ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-9

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

Da shigansa ganin yanayin Mai Martaba da hajiya Babba ka dai ya fahimtar da shi cewa akwai wani abu,domin gabadaya fuskar su ba annuri ko kadan, Hajiya karama kuwa da Fahad tamkar suna ruwan murmushi awajen.

Sallama ya yi, suka amsa Kan ya nemi gefe ya zauna kansa kasa.

Mai Martaba ya yi gyaran Murya tare da fadin, "FU'AD Me yake Kai ka fita cikin dare? Sannan me ka ke aikatawa cikin anguwar talakawa? Tsaya ma ba Kai ka dai ya kamata inyiwa wannan tambayar ba,A kirawomun Ado Driver,."

Dasauri Fahad ya ta shi Kiran Ado driver, "To Karamun Munafuki kazo Mai Martaba na kiranka tunda har da Kai ake hada kulalliya Wuce muje."

Gaban Ado ne ya yi mummunan faduwa haka Fahad ya tasa shi agaba har Falon Mai Martaba.

Suna zuwa Ado ya durkusa gaban Mai Martaba tare da Mika gaisuwa.

Ko Amsawa Bai ba , ya Kara maimaita Tambayar da ya yi wa FU'AD.

"Shin Me kuke zuwa yi cikin dare Kuma anguwar talakawa?"

FU'AD har cikin Ransa Ya shirya fadin Gaskiya ga Mai Martaba in dai zai ba shi damar magana.

Ado ya dago ya kalli FU'AD Kan ya Kara kallon Mai Martaba, FU'AD dai murmushi ya sake ma sa alamar ya sake ya yi bayani.

Mai Martaba ya Kara da, "Ado Wai ba tambayarka na ke bane?"cikin tsawa

Da Sauri Ado ya Fara fadin, "Mai Martaba Daman,Daman YAREEMA ne,yake zuwa gun wa.....

Sai ya yi shiru.

Mai Martaba ya ce, "gun wa? Ado kada ka bari Raina ya karasa dagulewa tabbas na San ka fi kowa sanin halina."

Zuface ta Fara keto wa Ado,Amman ya,ya iya ya Zama dole ya ba Mai Martaba amsa, ya cigaba da magana, " Talakawa muke kaiwa taimako."

Ko kadan FU'AD Bai ji dadin karyar da Ado ya yi, ji yake har aransa ba Dadi, domin ya tafka kuskure biyu kenan, na farko yiwa masoyiyarsa karya na biyu Kuma Ado ya yi ma, mahaifinsa,ko ince danginsa ma gabadaya karya.

Mai Martaba ya ce, "Naji na San YAREEMA zai iya abun da ya fi hakan ma,Amman tabbas ado kasa aranka duk sanda naji Cewa zancen da ka fadamun ya canja tabbas kashin ka ya bushe, Kuma daga yau na Kara tsaro agidannan FU'AD ba zai Kara fita ba Sai da kwakkwaran dalili,ko da Ni zai fita,ko Kuma zai je wajen Fadila, zan sa asanya min ido akan sa Sosai, duk sanda naji Cewa ya fita batare da izinina ko daliliba tabbas akwai matsala, sannan maganar talakawan da ake taimako,Ni zan ci gaba da bada komai da Kai na, ado Kai zaka ci gaba da raba masu, ba bukatar YAREEMA ya Kara zuwa wata unguwar talakawa ba ma wannan kadai ba,Ina fatan kunji,Kuma duk Wanda aka hadu da shi aka karya mun doka tabbas kun fi kowa sanin Ni waye."

Ado ya amsa da, "in Sha Allah Mai Martaba,angama."

Mai Martaba ya Mai alamar zai iya tafiya, Yana fita kuwa hajiya karama ta ce, "Ranka yadade sai nake ga kamar tsaurin ya yi yawa,da zai fi dai in aka ba shi Damar fita ko Ina Amman ban da ta talakawan, Hana shi fita da Kara tsaro akan sa kamar ba mafita ba....

Ba ta karasa maganar ba Mai Martaba ya Mata wani mummunan kallo Nan da Nan Tai shiru.

Ya ce, "Shin ke Zaki bani umarnin abun da zan yi wa gidana ko Aa? Kin Taba ganin nayi magana na sauya? Ki kiyayeni,ki fita sabgar hukuncina ki zauna lafiya."

Ta shi tayi kawai ta fice,haka ma FU'AD ya bita fuuu.

Mai Martaba ya kalli Hajiya Babba, "Madam na yi dai,dai ko?"

Murmushi ta yi tare da fadin, "Tabbas hukuncinka shine dai dai Mai Martaba,Allah ya ba mu ikon kiyayewa."

Da "Ameen" ya amsa Kan ya ce, "Allah ya yi maku albarka,Allah baku masu Muku biyayya kamar yadda kuke mun."

Ta amsa da Ameen itama.

FU'AD kuwa tun da ake maganar Nan har aka Gama kansa na kasa batare da ya kalli kowa ba.

Mai Martaba ya ce, "Ma Sha Allah, FU'AD kana iya tafiya."

Sallama ya yi ma iyayen na shi Kan ya fice.

**** Hajiya karama na zuwa Dakinta ta Fara bambami, "Kai Allah wadan naka ya lalace, wannan wani irin hukuncine,Sam Bai kamata ba Kuma Bai dace ba,nayi Abu Dan ahukunta shi Kuma sai ya Kara samun tsaron da ba hanyar da zamuyi amfani da shi? Wallahi da sake ba zan Taba yarda da wannan lamarinba,Ina da tabbacin cewa da Kai ne ka aikata hakan sai ya yanke mummunan hukunci Akan saboda shine 'Da ko?to Na rantse na Kuma rantsewa sai na ga bayan FU'AD tun da ko ta Ina muka bullo sai sun kauce to an Kai Ni makura, ko ta wani haline,ko da Ni zan rasa Raina Kai ka rayu tabbas Sai FU'AD ya bar duniya."

Fahad ya ce, "Hajiya Ni Kam dai ina Tunanin Ni ba Dan gidannan bane ko? Wariya da launin fatar ya yi yawa."

Hajiya karama ta ce, "Hmm Fahad ko da ace Kai ba Dan gidannan bane,indai nice Mahaifiyarka,dole ka Zama,bare Kuma kowa ya sani,kowa ya sheda Kai Dan gidannan,ganin wancen tsinanen yaron ne yasa kwata-kwata Mai Martaba baya takai Kuma Ni nasan ba komai bane bace asiri,kana ganin hajiya Babba haka ba karamar makirar mace ba ce, Kuma tabbas zan nuna Mata na kerata,shi Dan nata da take tutiya da shi inya bar duniyar za mu ga ya za ta yi, Fahad kar kaji komai kawai ka sa aranka cewa Kai ne magajin MASARAUTAR Nan Kai ne YAREEMAN MASARAUTAR Nan ba bu wani bayan Kai na fada maka Kuma na Kara fada."

Fahad ya yi wata muguwar dariya Kan ya ce, "Aradu za aga iskanci kuwa."

.ita ma dariyar ta yi.

(Kun ji mun uwar banza)

Da haka Fahad ya ma mahaifiyar ta sa sallama Kan ya yi gaba Ransa fes,ya na Mai jin dadin albishir din da Mahaifiyarsa ta Mai.

****FU'AD tun da ya koma daki ya rasa meke yi Masa Dadi gabadaya Hankalinsa ya tashi Sam Bai ace ya yi wa iyayensa karya ba,Amman Bai San me ado ke nufi da kin fadar gaskiyan ba.

Ta wani bangaren Kuma damuwarsa Bai San yadda zai yi,ya cigaba da ganin FARIDA ba,ji yake in ya daina ganin FARIDA tamkar an daina ganin walwalane afuskarsa.

Ban da Tunani ba abun da yake ta yi ,kwatsam ya ji wayarsa na ringing.

Kallo daya ya Mata ya Kara jin wani takaici ya sarkafe Masa zuciya.

Ba kowa bace face Fadila.

A silent ya sa wayar Amman duk da haka Bata daina Kira ba,kusan sau goma.

Ana 11 dinne ya yanke shawarar dagawa tare da Jin miye matsalar ta.

Yana dagawa ta ce, "Hello my darling."

Tsaki ya mata Wanda sai da ya amsa awayar.

Murmushi ta yi tare da fadin, "Na tabbata tsakinka ya kusa komawa kalmar so da kauna gareni, ba zan Taba damuwa da duk abun da za ka mun ba ayanzu domin na San komai ya zo karshe."

FU'AD ya ce, "Ok na ce ko zaki iya barina yanzu?"

Dariya ta yi tare da fadin, "Wooo so Ma Sha Allah Mah Husbee,Wallahi Kullum vioce din ka Kara Zaki yake kamar Sugar, karka damu zan barka ka huta,ai Inka huta kamar Nina huta, So ka kulamun da Kan ka kaji? Kada ka Bari ko kuda ya tabamun darling byeee byee,zan yi kewarka."

Tana Gama Maganar kiss ta yiwa wayar har sai da sautin ya Isa ga kunnan FU'AD.

Ba tare da ya Bari ta Kara wani shirmen ba katse wayar yayi.....

_YADDA ZAKI BIYA ASAMBADAKI A PAYMENT GROUP 300NE KACAL ACCOUNT NUMBER 1453215759 Acess Bank Aisha Abdullahi Sani,YAN NIGER KUMA 400cfc ZAKU BIYA TANAN,TURO DA KATI TARE DA SHEDAR BIYA KUMA TANAN ***,WA INDA BASA SON SHIGA GROUP KUMA 500 NE SHIMA TA ACCOUNT DIN DA KE SAMA_

MATAR POLICE 200 JAMEEL 200 ASHE HAKA SO YAKE 300

DUK MAI SON DUKA UKUNNAN ZAN BAR MATA A 600 MAIMAKON 800

URS XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH [7/15, 10:45 AM] Aminiya: *ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_