FREE PAGE-3
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*MY JASMINE😘😘WALIDA RANO😘😘SHAFA'ATU😘😘AISHA MUSA😘😘INA YINKU MASOYAN ASALI😘😘DIJAHTY INA YINKU OLL*
*MAH GROUP MEMBERS😫😫 YOUR SHARHIS AR URGENTLY NEEDED😟*
Rasa abun cewa yayi illa bin Yan falon da ido kawai.
Murmushi Hajiya Babba ta Yi tare da fadin, "An Gode da zabin Mai Martaba,Allah Kara nisan kwana."
Mai Martaba ya yi gyaran Murya, gareka Kai Kuma Fahad , "Kasan Hutunka ya kare ya kamata ka fara Shirin komawa makaranta ko?"
Karaf Hajiya Karama ta cafe, "Ni Gaskiya fa 'Dana ba zai koma garinnan ba,in Shima ba za abiya Masa kasar wajen ba abari mun yafe da karatun."
Cikin tsawa Mai Martaba ya ce, "Dakata Fatima! Ki tattara ki bar mun falonnan domin Kan ki batamun Rai Ni zan Bata naki,daga ke har Dan naki kuje kuyi abun da ku ka ga ya dace da ku."
Hajiya Karama ta tashi, Fahad shima ya bita fuuu suka fice afalon Tana mita.
Hajiya Babba ta kalli Mai Martaba tare da dunkufar da Kai, " Ranka yadade ayi Hakuri."
Murmushi kawai ya yi tare da kallon FU'AD ya ce, "Yawwa in ka huta anjima ayau nake so kaje ku gana da Fadila na shirya komai, shiryawarka kawai ake bukata."
Har cikin ran FU'AD Sam bai ji Dadin lamarin ba hasalima har ya fara jin tsanar sunan Fadila bare Kuma ita din,Amman ba yadda ya iya da umarnin mahaifinsa.
Murmushin dole ya kakalo Wanda banace ya Kai zuci ba ya ce, "An Gama Ranka yadade in Sha Allah bayan anyi sallar la'asar sai muje."
"Ma Sha Allah YAREEMA, Allah ya yi maka albarka, Allah ya farantama fiye da yadda ka farantamun." Cewar Mai Martaba cikin Jin dadi.
Haka kuwa akayi bayan FU'AD yaje ya huta ya yi sallah Kan ya fito cikin shigarshi ta manyan kaya, bluen shaddace da hularsa ban da kamashi ba abun da ke tashi, *Ban San wanne zan dauka ba shin shi ya haska kayan ko kayanne ya haska shi?Hhh ku zaban mana daya*
Kamar yadda Mai martaba ya tsaya da motoci uku za afita, na farko da karshe masu tsaro na tsakiya Kuma YAREEMA FU'AD ne ciki..
Haka ko tafiyar ta kasance har Isa sun su ga gidansu Fadila.
Tun daga wajen Gidan zaka San ba karamin Gida bane, ya kyeru iya kyeruwa.
Wani falo aka ajiye FU'AD ,da ka ga fuskarshi zaka San Sam babu walwala tatttare da ita.
**Sallama akeyi Mata Amman tamkar ba ta San anayi ba,kwance take amakeken gadonta hankali kwance take Danna wayarta.
Kusan minti biyar Wata matashiya na tsaye Amman Bata bi ko ta kantaba, can tayi tsaki tare da fadin , "Ke kuma menene?"
Cikin yanayin tsoro take fadin, "Hajiya Daman Momyce tace in sanar da ke cewa bakonki ya iso."
Wani tsakin ta Kara makawa da yafi na farko sai da ta kalle Yar Aiken sama da kasa tare da galleta da harara Kan tace, "Naje jeki."
Cikin sauri kuwa ta fice.
Kara gyara zamanta tai agadon ta cigaba da chatting dinta hankali kwance.
FU'AD kuwa na zaune afalo kamar an aJe gawar shanu,tun abun bai dame shi har ya Fara jin takaici.
Sai da ta Yi chatting dinta son Rai, ta Gama Duk nuku-nukunta Kan ta Sa azamar fitowa fuska amurtuke ko alamar murmushi Babu,aranta take fadin, "Ni Wallahi ba banzan da zan Bata lokacina Akan shi, suje suyita yi zasu gaji su barni."
Ko Sallama Babu ta shige Falon cike da kasaita,Ganin FU'AD ba ta San lokacin da ta furta ba , "Sallam Alaikum."
Kallon take ta kasa dauke ido gare Shi,Nan take Taji tsantsar so da kaunarshi ta shiga ranta ,abun mamaki wadda Bata dauki so akomai ba yau ta fada tarko ASHE HAKA SO YAKE!?
Kallonta ya yi Aba yadda ya iya, ganin ta shigo da gadara da iko Amman sun tafi lokaci guda ta bige da kallonshi, gyaran Murya ya yi.
Cikin Jin kunya ta dauka idonta Kan shi tare da durkusar da Kai.
Gabadaya cikinsun ba Wanda ya Kara magana, FU'AD na jin Izza irinta ta jinjinin sarauta , Fadila kuwa tazo ta ga abun da batai tsammaniba, domin gabadaya gayen ya tafi Mata da zuciya .
Kallon agogon hanunshi ya yi,ya ta shi tare da fadin, "Sai Anjima."
Ji Tai tamkar kada ya tashi haka Kuma tamkar kada ya daina magana,ita Kanta muryar ta shi ta tafi da zuciyar Fadila.
Ba yadda ta iya, abun mamaki ya shiga ranta Kuma ya yi Mata kwarjini.
Yana fita da gudu tayi cikin gida Tana Kiran Momy.
Abangarensa kuwa ko kadan Fadila Bata birge shi ba hasalima kallo daya ya Mata ta Kara fita Masa akai.
*WANENE YAREEMA FU'AD?*
YAREEMA FU'AD Matashine Mai kimanin shekara Ashirin Da Bakwai,Jinin Fulani Kuma na sarauta,Mahaifin shi Mai martaba Ilayasu Muhammad FU'AD, Sarki,Matashin biyu Hajiya Babba (Maryam) itace matarshi ta Fari,sannan Hajiya Karama (Fatima) ,Mai martaba mutum ne Mai ADALCI tun daga cikin gidansa har waje dama Al"ummarsa, baya taba magana biyu in ya yi to fa ya yi shikenan ba chanji, 'ya'yansa biyune kacal aduniya, YAREEMA FU'AD Dan Hajiya Babba da Kuma Fahad Dan Hajiya Karama, Mai martaba ya daura son Duniyar Nan Kan FU'AD Wanda zan iya alakantata da cewa soyayyar da yake yima mahaifiyarsa ce ta dawo kansa,Ba karamun kishi da haushin FU'AD da mahaifiyarsa Hajiya Karama take ba,Amman wani abun ba yadda yadda iya,domin daga Mai martaba har Hajiya Babba da FU'AD sun fi karfinta,tun Yana karami take tsafe-tsafenta Amman ko tayi abanza hakan Kuma bai sa ta fasa ba,akullum ta kance "muje zuwa dai watarana za adace" Dalilinta yasa Mai Martaba dauke FU'AD tun Yana shekara goma sha biyar ya Mai martaba ya maidashi kasar waje domin yin karatunshi gabadaya, Bata da BURIN da ya Wuce danta ya gaji babanshi Wato Mai martaba, Dan haka Fahad ya taso cikin kasaita da isa,zan iya cewa wani lokacinma yafi Mai martaba zakewa. FU'AD kuwa kwata-kwata Lamarin sarautar ma bai birgeshi Kuma bai da burin Zama Sarki,abunka da jini gashi dai da Izza cike da Mulki irin na sarauta Amman hakan Sam baya tsarinsa.
Gabadaya rayuwarshi ya yita ne cikin kadaice ba aboki ba kowa , ko akasar wajenma da masu tsaronshi,hakan yake da burin shima ya yi rayuwa kamar kowa,
FU'AD Farine dogo Mai saje,son kowa kin Wanda ya rasa, indai cikar Matashin Saurayine cike da kasaita to FU'AD ya kai, ba macen da zata gan shi bai birgeta ba,
Sam abun duniya bai dami FU'AD ba Yana so ya rayu kamar kowa yayi walwala cikin jamaa kamar kowa Amman tayaya??
*WACECE FADIL?*
Fadila 'Yace ga Attajiri,Hamshakin Mai kudi,minstern man peturt ALHAJI IBRAHIM, abokine ga Mai martaba, 'Yarsa daya tilo aduniya, fadila da maihaifiyarta Hajiya Amina, Fadila sakaliyar yarinyace ko ince ta taso asake,ba kwaba, ba tsawatarwa gun mahaifinta, Fadila na da wulakanci na kin karawa mussaman ga Maza in kace kana sonta to tamkar kirawo ma kanka wulakancine da tozarci.
Wannan Kenan
FARIDA na chemis gari ya Fara hadewa gashi ba kudi ahannunta , ba shiri ruwa ya barke,ruwa bai daukeba har karfe shida tayi, Kuma Oga Hamisu bai zo ba, hakan yasata kulle chemis din kawai ta shiga ruwan,sauri take acikin ruwannan harta ta isa gida.
Tana shiga Mama ta kama salati, "Inallillahi wa Inna ilaihir Raji un Amman Sam Baki kyautamun ba farida,cikin ruwannan Kika fito akafa Kika dawo ko? Kai Nikam ban San yadda xanyi dake ba Wallahi,Ina kudin motan Dana Baki?"
FARIDA tayi shiru.
Mama ta cigaba da magana, "nasani ai Zaki Rina anyi abun da aka Saba sarauniyar tausayi, to shi Oga Hamisun fa?"
"Mama bai zo ba,Kuma naga dare yayi shine kawai na fito kiyi hakuri." Cewar FARIDA.
Mama ta ce, "Allah ya kyauta ki canja Kaya in kinyi sallah ga abincin Nan ki dauka kici."
FARIDA na canja Kaya ta dauro alwala tayi sallah tashin da zatayi kawai numfashinta ya Fara sama-sama
Ahankali ta Fara fadin, "Ma.....
*** URS xayyeesherthul-humaerath
***
*ASHE HAKA SO YAKE!!*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
***
_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_
_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*
_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_
*TUKWICI*
_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_