5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUAR

CHAPTER 9

by @xayyeesherthulhumaerath

domin ingata karatu mussamman na yaran da iyayensu basu karfi,marayu ko marasa galihu.

Ina cikn gabar bincikena na ci karo da su sai na tuna cewa fa mun yi maganar inda hali muna son saiwa kowacce daliba kwamfuta kafin kammala samun wannan horon shiyasa kawai na shirya na tsara letter na tura masu karkashin DigitalCraft da dukkanin kudirorinmu to cikin ikon Allah sai gashi muna cikin sahun wa inda za abawa wannan tallafi."

Tsabar farinciki Javed bai san lokacin da ya rungume Farouq ba yana fadin,

"Ban san ma me zan ce maka ba,ban san taya zan nuna ma jin dadi da farincikina ka gamsu ba,tun da na sanka babu abun da ke fitowa daga gareka sai alkairi da son ci gabana,Na gode Oga,Na gode Allah ya saka da alheri ubangiji ya biya maka dukkanin bukatunka,ina ma ace akwai wani abu da zaka nema a gareni da na ji dadi na yi maka shi cikin jin dadi duk da cewa na san ban da abun da zan iya ma fiye da wanda kake mun."

Murmushi Farouq ya yi,"Yiwa kaine ai duk wanda ya zam silar ingata rayuwar wa inda basu da bangon jingina gini yake yiwa kansa a lahira,ladan dani da kai duka zamu samu,babban abun da kuwa zaka mun ka biyani ai ka jima da yimun tunda ka yarda dani kuma ka aminta dani."

Kara rungumeshi Javed ya yi yana,"Na gode,na gode sosai."

Shi ma Farouq ya rungumesa.

Sunata murna da farinciki kallon agogo Javed yyi ya ga 7:am

Da sauri ya mike yana "Oga nasan ba za mu wuce 8 a garin nan ba,ka shiga ka yi wanka bara inje in karbo mana abincin karyawa."

Tashi Farouq ya yi yana,"Okay to shikenan. "

Ya wuce toilet shi kuma Javed ya tafi dauko masu abinci.

Dukkaninsu sunyi wanka,sun ci abinci daidai lokacin aka sanar da su cewa Mai Martaba ya ce a fito za a tafi.

Kai tsaye dukkaninsu suka fita.

Kowacce tawaga ta kowanni gari sun shirya suma an fito ana bankwana.

Sarkin Bida ne yasa a kira masa Farouq,Farouq na zuwa ya dunga sanya mishi albarka sannan ya mika masa wata jaka.

"Wannan kyauta ce ta mussamman, ka cancanci riketa,kila a yanzu ba ka san dalili ba amman ka rike wata raba zai yi ma amfani kuma za ka fahimta."

Karba ya yi cike da fara'a yana godiya.

Sauran sarakunan sai zuwa suke suna gaisawa da Farouq kafin su tafi.

A cikin ransa shi kansa ya gagara fahimtar dalilin hakan da kuma abun da yasa suke nuna masa kauna.

Zasu je su shiga mota tare da javed kenan mai martaba ya ce aa sai dai Farouq ya zo motarsa su tafi.

"Tare a motata zamu tafi."

Mai Mai martaba ya fada yana shigewa cikin motar.

Da mamaki duk suka bi mai martaba da kallo.

To mai zai sa ya ce Farouq ya shiga motarsa?

Shi kuwa Farouq ba tare da tsoro ko shakka ba ya shiga cikin motar a zuciyarsa yana karanto adduar shiga abun hawa.

"Bismillahi, Allahumma inni as'aluka khayraha wa khayra ma fiha, wa a'udhu bika min sharriha wa sharri ma fiha."

Ya shiga ya zauna.

Tunda ya shiga motar nan kan Mai Martaba ya shiga sara masa tamkar za a fisge, kokarin dafe kan ya yi da karfi ya zauna.

Ina lamarin ya citura,da karfi ya ce,"A Dakata...."

Cikin firgici driver ya ja birki,yana jan birki duka sauran motocin ma suka tsaya cak.

"Yallaɓai,Lafiya?"

Nuna Farouq ya yi da hannu da alamar ya fita.

"Ya fita?"

Ya girgiza kai alamar eh.

Da mamaki Farouq ya bi shi da kallo,aka bude masa kofa ya fita.

Farouq yana fita Mai Martaba ya ji tamkar an zare masa azabar da yake ji.

Ya kalli security ya ce,"ka sa shi a motarsu Javed."

"An gama Ranka ya dade. "

Ya fada suna tafiya da Farouq,bude masa motar su Javed ya yi ya shiga kafin ya koma.

Farouq na shiga motar cikin yanayin rashin fahimta Javed ya kalleshi ya ce,"Ya lafiya dai."

"E, lafiya kamar Mai Martaba zai yi wayar sirri."

Farouq ya fada a gajarce.

Javed ya ce,"Okay shikenan. "

Nan aka ci gaba da tafiya suna yi suna hira, har suka isa cikin Mokwa.

Ana shiga Fada cikin hanzari Mai Martaba ya wuce bangarensa ko cikin fadarsa bai yi ba.

Yana shiga ya kulle kofa,ya fisge rawanin da ke kansa,babbar rigar ma ya jefar da ita tsakar dakin,hannu yasa a cikin aljihunsa ya dauko wani ɗan karamin tulu.

Yana budewa ya fara juya hannunsa wannan karamin mutumin ne ya kara fitowa.

Dariya mutum yake har yana tuntsirawa.

Shi ko Mai Martaba ya ɓata rai cikin yanayin fushi.

"Moli ka daina dariyar nan wannan lamarin yana da girma ba abun wasa bane."

Dariya ya ci gaba da yi sai da ya yi mai isarsa kafin ya ce,"Yo daman kai Abdul-Raheem kana ganin cikin sauki ake iya taɓa mai kusanci ga ubangiji? ai sai dai irinka masu Musa a baki fir'auna a zuci."

Ɓata rai Mai Martaba ya yi ya ce,"Ina ruwanka dani? Ni muyi abun da ya dameni,ke nan yanzu shi ba za mu iya taɓa shi ba ko yaya kake nufi?"

Dariya Moli ya yi kafin ya ce,"Za a iya samun nasara amman fa sai anci kwakwa na fada maka yaron sam baya wasa da lamuran ubangiji farilla da sunna kai har ma da mustahabi kuma taɓa irin wa innan akwai ƙalubale sosai bare shi har yanzu na rasa gane kan gabanshi bare bayanshi dole akwai manyan da ke tare da shi."

Mai martaba ya yi tsaki,"Yaron fa dan ƙasar malaysia ne ban jin cewa yana da riko da addini don yawanci yan kasashan wajen nan sukan fifita duniya ba wani practising addini suke ba."

Moli ya buga wata iska kafin ya kalli Mai Martaba,"Ku fa musuluncin da yawanku a bakine kawai yan nigeria su kuma yan kasashen waje musuluncinsu yawanci ga zuciya yake ba ga zahirin rayuwarsu ba,sannan wai kai yau ka yi tunanin za ka iya cutar da shi ne? kana son wasa da lafiyarka ko? Ka da ma kara wannan gigin cikin sauki."

Mai Martaba ya ce,"Eheen na yi tunanin zan iya kokarin dunkufar da shi ko samun wani abu dangane da shi amman maimakon hakan sai na fuskanci barazana yafi karfina ba zan iya zama inuwa guda da shi ba,ji nake tamkar mala'ika na kokarin zare raina."

Moli ya ce,"Ka sani komin makirci da karfin tsafinka kariyar ubangiji ta fi su tasiri,ka bani lokacin in gama bincikar shi din wane ne tukunna ta hakan ne kadai zamu iya samun damar sanya rauni ga karfin Adduoinsa sannan kuma ka dage wajen yin aikinka in zai samu bakinsa ya rufu kamar yadda akaiwa sauran duk da cewa ba mu san manufarsa ba."

Numfasawa Mai Martaba ya yi,"Wannan ba matsala zan yi kokarin rufe bakinsa tare da kawar da idanunsa akai na,amman nidai babbar damuwata ka samo mana mafita Don wallahi ni kadai na san azabar da na sha yau cikin mintuna kalilan ba don nasa ya fita ba inaga zan iya samun matsala babba kuma zaman wannan zoben tamkar barazana ce ga rayuwata."

Dariyar mugunta Moli ya ci gaba da yi,"Dole a karbo wannan zoben dolene,dole ne domin shi ma din wata kariyace a gareshi sannan kai ka cancanci sanya wannan zoben ba kowa ba."ya karasa maganar yana wasu irin yare da sambatu kafin ya ɓace ɓat lokaci guda.

Yana tafiya mai martaba ya dauko wani ruwa shi ba ja ba kuma ba yellow ba a cikin kwarya ya kafa kai yasha yana sambatu sannan ya diba ya shafa a fuska da kuma tsakiyan kansa.

Wasu fararen kaya ya dauka yasa kafin ya hau kan gadonsa ya kwanta ,"Tun ranar farko zuciyata bata aminta da wannan yaron ba,Zoben nan mallakina na ne ba na shi ba,dawo ya dawo hannunaaaaa."

Ya fada a zahiri yana shiga cikin bargo.

☆☆

Farouq suna shiga cikin Bangarensu bayan ya yi sallah sunci abinci Javed ya shiga cikin gida ya dauko jakar da Sarkin Bida ya bashi.

Hannu yasa a ciki ya zaro wani irin rawani mai kyau da sheƙi da daukan ido.

A zahiri Farouq ya ce,"Ko amfanin me wannan rawanin zai mun oho."

Ya na kokarin maidawa ciki sai ga zoben da ke hannunsa na sheƙi yana fitar da haske irin na jikin rawanin.

Tsayawa kallon ikon Allah ya yi.

Yana maida rawanin kuma sai wutar ta dauke,alamu dai sun nuna cewa wannan rawanin da zoben suna da alaƙa mai karfi.

Karfe ɗayan dare daidai,Farouq ya hango wani yazo masa a siffar mutane baƙinƙirin ƙato,kokari yake ta karfi zai kwace zoben da ke hannunsa.

Cikin karfin hali Farouq ya dunkule hannunsa yana ihu.

Sheƙe masa wuya mutumin ya yi,da kyar yake numfashi yana ta kokarin cire hannunsa a wuyansa,ɗayan barin kuma ya ƙara dunkule hannun.

Da kafarsa ya fara kokarin dukan mutumin.

Yana sa hannu kan zoɓen sai ya fara wani irin jan wuta yana hayaki.

Ja yake amman sam zoben yaki fita ya maƙale hannun Farouq tamkare da shi yazo duniya.

Tun suna yi a kwance har suka tashi suna dambe da juna,sosai suka sha dambe har Farouq ya jiwa wancen mutumin a fuska shi kuma ya cijesa a hannu.

Ganin bai da alamun samun galaba akan Farouq yasa shi ya gudu.

A tsorace Farouq ya farka daga mafarkin da yake.

Kamar yadda Manzom Allah SAW ya umarta ga duk wanda ya yi mummunan mafarki ya yi addua ,"Allahumma inni a'udhu bika min sharri maa ra’aytu."

Hakan Farouq ya karanta yana goge zufar da ta gama jiƙa masa jiki.

Jin yanayin jikinsa ya yi ya masa nauyi sosai,hasken da zoben yake yasa shi kunna wuta domin ya gagara daga hannun da zoben yake.

Yana kunnawa kuwa yaga jini na zuba ga alamar cizo nan asaman hannunsa daf da yatsan da zoben yake.

Cikin jin mamaki ya furta,"Ke nan ba mafarki na yi ba? A gaske hakan ya faru? To ina mutumin? Me yasa ban ganshi a dakin nan ba."

Ya karasa yiwa kansa tambayoyin yana tashi.

Duba lungu da sako na dakin ya yi,ba alamar mutum sannan kuma kofarsa ma tana nan a kulle kamar yadda ya bari.

Gajiya ya yi ya koma ya daure wajen cizon.

Ya koma ya kwanta kenan yana kashe

Motsi yafara ji a karkashin Gadonsa hakan yasa shi saurin sunkuyawa

Yana sunkuyawa yaga babu komai bare alamun wani abu,duk da hakan bai yarda ba ya kunna hasken wayarsa ya haska sai da ya tabbatar bai ga komai ba kafin ya koma yana ajiyar zuciya a kan gadon.

Ji ya yi barcin da ke idanunsa sun kafe kaf ya gagara komawa,hakan yasa ya tashi ya je ya yi alwala ya yi nafila.

Har gari ya waye bai koma ba karshe ma hira suka fara yi da Zoe sai da lokacin sallar asuba ya yi kafin ya yi mata sallama ya je ya yi sallar,yana idarwa kuwa wani irin barci ya cafkeshi take ya koma kan gado ya kwanta.

Kamar wasa Javed ya ga har karfe takwas ta yi Farouq bai fito ba kuma yasan yawanci bai cika barcin asuba ba,har an kawo masu abin karyawa ya ci nasa amman ba alamun Farouq,hakan yasa ya gagara jurewa ya tashi ya nufi dakin.

Buga kofar ya fara yi cikin magagin barci Farouq ya tashi ya bude.

Da mamaki Javed ya kallesa ,"Oga wai yau kaine da barci haka?"

Miƙa Farouq ya yi, "Wallahi kuwa wani irin sahihin barci ne ya kwasheni ina idar da sallah dake jiya ban wani samu dama ba."

Idon Javed jaraf akan hannun Farouq,"Subhanallah me ya sameka haka a hannu?"

Javed ya fada cikin yanayin nuna damuwa.

Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Ciwone na ji jiya da daddare a toilet,ka ga bara inyi wanka inzo." Ya fada maganar yana saurin wucewa domin katsewa tambayoyin Javed.

Wanka ya yi ya shirya sannan ya fita falon ya samu Javed,Zama ya yi ya fara karyawa,hayaniyar mutanen da ya fara jiyowa yasa shi dakatawa yana kallon Javed.

"Wannan hayaniyar fa lafiya kuwa?"

Javed ya ce,"Lafiya lau,ni na manta ma ashe yau ne ake murnar bikin Gani na nan mokwa,maraba da dawowa daga Bida da kuma murnar bikin Ganin na shekara sai da na fita dazu na gani."

"Oh Ma sha Allah,Shiyasa na ga ka dauko rawani kenan."

Farouq ya faɗa yana kallon rawanin dake gefen Javed.

"Yes kasan dole a naɗa asa kayan gargajiya ko mai martaba ya yi hukunci." Javed ya faɗa.

Farouq ya ce,"Nima ko ina sha'awar yin shiga irin takun nan kuma daman an bani kyautar rawani,da zan samu kayan sai insa."

"Me zai hana? Ai sai in baka akwai sabin kaya da ban saba kasan lokaci zuwa lokaci duk ake sabunta mana kayyayyaki irin na al'ada ko da baka da rawani ma ai dole a nemo indai kana son sawa." Javed ya fada cike da zumudi ya tashi ya je ya daukowa Farouq manyan kaya da alkyabba dukkanin su sabi fil ruwan ƙasa.

Da farinciki Farouq ya karɓa yana "aiko gasu kalan rawanin nawa har ma takalmin. "

Ya karasa maganar yana daukan takalmin.

Javed ya ce ,"To yanzu dai ka gama cin abincin naka zuwa bayan la'asar zamu shirya za a fara bikin in ka gama sai mu dau rawanin mukai a naɗa maka a ajiye sai sawa kawai."

Farouq ya girgiza kai yana fara kai luma abunsa.

Gida anata shige da fice ana gyare-gyare da girki girki da ma shirye-shirye domin duk da gidan cike yake da adon gargajiya da sarauta na yau ya bambamta da kullum domin an kara tsara komai cikin ƙawa.

Misalin Karfe Hudu daidai an fara taro kowa da kowa na gidan sun hallarci farfajiyan filin da ake taron hatta mai martaba anata raye-rayen da kaɗe-kaɗen gargajiya illa Farouq da Javed da suketa fama da rawani da kyar aka samu aka daidaita ya zauna.

Shigar sarautar ba ƙaramin kyau ta yi Farouq ba wanda ya zarce misali domin kuwa ba zai taɓa misaltuwa.

Javed ya ce,"Ya Subhanallah Oga ka ganka kuwa? Yoo ni ko sarki ban taba ganin yayi kyau cikin kayan nan kamar yadda ka yi ba,gaskiya tsaya inyi ma hoto tukunna in samu da na status a tiktok kuwa na san sai ka kaini viral ba makawa. "

Murmushi Farouq ya yi ya ce,"Kai dai baka da dama."

Hotuna Javed ya dunga yi masa,ya masu selfie tare sannan suka fita.

Jinin sarauta,izza da kamala,ƙasaita da duk wani shauƙi na sarauta sun gama bayyana ga takun Farouq,wani yanayi ya riski kansa na jin tsantsar ƙasaita da ba zai iya kaucewa hakan ba.

Cikin izza suke tafiya har suka isa farfajiyar taron,sheƙen da rawanin kansa da zobensa da suke shi ya fara aikawa da al'ummar wajen saƙon isarsa.

Kallon kallo aka fara yi yinyin da idannun kowa ya koma kansa.

Abba Malik na bude baki,"Abdul............"

Tsintar kansa da kasa ƙarasa sunan ya yi yana jin tamkar wani dutse ya maƙale masa a wuya.

Hajiya kaka kuwa kwakwalwarta ce ta fara dawo mata da rayuwar baya,tana so ta gano wani abu amman lamarin ya citura,dafe kanta ta yi tana,"Ina yake....ina yakeee."

Kilishi kuwa zare idanu ta yi cike da mamaki," lallai wannan ba mutum bane."

Ta furta a zahiri ba tare da ta sani ba.

Wani irin kallo mai martaba ya bisa da shi yana zare idanuwa "Zargi na ya tabbata zai juyar masu da tunani zai dawo da su,zasu fahimta,zasu tuna,baka isa ba,wallahi baka isa ba."

Ya karasa maganar ya ciro wani gari ya fesa.

Hajiya kaka na kokarin faɗuwa kenan Farouq ya yi saurin karasawa ya tareta,"Amarya ta ga angonta ya yi kyau ta tsure harda shirin faduwa. "

Ya fada cikin sigar tsokana.

Lamura sun ci gaba da tafiya amman gabadaya zuciyoyin Mai Martaba,Abba Malik,Kilishi da Kaka cike take fal da damuwa kuma a cunkushe mussamman Hajiya Kaka da Abba Malik da abun yafi daurewa kai.

Mutane sai zuwa suke ana hoto da Farouq yadda ake damuwa da yin hoto da Sarkin Al'adu wannan karan ko ta shi ma ba ayi gabaɗaya rububi ake akan Farouq kowa burinsa ya yi hoto da shi kuma mussamman da yake labarinsa ya baza gari kan abun da ya faru a Bida sai nuna shi ake ana ai shine ance dan baiwa ne.

Wani tsoho ne tukuf ya karasa inda Farouq yake ya shafa fuskarshi kafin ya ce,"Kai ne kadai zaka kawo karshen zalinci kai ne zai ka fito da tsagwaran gaskiya,ina rokon ubangiji da ya yi maka albarka kuma ya tsare ka da tsarewarsa tare da kariyarsa sannan ya maka lulluɓi da albarkarSa."

Farouq ya amsa da Ameen duk da cewa bai gama fuskantar abun da tsohon ke faɗa ba.

Hannu yasa a aljihunsa ya ciro wani dumin kudi ya miƙawa tsohon ya karba yana kara sa mishi albarka sannan ya tafi.

Janinah sai cizon yatsa take tana takaici,"shi wai wannan kowa sonshi yake ne? Sai kace Aljani Mtswwww. "

Ta ja tsaki tana kallonsa.

Suna hada sai ta galla masa harara.

Shi ko da murmushi yake binta.

An yi shagali anci an sha an watse.

Farouq ya bazu a social media yan nigeria mussamman mata sai reposting ake da ga Asalin Mijin Novel ya bayyana har da masu rubuta wasikar soyayya,lamura dai kala kala,suna zaune a falon Hajiya Kaka da dare Javed sai dariya yake yana nuna masu,"Oga ka baza capacity fa ka tashi kan yan matan nigeria ko ina aka bude lamarinka ke trending tiktok,Instagram,Twitter,Facebook har WhatsApp status kawai kaine harda me cewa ita in ba kai ba ba zata yi aure ba harta mutu. "

Caraf Hajiya Kaka ta taɓe baki tana faɗin,"Aiko dai saidai ta mutu ko ince su mutu ma don dai wannan kam nawa ne ni kadai,ko ba haka ba Mijin?" Ta fada tana kallon Farouq.

Daga mata gira ya yi yana,"Sosai ma Amaryata Yan matana ai daga ke ba ƙari ke ɗaya ce."

Janinah ma da taga abun yaƙi karewa ko ina ta bude shi ke yawo tuni taje tana nunawa Kilishi,wani yanayi da bata saba riskarta ciki ba ta ganta,"Aunty Kilishi kin ga ko ina fa hoton wancen banzan bakon ne."

Kawar da kai Kilishi ta yi tana,"Kin