je ki huta sai da safe ko yan matana."

Ya karasa maganar yana bata hannu suka tafa kafin suka fita suma suka koma bangarensu.

Bayan dukka sunyi wanka sunyi sallah gabadaya ko abincinma sun kasa ci mussamman Javed ya zauna ya yi shiru a falon.

Farouq ya zauna kusa da shi yana,"Ban san ta yadda zan fara baka hakuri ba domin dukkanin abun nan da ya faru nine sila,Don Allah ka yi hakuri gobe zan koma hotel in sha Allah ba zan so ace sanadina kana samun saɓani da family dinka ba."

Javed ya ce,"Ya Subhanallah ka daina fadan cewa za ka tafi hotel,ba wani hotel din da zaka tafi kuma ni ba abun da ka zama sanadi a gareni sai alkairi ni kawai na gaji da wannan tsarin ne na gidan nan ba zan jure ci gaba da rayuwa cikinsa ba ace wai mu bamu da yancin kanmu kwata-kwata? Ba mu isa muyi rayuwar da muke so ba sai wacce aka tsara mana? Ba zai yiwu ba ina ji araina akwai abun da ake aikatawa da ba daidai ba cikin wannan masarautar."

Farouq ya ce,"Ni dai ka yi hakuri kuma ka maida komai ba komai ba indai da gaske baka so in koma hotel to ka ci gaba da bin umarnin Mai Martaba za ka ci ribar rayuwa."

Javed ya yi ajiyar zuciya ba tare da ya ce komai.

Tashi Farouq ya yi ya dauko masu Drink da snacks ya mikawa Javed kafin ya zauna yana,"Yawwa ni kam ya batun wancen Bikin Ganin ne? yaushe ne? Ina son zuwa fa."

Javed ya yi guntun tsaki "wallahi ni na manta ma amman dai a cikin satin nan ne za a tafi ni fa lamuran gargajiyan nan ba sonsu nake ba a dole nake bi,kuma ni yanzu ban san ya za muyi ba mai martaba ya ce ka da ya kara ganinka akan abubuwan da suka shafi gidannan da ma Al'ada."

Farouq ya numfasa,"Alright ba matsala karka damu dani."

Javed ya ce,"Amman kuma kana son zuwa ai."

Farouq ya yi murmushi,"Eheen ina so amman kuma son da nake zai iya ja maka matsala ni kuma bana so in kara saka cikin wata matsalar."

Javed ya ce,'Kasan yadda za ayi?"

Farouq ya girgiza kai,"Aa sai ka faɗa."

"Zan bi ayarin yan gida mu tafi kai kuma sai in hadaka da wani ko cikin abokaina ne ka ga ba wanda zaiyi tunanin zaka je sannan kuma sai ka yi kokarin yadda baza ka gamu da Mai Martaba ba, ko kilishi dama sauran yan gidan."

Farouq ya ce,"Ba matsala zan so ma inje ni kadai domin in kara ganin gari karka damu komai zai tafi daidai In sha Allah."

Da haka suka dan yi hira kafin Javed ya fara tafiya daki ya kwanta ya bar Farouq shi kadai.

Waya suka dunga yi da Zoe yana tsokanarta tana tsokanarsa sunata dariya sai da ya kalli agogo ya ce,"Madam yanzu a Nigeria karfe uku ne,ina son inyi Tahajjud Prayer."

Zoe ta ce,"Ah Har cikin dare kuna Sallah kenan ban da guda biyar din da kuke yi?"

Farouq ya ce,"Nop Wannan Ita ba farillah ba ce sunnah ce ma ana ba wajibi ba bace amman kuma tana cikin sallar da ake matukar so a cikin musulunci kuma tana da matukar muhimmanci domin yana ƙara kawo kusanci tsakanin bawa da ubangiji sannan ana yinta ne karshen rabi na dare lokacin aka dauka a matsayin mafi alheri don sallah da addua tare da tabbatuwar biyan bukatu domin a lokacin Ubangiji yana amsa bukatun bayinsa babu shamaki."

Zoe ta numfasa ta ce,"Da kyau kuma har guda nawa ake yi?"

"Ba adadi zaki iya yin raka'a biyi ma kiyi sallama ki roki ubangiji shikenan wannan raka'a biyun ta fi duniya da ma abun da ke cikinta inko kina so zaki iya yin takwas har fi ma." Farouq ya faɗa.

"Kenan dai ita wannan sallar in anyita ana samun biyan bukata ko?"

Farouq ya ce,"Yes In sha Allah mussamman kasa aranka zaka samu abun da kake nema din wajen ubangiji. "

Zoe ta ce,"Sai na ji ina son yi da ace ba matsala zan iya da yau na tayaka nima in roki Allah ya biya mun bukatuna kuma ma time dinmu ba daya ba zan iya?."

Farouq ya yi murmushi,"Mai zai hana? Ai kuma yanzun dare ne ba sai lokaci daya ba,yanzu zan je da wayar toilet muyi alwala kiyi duk yadda na yi sai muzo mu yi sallar ma tare."

Hakan kuwa aka yi suka yi alwala yana mata bayani ta dauko gyaranta ta yi rolling ta dauki wani dankwali ta shimfida matsayin sallaya suka fara sallah tana kallon yadda Farouq yake ita ma tana yi har suka idar.

Rufe ido ta yi ta daga hannu sama tana addua ,"Allah ka bani komai da komai ka kara mun kyau,kudi,jin dadi,lafiya,hutu da komai da komai Allah jikina ya yi kyau sosaiii."

Da karfi take adduar idonta a rufe.

Dariya ce ta suɓucewa Farouq ya ce,"To Amin wato harda kyau bayan wanda kike da shi."

Alama ta masa da hannu a baki ,"Shiiiii." Ka yi shiru.

Ta ci gaba da cewa ,"Allah kasa in samu masu zuwa Nigeria in dauko Farouq in gudo da shi."

Shi dai kallonta yake kawai yanata dariya.

Sai da ta gama jero adduointa kafin ta ce,"Eheem kai ba kasan ba kyau mutum na addua ana magana ba zaka sani."

Ya yi dariya,"To ai na ga kin dage ne harda batun kyau."

Sigina ta masa ta ce,"Eheen naka wasa ne sai ka kasa ganeni ai innazo daukanka." ta karasa maganar tana hamma.

Farouq ya kara dariya kafin ya ce,"To Shikenan yanzu dai kije ki kwanta ni zan fara aiki."

"Alright Goodnight. "Ta fada.

Farouq ya ce,"Nighty Night byee."

Da haka suka katse kiran ya dukufa kan System kamar yadda ya saba.

Yana kunnawa ya ga alamun yana kokarin kawo masa hari system din ta nuna akwai matsala.

Cike da mamaki ya fara bi ya rasa gane wane ne ke son bincikar bayanansa duk da cewa yasan ba za a taɓa samu ba muddin in ba shi ya bada kofar hakan ba.

Abun da ya matukar bashi mamaki shine da ya duba location ya ga abun da ake son yi din a gidan ne.

A tunaninsa error ne ko kuma location dinsa system din ke basa amman duk dubawan da zai yi babu shakka mai kokarin bincikarsa na cikin gidan.

Dakin Javed ya je ya gansa yana barci cikin kwanciyar hankali har system dinsa ya kunna amman bai ga wani abu makamancin hakan ba.

Ji ya yi kansa ya fara ciwo domin abun ya daure masa kai matuka.

Ya dafa kansa yana zama gefen gadon tare da tafiya dogon nazari.

Misalin karfe Goma na safe Kilishi ce zaune da Janinah a falonta.

"Aunty Kilishi ni wallahi jiya na ji haushi sosai da Mai Martaba bai kori wancen gayen ba."

Tsaki Kilishi ta yi kafin ta ce,"Ke ko ni Janinah? Wallahi da abun na kwana araina ban san dalili ba amman kullum inna gansa kara tsanar yaron nake wallahi amman kar ki damu faɗan yanzu nawa ne ba naki ba,ni na san matakin da zan dauka sai ya yi danasanin zuwansa kasar nan inma da gasken zuwa ya yi bare kuma shigowarsa gidan nan."

Ta karasa maganar tana cije baki.

Janinah ta ce,"Aunty ki fadamun in tayaki mana."

Murmushi Kilishi ta yi kafin ta ce,"Kar ki damu zan fada miki bari in kammala shirina."

Farouq na office a digital craft kokarin bincikar mai bin diddigin sa yake tun jiya yanata fama karaf ya ji wayarsa na kara alamar shigowar sako.

Yana dauka......

Ya ga text message ne aka turo "Ko da ka shahara tarwatsa tsari da shirin wasu,ina jadadda maka cewa ba za ka taɓa kaucewa nawa ba,kila kana jin kanka cewa yanzu kana rayuwa ne a fili saɓanin cewa ni kallonka nake a cikin rami mai zurfi takurararre cike da duhu mara misaltuwa."

Murmushi Farouq ya yi ya gyaɗa kai kawai ya ajiye wayar yana ci gaba da duban system dinsa.

Shigowar Javed ne ya katse shi da fadin,"Oga Mun gama,lokacin ka ne yanzu."

Tashi ya yi yana ,"Okay to."

Tashi ya yi ya tafi lecture room din.

"Good morning class."

"Morning Sir."

Suka amsa

"OYaa On your systems Yau za mu yi bayani ne akan White Hat Hacker,na san da cewa dukkanin ku kun san wane ne White Hacker to amman ta ya yake gudanar da aikinsa na shiga na'ura? Me da me yake bukata?"

Ya karasa maganar yana zama gaban system dinsa kafin ya ci gaba

"Karku manta sai har an bashi izini kafin yake fara gudanar da aikinsa kuma abu na farko da yake yi shine Binciken tsaro wato

(security assessment) sai kuma gwajin shigarwa (penetration testing) a karkashinsa shi ne ake kirkirar kwayoyin yanar gizo da kirkirar hanyoyin kariya masu inganci da karko

Kayayyakin amfani da aikinsu