ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-12

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*JUST FOR U AMINIYA, MARYAM NASIR, (MANAB,YAR BABA) KUMA BLACK GIRL🤣 ARADU AMINIYA KINA XAMANI NICK NAME HAR NAWA? GA KUMA 3K🤣,KOMA YA DAI INA SONKI IRIN SOSE DINNAN🥰ALLAH YA HIRYAMU MU RAGE HALIN😂*_

Yadda haya'kin ke bugar hancinsa, ya sa ya fara gani bibbiyu, kafin a farga sai ganinsa aka yi a 'kasa .

Kasancewar ya na shiga gidan, cikin gida ya yiwa tsinke a 'kafa, ba tare da ya nufi shashensu ba, shi ya sa fad'uwarsa ta kasance a idanun mutane da yawa, ciki har da 'yan gulmar Hajiya 'Karama.

Lokacin da labarin ya riske kunnen Hajiya Babba, tana zaune akan sallaya, hankalinta ba 'karamin tashi ya yi ba, amma da ya ke ita maca ce mai tsananin tawakkali, d'aga hannayenta duka biyu ta yi sama ta ce,

*"فسبحان الله المعطي والمتلقي متى شاء"*

Shi ne abin da Hajiya Babba ta iya cewa kenan, kafin ta mi'ke ta nufi shashen Mai Martaba, duk da ta san zuwa yanzu labari ya riskesa.

Ko da munafukar Hajiya 'Karama ta kai mata rahoto, wani shaid'anin murmushi ta saki ta ce

"In kere na yawo, zabo na yawo, wata ran dole a had'e."

Ta fad'a tare da kecewa da wata mahaukaciyar dariya.

Fahad ma ransa fari sol domin daga shi har mahaifiyar sa ba su da burin da ya Wuce ace FU'AD ya bar duniya.

Hajiya Karama ta kalli Fahad cike da Hamshakin Murmushin.

Shi ma murmushin ya mai da Mata tare da fadin, "Hajiyata tabbas na San wannan aikin ki ne, shiyasa nake Kara Alfahari da Ke akullum,Allah yasa Kar ya tashi."

Hajiya karama ta numfasa, "Ai Ina tabbatar ma ka cewa ba zai farka ba, ya tafi kenan,to ma ya tashi Mana, wallahi tallahi kaji na rantse FU'AD ya ta shi agidannan sai na Mai, Mai gabadaya na sa Mai guba yaci ya mutu."

Dariya da shewa dukkansu suka yi Kan suka fice tare.

_______________★★★

Zuwa yanzu labari ya bi lungu da sa'ko na cikin garin, babu inda labarin bai je ba a garin. Hankulan mutane ya bi ya tashi, musamman ma da aka ce, tunda ya fad'i har warhaka bai farfad'o ba.

Kamar yadda labarin ya ba za gari haka labarin ya zo gidansu FARIDA, wacce tunda ta ji wannan labarin ta zama wata iri, hankalinta in Kai dubu to duk sun tashi, a gefe kuma ga rashin samun Adonta a waya da ya addabeta, saboda ba su ta'ba kaiwa irin haka bai kirata ba, kasa jurewa ta yi har sai da ta kirasa, wayar na ringing ba a d'aga ba.

Take ta 'karasa tashi fiye da farko, ga shi zuciyarta da kunnuwanta na son jin ya ya yake, domin ita kanta ba ta san son Adonta ya yi mata wannan dam'kar ba.

Atunaninta damuwarta biyune na Ado da Kuma YAREEMA FU'AD.

Amman zuciyarta Abu dayane ya damketa Wanda take ji har cikin ranta, tsabar damuwa ciwonta na kokarin ta shi, Rasa sukunin da ta yi ne ya sa ta je ta d'auro alwala, ta shiga kaiwa Allah kukanta, wanda ba ya barci ko gyangyad'i, mai rahama da jin 'kan bayinsa, ba ta gushe ba har sai da ta fara jin natsuwa na sakko mata, wannan dalilin ne ya sa ta d'auki alkur'ani, ta fara karantashi cikin bawa ko wane harafi hak'kinsa.

____________★★★

Tun da Hajiya Babba ta ga halin da d'anta ke ciki, sai ba ta yi sanya ba ta sa a yi masa saukar alkur'ani, sannan ta bawa Mai Martaba shawarar, cewa su mi'ka kukansu ga Allah gagara misali, mabuwayi mai mayar da matacce rayayye, mai mayar da rayayye matacce.

Haka kuwa aka yi, sun raya wannan kwana biyun akan sallaya, tare da karatun alkur'ani mai girma, tare da addu'o'i.

A ranar da ya cika biyu cikin ikon Allah a ranar ya farfad'o, masoya sun yi farin ciki, ya yinda ma'kiya kamar sa had'iye zuciya.

Sai dai Kash FU'AD ya tashi da wani azababben ciwon kai Wanda ko magana baya iyawa, Hajiya Babbace ta zo ta yi Masa addu'o'i tare da shafa Masa akai cikin ikon Allah kuwa Kan ya Dan lafa Masa, murmushi ya sake kawai Yana kallon kowa da ido batare da ya ce komai, FARIDA ce tazo Ransa ,tunanata kadai yasa shi cikin wani Farinciki wanda duk Wanda zai kalli fuskar shi zai fahimci cewa Yana cikin yanayi na Nishadi.

Sosai mutane 'yan uwa da jama'ar gari su ka yi murna, ciki kuwa harda FARIDA da FADILA.

FARIDA alwala ta d'auro tare da nafila raka'a biyu na godiya ga Allah. Sosai ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa na shigarta, duk da rashin jin Adonta na damunta, amma a mamakinta a cikin d'ari na damuwarta sittin sun sauka, haka ya sa ta cigaba da addu'o'in kariya ga Adonta.

FADILA kam rantamowa su ka yi domin ganin YAREEMA FU'AD cikin tsananin farin ciki, dama tunda abin ya faru kullum suna ziyar zuwa dubosa.

Wani abin tashin hankali da ya samesu shi ne, sam YAREEMA FU'AD ya manta FADILA, da ya ganta harda wata 'yar zabura sai da ya yi tsabar tsorata, abu kamar wasa sai ga YAREEMA FU'AD ya birkice musu akan FADILA tsoro ma ta ke ba sa.

Wannan lamarin ba 'karamin dagula lissafin mutane ya yi ba, musamman ma Mommy da FADILA, Hajiya ta so a nutsu a nemo bakin zaren, amma sai kula da YAREEMA FU'AD ya ce,

"Ki gafarce Ni ranki ya dad'e, a iya abin da ya faru ya nuna ga dukkan alamu YAREEMA FU'AD ya manta da FADILA a babin rayuwarsa, ya kamata a bar YAREEMA ya huta, domin in aka ce za a matsa masa da maganarta ko ganinta, babu shakka abin zai ta'ba 'kwa'kwalarsa, a barshi nan da wani lokacin a ga ikon Allah."

Jinjina kai Hajiya Babba ta yi, kafin ta ce da likintan masarautar komai, Hajiya 'Karama ta ce,

"Wannan abu daga ji shiryayye ne, ta ya za a ce ya gane kaf d'inmu amma ita kad'ai ya ka sa ganeta, wannan ai zancen banza ne, shiryayye ma kuwa."

Tana gama fad'ar haka ta fita ranta a jagule. Hajiya Babba kam raka ta kawai ta yi da idanu, dan in tace za ta fad'i wani abu, haka za a ce kare d'anta take yi, kaf ta kuma ta gama karantar abin da Hajiya 'Karama ke nufi, sai dai babba babba ne a ko Ina, shiyasa ta yi shiru, haka aka rabu rayuka Babu dad'i.

Sati d'aya FADILA na hanyar gidansu FU'AD, wai ko za a dace FU'AD ya tunota, amma har yau zancen d'aya ne bai ganeta ba, a 'karshe ma zuwan yau da ta yi, har suma sai da FU'AD ya yi dan tsoro, wannan ba 'karamin d'aga hankula ya yi ba, hakan ya sa a hujajan su ka nufo gida.

Wannan lamarin ba 'karamin farin ciki ya sa Hajiya'Karama ba, domin hatta bayi da kuyanginta sun shaida haka. Dan jin kanta take a sama tana shawagi a iska dan dad'i.

__________★★★

A gidansu FADILA kam, wannan tashin hankali da ya fad'o musu, domin FADILA suma ta ri'ka yi, ko da aka yayyafa mata ruwa ta farko, sai ta hau sambatu iri-iri ta 'kara komawa 'yar gidan jiya, ba su suka samu nutsuwa ba sai da kira likita ya yi mata alurar barci.

Barcin FADILA ya sa suka samu nutsuwar fuskantar d'ayan tashin hankalin. Ba su day abin fad'a, amma hankalinsu in ya kai china to ya dawo jos. Fita Daddy ya yi ya nufi masarautar cikin tashin hankali.

Fitar Daddy ya sa Mommy ta fad'a duniyar tunani, tare da fara 'kulle-'kulle azuciyarta.

"Shin Abun da su kayi wa FU'AD ne ya jefashi cikin wannan halin ko kuwa? Anya kuwa babu wani boyayyen sirri game da hakan?" Abun da zuciyarta ke ta saka Mata kenan.

_YADDA ZAKI BIYA ASAMBADAKI A PAYMENT GROUP 300NE KACAL ACCOUNT NUMBER 1453215759 Acess Bank Aisha Abdullahi Sani,YAN NIGER KUMA 400cfc ZAKU BIYA TANAN,TURO DA KATI TARE DA SHEDAR BIYA KUMA TANAN ***,WA INDA BASA SON SHIGA GROUP KUMA 500 NE SHIMA TA ACCOUNT DIN DA KE SAMA_

MATAR POLICE 200 JAMEEL 200 ASHE HAKA SO YAKE 300

DUK MAI SON DUKA UKUNNAN ZAN BAR MATA A 600 MAIMAKON 800

URS XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH [7/15, 10:45 AM] Aminiya: *ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_