ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*ALLAH YA BAKI LAFIYA MATAR SOJA👏ALLAH SA HAKANNE MAFI ALKAIRI ,ALLAH BAKI IKON CIN JARABAWAR KI*_

_*ASHE HAKA SO YAKE FANS GROUP INA YINKU OLL😍*_

Wani hamshakin tsaki ta sake, tare da fadin, "Dalla wai Miye haka,wannan wani irin turarene Mai Wari?" Takarasa fada tana toshe hanci tare da saurin tashi.

Tsayawa Fahad ya yi cike da takaici,kokarin daga Hannu ya yi domin marinta, nan da Nan ta rike Masa Hannu tare da Danna masa Marin Kan ya Kai Mata, suman tsaye ya yi, Yana Mai mamaki cike da takaicin shi Wai Yau mace ke Mari,maganar turare Kuma tabbas turarenshi baya Wari illa kamshi, shin wannan wace irin yarinyace?"

Sake Masa Hannu tai tare da kallonshi sama da kasa cikin yanayin wulakanci ta Kara sake wani Hamshakin taking Kan ta dubu kawayen nata.

Batare da ta ce masu komai ba ta Fara tafiyarta, kasancewar sun San halinta yasa ko tanka Mata Basu yi ba,binta abaya kawai suka yi kamar jeloli.

Fahad kuwa har Yanzu mamaki ne fal cikin Ransa, ji yake tamkar yaje yasa adaka Masa ita. "Shin Wai ta ma San ni waye kuwa? Tabbas ga dukkan alamu Bata sanni ba, ko da yake wannan Yarinyar ga yanayinta koma waye zata iya yi Mai fitsara, Amman ba shakka sai na koya mata darasi." Abun da yake ta laburtawa kenan aranshi, kasancewar daga shi sai drive suka fito batare da masu tsaro ba.

Fadila kuwa tuni ta shige mota Tana hababin masifa , "Ni nafara gajiya da wannan rayuwar,Haba ace ba dama mutum ya fita sai Maza su Fara binsa."

Rumy ta ce, "Tsaya Gimbiyar mu ince Baki San shi wancen din wanene ba ko?"

Cikin fushi ta ce, "Waye shi kuwa ban da banza?"

Rumy ta yi Murmushi, "To wannan Sunanshi Fahad Kanin Mijinki YAREEMA FU'AD."

Gaban FADILA ne ya yi saurin faduwa ta na, "Dan Allah Rumy kin san bana son wasa shine baku fadamun tun alokacin ba?"

Rumy ta ce, "Taya zamu sanar dake bacin Baki bamu Damar hakan ba? Kuma Ni azatonama YAREEMA FU'AD ne ya Aiko shi gunki."

Cikin Sauri FADILA ta bude kofar mota, fara zura ido Tai ko zata ga Fahad Amman ba shi babu Labarinsa,ga dukkan alamu ya bar wajen.

Dafa Kanta Tai cike da takaici Tana Allah wadai da irin halinta.

Gabadaya jikin FADILA ya yi Sanyi garin wulakanci ta Yau ta wulakanta Wanda zai damenta.

Banda sak'e-sak'e ba abun da take acikin ranta.

****Fahad kuwa tuni ya shige mota

Zuciyarsa ban da zafi da kunar abun da Fadila ta Mai ba abun da yake ji,kwatsam kamar ance ya kalli gefensa Kamar ankara zubararsa ya Kara juyawa da kyau kallonta kawai yake ba kakkautawa gabadaya ta Gama tafiya da shi, FARIDA ce ke tafiya gefen titi Tana kokarin zuwa Chemist, azuciyarsa yake fadin, "Alhamdu Lillah Wallahi irin wannan na ke so nikam me zanyi ma da waccer bakar kodaddiya." Kan ya ankara farida ta zo Tsallaka titi,wani Mai Nafe ya Sha gabanta, Kan Fahad ya waiga ba FARIDA ba labarinta , wani irin tsakin takaici ya sake, azahiri yake fadin, "Koma wacece ko Yar wanene,ko a Ina take tabbas sai wannan ta Zama mallakina."

Da haka suka karasa Gida Abu Yama Fahad biyu ga na Fadila ga farida.

Ya na komawa gida cikin zafin Rai yake sanar da Hajiya karama abun da Fadila ta Mai.

"Hajiya Ni Wallahi ba zan juri wannan wulakancin ba tabbas sai na dau mataki,ba ki ga Yarinyar ba fa,Ni Sam ma batai kalar tsarin macen da nake son Aura ba,Wallahi bana sonta Kuma tabbas sai na dau mataki Kanta."

Da Sauri Hajiya karama ta dakatar da Fahad, "Haba!! Haba Fahad karka Maidomun aiki da muradina baya Mana,miye Dan ta wulakanta ka ta marekan? Damuwar dayace kawai ta soka, in ta soka duk wannan ba matsala bane,tabbas ni da kaina nama wannan alkawarin FADILA ta shigo gidanmu sai mun wulakanta ta mun tozartata fiye da yadda kake tsammani,Amman kafin Nan fa,ta shigo gidannan mu cika burinmu."

Fahad ya ce, "Haba Hajiya wani irin burine wannan da har sai an wulakanta Ni?"

Matsowa Tai tare da janyo 'Dan nata jikinta Tana, "Fahad Dan Allah kabani hadin Kai,wannan duk abun da kake Dan Kai nake,domin kasamu rayuwa Mai inganci, Ina matukar bukatar hadin kanka, tabbas in wannan burin nawa ya cika sai kafi kowa Jin Dadi,Ban damu da farincikina ba ma, bare na wasu, farincikinka da walwalarka shine Kan gaba fiye da na kowa, Koda kaf duniya zasu zubda kwalla indai Kai zan ga murmushi afuskarka tabbas burina ya Gama ciki, Fahad! Ka Sani zan iya komai Akan ka."

Fahad ya yi murmushi, "Ni nasani Hajiyata,Kuma ba zan baki kunya ba in Sha Allah,duk yadda za ayi sai FADILA ta soni ko ma ta wace hanyace tabbas."

"Yawwa yaron kirki na San zaka iya abun da ya fi hakan ma."cewar Hajiya karama.

Haka suka ci gaba da hirar tare Tunanin yadda zasu ci gaba da bullowa lamuran

****FU'AD zaune Gaban Hajiya Babba

"FU'AD Ina matukar Alfahari da samun 'Da kamarka arayuwa,Ina fatan rayuwarka ta dauwama a haka har karshen numfashinka, banace kana son Fadila ba Kuma banace baka so ba, Amman tabbas biyayya ga iyaye nada matukar mahimmanci, ka ci gaba kada ka fasa."

FU'AD ya yi murmushi tare da fadin, "In Sha Allah Hajiyata."

Albarka Sosai Hajiya babba ta Sa ma 'Dan nata tare da yi ma shi nasiha.

FU'AD nata neman hanyar fita Amman ba dama Mai martaba ya kafa ya tsare, Wata dabarace ta zo mi shi ya dau takarda tare da Kara yin rubutu kamar na ranar "KI NA BIRGENI." ya bawa Ado drive yaje ya ajiye jikin kofar chemis din.

Duk da bai fita Ganin farida ba Amman sakon takardar Nan yasa shi Farinciki.

Haka kuwa akayi FARIDA na zuwa ta tarar da takardar kamar ranar dai murmushi ne kawai ya bayyana afuskarta,kamshin turaren da ke jikin takardar ta shek'a tare da numfasawa Kan ta sata cikin jakarta.

****

FU'AD na kwance yanata Tunanin yadda zai bullowa lamuransa, na farko dai Bai son bacin Ransa,na biyu Yana son FARIDA sannan na uku baya Fadila ya ya zai yi?

Kiran da akace Mai martaba na ma shi ne ya tsayar da shi Kan wannan nazarin da bai San mafitaba.

Yana zuwa Mai martaba ya sanar da shi cewa akwai bukatar yaje yaga Fadila yau.

Cikin Ransa Sam Bai ji Dadi ba Amman azahiri murmushi ya Yi.

Ado drive ne ya daukeshi suka nufi gidansu Fadila.

Dadynta na sanar da ita FU'AD na hanya,Nan da Nan ta fara shiri tsabar xumudi Zama Tai afalon Tana jiran isowar abincin ruhinta.

Yana shiga......

_YADDA ZAKI BIYA ASAMBADAKI A PAYMENT GROUP 300NE KACAL ACCOUNT NUMBER 1453215759 Acess Bank Aisha Abdullahi Sani,YAN NIGER KUMA 400fcfa ZAKU BIYA TANAN,MA SU TURO DA KATI TARE DA SHEDAR BIYA KUMA TANAN ***,WA INDA BASA SON SHIGA GROUP KUMA SAI DAI ATURA MASU TA PRIVATE 500 NE SHIMA TA ACCOUNT DIN DA KE SAMA_

MATAR POLICE 200 JAMEEL 200 ASHE HAKA SO YAKE 300

DUK MAI SON DUKA UKUNNAN ZAN BAR MATA A 600 MAIMAKON 800

URS XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

[7/15, 10:45 AM] Aminiya: *ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_