5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUAR
CHAPTER 10
ga Janinah kije da safe zamuyi magana yanzu kaina na ciwo."
Ba yadda Janinah ta iya haka ta fita amman zuciyarta cike fal da tarin tambayoyi domin bata taɓa ganin Kilishi a yanayi na damuwa kamar na yau ba.
Dakinta ta wuce ta kwanta abunta.
Shi kuwa Mai Martaba Moli ya gayyato cikin fushi da ɓacin rai yana yi mishi magana,"Shin ka ga rawanin da ya sanya? Ka ga rawanin da ke kanshi? Ka ga yadda siffarsa ta kasance a cikin kayan nan? Ka kasa gano mun shi wane ne tawagarka ma sun kasa,kenan yafi karfinku? Anya ma mutum ne kuwa? Na ce anya ma mutum ne kuwa? Na fara tantama wannan ba mutum bane,kuna gani za a gaba bayana,kuna gani karshena zaizo."
Ya fada yana buga bango.
Dariyar muguntar da Moli ya saba ya yi kafin ya tsagaita ya ce,"Kai Abdul-Raheem Hattara dai na ce hattara dai,wannan yaron mutum ne kamarka na fadama na sake fada ma mutum ne kamarka kusancinsa ga ubangiji ne mai girma sannan lamarinsa dauke yake da matukar sarƙaƙiya aiki akansa muke ba dare ba rana wanda sanadinsa har wani cikin yarana ya samu matsala,ba shi bane wanda kake tunani domin ba zai taɓa zama shi ba don ya sa wannan rawanin in zaka kwantar da hankalinka ka kwantar."
Cikin fushi mai martaba ya ce,"lamarin ya kai ni makura kuma cikin daren nan zan dauki matakin da kuku kasa dauka."
Dariya Moli ya fara yana,"Ka dauka,ka gwada dauka za ka kai kanka ga tona ramin da ka birni."
Ya ci gaba da dariya kafin ya ɓace.
Dare ya yi,kowa ya tafi daki sunyi barci.
Karfe Ɗaya Daidai Farouq na zaune gaban System sai ji ya yi ana taɓa kofarsa.
Zura key aka yi aka bude aka shige,wani mutum ne dauke da wata doguwar bakar riga data rufeshi daga sama har ƙasa.
,“Lā ilāha illā anta subhānaka innī kuntu mina-ẓ-ẓālimīn.” Farouq ya furta cike da firgici.
Daga abun da ke fuskarsa ya yi,ya bude.
Suna haɗa ido ya ga mai martaba ne.
Wani irin faduwar gaba ya ji yana ja da baya.
Mai martaba ya ce,"Kai wane ne? Ka fadamun kai wane ne?"
Farouq ya ce,"Ni ba kowa bane kuma nima ban san ni wane ne ba."
Cikin Fushi Mai Martaba ya zaro wuƙa yana shaƙo Farouq,"Ka faɗa mun kai wane ne ko in kasheka."
Cikin daurayi Farouq ya ce,"Sai dai in ka kashenin bare kuma ba ka isa ka kasheni ba har sai in kwanana ya kare."
Kara sa masa wukar ya yi akan wuya yana,"Ba zaka fada ba kenan? Zan iya kasheka yanzu in kashe banza anan ba tare da kowa ya sani ba,amman a halin yanzu nafi son insan kai wane ne sannan kuma ina Umartarka da safiyar gobe ka shirya ka bar kasar nan tun kafin ni da kaina ɓatar da kai."
Farouq ya ce,"Kai ya kamata in tambaya ni wane ne,sannan kuma baka isa ka ɓatar dani ba in kana hakan kana cin nasara to ka gwada akaina ka ga ko zaka ci."
Shaƙesa ya yi yana kokarin daba masa wukar Farouq ya yi saurin kaucewa ya kwantar da shi yana karbar wukar shima yasa mishi kan wuyansa yana,"Ni ba zan kasheka ba,amman zanyi ma illar da sai ka ji cewa dama mutuwar kayi,kuma ina umartarka da ka bar dakin nan tun kafin in tarama jama'a,sannan kasa aranka ba zan taɓa barin gidan nan ba sai aiwatar da kudirina."
Murya na rawa Mai Martaba ya ce,"Daga sai in fita to don Allah ka barni karka tada kowa."
Daga shi Farouq ya yi da wukar a wuyansa har sai da ya hankadeshi waje kafin ya kulle kofarsa ya jefar da wuƙar gefe.
Ficewa daga masarautar Mai Martaba ya yi cikin daren ya shiga wani daji yana tone tone.
Shi ko Farouq ajiyar zuciya ya yi ya koma ya ci gaba da aikinsa da yaga ma ba zai iya ba karshe kwanciya ya yi.
Yana fara barcin babu wanda yake mafarki illa wannan tsohon da ya yi masa addua da yamma.
Kasa hakuri ya yi karfe hudun asuba ya je dakin Javed ya tasheshi.
"Lafiya Oga?"
Javed ya fada.
Farouq ya ce,"Lafiya lau,kasan gidan wannan tsohon da ya yi mini addua dazu?"
Javed ya ce,"E kwarai a cikin gari yake."
Farouq ya ce,"To muna idar da sallar asuba zaka rakani Don Allah ."
Javed na washe barcin da ke idonsa ya ce,"Lafiya kuwa?"
Farouq ya ce,"Lafiya lau ina so in kara masa abun da na basa ne."
,"To kuma shine da asuba bazamu bari sai safiya ba?"
Farouq ya ce,"E ba zan iya hakura ba mafarkinsa nake."
Suna yin sallar asuba kuwa suka fice daga masarautar.
Wani ķaramin gidan laka ne da duk ya gama jin jiki ya rurrushe duk an yi ciko da leda.
Javed ya ce,"ga gidan nan....
kallon Gidan Farouq ya yi yana,"To ka ɗan taimaka ka yi muna sallama da shi mana."
Javed zai yi magana kenan sai ga Tsohon ya dumfaro inda suke,ga dukkan alamu daga masallaci yake,tsoho ne tukuf da kyar yake tafiya da sanda.
"Ah Javed kune? Ince dai lafiya?"
Javed ya kalli Farouq ya ce,"Lafiya lau Baba Bakonane ke son ganinka ya ce sai mun zo yanzu na yi na yi ya bari sai safiya yaƙi."
Wani matsakaicin Murmushi ya yi ya ce,"Daman nasan za a rina,Ɗan samari sannunka ko zamu ƙarasa soro ne?"
Farouq ya ce,"E gaskiya zan so hakan,yanzu kai Javed ka koma gida kar a fahimci bama nan in mun gama da Baba zan tawo."
Javed ya kallesa yana,"Okay to amman dai zaka gane hanyar ko?"
"In sha Allah. " Farouq ya fada.
Baba ma ya ce,"ko bai gane ba ai na rako shi."
Tafiya Javed ya yi ya barsu,suka shige zauren gidan sannan suka zauna kan taburma.
Baba ya ce,"Mene ne tafe da kai yaro?"
Gyara zama Farouq ya yi da kyau kafin ya ce,"Cikin mafarkina ya nuna mini cewa kana dauke da hasken da zaka fiddani daga duhun da nake ciki in daina lalube sannan kuma zuciyata ta ƙara gasgata mun hakan ya yin da ruhina ya aminta da cewa lallai akwai abun da ka sani game dani."
Numfasawa Baba ya yi kafin ya ce,"Ina mahaifinka?fatan yana cikin ƙoshin lafiya?"
Daga kai Farouq ya yi yana yiwa Baba kallon rashin fahimta cike da tuhuma.
"Mahaifina? Shi ne abun da nake nema Baba,kuma shi ne nake jin cewa kana da masaniya akan inda yake domin har yanzu na gagara gasgata shin wane ne mahaifina cikin gidan masarautar al'adu,Mai Martaba ko Abba Malik? Sam babu mahaifina ciki,shi na zo nema amman na lura da cewa tamkar babu shi ma a duniya da tarihin masarautar abun da na riska ya bambamta da abun da mahaifiyata ta sanar mini."
Baba ya ce,"Na ji mamaki matuka da kace mahaifinka ka zo nema,domin a tunanina mahaifinka ne ya turoka domin daukar fansa indai hakan ya tabbata abun da kake fada to tabbas lamarin da girma yake."
Farouq ya ce,"Babu shakka Mahaifiyata bata ƙara sa mahaifina a idanunta ba tun daga ranar da ya kaita filin jirgi domin komawa ƙasarta har kawo yanzu da nake zaune a gabanka."
Girgiza kai Baba ya yi kafin ya ce,"Gatan da zanyi maka bai zarce ace in baka tarihin abun da na sani ba domin kila a ciki zaka samu hasken da kake da buƙata."
Gyara zama Farouq ya yi yana fuskantar Baba
" Nine Malami na farko ga gidan sarkin al'adu tun lokacin da Kakanku ke raye Mai Martaba Abdul-Alim,ni ke bincike da shige da fice kan duk wani abu na tsaro da tsafi dake guduna cikin masarautar domin kuwa ni amintacce ne kuma amini ga Mai Martaba hakan yasa na san komai shige da ficen wannan gidan,Mahaifinka su biyu Allah ya fara bawa mai martaba da shi da ɗan uwansa Abdul-Raheem wanda ya kasance sarkin al'adu na yanzu kasancewar kakarku ta yi jinkirin haihuwa an sha shige da fice kafin zuwansu duniya wanda har kai ga dukkanin su ana haifarsu muka fara duba taurarin rayuwarsu akaron farko Maihafinka Abdul-Rasheed da yake babba manuniya ta nuna cewa shine ya cancanci gadar sarautar kakanku domin shi ne ya gado kyawawan dabi'u irin nasa saɓanin Hussaini Abdul-Raheem
Dukkaninsu sun taso cikin gata da soyayya matuka ya yin da suka fara girma sun kammala karatuk sakandare sai Mahaifinka ya buƙaci da a turasu ƙasar waje domin yin karatu a bangare kimiya wato na'ura,
A lokacin an haifi Baffanku Abdul-Malik da Khaleesa
Mai Martaba ya amince da hakan amman sai dai inda gizo ke tsaƙar shine Abdul-Raheem sam karatun baya gabanshi saboda zaɓin Abdul-Rasheed ne ba na shi,baya karatun kuma ba ya maida hankali illa sanyawa mahaifinka karar tsana da ya yi ganin cewa Mai Martaba na matukar ji da shi da kyawawan dabi'unsa.
Har ya kai ga Abdul-Raheem kullum yana cikin shiga da rayuwa irinta sarauta tsangwama da kyarar mutane kuwa ba a magana duk da cewa mai martaba na kokarin tsawatar masa amman ba hakan ke sawa ya daina ba sai dai ya rage aikatawa a gaban idanunshi,shi kuwa Mahaifinka tamkar ba ɗan gidan sarauta ba,rayuwa yake daidai data kowa cike da girmamawa.
Karshe Abdul-Raheem daga zuwa hutu yaƙi komawa makaranta ya zauna a fada,shi kuwa Abdul-Rasheed sai da ya kai wani babban mataki da ba zan iya cewa mene ne ba tunda ba bokon muka yi ba amman dai bana mantawa dawowarshi an shirya shagali mai girma na tarɓarsa wanda bikine da ba a taba yin irinsa ba a tarihin mokwa inda ya haɗa manyan sarakuna na nigeria da kewaye wannan bikinma ba ƙaramin tadawa Abdul-Raheem hankali ya yi ba domin kuwa gagara boye hassadarsa ya yi ban mancewa har tsoron shi mahaifinka ya fara ji ya dakesa ya bigesa kuma ya kwace masa abubuwa amman mahaifinka bai taɓa faɗa ba ita kuwa kakarku data fahimci hakan sai ta sanya aka raba masu ɗaki amman duk da hakan bai tsira ba
ana cikin hakan ya samu aiki a kasar Netherlands inda ya koma cen na tsawon shekara uku cif ina kyautata zaton cewa anan ne ya haɗu da mahaifiyarka suka fara soyayya wanda har tsautsayi ya gifta tsakani akai yi cikinka ba tare da aure ba,ganin hakan ya sa mahaifinka dawowa gida da ita bayan ta musulunta iyayenta sun gujeta kan cewa zai aureta inta haihu,bai sanar da kowa cewa tana dauke da ciki ba illa ni kadai domin a lokacin kakanku na jinya kwance babu lafiya rai a hannun Allah.
Hakan yasa Abdul-Raheem ne ke kula da duk lamura na masarautar kuma daman abun da yake da buri kenan.
Zuwan mahaifinka da mahaifiyarka ya ce sam ba za a shigan masu da kafura cikin ahali ba su ba za su abun kunya ba,a lokacin Khaleesa duk da tana da ƙarancin shekaru amman ta bawa Abdul-Raheem goyon baya sosai domin tare suka yi shige da ficen da don dole sai aka sa mahaifinka ya nemawa mahaifiyarka tikitin gaggawa na komawa kasarau domin kuwa lamarinta har sai da ya kai ga mai martaba babban sarki na bida ya shiga ciki lamura dai marasa dadi sosai cike da tozarci da cin mutunci duk yadda na so domin kwantar da lamarin abun ya cutura sai da na zam ɗan kallo,
Bayan mahaifiyarka ta koma ba jimawa Allah ya dauki ran mai martaba ya yin da aka fara shiri gadan gadan domin naɗa Abdul-Rasheed nan fa Abdul-Raheem ya fara sabon shiri da na shi aikin,kowa ya san Abdul-Rasheed ne ya cancanci zama sarkin al'adu kuma shine wasiyar mai martaba.
Hakan yasa Abdul-Raheem ya shiga ya fita ya fara kokarin duk yadda zaiyi ya yiwa mahaifinka Kurciya mai dauke da mutuwa da yazo mun da lamarin naki aminta da hakan karshe sai ya fita sabgata ya bi hanyoyinsa tare da shiga kungiyoyi domin tabbatar da burinsa.
A karshe ya yi sa'a domin kuwa an wayi gari an tashi babu Abdul-Rasheed babu labarinsa kuma bakin kowa a rufe babu wanda yake batunsa tamkar anyi ruwa an dauke,ya rufe bakin kowa ta yadda kowa zai manta da batunsa inko mutum ma yyi kokarin tunasa ko tada zancen karshe ya kan iya rasa ransa,Don dole aka naɗa shi sarkin al'adu na mokwa ya yin da ni kuma ya yi fatali dani daga cikin gidan tunda dai ni ba zai iya mun komai ba kar tasan kar ne,to wannan shi ne dalilin da yasa ba ka jin ana batu ko labarin mahaifinka hatta kakarku da ta fara tuna shi take ficewa a hayyacinta domin ya riga ya yi aiki mai karfi akan hakan sannan yanzu abun da zaifi daure masa hankali shine bai san da cikinka ba kuma a tunaninsa yanzu mahaifinka baya raye tunda kurciyar mutuwa ya yi masa, mun yi artabu sosai nayi kokarin hana shi aikata hakan amman na gagara yana amfani da shedanun aljanun da suka fi karfina ni kuwa ina ganinka jikina ya bani cewa kai Ɗan Abdul-Rasheed ne."
Idanun Farouq ya yi jajur
Ba don namiji bane kuma jarumi hawaye ba zai taba saurin tsayuwa daga idanunsa ba bare ƙin zuba.
Wata irin ajiyar zuciya ya yi
"Kenan dai yanzu ba asan inda mahaifina yake ba? Yana raye ko baya raye ?"
Baba ya ce,"Kwarai kuwa amman ina ji araina cewa yana raye,kuma yana rayuwa mai inganci da jin dadi,kai zaka nemo shi amman ka sani sai ka yi taka tsantsan da Abdul-Raheem mutum ne mai hatsari matuka yana kuma girmama al'ada da kiyayeta ba kadan domin ta hanyar yake samun aiwatar da munanan lamuransa nima zan taimaka maka iya yina har mu kai ga cin nasara domin akwai wani babban sirrin da na gano nake son sanar da mahaifinka in Allah yasa ka nemo shi."
Farouq ya dafe kai yana,"Na fahimta,tabbas na fahimta kuma ba makawa indai mahaifina na raye cikin duniyar komai nisa da fadin inda yake zan nemoshi da karfin ikon Allah."
Baba ya ce,"Allah ya baka iko amman ina kara jaddadda maka cewa ka yi a hankali domin kuwa cikin daren jiya ma na jiyoshi yana zama da manyan muƙarabbansa iblis,ifrit,da su zalambur,kuma duk akanka suke aiki."
Wani irin yanayu Farouq ya fara ji duk da cewa a zaune yake amman jiri yake ji idanunsa na kokarin rufewa.
Murya na rawa ya ce,"Baba bara in tafi zan dawo."
Baba ya ce,"zaka iya tafiya ko in rakaka dai?"
"Aa na gode zanje ka zauna."
Ya fada yana tafiya.
Har gari ya yi haske rana ta fito.
Tafiya Farouq ya dunga yi kamar ɗan maye,a hankali har ya shiga part din Javed.
Yana shiga kuwa ya faɗi a kasa tum tamkar wanda aka hankaɗa.
Da sauri Javed ya tashi ya karasa....
Dakyar Javed ya yi kokarin daga shi ya shigar da shi ɗaki yana,"Subhanallah Oga me ya faru? Lafiya?"
Daga masa kai ya yi alamar eh yana ajiyar numfashi.
Raɗaɗi da azabar da kansa ke yi masa tamkar zai tsage hakan yasa shi saurin rike wajen,daga kan har gangar jikin ko ina ya dauki wani irin zafi tamkar wuta.
Javed da yaga lamarin kara girmama yake ya rasa yadda zaiyi da gudu ya fita ya kira BabanGanye.
Aiko yana zuwa ya tafa kan Farouq da jikinsa sannan ya ce,"Harda ciwon kai ne ko?"
Nan ma daga masa kan kawai Farouq ya yi ba tare da iya furta komai ba.
BabanGanye ya kalli Javed yana fadin,"Daman ko dazu na kammala dafa ganyen dogon yaro (Neem) da na ganyen ɗanyen allayahu wa inda daman su haɗi ne mussamman domin maganin ciwon kai da zazzabi mai tsanani ka ga ke nan anyi sara akan gaɓa In sha Allah yana sha nan da yan mintuna zai samu sauƙi amman in ce dai ya ci abinci?"
Javed ya ce,"Aa Baba bai ci ba gaskiya."
BabanGanye ya ce,"Dole sai ya ci abinci domin kuwa babu dama ya sha ruwan maganin nan ba tare da ya ci abinci ba akwai matsala ko yane ana bukatar ya ci wani abu tukunna."
Tashi Javed ya yi yaje ya haɗawa Farouq kakkauran ruwan shayi,ya tallafa masa ya zauna sannan ya samu ya sha ɗan kadan.
"Yawwa to da babu dai gwara babu dadi yanzu bara muga ko nan da mintuna biyar ne ruwan shayin ya dan sauka da kyau sai asha maganin,ka san fa ba sai maganin bature bane ake so aci abinci kafin asha,hatta namu ma na gida yana da ƙa'idoji,dokoki da kuma tsari." BabanGanye ya faɗa.
Sai da ya dan hutu na mintuna kafin aka bashi ruwan maganin ya sha rabin kofi.
BabanGanye ya zuba masu wani a gora sannan ya ce,"Ga shi nan zuwa yamma zai iya kara shan rabin kofi,sannan kuma a tabbatar ka da asha ya zarce kwana uku duk da dai ma na san iya shan na yau ya isa zai samu sauki."
Javed ya ce,"Ok To Baba Allah saka da alkairi mun gode sosai."
"Ameen Allah kara sauki ko."
Ya fada yana kallon Farouq wanda idanunsa a rufe ma suke kam,haka kuma dayan hannunsa na kan kanshi ya kankame ban da ruwan hawaye babu abun da ke kwarara daga idanunsa.
Zama Javed ya yi kusa da shi yana,"Oga ko dai wani abu ya faru ne? BabaMalam dinne?"
Girgiza masa kai Farouq ya yi.
Ban da tuna maganganun Baba babu abun da yake yi mussamman "Aka samu cikinka ba ta hanyar aure ba...Ya yi wa Mahaifinka kurciya mai ɗauke da mutuwa."
Wa innan maganganu biyun ne suka dunga yawo a kwakwalwar Farouq.
"Me yasa Maah bata faɗa mun cewa bata aure aka same ni ba? Me yasa? shin yanzu mene ne matsayin rayuwata? ke nan ba musuluntar da mahaifiyata ta yi ba ne kadai zai zame mun za me mun kalubale ba harda kasancewata a matsayin wanda aka haifa ta haramtacciyar hanya? duk da cewa ban ta so da son duniya da abubuwan da ke cikinta ba amman babu shakka a yau na kara jin cewa dama ace ban kasance a cikinta ba, Astagfirrullah! Ubangijina na tufa ka yafeni amman a yau kai kadai ka san zafi da ƙunar da nake ji a cikin zuciyata,na so in maida komai ba komai ba in nemo mahaifina amman kuma yanzu ji nake na gaza ba zan iya ba!