FREE PAGE-7
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*NA MANTA BAN SA PAGE BA NA SHEKARAN JIYA TO PAGE 6 NE WANNAN KUMA 7*
*MAH GROUP MEMBERS ACIGABA DA SAMBADA SHARHI HILIS😍I HEART U OLL*
Wani takaicine ya sarkafe FU'AD azuciya,kallo daya ya yi mata sannan ya yi gaggawar kau da Kai, acikin zuciyarshi kuwa wani gajeran tsaki ya sake.
Can gefe ya zauna, Da Murmushin ta, ta taso tare da nufowa gare shi.
Zama Tai daf da shi, ya yi saurin matsawa tare da Kara kawar da Kan shi.
Murmushi ta sake tana"Honey, ba ka son kallona ma? Laifin me nayi haka ne Wai? Zan iya juran komai Amman ban da rashin kulawarka gareni ko yayane ya kasance Ina samun kulawa daga gare ka please!."
Shiru FU'AD ya yi ba tare da ya ce komai ba.
Kara matsowa tayi daf da shi jikinsu na gogan juna, karaf ta rike hannun shi Tana fadin, "I Love you FU'AD, I really really Love you, Dan Allah ka yarda Dani can't live without FU'AD please,ka da ce ba ka Sona ko da wasane please ka min wannan alfarmar,ko me ka ke so ,zan yi wallahi,what ever in dai hakan zai Faran ta ma Kuma za ka Soni."
Gabadaya Ta Gama sakarwa FU'AD jiki da irin rikon da Tai mai, kokarin jenye jikin shi daga kusa da ita ya yi, sannan ya yi saurin fisge hanun shi daga nata.
Kallon ta ya yi cike da takaici ya yi tsaki Kan ya ce, "Ba ta yadda za ayi na so Mace kamar ki, ba wai kamar kin ba Mai irin halinki ma, Sam wannan ba dabi'a ba ce Mai kyau, ki nuna karara za ki iya sadaukarmun da komai na ki Dan kawai in so ki? Ko da wannan ba dabi'ar ki ba ce, to tabbas aguna dabi'ar ki ce, Kuma ba yau ba, ba gobe a haka zanna kallon ki tun da kin nuna ba ki damu da mutuncinki da kimar ki ba na 'ya mace."
Ya Kara kallon ta sannan ya sake tsaki cikin fushi ya fice a dakin.
Yana futa FADILA ta fada kasa, kuka ta Fara bilhakki da Gaskiya, ta na matukar son FU'AD fiye da tsammanin ta, domin kuwa a zahirin Gaskiya ita ba mutuniyar Banza ba ce, hasalima ba namijin da ya Taba rike hannun ta, Amman yau kaddara da son FU'AD yasa ta nemi zubda kimar ta na 'ya mace, tabbas littafin Xayyeesherthul-humaerath na BABU RUWAN SO ya fadi Gaskiya,bar FADILA da wulakanta Maza tare da nuna cewa tafi karfin su ne ya Fara bin ta ko Yaya?
Momy da ke sama Sai da ta jiyo sautin Kukan FADILA a firgice ta fito.
Da Sauri ta daga ta Tana fadin, "Lafiya? FADILA Mai ya faru? Lafiya ki ke kuka?"
Cikin shashshekar kuka take fadin, "Momy Ina Son FU'AD wallahi Ina son shi can't do without him Momy." Ta Kara fashewa da kuka.
Momy ta Rumgumeta Tana share ma ta hawaye , "Haba FADILA na ga dai FU'AD dinnan an Gama komai shin Wai shi ya ce baya son ki ne?"
FADILA ta ce, "Eh Momy kuma ya ce ba zai Taba Sona ba."
Momy ta yi murmushi , "Amman ai Mahaifinsa ya nema mi shi Auren sa ko? Kuma tabbas kin San Mai martaba baya Magana biyu, Dan haka kabar ma wannan damuwar tun yanzu maganar FU'AD ya so ki kuma kamar anyi an Gama in dai na cika Mahaifiyar ki Kuma Ina Raye aduniya, Maza ta shi ki share hawayen ki Fadilan Dady."
FADILA tayi saurin ta shi, ta ce, "Momy da gaske FU'AD zai so ni kamar yadda na ke son shi?"
Momy ta Kara sakar Mata da murmushi, "Na mi ki wannan alkawarin FADILA in dai Ina numfashi tabbas Sai FU'AD ya so ki fiye da yadda ki ke son shi ma."
Fadila ta rungume Mahaifiyar ta ta, Tana share hawaye, "Thank you Momy, I love you Momy."
***********
FU'AD kuwa Yana komawa gida dakinsa ya nufa domin zuciyarsa ban da radadi ba abun da ta ke yi Mai.
A Daren yau ya kudiri Niyar Zuwa ganin FARIDA Amman ta Yaya?
Satan hanya ya Kuma yi tare da Ado driver suka fita.
Suna fita FU'AD ya ce, Malam Ado ga Wata alfarma ma ka karamun Dan Allah,kayan ka na ke so ka bani insa inda hali mu Fara biyawa ta gidan ka."
Ado ya wage Baki, "Subhanallah Ranka yadade kayana Kuma? Ta ya ma za ka iya sa kayana ka mun Rai ya shugabana."
FU'AD ya yi Murmushi , "Ehen Kayanka na ke son sawa,kar ka manta Kai da Kan ka, ka kawo mun labarin FARIDA ba ta son masu kudi, Dan haka Ina so na kasance cikin talauci na Yan wasu lokuta na farko zan dandana dacin da talaka ke ji wajen rayuwa, na biyu Kuma zan tarbi Soyayyata ta hanya mafi sauki."
Ado ya ce, "Ranka yadade Amman Kuma ai Kai Tana yin ka,Ina da tabbacin ba za ta Taba gudun ka ba."
YAREEMA FU'AD ya yi murmushi , "Ado abubuwan da yawa hakan ma Jarabawace zan yi gareta da Kuma gareni ni Kai na,damuwata kawai ka bani hadin Kai."
Ado ya numfasa, "To Ranka yadade,Amman Allah raba mu da shiga tarkon Mai martaba."
Murmushi kawai FU'AD ya yi suka kama hanya.
Gidan Ado suka nufa ko ince shagon ado wani Dan karamin shago da yake Haye awata agunwar talakawa.
Kayan ya karba yasa, YAREEMA ya badda kama tamkar wani almajiri. Sannan suka kama hanya
Sai da su ka Fara biyawa ta chemist , Oga Hamisu suka tarar ga dukkan alamu FARIDA ta ta fi gida.
Hakan yasa su shawarar bin ta gida.
Suna Isa ta bayan layin ado ya yi parking, sannan YAREEMA ya ce, "Yawwa Malam Ado bani aron wayarka."
Mika Masa ya Yi, YAREEMA ya Tsaya kallon wayar abar tausayi,baby Nokia ce ba karamin jiki ta ji ba,domin da kyar ta ke dannuwa.
Kofar gidansu FARIDA ya je ya Tsaya tare da tura yaro ya kirawota.
Zaune take Tana karatun Al-qur'ani, aka Yi sallama, Farisa ta amsa.
Yaron ya ce, "Wai FARIDA ta zo inji wani awaje."
Da Sauri FARIDA ta ce, "Farisa Dan Allah kice bana nan, bana son damuwa wallahi."
Mama ta ce, "Aa Bai kamata Farisa jeki ga waye tukunna."
Farisa ta fita, Sallama tayi tare da gaishe da FU'AD, "Kai ne ka ke neman Anty FARIDA?"
FU'AD ya ce, "Eh ko ba ta Nan ne?"
Farisa ta ce, "Aa ance inzo in dubane ta na zuwa."
Ba tare da ta jira Mai zai ce ba ta shige gida.
"Anty FARIDA ba irin wa'inda suka Saba zuwa bane,wannan Kam ma fa kamar almajiri Yasin." Cewar Farisa Tana dariya.
Mama ta ce, "Ya Miki kyau da dariya,ke Kuma tashi kije."
Ba musu FARIDA ta tashi ta sa hijabinta har kasa ta fita.
Tana fita.......
_YADDA ZAKI BIYA ASAMBADAKI A PAYMENT GROUP 300NE KACAL ACCOUNT NUMBER 1453215759 Acess Bank Aisha Abdullahi Sani,YAN NIGER KUMA 400fcfa ZAKU BIYA TANAN,MA SU TURO DA KATI TARE DA SHEDAR BIYA KUMA TANAN ***,WA INDA BASA SON SHIGA GROUP KUMA SAI DAI ATURA MASU TA PRIVATE 500 NE SHIMA TA ACCOUNT DIN DA KE SAMA_
MATAR POLICE 200 JAMEEL 200 ASHE HAKA SO YAKE 300
DUK MAI SON DUKA UKUNNAN ZAN BAR MATA A 600 MAIMAKON 800
URS XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH [7/15, 10:45 AM] Aminiya: *ASHE HAKA SO YAKE!!*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
***
_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_
_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*
_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_
*TUKWICI*
_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_