MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 20

by @maimunabala209

MATAR GIDA 020



SHUUKRAN /022



P20 



A hankali Baba ya cire idonsa daga kan Amirah ya mayar da hankali kan azkar ɗinda yake, bayan wasu ƴan mintina ya shafe addu'a murya can ƙasa yaya Nasir ya ce ''barka da hutawa Baba" shiru Baba ya yi bai ce komai ba idonsa kan Amirah da ta sa kai ƙasa muryar Baba ne yasa ta ɗago a hankali tana son yin magana amma ta ƙasa Baba ya ce ''daga ina kike?" maganar ya sarkafe mata a mokoshi ta ƙasa furta komai yaya Nasir ne ya ce ''gidan ƙawarta ta tafi Rumaisa'' Baba ya yi shiru na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''me yasa ba ki zo gida ba? ko gidan iyayen mijinki'' nan ma Amirah ta yi shiru bata ce komai ba, haka ma yaya Nasir shiru ya yi yana sauraran Baba yadda yake yiwa Amirah faɗa cewar tunda yana raye iyayen mijinta suna raye bai kamata ta tafi wani wajen ba,haka dai Baba ya yi ta mata faɗa daga karshe ya daura da nasiha bayan doguwar nasihar da ya yiwa Amirah ne ya ce ta dauki jakarta ta shiga cikin gida babu musu Amirah ta tashi jiki babu kwari ta shiga cikin gida, a nan parlour ta haɗu da Aunty matar Baba cike da girmamawa Amirah ta gaishi ta babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwar Amirah ta wuce ɗakinta da tun kafin ta yi aure take zama a ciki,bayan auren Amirah Aunty ta so yaranta su koma ɗakin amma Baba ya ce 'a'a su zauna a ɗakin su,gaba ɗaya bangaren ɗakuna uku ne kowanne da bayi a ciki sai parlour da kitchen ɗaki ɗaya Aunty ke ciki ɗaya koma yaranta na ciki dake duka mata ne su biyu sai yanzu da take goyun jariri ɗan watanni biyar,ɗaya ɗakin kuma na Amirah,bangaren Baba daban yake ɗakuna biyu kowanne da bayi a ciki sai parlour da daining space,su kowa yaran maza ɗakunan su a waje yake daga shiga gidan ɗakunan su ne jeri tare bayi daga can gefe,bayan shigar Amirah ɗaki bathroom ta wuce da niyyar alwala amma sai taga ya yi ƙora sosai hakan yasa ta fito parlour ta mayar da dubanta ga Aunty dake zaune kan kujera one sitter ta sha ƙwalilliya cikin wata koriyar atamfar ciganvi cike da girmamawa Amirah ta ce ''Anty dan Allah  in akwai kilin ki bani na wanke bayi ya yi datti sosai'' ba tare da kallon inda Amirah ke tsaye ba idon Anuty kan tv ta cewa ƴar aikinta ta je ta dauki kilin cikin store ta kawuma Amirah ba'a dauki lokaci mai tsawo ba ƴar aikin ta kawowa Amirah kilin Amirah ta sa hannu ta karɓa daga hana ta wuce ɗakinta,bayan shigarta ɗaki ne taga karfe huɗu saura mintina goma hakan yasa ta ajiye kilin ɗin kan gado ta wuce bathroom ta dauro alwala,bayan ta idar da sallah ta yi addu'a ta shiga gyaran ɗakin da bathroom,karfe shidda daidai na yammacin wannan ranar Amirah ce zaune kan darduma cikin ɗakinta sanye take cikin wasu riga da wando masu tsamtsi kalar toka ta zura dogon hijab hannuta riƙa da calbi tana jiran kiran sallar magrib,sanyin na'urar AC haɗe da kamshin mai da turaren Amirah yasa wani khamsi haɗe da sanyi ke tashi cikin ɗakin na yanayi mai kwantar da zuciya haka nan ta kasance har lokacin da aka fara kiran sallah bayan ta idar da sallah ne har sannan tana zaune kan darduma ƴar aikin Anuty ta shigo ɗakin hannunta riƙe da kolar tuwo da miya ta dire gaban Amirah 

















Amirah ta idar da sallar isha'i ta ci abinci ta wanke baki ta dauki remote ɗin AC ta rage gudun AC tare da kashe wutar ɗakin gaba ɗaya,hasken farin wata da ya haska ta tagar ɗakin ne ya sa ɗakin yin haske kaɗan,ba tare da ɓata lokaci ba Amirah ta shige bargo tana karanto addu'ar bacci tare da rintsa idanunta,muryar Aunty ta ji a kofar ɗakin tana sallama tare da bugun kofar a hankali,a hankali Amirah ta ɗago kanta daga matashi tana mamakin mai kuma zai shigo da Anuty ɗakinta a wannan lokaci harda dai dare bai yi ba sosai ba lokacin karfe tara ne da ƴan mintina cikin sanyin murya Amirah ta amsa sallamar tare da faɗin ''shigo'' Anuty ta buɗe kofar tare da kallon gadon da Amirah ke kwance ta ce ''Babanku ne ke kiran ki'' tana gama faɗin haka ta juya ta fita daga ɗakin Amirah da mamaki ya gama cikata ta yunƙura ta tashi zaune tana tunanin me kuma ya faru da Baba zai aika a kirata a wannan lokaci,haka dai ta tashi jiki babu kwari ta dauki hijab ɗinda ta yi sallah ta zura bata tsaya ko ina ba sai parlourn Baba 











Tun daga bakin kofar parlour Amirah ta jiyu kamshin turaren Ɗalha amma bata yi tunanin shi ɗin bane a tunaninta iska ce ta koro khamsin turaren daga wani waje ba tare da wani dogon tunani ba ta ƙusa kai cikin parlour bakinta dauke da sallama,numfashinta ne ya kusa tsinkewa ganin Ɗalha da Muhsin zaune gaban Baba kansu a ƙasa sun ƙalmashe ƙafafu Amirah ta ji kamar ta juya ta bar parlourn amma babu dama hakan ta dauki a ƙalla mintina huɗu tsaye kofar parlour saida Baba ya yi mata magana kafin ta saita nitsuwarta ta karasa shiga parlourn,zama ta yi can nisa da Ɗalha ko da wasa bata yarda ta kalle fuskarsa ba,sosai take jin tsanarsa a zuciyarta muryar Baba ne ya katse mata tunani inda ya ce ''ɗazu bayan tafiyar Nasir na kira Alhaji (mahaifin Ɗalha) na shida masa cewa kin dawo gida duk tsawon kwanakin nan kina can garin Kaduna gidan ƙawarki ya nuna farin cikin sa sosai har ita mahaifiyar mijinki mun yi waya da ita,ta ce ta kira wayar ki a kashe haka dai muka gama magana da su,to bayan mun gama magana ina zaune kofar gida mijinki ya zo tare da aminsa ya ce min ya fahimci kuskurensa a ba ki hakuri kuma ya maida ki'' Amirah bata san abinda ta ji a lokacin ba farin ciki ko akasin sa wani irin sanyi ta ji a zuciyarta lokaci guda ta ji kaso sittin daga ɗari na damuwowinta an yaye mata su,nan dai Baba ya shiga yi masu nasiha kan zamantakewar aure karfe goma da rabi Baba ya kalle Amirah ya ce ''je ki dauki jakarki ki bi mijinki sai da safe Allah ya yi maku albarka ya kawar da shiɗan a zaman ku''Ɗalha ya amsa da ''ameen'' murya can ƙasa,tun da Amirah ta shigo parlour sai yanzu ya yi magana, Amirah ta yi magana murya can ƙasa ta ce ''yanzu zamu tafi Baba?" Baba ya ce ''eh da wani abun ne?" cikin kwantar da murya Amirah ta ce ''na ga dare ne'' Baba ya ce ''babu komai Allah ya tsare hanya'' Ɗalha da Muhsin suka amsa da ameen Amirah ba ta sake cewa komai ba ta tashi jiki babu kwari ta wuce ɗakinta ta haɗa kayanta daga nan ta sallame Anuty da Baba 

















Bayan Amirah ta fita waje ta ta ga Muhsin tsaye jikin mota yana danna waya inda Ɗalha na zaune cikin mota,cikin yanayinta na sanyi ta taka har inda motar Ɗalha yake ta kalle Muhsin da har sannan hankalinsa na kan wayarsa sallama ta yi masa Muhsin ya amsa fuska sake Muhsin na shirin magana Amirah ta ce ''amma ba Kaduna zamu tafi da daren nan ba?" Muhsin ya sosai ƙeya ya ce ''eh to na ce masa mu kwana gidan Ammi gobe mu wuce amma ya ce yafi son mu tafi yanzu'' Amirah ta ce ''oky'' daga haka ta buɗe kofar baya ta shiga,bayan ta zauna cikin mota a hankali ta ɗago kai ta kalle madubin gaban mota idonta ya sauka a fuskar Ɗalha ya ƙura mata ido kamar yau ya fara ganinta Amirah ta yi saurin kawar da idonta shi kuwa Ɗalha idonsa a kanta yana ƙare mata kallo wani irin kyau yaga ta yi masa ta ƙara haske amma ta rame kaɗan ƙwayar idanunwanta sun yi fari ƙal,ƙasar idanunwanta sun ɗan yi baƙi kadan saboda yawan kuka,tun ɗazu da Ammi ta kirasa lokacin yana hanya zuwa kwashe yara a makaranta ta ce masa Amirah ta dawo ya ji gaɓa ɗaya ya ƙasa sukuni ya ji sam bazai iya kaiwa gobe ba tare da ya haɗa ido da Amirah ba, kamar yadda Ammi ta ce masa,ganin yake kamar Amirah zata sake goduwa kafin gobe gani yake kamar zuwa gobe za'a ce masa ba'a san inda take ba,Allah Allah ya ke ya haɗa ido da ita wani irin ƙima da darajarta yake je cikin zuciyarsa,kullum sai yai ta mamakin yadda take tafiyar da al'amuran gidan da yara sati ɗaya tal rabonta da gidan, wannan satin ɗaya a wajen Ɗalha ya fi wata guda tsabar wahala da aiyukan gida da ya sha a wannan kwanakin,gani yake ko albashi zai riƙa yiwa Amirah bai biya ta ladan hidima da gida da take ba,hakan yasa tun kafin dawowarta ya sawa zuciyarsa salama ko da wasa ba zai sake ƙorafi kan Amirah bata kula da gida da yara ba,duk wani taimako da take buƙata zai taimaka mata,ya rinƙa jin kunyar abubuwan da ya yiwa Amirah,ko a gaban waye zai yarfa ta bai damu ba,lokacin da Baba ya ce masa duk kwanakin nan Amirah na gidan ƙawarta Rumaisa,tsaf ya tuna da wulaƙancin da ya yiwa Rumaisa dama sauran ƙawayen Amirah amma gashi an waye kawar Amirah ce ta riƙe Amirah har kuma ta bata shawarar ya kamata ta dawo garesa









SHUUKRAN/022