ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-1/2

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

SATURDAY 12:10pm 5/06/2021

*AMINU KANO INTERNATIONAL AIR PORT*

Wani matashin saurayi na hango tsaye ga dukkan alamu saukarsa a jirgin kenan, fuskarsa cike take fal! Da walwala. Rufe idanunsa ya yi yana me sheƙar ƙamshin ƙasar ta shi cikin jin daɗi ya furta, "Alhamdu Lillah."

Zuwan wani bawan Allah ne ya sa shi bude ido, "Barka da zuwa Yallaɓai."

Murmushi ya yi kawai ba tare da ya ce komai ba.

Cikin sauri ya ja akwatin da ke gefensa suka karasa inda ya yi parking motar, da sauri ya buɗe masa motar sai da ya shiga kan ya aje akwatin a baya.

Kasancewar Yasan *FU'AD* bai son gudu a mota a hankali yake tuƙin, ganin shiru ya yi yawa yasa shi fara magana, "Ranka ya daɗe gaskiya mun yi matuƙar kewarka a fada, musamman mu da muke ma'aikata. Ina ga su Hajiya Babba kuma, balle ace mai martaba da kullum maganarsa kenan *YAREEMA FU'AD*. Ranka yadaɗe fatan dai ka dawo kenan ba za ka kuma koma wa ba, domin yau ba iyaka fada ba gabaɗaya ilahirin birnin Kano sun shirya tarban adalin shugaba."

Duk maganar nan da Ado driver ke yi FU'AD bai ce ƙala ba sai murmushi da ke bayyana a fuskarsa har cikin ransa farinciki yake ji na musamman, yau ga shi a kasarsa yana kallon al'umma. Gani yake tamkar wata sabuwar duniya ya shigo, ashe haka ake rayuwa a kasata? Abin da yake Tambayar kansa kenan yayin da yake ta kalle-kalle ta windown motar. "Tabbas ni'ima na inda al'umma take ina son kasata, Kuma ina alfahari da ita a ko ina."

A zuciyarsa yake duk maganganun nan.

Ado ne ya ƙara fargar da shi ta hanyar faɗin, "Yallaɓai gaskiya na ji daɗin dawowarka ba kaɗan ba wallahi ka...

FU'AD ya katse shi da faɗin, "Oh Ado har yanzu kana nan da wannan surutan naka, ba ka gajiya da magana ne wai?"

Kai ya fara sosa wa tare da faɗin, "Ah yallaɓai ai maganar ce akwai daɗi musamman ga mutanen ƙwarai irin ku."

FU'AD ya yi murmushi, "To na ji, yanzu dai kalli gabanka na zaƙu inje ga fada."

Ba yadda Ado Driver ya iya haka ya yi shirun nan dole, tafiya suka ci gaba da yi cikin kwanciyar hankali, kwatsan go-slow ya tsayar dasu, ko a jikin FU'AD tamkar a kunna ma shi T.V haka ya dasa idanunsa ga kallon titin da mutanen da ke ta shawagi a wajen.

Kamar an ce ya juya, karaf! Idanunsa suka yi tozali da wata matashiyar budurwa da aƙalla ba za ta wuce shekara ashirin ba a duniya, fitowa ta yi daga cikin NAPEP. Da ka ga yanayin kayan da ke jikinta ba tare da an ce komai ba za ka fahimci cewa 'yar talakawa ce, tsallaka wa ta yi kamar za ta ci gaba da tafiya, wani tsoho ta rike wa hannu tana sakin murmushi. Tsallakar da shi ta yi, sannan ta ce: "Baba ka daina fita kai kaɗai kaji, ka ga tsufa ya fara kama kae

Ya ce: "Na gode 'yar nan Allah ya yi miki albarka, Allah biya miki dukkan bukatunki na alkairi duniya da lahira,l. Allah yasa ki gama da iyayenki lafiya, sannu 'yar albarka inSha Allah rayuwarki za ta yi kyau fiye da tunanin me tunani."

Murmushin nan dai da baya gushewa a fuskar *FARIDA* duk rintsi yanzu ma shi ta yi tare da fadin, "Amin ya Allah na gode Baba."

Duk Abin nan idon FU'AD na kanta ya kasa ɗauke wa, ganin ta koma cikin NAPEP ɗin ne ya ƙara tabbatar wa da FU'AD cewa don taimakon tsohon ne kawai yasa yarinyar ta fito.

Har a ransa yake jin yarinyar ta yi matuƙar birge shi, dama akwai masu tausayi haka? Kuma cikin talakawa? Kasa jure wa ya yi, ya ce: "Malam Ado ka yi mini wani taimako mana, ina so na sauka in shiga NAPEP ɗin can, ka tafi gida zan zo daga baya."

Ado ya buɗe baki, "Yallaɓai! Ka rufa mini asiri don Allah, idan na koma fada ba tare da kai ba, ai ba mai martaba ba jama'ar gari ma kaɗai sa nemi tsine mini."

FU'AD ya kalli Ado cikin yanayin ɓacin rai.

Nan jikin Ado ya yi sanyi domin ya san ba ƙaramin Abu bane zai kawo ɓacin rai fuskar YAREEMA FU'AD.

Cikin sauri ya buɗe masa ƙofar tare da faɗin, "Takawarka lafiya YAREEMA FU'AD ɗan sarki jikan sarki kuma me jiran gado da yardar Allah. Allah kare mana kai duk inda za ka sa kafarka, farincikinka shi ne farincikinmu Allah ja kwana adalin shugaba."

Tafiya FU'AD ya yi ba tare da ko waiwaye ba, cikin sa'a kuwa go-slown ya ragu motoci da NAPEP sun fara haramar tafiya kenan ya yi saurin tsayar da wanda FARIDA ke ciki, tunda ya shiga kanta na ƙasa ko ɗago wa ba ta yi ba, karatun littafin da ke hannunta kawai ta sa a gaba.

FU'AD na son yi mata magana amma ya gagara kuma ya rasa dalilin hakan, tunda ya shiga ban da kallonta ba abin da yake, ita ko ba ta ma san yana yi ba.

Ya buɗe baki da niyyar yi mata magana kenan kan ya furta ta ce: "Bawan Allah ɗan tsaya please minti biyu."

Tsayar da NAPEP ɗin ya yi a gefe ta fito daga Mai NAPEP har FU'AD bin ta da kallo kawai suke, wajen wasu garagu ko in ce nakasassu kawai ta nufa. Hannu tasa a jaka tare da ciro 'yan canjinta gabadaya kuɗaɗen sun ji jiki, naira hamsin ne kawai amma 'yan canji goma daya da ashirin biyu. Ga dukkan alamu su kaɗai ne kuɗin da ke gare ta, amma ta za ɓi da ta yi sadaka da su fiye da ta ci, kasancewar su uku ne manyan ta ba wa ashirin-ashirin ɗin, ƙaramin yaron kuma ta ba shi naira gomar. Kamar kullum addu'o'i suka dinga surfa mata tare da sa mata albarka.

Wannan al'adar FARIDA ce a kullum kanta wuce wajen aiki sai ta tsaya wajen bayin Allahn nan ta ba su sadaka, wani lokacin har abinci take ɗauko wa daga gida ta kawo masu, idan kuwa kuɗin mota ne kaɗai gare ta ba ta da na ba su sadaka, duk da kasancewar nisan da ke tsakanin gidansu da wajen aikinta ta zaɓi da ta zo a ƙafa ta yi musu wannan sadakar dai kafin ta wuce.

Juyo wa ta yi ta dawo NAPEP tana fadin, "Don Allah ku yi haƙuri na ba ta muku lokaci."

Shi ko FU'AD kallonta kawai yake cike da mamaki fal! Zuciya, "Wai shin dama haka talakawan suke? Lallai indai hakane, talakawa ma sun fi masu kuɗi samun nishaɗi da sukunin rayuwa."

Yana ta tunani a ransa kala-kala bai ankare ba sai ji ya yi ta ce: "In an samu waje zan sauka a nan."

Malam Ado kuwa ya isa fada duk an taro kowa na jiran fitowar YAREEMA sai ga Ado shi kaɗai, da sauri Hajiya Babba ta ƙarasa, "Ya haka? Ado kada ka zo mini da mummunan labari, kada ka ce mini wani abu ya faru da YAREEMA kada ka kuskura ka fada mini."

Jiki na rawa Ado ya ce: "Ranki ya daɗe, YAREEMA ya iso kuma yana cikin ƙoshin lafiya, amma...

Sai ya gagara ƙarasa wa.

Cikin tsawa Hajiya Babba ta ce: "Amma me? Na ce maka amma me?

Ado ya ce: "Amma yana zuwa, sauka ya yi a motar wai zai yi wani abu."

Cikin ɓacin rai Hajiya Babba ta kalli Jakadiya tare da fadin, "Ba ni wayata, tabbas idan YAREEMA bai dawo kafin shigowar mai martaba ba akwai babbar matsala a fadar nan. Kai Kuma Ado za ka yi bayani ne kafi kowa sanin halin mai martaba akan maganar YAREEMA."

*****

Farida kuwa sauka ta yi tare da kallon Mai NAPEP, "Na baka kudin ko?"

Ya ce: "E Hajiya."

Zai ja NAPEP kenan FU'AD ya ce: "Malam ɗan tsaya ina jin nima a nan zan sauka."

Haka kuwa aka yi.

Ya sauka tsaya wa ya yi yana kallon inda FARIDA za ta yi, nan ko ya ga ta tsaya wajen wani ƙaramin Chemist, hannu ta sa a jaka tare da ciro key, sai da ta yi addu'o'i kafin ta buɗe. Yana tsaye yana kallon ta ƙoƙarin ƙarasa wa gare ta ya yi karaf sai ga kiran waya ya shigo masa.

Lambar Hajiya Babba ce cikin sauri ya daga tare da kara wa a kunne.

"FU'AD abin da ka yi ka kyauta kenan? To maza ka faɗa mini inda kake Ado ya dawo ya ɗauko ka." Cewar Hajiya.

FU'AD ya ce: "Aa ba sai ya zo ba gani nan a hanya Hajiya."

Cikin fushi take maganar, "Shekara nawa rabon ka da ƙasar nan ta yaya za ka ce mini wani ga ka a hanya idan ba ɓacewa kake son ka yi ba, ina kasani? Na ce ma ka fada mini inda kake ka tambaya a faɗa maka ina ne nan."

FU'AD ya ce: "Hajiya Allah ki ba ni 5 minutes zan iso gida yanzu."

Katse wayar ta yi tare da kallon Ado.

"Tabbas kaje ka nemo YAREEMA duk inda yake kafin dawowar mai martaba, inda ba haka ba kuma ka san me zai biyo baya. Duk abin da ya samu YAREEMA alhaki akanka."

Ta faɗa tare da tafiya nan kuyangunta suka fara bin bayanta.

Hajiya ƙarama kuwa da ke laɓe ta window hamdala ta yi tare da faɗin, "In Sha Allah FU'AD ba zai shigo fadar nan ba."

Ba yadda Ado ya iya haka ya koma neman YAREEMA.

Shi ko suna kammala waya da Hajiya Babba ya hau wani NAPEP ɗin.

****

Abin mamaki gwanin sha'awa gabaɗaya ma'aikata, 'yan uwa da abokan arziki duk sun cika gidan maƙil! Al'umma a nata shagalin bikin zuwan YAREEMA.

Saukarsa kenan ya tsaya yana kallon MASARAUTAR ta su cike da kewarta da ya yi na shekaru, amma ta wani ɓangaren hankalinsa na kan FARIDA ji yake tamkar ya koma ya tsaya ya yi ta kallonta kawai.

Gabaɗaya fadawan jeru wa suka yi tare da durƙusa wa a bayansa da gefensa, masu kiɗe-kiɗe da bushe-bushe na yi masu fadanci tare da jinjina nayi, *MARABA DA DAWOWAR YAREEMA ƊAN SARKI JIKAN SARKI, KUMA SARKI DA YARDAR ALLAH, ADALIN SHUGABAN DA BABU KAMARSA, TAKAWARKA LAFIYA SHIGABAN ƘWARAI. KA YI GADON ADALCI DA KAMALA BABU WANI GABANKA KAI ƊAYA TILO FARINCIKIN MASARAUTAR ADALAI.*

Haka suka ci gaba banda kiɗan saurauta da kirari ba abin da ake yi wa FU'AD shiko a ransa sam ba ya son wannan abubuwan, da yana da damar hana su da ya hana. Amma ba yadda ya iya wannan al'adar gidansu ce.

Sai da suka raka shi har fallon Hajiya Babba sannan suka fito.

Da farinciki ta ƙarasa gare shi tare da faɗin, "Barka da dawo wa Yareema magajin sarki, amma ka san tabbas ka kusa ɓata mini rai kuwa?"

Sunkuyar da kai ya yi tare da haɗa hannayensa biyu, "Afwan ranki ya daɗe, ba a son raina na yi hakan ba amma ba za a kuma ba inSha Allah."

Murmushi ta saki, "To Allah ya sa, yanzu ka je ka yi wanka, ka fito ka ci abinci kafin mai martaba ya dawo."

"An gama ranki ya daɗe uwargidan mai martaba." Cewar FU'AD yana dariya.

Kallon shi Hajiya ta yi, "An girma ma ba a daina tsokana ba, kana nan da halinka."

Murmushi ya yi kawai ya nufi dakinsa

Yana shiga kuwa ya yi wanka ya yi sallah, sannan ya fito cikin shigar ƙananun kaya.

Da mamaki yana fito wa ya gan su jere su uku suna jiranshi, daya da alkyabba a hannu, dayan takalmi, daya kuma rawani.

Cikin takaici ya kalle su tare da faɗin, "Wannan fa?"

Daya daga cikin su ne ya ce: "Hajiya Babba ce ta umarce mu da mu sanya maka domin mai martaba ya iso kai kaɗai yake jira."

FU'AD ya ce: "Ok ni kam ba na bukatar wannan kayayyakin ku aje su don Allah."

Ba tare da ya jira amsarsu ba ficewarsa ya yi kawai kai tsaye cikin izza da mulki.

Bin bayansa suka yi har cikin fada, Hajiya Babba ce a hannun dama na gefen sarki, Hajiya ƙarama kuma a ɓangarensa na hagu, sai Fahad da ke gabanta zaune.

Da sallamarsa ya shiga Hajiya Babba buɗe baki ta yi tana kallonsa cike da mamaki, FU'AD bai sa kayan da ta tura masa da su ba, kallonta mai martaba ya yi, "Hajiya ina kayan da na ce a ba wa YAREEMA?"

"Afwan ranka ya daɗe na aika da su kamar yadda ka buƙata amma ban san dalilin rashin sawar YAREEMA ba." Cewar Hajiya.

Ba ƙaramin daɗi Hajiya ƙarama ta ji ba wanda har sai da farinciki ya bayyana a fuskarta, kallon Fahad ta yi tare da sakin murmushi ga junansu.

Durkusa wa FU'AD ya yi ya gaida mahaifin nasa cikin girmamawa sannan ya gaida Hajiya ƙarama, bayan ya gaisa da ɗan uwansa Fahad ne yake faɗin, "Ayi mini hakuri mai nartaba sun kawo mini kayan amma a gajiye nake ba zan iya sa su ba a halin yanzu."

Maimakon faɗa ko nuna ɓacin rai murmushi ne ya bayyana a fuskar mai martaba tare da faɗin, "Hakane fa kana da buƙatar hutu, yanzu dai mu je falo a ci abinci kafin a fara ba ni labarin ƙasar waje."

Kamar yadda mai martaba ya umarta falo aka nufa domin cin abincin.

Shiru ɗakin kowa na cin abinci, mai martaba ne ya katse shirun tare da faɗin, "Ma Sha Allah, wannan ranar na ɗaya daga cikin abin da nake burin gani a raina tunda ka zo duniya har kawo yanzu. Kuma Alhamdu Lillah! Ga shi na gani ka kammala karatunka lafiya, saura ɗaya wato aure. Wanda shi ma zan iya cewa an kammala komai dawowarka kaɗai muke tsammani, kamar yadda ka sani aminina Alhaji Ibrahim Ministern Man Petur, to 'yarsa Fadila ta tasa ita ma ta kammala karatunta kamar yadda ka kammala naka, ina me yi maka albishir da cewa an ba ka Fadila ranar aure kawai muke jiran sa wa."

Nan take gaban FU'AD ya faɗi, zufa ce ta fara keto masa...

*Sharhinku shine karfin gwiwar cigaba da typing dina🥰*

***

Urs xayyeesherthul-humaerath

*ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨

*SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_

_*Gidan Karamci🥰cike da Aminci, NOBLE WRITERS ASSOCIATION Abun alfaharina😘Ina Sonku😍*_