ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-12

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*YSN YAU ASALIN GUNTUN FEJINE☹️DA BABU GWARA BA DADI AI KO?🤣*_

Dumfarosa da FADILA tai ya Kara birkitasa Jinsa yake wani iri, idanunsa na kallon tsantsar kyau atattare da FADILA, murmushi ta ke sake Masa ya yin da idanunsa ke kallon hakoranta na sheki,ba ta re da ya ankare ba Shi ma tsintar kasansa ya yi da sakar Mata wani kayattacen,Hamshakin Murmushin kasa daga idanunsa daga gareta ya yi.

Zama Tai agefensa Amman har Cikin Ransa ji yake tamkar ya damkota.

Wani irin Farinciki Fadila ta ji aranta domin ga dukkan alamu FU'AD ya Fada tarkonsu.

Ta shi Tai Tana wani irin jujjuyawa tare da fari da idanunta, shi ko FU'AD ya yi suman zaune domin Ban da kallonta ba Abun da ya ke aikin yi.

Tawowa tai kamar zata karaso gare shi Sai Kuma ta tsaya, drinks din ta zuba Masa akofi tare da Mika Masa cike da wani matsiyacin kallo.

Karba ya yi tunda ya kafa Kai sai da ya shanye tas Kan ya dago kallonta ya yi ya sake Mata murmushi ita ma ta sake Masa tare da fadin, "Barka da dare darling."

"Barkanmu ya ki ke farincikina?" Cewar FU'AD da maganar ce kawai ke fita batare da ya sani ba.

Murmushin Mugunta Tai kan shagwabe, "Ni Kam bana lafiya tun da kace baka Sona Kuma ba zaka Soni ba."

Nan take FU'AD ya wage Baki, "Ni na Isa Taya ma zance bana son Sarauniya Kyakkyawa,Kuma Gimbiyar Mata."

FADILA ta ce, "Umm to ya nzu kace kana so na Kuma zaka aureni."

FU'AD kamar ankamar da Shi da tai maganar.

Kallonshi tai ta kara cewa ,"Ba zaka ce kana Sona zaka aureni ba? Zan yi kuka wallahi." Ta karasa maganar Cikin shagwaba.

FU'AD ya ce, "Ina, Ina,Ina sonk ki."

Wani irin tsalle FADILA tai Dan murna saura kiris ta fada kansa ya kauce.

Sannan ta Kara cewa" to ba ka ce zaka aurenin ba? Ganin ya yi shiru ya sa ta yin tsaki , "Nama tuna ai wannan dole ko ba ka fada bama."

Dadyntane ya shigo tare da fadin, "Ah FU'AD baka tafi ba? Dare ya yi ai Fatan kun kammala tattaunawar."

FADILA ta yi saurin fadin, "Aa Dady sai dai ko gobe muka rasa."

Murmushi Dady ya yi, "To shikenan Fadila ,yanzu dai FU'AD ka Tashi ka koma gida goben inda hali ka dawo ku karasa maganar ko?"

FU'AD kallon Dady ya yi Kan y juyo ga Fadila batare da ya ce komai ba kamar wawa.

Fadila ta sake ma sa murmushi tare da fadin , "Gudnyt Darling gobe ka dawo mu karasa maganar."

Sai alokacin ya iya furta , "Gudnyt."

Tare da Dady suka fita suna gaisawa.

FADILA kuwa aguje ta shiga gida Tana Fadawa Mumynta FU'AD ya Zama nata.

Dariya Mumy tai, "ai na lura da yadda ya kidime kadan kenan ma Ina Fada Miki 'Yata in mukaso sai FU'AD ya Zama tamkar Dan da Kika Haifa acikinki Dan biyayya gare ki."

Fadila ta ce, "Mumy Kinga wani irin kallon da yake yi mun kuwa?"

Dariya Suka yi dukansu atare.

FU'AD kuwa ban da ciwo ba Abun da Kan sa ke yi masa.

FADILA sun Gama nasu Hajiya karama ta Fara nata.

Bin gidan tai da hayaki ta ko ina.

FU'AD na shiga gidan hayakin ya Fara sheka,ji ya yi ciwon kansa ya karu Nan take yadaina gani Kan kace miye FU'AD ya fadi kasa warwas.

***

Urs xayyeeshertu

[7/15, 10:45 AM] Aminiya: *ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_