FREE PAGE-4
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*WACECE FARIDA?*
FARIDA 'Yace ga marigayi Mallam Ibrahim tare da Mahaifiyarta Hafsa, Itace 'Yar fari sai Kanwarta Farisa Mai shekara goma Sha biyar,ita kuwa FARIDA na da shekara Ashirin aduniya,Iyayensu talakawane sosai domin sai an fita ma Kan asamo masu kudin abinci,hakan Kuma bai kashewa Mallam Ibrahim gwiwa ba Dan sai da yasa FARIDA ta yi karatun secondry ta ,ita kuwa Farisa Bata samu damar kammalwa Allah ya dauki ran Mahaifinsu, Nan mahaifiyarsu Bata zauna ba ta Fara sana'ar abincin siyarwa,ita Kuma FARIDA Allah yasa ta samu wani bawan Allah ya dauketa jiran chemis,da haka suka cigaba da rayuwarsu.
FARIDA Fara ce sol doguwa Kuma kyakkyawa Amman Sam kyanta baya rudarta, ta bar Kanta ayadda Allah ya yi ta batare da Kai Kanta gaba ba. FARIDA nada matukar tausayin talakawa domin ita tasan yadda ta taso, Koda naira biyarne kadai gareta Bata kyashin yin sadaka da ita,Tana rayuwarta cikin walwala da Nishadi, Ba abun da farida ta tsana fiye da masu kudi,domin duk kallon kudin goro take yi masu,masu son Kan su tare da wulakanta talakawa, mussaman aduk Lokacin da ta tuna jinyar Mahaifinsu yadda yadda suka dunga neman taimako masu kudi na wulakanta su sai ta zubda kwalla ,, Tana da ciwon Athma Wanda yake yawan tashi mussaman alokacin damuna ko sanyi, hakama in ranta ya bacihaka take fama,duk da kasancewar attajirai da yayan masu kudi na binta,Bata taba bi takansu,wasu Dan kyanta,wasu Kuma Dan su Bata Mata tarbiya,arayuwarta ba Wanda yake birgeta kamar Dan gidan sarkin su YAREEMA FU'AD , Duk da kasancewar Bata San shi ba,Amman labarinsa da halaiyasa Duk Tana ji,Kuma ya na matukar birgeta,Tana da burin ganin shi arayurwata.
SHIN KO BURIB FARIDA ZAI CIKA? KU BIYONI ASANNU DAN JI AMSAR
Wannan Kenan!
Cigaban labarin...
"Mah....mah num.....fa..." Bata karasa Fada ba kawai ta sume,cikin firgice Farisa da ta idar da sallah take kwallawa Mama Kira.
Nan da Nan suja jajebeta sai asibiti, rayuwa ko mutuwa,abun mamaki kusa cikin sa'a Allah ya dawo da ita hayyacinta, ba adauki wani lokaci ba ta Gama warewa kamar ba ita ba, Nan da Nan kuwa aka sallamesu sai gida.
*****
Ko da FU'AD ya koma gida bai ce da kowa komai ba, illa Hajiya Babba da ta tambayeshi, "FU'AD Ina fatan dai kun sasanta da FADILA?"
"Eh " kawai ya ce batare da ya Kara fadin komai ba, azuciyarsa kuwa addua yake , "Allah yasa ta ce ban Mata ba,domin Nikam har ga Allah bana so Kuma Bata mun ba Sam."
Da wannan takaicin yatafi dakinsa.
A bangaren FADILA kuwa daren Ranar kasa barci tai,ji tai tamkar ta ga FU'AD gabanta ta ta kallonshi ko zai zame Mata abinci ba zai taba ginsarta ba,da Tunanin har tai barci.
Wa she gari
FADILA ce zaune agefen Dady,da Mumynta suna karyawa, Dady ya ce, "Au fa Na manta Fadila jiya ya kuka kare da FU'AD shin kun sa santa kuwa?"
Cikin Sauri ta furta "Eh."batare da ta ankare ba.
Murmushi Dady ya yi tare da fadin, "Oh FADILA wannan amsa haka? Gaskiya 'Dana ya cire tuta,Daman haka nake da buri,tunanina wajenkine matsalar dama,Kuma gashi kin Bani mamaki."
Mumy tai murmushi Tana, "ALHAJI ai jiya ninaga abun mamaki FARINCIKIN da Ban taba gani fuskar FADILA ba jiya na gani, tun daga Nan na fahimci cewa anyi dace."
Kunyace ta kamata batare da tace komai ba ta rufe fuska Tana dariya ta nufi dakinta da gudu.
Dadyne ya kalla Mumy,. "Tabbas nafi kowa farincikin wannan tunda har Fadila ta amince,burina kenan Kuma Ina sa ran ya cika kenan."
Mumy ta ce, "Hum ALHAJI kenan ai inaga duk farincinka ba Kai Ni ba,yanzu dai zamu Fara hidimar biki tun yanzu."
Dady ya yi dariya, "Bari kawai Yar Minister za ta Auri Dan SARKI ko in ce sarkin ma gabadaya,Bari ma in Kira Mai martaba ba in Mai albishir,na San karkari bikinnan ba zai zarce wata uku ba,In ma ya Kai kenan."
Nan take Dady ya Kira Mai martaba ya sheda Masa halin da ake ciki.
Aikuwa Mai martaba ya ji Dadi sosai Nan da Nan shima yasa afara shirin shagalin biki.
Kamar an tsikari FU'AD fitowarshi daga daki kenan ya yi waje neman drive ya fita da shi.
Layin da ya ga FARIDA ya ce suje,Aiko tun ahanya yake leke leke ko zai hangota Amman bai ganta ba, har suka Isa bakin chemis din Amman akulle,sunfi Awa daya ba FARIDA ba labarinta, wani irin zafi FU'AD ya Fara ji azuciyarsa ba yadda ya iya Mai martaba ya na nemansa haka suka bar wajen Amman Sam ran shi ba Dadi,Kan su bar wajen wata ta karda ya aje Mata jikin kofar shagon yadda Tana budewa zata gani.
Juyawan su FU'AD kenan kuwa sai ga FARIDA ta Sauka anafe.
Tana zuwa kofar chemis din kamar kullum addu'o'i ta Fara Kan ta bude,ganin ta kardar da Tai ne yasa gabanta saurin faduwa, "Subhannallah "abun da ta iya Fadi kenan.
Ba tare da ta taba takardar ba ta shige shagon, ta rasa dalili Amman tsoron ta takardar take ji har cikin ranta, Tana shago Amman hankalinta na kai,kamar an tsikareta ta fito cikin hanzari ta daga, haka taga an rubuta *_KI NA BIRGENI_* tsintar Kanta da sakin wani Hamshakin murmushi da Bata San dalilinsa ba tayi,koma tayi shago tare da sa takaddar ajakarta.
YAREEMA na komawa gida aka sanar da shi cewa Mai martaba na jiranshi Aiko cikin Fada ya Wuce take.
Yana zuwa Mai martaba ya Fara shi Masa albarka, "Tabbas ka ciki Magina FU'AD,Allah ya yi maka albarka, ALHAJI ya kirani ya sanar Dani komai,kun daidaita da Fadila to ma Sha Allah, Alhamdu Lillah Daman wanna shi ne burinmu,Tabbas kun cika 'ya'yan halak Ina matukar alfahari da Kai FU'AD, yanzu Shirin shagalin biki kawai za afara."
Tun da Mai martaba ya Fara maganarnan ban da zufa ba abun da ke ketowa daga jikin FU'AD, takaici yake ji har cikin ranshi ace Wai Fadila ta amince da shi.
Ba yadda ya iya haka ya bar Fada cikin sake-sake, fitowar Shi keda wuya ya tarar da Hajiya Karama, munafukin murmushi ta Mai tare da fadin, "Ah FU'AD ango fatan dai Amaryar tayi ma? In Bata ma ba karka damu sai Dan uwanka ya Aureta kawai."
Kasancewar FU'AD ba Mai son magana bane, murmushi kawai ya yi Mata sannan ya Wuce dakinsa.
Kwance yake Kan gadonsa Yana Danna waya,katsam sai ga Kira ya shigo Masa da sabuwar number,kamar ba zai daga ba, ya daga tare da karawa akunne batare da yace komai ba, adayan bangaren Kuma Fadila ce ke fadin, "Assalamualaikum."
Amsawa ya yi da"Wa'alaiki Salam."
Murmushi tayi tare da fadin, "YAREEMA FU'AD, na San ba ka San da wa ka ke magana ba ko?"
Ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba.
Ta Kara da, "To Amaryar ka ce Fadila,fatan kana Lafiya?"
Wani irin murmushin takaici ya yi tare da fadin, "Lafiya Lau."
Zata Kara magana ya yi saurin katseta, "Sai Anjima."
Tsayawa Tai Tana kallon wayar cike da mamakin Kanta, ita da ke kashewa SAMARI waya yau ita ake kashewa? Kwanci tayi ta Fara kuka kawai.
FU'AD kuwa FARIDA kawai yake hangowa har cikin Ransa yau ya kudiri niyar fita ko da daddarene zai saci hanya ya fita,ji yake ba zai iya wata walwalaba batare da ya ga FARIDA ba.
Dare Misalin karfe 8 har yanzu FARIDA Bata samu damar ta shi a shago ba, kasancewar Yau Oga Hamisu na Nan Kuma masu siyan magani sun Mata yawa.
Shi ko FU'AD Ado drive ya Kira ya lallabashi tare da fadin, "Ina son siyan wani magani ka Kai Ni chemist din Tudun wada Mana."
Ado ya ce, "Yallabai Mai zai Hana ka rubutamun in siyoma ko Kuma muje chemist da ke bakin Titin unguwar Nan Mana."
FU'AD ya ce, "Babu anan Kuma Ni nafiso inje da kaina."
Ado ya ce, "Amman Mai martaba ya Hana fitarka batare da kwakkwaran dalili ba."
FU'AD ya dakatar da ado, da kyar Yasamu hanyar shawo Kan Ado suka nufi chemis din.
Sunci sa'a kuwa ba su tashi ba Amman ba mutane sosai.
FU'AD ne ya fito da Kan shi ya nufi chemist din Yana shiga.....
Mah group members ku ta rashin sharhi nikuma zanta fiddaku
New members in kinsan bakwa sharhi Dan Allah karku shiga👏 ***
URS Xayyeesherthul-humaerath
*ASHE HAKA SO YAKE!!*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
***
_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_
_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*
_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_
*TUKWICI*
_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_