5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUAR
CHAPTER 7
wato Utilizing tools
Na farko akwai Nmap: Don nazarin hanyoyin sadarwa da gano na'urorin da ke haɗe (for network scanning and identifying connected devices)
Na biyu Metasploit: Don gunadar da hare-hare da kuma gwajin rauni (for executing attacks and testing)
Na uku WireShark: Don nazarin zirga-zirgar bayanai a cikin hanyar sadarwa (for analyzing data traffic within the network)
Sai kuma Access Control tsarin kariya ke nan
Suna amfani da tsarin kariya domin tabbatar da cewa suna kan tsarin da aka ba su izinin aiki akai.
Sannan Tantancewa da rahoto ma ana Evaluation and Reporting
Bayan an kammala gwaji ana tantance bayanai kafin a rubuta rahoto wanda ya kunshi raunin da aka gano da shawarwarin yadda za abi domin yin gyara.
Wannan kenan kafin kuma su shiga kan aikin inganta tsaron,yana da matukar mahimmanci abi wannan matakan domin in babu su ba za a taba samun abun da ake nema ba kenan kuma akwai bukatar ku fahimta da kyau."
"Yes Sir."
Suka furta.
Tun kafin ya bada izinin tambaya Meemah take ta daga hannu.
"Go on Memah." Farouq ya fada.
Tashi ta yi ta ce,"Sir yanzu kenan ko waya tace nasa security wanda ba mai karfi ba akwai wanda yana iya zuwa zai cire?"
Farouq ya ce,"Sosai ma,musamman ku da ke sa password ko pin mara karfi fada mun password dinki inji yanzu zan iya fada miki cikin minti nawa zan iya kwamushesa ba tare da kinsani ba ma ."
Ta ce,"Mima12 ne Sir."
Farouq ya ce,"A cikin 11 minutes zan iya cire password din wayarki ko kasa da hakan ma,shiyasa da an samu kuskure an sace wayoyinku cikin sauki ake kwasar bayananku, yanzu tunda kin fadamun wannan canja wani ki bani in gwada cirewa."
Canjawa ta yi ta bashi wayar.
Cikin 8minute kuwa ya cire password din sunata mamaki.
Meemah ta ce,"To Sir a koya mana yadda ake cirewa kuma a koya mana yadda zamu sa security mai kyan da ba za a iya canjawa cikin sauki ba."
Farouq ya ce,"For now dai yanzu koya muku yadda zakuna duba karfin password kafin kusa ako ma miye naku amman yadda ake cirewa ba mu zo nan ba."
Suka amsa da ,"Okay Sir."
Farouq ya ce,"Yawwa dukkanin ku ku shiga Google a systems din ku ku yi searching Password Strength Meter. "
Cike da zakuwa dukka suka yi.
Farouq ya ce,"Kowa ya yi?"
Suka amsa
"Okay za ku ga an rubuta TYPE A PASSWORD ko kamar haka."
Ya nuna masu a system dinsa.
Ya ci gaba da fadin,"Yawwa nan zai na fada mana karfin password din da zamu rubuta da lokacin da za a iya dauka kafin a iya cirewa yanzu ni bara in gwada rubuta nawa so simple amman kuma very strong bari mu ga na rubuta [U@M@R_F@R@Q],kun ga dai yadda na rubuta ko me kuka sunsa?"
Karantawa suka yi duka
"Very Strong Password,Time to track your password 1million years. "
Suka karasa fada cike da mamaki suna bude baki.
Farouq ya ce,"To yanzu kowacce ta rubuta a system dinta muga."
Dukkaninsu suka rubuta hakan ya fito sunata jin dadi.
"To yanzu kunga anan zaku iya rubuta kowanni kalan password ku duba ingancinsa kafin kusa a wayarku ko a system dinku zai na indicating maku in mai kyau ne ko akasin hakan."
Da murnar su suka ce,"Thank you Sir."
Fita ya yi ya barsu sunata faman gwada password kala kala.
Farouq na komawa office ya samu Javed na waya Yayansa ya kira yana sheda masa cewa gobe zasu wuce bida domin jibi za a fara bikin gani.
Javed na gama wayar ya ce,"Yawwa ka ga daman yau za a tafi hutu ba mu da matsala dangane da makarantar nan domin jibi ne ma wai ashe za a fara bikin zamu koma gida da wuri domin inje in fara shiri."
Farouq ya ce,"Okay to shikenan Allah ya kai mu amman ni nidai ina so inji tarihin garin bida dinnan da aketa batun acen asalin sarki yake."
Javed ya ce,"Wannan in ka samu Hajiya Kaka ai labarin tarihi sai ka ture ta sha bamu amman yanzu innace zan fada ma na tabbatar da cewa ba zan baka in details kamar ita ba."
Farouq ya ce,"Ai ba na ma son naka ni da nake da Mata guda,yau muna komawa a part dinta zan tare gaskiya. "
Dariya Javed ya yi ya ce,"To mai mata."
Da haka suka kammala wuninsu na ranar har suka koma gida kamar yadda mai matarba ya umarta kuwa akwai mai binsu duk inda zasu je.
Bayan sun koma masarauta sun idar da sallar isha Kai tsaye bangaren Hajiya Kaka suka nufa tana zaune an wage kafafu da hannaye duk an rufesu da leda.
Farouq ya bude baki,"Ah Me zan gani?"
Hajiya Kaka ta ce,"Lalle mana ado ai na yi maka angon."
Zama ya yi daf da ita yana,"Ai kuwa dole in biya kudin wannan ado."
Hajiya kaka ta cuna karamin bakinta tana,"Yoo ba ma dole ba ai wajibi ne a gareki."
Farouq ya ce,"To ni yanzu ba ma wannan ba so nake abani tarihin kasar bidan nan tunda ni dai ba zan samu zuwa ba aiki zai mun yawa."
Hajiya Kaka ta gyara zama,"Tabbas kuwa ka zo gidan tarihi ka karkade kunnuwanka da kyau ka saurareni."
Hannu Farouq yasa a kunnuwansa yana karkadewa suna dariya.
Hajiya Kaka ta ce,"Yawwa Bida na ɗaya daga cikin birnin da suke sahun farko a jahar niger a Nigeria.
Domin ta kasance matsayin cibiyar kasuwanci tun daga zamanin da kakanni da kakannin kakanni domin ta kasance hanya mai mahimmanci ga masu safarar kayayyaki daga arewa zuwa kudu.
Haka kuma birin yana da tarihi mai zurfi a fannin addini, tare da kasancewar shi a matsayin wurin taron al'ummar musulmi.
Bida an kafa ta a farkon ƙarni na 19 kuma ya zama sananne a lokacin Jihadin Fulani da Usman dan Fodio ya jagoranta. Birnin ya zama muhimmin cibiyar kasuwanci da ilimin Musulunci, wanda ya taimaka wajen yada addinin Musulunci a wannan yanki. Masarautar Nupe, wanda Bida ta kasance cikin ta, ta taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin siyasa na tsakiyar Najeriya.
A cikin shekarun baya bida ta kasance gida ga masarautar Bida wacce ta kasance daya daga cikin manyan masarautu a Nigeria kuma masarautar ta yi fice wajen bunkasa al'adun gargajiya da kuma gudunar da harkokin zamantakewa a yankin.
Sannan tana da kyawawan wurare da suka shahara kamar su gidan sarauta da kuma wuraren tarihi da ke jawo hankalin masu yawon bude ido haka kuma birnin na da alaka da harkokin noma inda manoma ke samar da kayan amfanin gona da dama to wannan ita ce bida kuma kuma garin su Matar Abbanku Malik kenan domin yar sarki ce wato babban sarki kenan da su mokwa karkashinsa na ma manta Jahar bida na bawa Al'adu muhimmici matuka
Bida tana da shahara wajen sana'o'in gargajiya, musamman a fannin tukwane da zane-zane. Hakanan birnin yana da shaharar bukukuwan al'adu na shekara-shekara, wanda ke nuna arzikin al'adun mutanen Nupe, ciki har da kiɗa, rawa, da tufafi na gargajiya kamar dai yadda yanzu muke shirin tafiya bikin Gani.
Hakazalika
A zamanin yau, Bida ta ci gaba da girma, tana zama muhimmin cibiyar gudanarwa da kasuwanci a Jihar Neja. Hakanan birnin yana da manyan makarantu, wanda ke taimakawa wajen bunkasa ilimi a wannan yanki kasan duk da mun tsufa amman ba ma gajiya da sauraren redio domin jin ya duniyar da lamuran cikinta suke tafiya."
Farouq ya numfasa ,"Ma sha Allah ai kuwa tarihi ya fita fes to amman yanzu ke nan ban da mokwa akwai wasu garuruwa da ke karkashin bida?"
Hajiya Kaka ta ce,"Kwarai kuwa akwai Mokwa nan ke nan inda muke sai
Katcha
Yawwa akwai agaie ma dukkaninmu muna karkashin masarautar Bida ne."
"Kenan yanzu duk yan garuruwan cen ma zasu tafi bida shagalin bikin Gani?"
Farouq ya fada.
Hajiya Kaka ta ce,"Kwarai ma kuwa ai nan ne tushenmu duk."
Farouq ya ce,"To shi kuma wannan Bikin Ganin fa mene ne ma anar yinsa? Kuma kwana nawa za ayi ana yi?"
Tashi Javed ya yi yana,"Oga in ka shigo ma hadu na lura wannan zantukan naku ba mai karewa ba ne."
Kafin Farouq ya amsa caraf Hajiya Kaka ta ce,"Yo dole ka tashi mana kana nan da takunannen hanci kamar sabuwar kalwa yara basa son jin tarihi da al'adunsu sam sam bare ma ku koyi riko da su sai shegen.... kafin ta karasa tusa ta suɓuce mata ga shegen wari ga kara kamar an fasa bomb.
Javed ya kalleta ya ce,"Oku (sannu) ganin yadda ta karkace kafin ta sambado tusar yasa bayan ya ce mata sannu ya fashe da dariya,Farouq ma dai ya gagara rike dariyar toshe hanci ya yi yana yi.
Tsaki Hajiya Kaka ta yi ta ce,"Cuta ce dai na fitar ba wani abu ba kuma kwai na ci dafaffe guda takwas dazu abuna ahto inma zaku bude hanci ku bude wannan iskar da na fitar ma ta albarkace zasu samu."
Da gudu Javed ya fice yana,"ni dai na yafe wa wannan albarka Oga akwasa da kyau."
Ya karasa yana dariya.
Hajiya Kaka ta ce,"Rabu da shi bara in ci gaba da fada ma yawwa Bikin Gani.....l
Bikin Gani na daya daga cikin manyan bukukuwan al'adu da ake gudanarwa a Bida. Wannan biki yana da matuqar muhimmanci ga mutanen Nupe da kuma al'ummar da ke zaune a Bida.
Ma'anar Bikin Gani kuwa
Bikin Gani yana nufin bikin da aka shirya don nuna al'adun gargajiya, kiɗa, rawa, da sauran abubuwan al'adu na musamman. Ana gudanar da wannan biki a kowanne shekara, kuma yana jan hankalin mutane daga sassa daban-daban na Najeriya da ma waje.
A lokacin bikin, ana gudanar da wasannin kwaikwayo, gasa tsakanin matasa, da kuma nune-nunen kayan tarihi. Hakanan ana jin dadin kiɗan gargajiya da rawar al'adu da suka shahara a cikin al'ummar Nupawa.
Sannan Bikin Gani yana ba da dama ga matasa da su yi koyi game da al'adun su da kuma yadda za su ci gaba da su a cikin zamani. Hakanan yana karfafa haɗin kai da zaman tare tsakanin al'umma.
Domin kuwa Bikin Gani a Bida yana zama wata hanya mai kyau ta bayyana kyawawan al'adun gargajiya da kuma taron al'umma, yana kara dankon zumunci da haɗin kai a tsakanin masu halartar biki."
Farouq ya numfasa,"Ma sha Allah abun birgewa kuma kwana nawa ake yi ana shagalin?"
Hajiya Kaka ta ce,"Kwana Uku ne amman mu wani lokacin har mako guda muna yi bida mu huta da ke muna da bangare guda namu da ake ware mana a cen gidan Mai Martaba Babba."
"Gwanin Sha'awa,Yanzu bara in barki ki kwanta in tafi dare ya yi."
Hamma Hajiya Kaka ta yi ta ce,"Aiko kamar ka san na fara jin barci,Bara in kira yarinyar nan ta zo a kunce lallen nan."
Sallama suka yi Farouq ya tafi Javed har ya dade da barci kai tsaye dakinsa Farouq ya wuce.
Gari na wayewa gida ya cika fal anata shige da ficen shirin tafiya Bida.
An jero motoci bisa tsari masu tsaro a gaba kafin motar mai martaba sannan ta sauran mutanen gida.
Farouq na cikin bangarensu ko fitowa bai yi ba tunda
Misalin karfe Ɗaya na rana suka dau hanya bayan sunyi sallah sunci abinci.
Da ke ba tazara sosai awa biyu da mintuna suka yi a hanya kafin suka shiga cikin garin Bida.
Kai tsayen Bangaren da aka tanadar masu suka wuce,suka wuta suka ci abinci sannan suka yi sallah.
Daga nan Mai Martaba Sarkin Al'adu ya tafi ganawa da Sarki Mai Martaba na garin Bida.
Cikin dare Farouq ya isa garin da ke da yamma ya bi motar haya,yana isa TASTE PALACE HOTEL ya sauka domin da ya tambayi Javed hotel mai kyau nan ya yi masa recommending kuma da ya duba google ma ya ga alamun ingancin hotel din hakan yasa ya wuce nan kai tsaye.
Sai da Javed ya tabbatar da cewa Farouq ya iso cikin koshin lafiya kafin hankalinsa ya kwanta ya yi da Farouq dinma akan zai je hotel din su gana ya ki fir gudun kar a samu matsala cewar Farouq haka Javed ya hakura dole ba don ya so ba.
Daren ranar kuwa Farouq bai yi barci ba gabadaya kwana ya yi yana bincike tare da wasu ayyukansa.
Misalin karfe goma na safe ya shirya cikin kananun kayansa ya sanya pacing cap sannan ya dauki wani bakin glass mai dan girma yasa.
Yanayin yadda ya yi shigar zai yi wahala mutum ya ganesa ba in ba wanda ya yi masa sani sosai ba.
Masarautu Bida ya nufa cikin sa'a kuwa yana taran wata taxi cike take da matasa suma can zasu hakan yasa shi jin dadin bin ayarin nasu.
Ya shiga shima tamkar sahun yan gari ya zauna cikin wa inda suka je tare,Javed ne ya masa test kan har yanzu bai gan shi ba.
Farouq ya maida masa da cewa ,"Ni ko na ganka cikin tawagar mai martaba ya karasa rubutawa ya na daga masa hannu.
Murmushi Javed ya yi yana girgiza kai,"Tabbas nima na ganka to Maddalla. "
Anyi wasan kwaikwayo na al'adu sannan kowanni gari sunzo sun kafa dandalin abun da suke saidawa cike da alfahari haka kuma an yi nune-nunen kayan tarihi na gargajiya sannan anci ansha da abincin gargajiya kala kala sai wanda mutum ya zaɓa kamar su cingini (sakwara),Ezo (wake) Kunu ,Akara (Alale),tuwo,Ɗankuwa,Kuli_kuli da dai sauransu.
Da ke ranar farko ne an gama shagalin da wuri kowa ya watse wanda gobe zasu gabatar da rawa da abubuwan sarauta na gargajiya.
Ba wanda ya lura da Farouq har aka watse.
Ya karbi number ɗaya cikin wa inda suka zauna tare.
Rana ta biyu
Ranace ta mussamman domin ba iya mutane ke kasancewa wajen ba harda aljanu da sukan iya yin shiga a siffar mutane,cika ake na mussamman abubuwa da yawa na wakana ciki harda tsafe-tsafe da bori.
Wajen taro ya dau harama sarakai kowanne na rufa tare da tawagarsa yan bori ne suka fara anata fama.
Sarkin Raki wanda Aljani Sarki Fahad ne akansa kamar an tsikaresa ya juya inda su Farouq suke, suna haɗa ido ,Farouq ya ji zuciyarsa ta fara bugun tara-tara da sauri ya kawar da kai yana sunkuyar da kai,bai san dalili ba amman babu shakka ya ji nauyin ci gaba da Kallon Sarkin Raki.
Kafin ya ankare ji ya yi an riko hannunasa yana daga kai ya ga sakice ta rike hannunsa,jan sa zuwa filin borin ta yi ta tsayar da shi rawani ta dauko ta fara naɗamasa tana yi sauran suka zagaye shi suna rawa,nan fa fada ta rikice kowa na son ganin wane ne wannan domin dole zai kasance na musamman ne,abune da bai taɓa faruwa ba a tarihin Bikin da ma masarautar.
Tana gama naɗa mashi ta fara yi masa Kirari ita da Sarkin Raki da sauran kujerar sarauta wacce take cikin na Sarkin Bida ta zaunar da shi daf da Babban Sarkin suna ci gaba da yi masa Kirari.
Ana zaunar da shi Mai Martaba Sarkin Al'adun mokwa idonshi idon Farouq bai san lokacin da ya tashi tsaye ba gabansa na wani irin mummunan faduwa.
Sai ji yake zufa na keto masa ta ko ina,Shi ko Farouq kara zagayeshi aka yi ana yi masa wasu lamura,wani irin zobe Saki ta dauko ta dauko a jakarta mai kyalkyali zata sanya masa zoben kenan tana fara zurawa a hannunsa gari ya hade nan take akayi wata tsawa cikin sa'i guda wani irin ruwa ya barke.
Sarkin Bida ya ce,"Tabbas akwai babban lamari tare da wancen bawan Allahn domin ba lokacin damuna muke ba,kuma ba kowa yake iya samun wannan zoben ba bare har a sanya masa kai tsaye daga masarautar Sarki Fahad zoben ke fitowa."
Wani irin zazzaɓi ne ya rufe Farouq take idanunsa suka kada suka yi jajur cikin karfin hali ya rufesu ruf.
Mai Martaba Sarkin Al'adu ne ya tashi zai karasa gareshi cikin sauri Saki ta......
Ta dakatar da shi tana fadin,"Hattara dai."
Ba yadda ya iya ya koma ya zauna yana wani irin muzurai,babban abun da ya fi damunshi shi ne ya rasa gane wane ne Farouq kuma da wacce manufa yazo,duk kokarinsa ya gaza fahimta shi dai tun ganinsa na farko jikinsa ya bashi cewa akwai wani abu,to mene ne wannan abun? "Sirrin da na binne?" Ya furta a zuciyarsa.
Da sauri ya kawar da kai yana girgiza hannunsa da ke kan cinyarsa azahiri ya furta,"Aa bai isa ba,ba zai yiwu ba,na rufe kowacce kofa,ba mai iya budewa."
Bai san cewa duk furucin da yake azahiri bane sai da ɗaya cikin fadawanshi ya yi magana,"Ranka Ya dade lafiya?"
Tukunna ya dawo hayyacinsa yana wani irin numfashi da haki,"Lafiya,lafiya ba komai,ba komai. "
Ya karasa maganar yana ajiyar zuciya.
Yanayinsa duk ya firgice.
A cikin ransa ya ci gaba da saƙawa,"Sai dai wani lamarin ba dai sirrin da na binne ba jinin mu ma basu isa ba bare wani bare,ka kwantar da hankalinka ka da a fahimci wani abu. "
Da hakan ya yi kokarin maida hankalinsa waje guda a zahiri wanda kuwa a badini sai saƙe-saƙe yake duk da cewa zuciyarsa na ƙara jaddada masa cewa abun da yake tunani ba zai taɓa faruwa ba domin ya riga da ya rufe dukkanin wata ko ƙofa ko alama.
Farouq kuwa idanunsa kankamewa suka yi a rufe,cikin sauri Sagi ta je tasa wani ƙoƙo daidai inda ruwan saman ke zuba ta taran masa.
Tana zuwa ta buɗe bakinsa ta fara zuba masa ruwan yana sha sannan ta shafa masa a fuska.
Take ya nemi zazzaɓin da yake ji ya rasa idannunsa kuwa fari kal suka dawo da da yadda suke ma a baya saɓanin canja kalar da suka yi cikin ƙaramin lokaci.
Murmushi Sagi ta yi ta kallesa ta ce,"Sannu da kokari ko,Babu shakka kai hasken fitila ne da kan iya haskaka al'umma ko da kuwa kana cikin duhu,bare ma duhu bai isa ya kara bin hanyar da kake ba ko tunanin kai maka farmaki,ka fi karfinsu ba za su taɓa iya ja da kai ba in ko suka yi gigin hakan daidai yake da kokarin salwantar da rayuwarsu da tushensu."
Gabadaya jawaban da take ya sanya Farouq shi ga cikin ruɗani da rashin