ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-11

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

Cike da takaici Fahad na cizan harshe ya bar anguwar ba ta re da son Ransa ba,Ji yake aransa ko da ganinta ya yi zuciyarsa za ta yi Sanyi bare Kuma ace ya biya bukatarsa.

**** FU'AD na kwance ban da Tunanin yadda zai yi ya bar gidannan da dare ba abun da yake yi,Mai Martaba ne yasa akirawosa fada.

Gabansa na faduwa haka yaje tare da rusunawa gaban Mai Martaba.

Numfasawa Mai Martaba ya yi tare da fadin, "To Alhamdu Lillah ansa Ranar aurenku da FADILA GOMA GA WATAN BAKWAI in Sha Allah Dan haka dole afara shirye-shirye gadan gadan domin bikin bana wasa bane,Ina so ayi bikin da ba a taba irinsa ba atarihi da ma MASARAUTAR Nan gabadaya Kuma ba za akara irin sa ba, YAREEMA ka sani cewa Kai ne dayana na fari Wanda na fifita son komai Akan kamai ba Dan komai illa cewa kallonka nake tamkar mahaifina, aduk sanda na kalleka na Kan ji Sanyi araina, kamar yadda Allah jikan Mahaifiyata ke fadamun tamkar mahaifina ka ke ba iyaka sunan ka gada ba tamkar Allah ya daukesane ya kawoka madadinsa, ba kamanin kadai ba,halaiyyar da dabi'unku ba bu bambamci, YAREEMA na maka zabin Mata Kuma nayi Farinciki da amincewar da ka yi duk da Ban San cewa kana sonta ba ko aa Amman tabbas wannan shine biyayya ga iyaye ,Kai za a Kira da sunan 'Da na gari,Ina Fatan har in koma ga Allah ba zan ga Ranar da zaka bakantamun ba domin Ban da burin ganin wannan mummunan Ranar.

Tunda kazo duniya ake kokarin kawar da kai,ba wayonmu ba,Kuma ba dabararmu ba nida mahaifiyar ka Allah ne Mai kareka akullum,da Kuma addu'o'in tare da ibadar da bama wasa dasu akullum, ka cigaba da addua Allahne Mai karewa Kuma zai ci gaba da kareka aduk inda kake YAREEMA,Allah ya ma albarka,yanzu Ina so ka shirya anjima da daddare za ka gidansu Fadila kuje ku Fara lissafin Abubuwan da yakamata asiya na Bukata ko ince shagalullukan da kuka ga za ku yi, ka shirya zaku fita da Ado."

Kan FU'AD akasa ya ce, "Na gode Abba in Sha Allah zan kasance Mai yima biyayya akullum."

Mai Martaba ya yi murmushi tare da fadin, "Bakomai ta shi kaje ,Kan ku tafi zan ba ado sako akaiwa 'Yar tawa."

Murmushi Shima FU'AD ya yi kawai ya fita, aransa Farinciki ya ke yasamu hanyar ganin FARIDA mantawa yake da zancen wata FADILA ma.

Hajiya karama najin motsin fitowar FU'AD ta labe agefe da Sauri, cizan yatsa take Tana fadin , "Kambun cen, lallai ma, yo ai Daman na San kasan abun da nake,Amman ba yadda za ayi Dani,yadda aka ganni haka Kuma dole za abarni,Dan yanzu ma na fara, da banyi komai ba Wallahi domin yanzu ko rayuwar FU'AD ko tawa agidannan dai Kam,da ka ke Maganar biki ma duk kayi na Banza domin bikinnan da Fahad za ayi ba dai shi Dan lelenba,duk kunyi na Banza zaku ga Mai zai faru akarshen." Tsaki Tai sannan ta shige bangarenta.

FU'AD na shiga cikin dakinsa wani irin Farinciki ne ya ziyarci zuciyarsa, ko ba komai sanadin FADILA zai ga Farincikinsa FARIDA.

Tun alokacin ya Kira Ado driver ya sanar da shi, murmushi Ado ya yi , "To Yallabai Amman dai kasan abun da Mai Martaba ya ce,Kuma Ina Jin tsoro Wallahi bama Wai Ni kai na nake ji ba,damuwata Kar yayi fushi da Kai."

FU'AD ya ce, "Kar ka ji komai Ado in Sha Allah ba abun da zai faru sai alkari,tunda Alkairinne dai azuciyoyinmu na gode da kokarinka gareni."

Nan suka shirya yadda tafiyar zata kasance zuwa gidansu FADILA da kuma FARIDA.

Tunda FADILA Da Mumynta suka ji cewa FU'AD zai zo suka Fara shirye-shirye tun Rana aka Fara bade gidan da hayaki kala kala,da turaruka daban daban,hatta ruwan moping sai da aka zuba wani magani Kan ayi, girke-girke kuwa anyi su sunfi kala goma, Kai kace wani Hamshakin taro za ayi.

Misalin karfe 7:30 nadare Mumyn FADILA ta Mata wanka da wani irin ruwa, Koda ta fito sai da aka Kara Mata hayaki da wani irin turaren itama.

Wata irin Fitacciyar Abaya ta dauko Mata,abinka da Mai jiki ta na sawa ya Kara fito Mata da surar jikinta.

FADILA ta ce, "Mumy FU'AD fa Bai son irin haka."

Wani Hamshakin Murmushi Mumy ta yi, "To yau zai so,Ni na fada Miki zai so Fadila."

Dariya FADILA tai Tana, "Ina Sonki Mumyna,Allah bar mun ke."

Nan da Nan aka jera kayan abinci afalon aka Kara badesa da kamshi daga Fadila har abincin jiran zuwa FU'AD kawai suke,ji take tamkar taje ta daukosa da Kanta.

FU'AD kuwa ya shirya tsaf sai dai Bai yi wani adon azo agani ba kayan sawansa na gida yasa, abun ka da Mai kyau duk da hakan ba karamin kyau ya yi ba.

Mai Martaba ne yasa Ado ya kirawosa domin dare na yi yaci ace yanzu suna gidansu Fadilan.

Suna fita FU'AD ya ce, "Ado Ina son zuwa gidan su FARIDA fa Kan muje cen."

Ado ya zaro ido, "To Yallabai ya za ayi kenan?"

Murmushi FU'AD ya yi, " kamar waccen Ranar dai mu Fara zuwa dakinka in canja Kaya Sai mu nufi gidan ba za mu Bata lokaci ba in Sha Allah."

Ba Yadda Ado ya iya haka ya bi umarnin YAREEMA.

Cikin sauri ya Chanja kayan ya fito Kan suka nufi gidan su FARIDA.

Tsayawa ya yi akofar gidan ya tura yaro, FARIDA na Jin Sallamar kuwa ta Tabbatar da cewa shi dinne, amsawa tayi da ace Tana zuwa Kan sa hijabinta har kasa ta fito.

Agefe ta tsaya tare yi Masa sallama, bayan ya amsa ta gaishesa.

Cikin sakin fuska ya ke amsawa Kan ya ce, "abar mun nima nayi daya Mana kin kwashe ladan Sallamar ta gaisuwar ma ba za asamun ba."

Murmushi FARIDA ta yi, "In kana so ai sai in bar ma ka ma duka."

FU'AD ya ce, "Aa Ni na isa sai dai mu raba kawai."

"To shikenan araban Amman nawa zai fi yawa."cewar FARIDA.

FU'AD ya yi dariya, "Wannan ai wayone karara Amman ya zan yi, tunda sammuwane dole in karba."

Kamar ance ya duba ya kalli agogon wayar Ado Dake hannunsa karfe Tara saura, Bai San lokacin da ya bude Baki ba, can Kuma ya ce, "Kinga dare ya Fara yi ki bani amsata kada Mama ta Miki Fada."

Kunyace ta kama FARIDA ta wuce zata shiga gida da gudu,Kan ta juyo ta ce, "Na Amince."

Ta karasa da gudu.

Murmushi FU'AD ya yi , Yana Hamdala azuciyarsa,cikin sauri ya bar wajen Yana zuwa Ado ya ce, "Yallabai dare fa ya yi."

FU'AD ya shige motar tare da fadin, "muje da sauri in canja kayannan sai Wuce can."

Haka kuwa akayi.

Ran FADILA da Mumynta ya Gama jagulewa domin duk atunaninsu FU'AD ya Bata ma su shiri.

Kamar daga sama suka jiyo sallamarsa.

Yana shiga Falon wanna kamshin ya daki hancinsa Nan da Nan yanayinsa ya Fara sauyawa,Kan sa ya Fara juyawa cikin minti daya Kuma ya ji sa garau Amman yanayin jikinsa ya sauya sai kamshin da ke Kara shigewa makogaronsa.

FADILA ce ta tawo da fara'arta Tana washe Baki......

_YADDA ZAKI BIYA ASAMBADAKI A PAYMENT GROUP 300NE KACAL ACCOUNT NUMBER 1453215759 Acess Bank Aisha Abdullahi Sani,YAN NIGER KUMA 400fcfa ZAKU BIYA TANAN,MA SU TURO DA KATI TARE DA SHEDAR BIYA KUMA TANAN ***,WA INDA BASA SON SHIGA GROUP KUMA SAI DAI ATURA MASU TA PRIVATE 500 NE SHIMA TA ACCOUNT DIN DA KE SAMA_

MATAR POLICE 200 JAMEEL 200 ASHE HAKA SO YAKE 300

DUK MAI SON DUKA UKUNNAN ZAN BAR MATA A 600 MAIMAKON 800

URS XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH [7/15, 10:45 AM] Aminiya: *ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_