MATAR GIDA PAGE 19
MATAR GIDA 019
SHUUKRAN/022
P19
Washe gari juma'a bayan Rumaisa ta tura yara makaranta ta shiga ɗakin Amirah ta tarar Amirah zaune bakin gado tana shafa mai da alama bata daɗe da fita daga wanka ba,ledar jiya Rumaisa ta kalla tare da gwangwanin madara ta ga yana nan inda ta ajiye da alama ko taɓa ledar Amirah ba ta yi ba,waje Rumaisa ta samu ta zauna tana ƙarewa Amirah kallo ba tare da kallon inda take ba Amirah ta ce ''barka da safiya'' taɓe baki Rumaisa ta yi kafin ta ce ''kin tashi lafiya?" Amirah ta ce ''lafiya ƙlau alhamdulillah'' daga haka shiru ya biyo baya bayan wasu ƴan sakanni Rumaisa ta ce ''ba ki fara amfani da magungunan ba?" Amirah ta yi shiru ba ta ce komai ba body lotion ɗinta ta mayar cikin jakar kayanta kafin ta tashi ta nufi wajen saif ɗake ɗakin ta fidda wata koriyar doguwar riga ta fara ƙokarin sa rigar har sannan tana sanye da hijab a jikinta,Rumaisa ta ce ''magana naki maki'' nan ma shiru Amirah ta yi kamar ba za ta ce komai ba can ta ce ''zan yi amfani da su amma ba yanzu ba,sai na koma'' cike da mamaki Rumaisa ta ce ''ikon Allah to aiy yanzu ya kamata ki fara amfani da su kafin ki koma sun bi jikin ki,na yi magana da wacce take dafa min kaza ta ce jibi zata aiko min dan Allah Amirah ki cire damuwa ki yi hakuri ki rungumi mijinki,na tabbata yanzu ya yi nadama sakin ki da ya yi da yawa yawan maza basu sanin amfanin matansu sai bayan sun rabu da su,ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki ki mayar da lamurran ki ga Allah wallahi za ki sha mamaki sai ki ga amarya ta yi maganin sa,an yi haka ya fi a ƙirga dan Allah ki yi hakuri'' bayan Amirah ta gama shirya kanta cikin doguwar riga zama ta yi bakin gado ta mayar da dubanta ga Rumaisa ta ce ''har yanzu zuciyata zafi take min,ko na koma gidan bazan iya sakin jiki da shi kamar da ba'' Rumaisa ta ce ''aiy ba dole ki saki jiki da shi daga komawarki ba hasali ma saboda yaran ki za ki koma'' shiru ne ya biyo baya can Rumaisa ta ce dan Allah ki daure ki fara amfanin da magungunan'' Amirah ta ce ''insha zan fara amfani da su''shiru Rumaisa ta yi na wasu ƴan mintina kafin murya can ƙasa ta ce ''in ba za ki damu ba ina ganin ko za ki tafi ranar talata in Allah ya kaimu'' Amirah bata kalle inda Rumaisa ke zaune ba ta ce ''na sani Baba ya yi fushi da ni ƙila yana can yana yawan tunani,duk sanda zuciyata ta ce min kar na koma gidan Ɗalha Babana nake tuna na sani zaifi kowa shiga damuwa,matsalata ɗaya ban san yadda zan tunkari shi ba'' shiru Rumaisa ta yi tana tunani can ta ce ''ba lallai ki je gidan Baba direct ba za ki iya zuwa gidan ɗaya ɗaga cikin yayunki maza wanda ki da fahimta a cikin su,ko gidan wani ɗan uwan Baba ko ƴan uwan Ummanki''Amirah ta ce ''kin manta dangin Umma ba a nan suke ba mahaifiyata daga Chadi take,mahaifina ne ɗan kano ɗan a karamar hukumar takai,shima Ɗalha iyayensa ƴan Kano ne mahaifinsa da mahaifiyarsa duk daga karamar hukumar takai suke unguwarsu ɗaya,unguwar chidari gidan kakana da kakan Ɗalha unguwa ɗaya suke makwabta ne'' Rumaisa ta ce ''ikon Allah to yanzu dai gidan wa za ki je daga nan?" Amirah ta ce ''gidan yaya Nasir,zan yi masa bayanin komai zan ce masa tun da na bar gidan Ɗalha gidan ki nake bazan faɗa masa na zauna a hotel ba'' Rumaisa ta ce ''haka ne''
Yau karfe 8:00am na safe Ɗalha ya zuba yara a makaranta daga nan ya wuce office tun tafiyar Amirah sai yau ya kai yara makaranta karfe takwas kullum karfe tara zuwa goma suke zuwa makaranta,kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yau ɗin yana cikin salama,karfe huɗu da mintina arba'in ya bar office bai tsaya ko ina ba sai makaranta su Sudais tun a hanya sun cika sa da surutu Ummu Abiha da Sumayya sun faɗa masa cewar an basu hair style ya kai su gidan kitso gobe shi dai ya yi shiru bai ce komai can Suhail ya ce ''Dady ka san gidan ƙitson?" Ɗalha ya ce ''ban sani ba'' bayan komawarsu gida yau ma kamar bayan Ɗalha ya dafa masu abinci ya taimaka masu da homework ya yi masu wanka karfe tara daidai duk sun kwanta hakan ya bawa Ɗalha dama gyaran gidan karfe sha ɗaya daidai ya gama aiyukan gidan har uniform ɗinsu ya wanke gudun kar ya manta ranar monday su tashi babu uniform ɗinda zasu sa,kwanciya ya yi shiru kan bed yana tunanin yawan aiyukan gida da ya riƙa yi bayan tafiyar Amirah har wani rama ya yi lallai Amirah na ƙoƙari sosai duk wannan aiyukan ita kaɗai take yinsu ta sha roƙonsa ya sama mata ƴar aiki da zata riƙa taimaka mata da aiyukan gida amma yana ganin lalaci ne kawai da kazanta yasa Amirah cewa a sama mata ƴar aiki,wayarsa dake daure gefin side drower ya dauko da niyyar kiran layin Amirah tarin miss calls ɗin Unaisa ya gani,bai kira Unaisa ba sai kiran layin Amirah ya kira yau ma kamar kullum wayar a kashe ya kira har sau biyar amma wayar a kashe hakan yasa ya hakura ya ajiye wayar,can cikin bacci ya ji alamar shiga kira a wayarsa laluɓar wayar ya yi kafin ya amsa kiran wayar ta katse ba tare da duba wanda ke kira ba Ɗalha ya kashe wayar gaba ɗaya saboda ba ƙaramin gajiya ya yi ba,washe gari karfe sha ɗaya na safe Ɗalha ne zaune tare da yaran sa cikin wani babban salon na gyaran gashin yara mata Ɗalha ya ce a fara wankewa yaran kai kafin a yi masu kitso kamar yadda ya faɗa hakan suka yi basu bar salon ɗin ba sai karfe biyu na rana Ɗalha ya biya kuɗin wanken kai da kitso su uku kawai dubu sha ɗaya harda ɗari biyar cikin zuciyarsa yana mamaki daman haka Amirah ke biyan ƙudin gyaran kan yaran tunda yake da ita bai taɓa biyan ƙudin ƙitson yara ba,a nan gefen salon ya siyawa yaran abinci nan cikin mota suka ci abinci Allah ya taimake Ɗalha tun fitowar su basu yi faɗa ba amma fa sun sa shi magana ya koma kamar wani zararre cewa ya ke ''kai bari ke tashi a wajen kai bani wannan ke ajiye waccan'' haka ya yi ta fama bayan sun gama cin abinci ya wuce da yaran maza wajen aski an masu aski daga nan ya wuce gidan su Unaisa,Ɗalha ya dauki a ƙalla mintina arba'in zaune cikin mota yana jiran Unaisa ga unguwar babu yara ya kira layin wayarta ya fi a ƙirga amma bata ɗaga ba daga karshe ya tura mata saƙo ya ce yana jiranta waje nan ma ta buɗe saƙon amma bata masa reply ba ganin yamma ya fara ƙaratuwa yasa Ɗalha ya ja motarsa ya mayar da yara gida
Ranar talata karfe uku da rabi na rana Amirah ce durkushe gaban yaya Nasir,tun azahar ta sauka garin Kano lokacin da ta zo yaya Nasir yana kasuwa matarsa Bilƙisu ce ta kira sa ta shida masa cewa ga Amirah ta zo,babu shiri yaya Nasir ya baro kasuwa zuwa gida sosai hankalin su ya tashi kwanakin baya da aka rinƙa nima Amirah shekaran jiya Lahadi Baba ya sa aka yi sauƙan Alkur'ani duk inda Amirah take Allah (S W T) ya baiyana ta sosai yaya ki yiwa Amirah faɗa ya nuna mata abinda ta yi ba daidai ba ne Amirah bata ce masa komai ba ya yi faɗan sa ya gama daga baya ya tambaye ta inda ta tafi tsawon kwanakin nan,nan Amirah ta ce masa gidan Ƙawarta take bayan Amirah ta gama masa bayani ne yaya Nasir ya ce ta dauki jakarta su tafi gidan Baba,Baba na zaune kan darduma cikin parlour da alama bai dade da idar da sallar la'asar ba,kamar a mafarki ya ga Amirah tare da yaya Nasir sun shigo parlour da ido Baba ya rinƙa bin Amirah ta kallo har ta zauna idon Baba a kanta
SHUUKRAN/022