ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-5

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*ASHE HAKA SO YAKE FANS GROUP WORDS CAN'T EXPRESS HOW APPY AM I WITH UR LVLY COMMENTS😍😍IYA WUYA INA YINKU IRIN TOTALLYN NAN💞💞*_

Ya ce, "Assalamualaikum Alaikum."

Alokacin FARIDA ta dago tare da fadin, "Wassalam Alaikum,Yallabai me za abaka?"

Rasa bakin magana ya yi ya Tsaya kallonta kawai.

Gajiya Tai da shirun ta ce, "Yallabai me za abaka dare na yi Ina son tafiya gida."

Oga Hamisu ya dago ya kallesu Yana, "Oh FARIDA ta shi kije dare Kam ya yi nakarasa sallamarsu."

Cikin Sauri FU'AD ya ce, " Maganin ciwon Kai za abani."

FARIDA ta Mika Masa ya miko mata wata dagajajjiyar naira dari da ya karba wajen Ado drive.

Duba Masa chanji Tai ta bashi sannan ta yiwa Oga Hamisu sallama,kusan atare suka fita, shi dai idon FU'AD na Kan FARIDA ya kasa daukewa,ji yake har cikin ranshi ko Mai Tai birgesa take.

Komawa motar yaiy da sauri tare da fadawa ado cewa yabi napep din da FARIDA ta shiga har su ga inda za ta.

Haka kuwa suka dunga lulukawa cikin wata anguwa da Kai kace karkace,gidajen wajen abun tausayine bare Kuma mutanen ciki.

FARIDA ko da Bata ma San anayi ba hankalinta kwance ta Sauka a napep tare da biyin Mai napep din ta shige gida.

Kallon gidan ya yi cike da mamaki, Nan da Nan ya ji tausayin FARIDA ya kamashi sosai,Ashe Daman anan take rayuwa? Lallai akwai talakawa aduniya, duk da kasancewar Tana rayuwa a kaskantaccen waje Amman ba za ka Taba fahimtaba,domin fuskarta akullum fal tare da walwala cike da Farinciki.

FU'AD ya kalli Ado tare da fadin, "Mallam Ado ataimakamun da bayani game da yarinyar da ta shiga gidancen Ina son bayanai game da ita.

Nan take kuwa Malam ado ya ce, "An Gama Yallabai, ka koma mota in Sha Allah cikin minti biyar zan samoma duk abun da ka ke da bukata.'

FU'AD ya koma mota yanata sak'e-sak'e kala-kala aranshi "indai hakane wasu takalakawan sun fi masu kudi rayuwa cikin farinciki da walwala,har ranshi ji yake da zai samu wannan damar da shi ya rayu kamar kowa ya yi abokai kamar kowa, shima anga walwala afuskarshi kamar kowa Amman ta Ina? Ko in ce tayaya!?

Ado ba inda ya nufa sai wajen wani Mai shayi dake gefen gidansu FARIDA, ya samu abun da yake so kuwa yadda yadda kamata, hakan ya sa shi dawowa cikin kankanin lokaci.

Kan ya Gama Zama FU'AD ya ce, "Ya dai fatan ka samomin komai yadda ya dace."

Ado ya ce, "Eh to kusan hakan ne yallabai, Sunanta FARIDA, Allah ya yi ma Mahaifinsu rasuwa, itace yarsa ta fari sannan kanwarta, tayi karatun secondry ta kammala, yanzu abinci mahaifiyarsu ke saidawa acikin gida, ita Kuma Tana aikin Saida magani awani chemist, acewarshi dai Yarinyar Tana da matukar hankali da nutsuwa,ga tausayi, kyauta tare da sadaka, ko kadan abun duniya bai rufe Mata ido ba, duk da kasancewar Attajirai da 'Ya'yan masu kudi na binta Amman ko kadan basa gabanta Kuma Bata taba bi ta kansu kasancewar kyakkyawa baya gabanta mutuncinta da darajarta na 'ya mace yafi Mata komai kamar yadda Mahaifinsu ke yawan Fada masu akullum cikin nisiharsa.

FU'AD ya ce, "Ma Sha Allah."

Ado ya katse shi da fadin, "Yallabai akwai matsala guda fa, ba Wanda Yarinyar ta tsana aduniya fiye da masu arziki, gabadaya kallon kudin goro take yi masu Kan cewa basa da adalci tare da tausayin talakawa,mussaman su da sanadin Rashin taimakon masu kudi ne yasa Rashin Mahaifinsu duk da kasancewar ba Wanda zai Kara kwana aduniya in kwananshi ya kare Amman da sanadin wulakantasu da akayi."

FU'AD ya yi shiru Chan Kuma ya ce, "Wannan ba wata matsala ba ce in Sha Allah."

Ado ya Kara da , "Labari Mai Dadi Ranka yadade, Bata da Wanda take da burin gani arayuwarta fiye da YAREEMA FU'AD, tun da taji labarina kana son talakawa Kuma kana taimakonsu ka ke birgeta."

Wani Hamshakin Murmushi FU'AD ya yi tare da fadin, "Bakomai yanzu mu koma Fada kada Mai martaba yanemeni."

Nan take kuwa suka juya gida.

Was she gari

*****Hajiya Karama ce zaune da Fahad adaki.

Duban shi Tai ta ce, "Ni fa Fahad wani lokacin kana bani mamaki kana Abu kamar bani na haifeka ba, Tabbas Ina so ka bi ta wata hanyar kasan inda zaka bi FADILA Ta soka koma ta yayane, Ina da tabbacin Alhaji ba zai Mata dole ba,Dan haka Ina so kayi Abu kamar namiji in ma kyanne kana da shi, Ban ga ta inda FU'AD ya bika ba,ta wani bangaren ma nasan zaka fi birgeta,tunda shi wancen meyasani? Magana ma ba saba yi yayi sose ba,bare ya San kalaman da zai yi ma budurwa,Inaga hanyar da zai bi Dan shawo hankalinta."

Fahad ya kyalkyale da dariya, "Woo woo Hajiyata Wallahi kwanyarki na ja, Kuma fa hakane wancen ai kawai sunan MUTANE yake amsawa domin muna mutum ne ba mutum ba, Koda Yana sonta ma ba iya Fada zai ba,hankali kwance zan sace zuciyarta,Inna so ma ayau dinnan."

Hajiya Karama ta tashi Tana zagaya dakin, "Yawwa in kamun Wannan sauran aikin ka barsu wajena,Amman Kan ka tafi ga turarenan ka fesa ajikin ka,ka tabbatar ta shek'a ko yane, daga Nan an Gama batun."

Fahad ya Kara shekewa da dariya, "An Gama Sarauniyar Hajiyata yanzu bara ma kiga zan tsara yadda za ayi mu hadu yau."

Fita ya yi cikin Sauri yasa akayi Masa binciken inda yau Fadila za ta kasance a weekend,Daman ta Kan fita wajen shakatawa da kawayenta duk sati.

Ba Bata lokaci kuwa ya samu bayanan komai,Nan take ya Fara Shirin haduwarsa da Fadila ,

Kwalliya ta Chaba, cikin Abayarta pitch kala,Mai adon Baki,tare da stons golden, takalminta Baki jakartama haka,ba karamun kyau Fadila Tai ba,tsayawa Tai amadubi Tana kallon Kanta, "Yanzu Dan Allah me ya rageni da har FU'AD ba zai nunamin so ba? Atunanina na cika cikakkiyar macen da kowa zai yi burin aure."

(Ni ko nace Mahaifinki dai nada arzikin da kowa zai yi burin aurenki.)

Ta cigaba da magana, "Ko ta Ina,ko tayaya Wallahi,na rantse da Allah FU'AD sai kasoni,ba yan taba zubda kwallana abanza ba."

Tana cikin maganganun Nan wasu yam Mata biyu suka shigo Suma din dai abayarce ajikinsu,.daya tasa Blue dayar Kuma purple, Rumaisa ce ta Fara magana wadda ake Kira da Rumy, "Haba FADILA munata jiranki fa."

Fadila ta juyo tare da fadin,"na Gama muje."

Mery ta ce, "Anya kuwa Lafiya? Tun shekaran jiya fa Ina lura da yanayin gimbiyar ya sauya."

Fadila Tai shiru kawai suka fita.

Sai da Suka shiga mota Kan Fadila ta ce, "Rumy,Mery, Wallahi Ina son YAREEMA FU'AD, ASHE HAKA SO YAKE? gabadaya tun da na gan shi na kasa sukuni zuciyata ban da Labarinsa ba abun da take kawomun."

Rumy Tai dariya, "To miye abun damuwa anan,abun da Daman ya kasance mallakinki Dan kin so shi ai ba matsala bace."

FADILA ta ce, "Amman shi Ban ga alamun Sona atattare da shi ba ko kadan."

Merry ta ce,"Wannance damuwarki? An Gama Gimbiyar mu kamar FU'AD ya so ki fiye da yadda kikeson shi ma in Sha Allah."

Da wannan batun suka karasa wajen,ban da murmushi ba abun da ke bayyana afuskar Fadila Wanda ni dai banji me suka Fada mata ba da har yasanyata farin cikinnsn.

Fahad kuwa na ganin isowarsu ya Kara bunka turaren da hajiyarsa ta ba shi.

Cikeda kasaita ya fito amotar tare da numfar inda su Fadila suke.

Kamshin turarensa ne ya Fara dukan hancin Fadila da yayi saurin sata dagowa ta kalleshi......

_YADDA ZAKI BIYA ASAMBADAKI A PAYMENT GROUP 300NE KACAL ACCOUNT NUMBER 1453215759 Acess Bank Aisha Abdullahi Sani,YAN NIGER KUMA 400fcfa KUMIN MAGANA ZAN BAKU TA INDA ZAKU BIYA,,,,MA SU TURO DA KATI TARE DA SHEDAR BIYA KUMA TANAN ***,WA INDA BASA SON SHIGA GROUP KUMA SAI DAI ATURA MASU TA PRIVATE 500 NE SHIMA TA ACCOUNT DIN DA KE SAMA_

MATAR POLICE 200 JAMEEL 200 ASHE HAKA SO YAKE 300

DUK MAI SON DUKA UKUNNAN ZAN BAR MATA A 600 MAIMAKON 800

URS XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

*ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_