ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-13

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_Saura Peji Uku free pages ya Kare😁😁ahanzarta ajo abiya_

Dady na fita ba inda ya nufa sai masarauta,ko da Mai Martaba ya gan shi Bai yi mamaki ba domin kuwa ya San matsalar dai ita ce guda Kan FU'AD.

Kasancewar Aminnin sa ne Kuma batun su Bai da alaka da masarauta hakan ya sa shi fadin su kebance zuwa falonsa na cikin gida.

Zama sukai tare da gaisuwa daga bisani Dadyn FADILA ya Fara jawabi, "Ranka ya dade gaskiya akwai matsala wadda mun kasa fuskantarta bare ma ko munce za mu fuskanta da kan mu ba iyawa za mu yi ba,amman ya fi karfinmu kuma ya fi karfin tunaninmu atakaice dai Fadila na nan kwance ba lafiya mun ka sa gane inda lamarin ya dosa."

Gyaran Murya Mai martaba ya yi Kan ya ce, "To A gaskiya dai Kam wannan lamari kwai sarkakiya gabadaya ma, Abu na farko da Zan ce shi ne, mu Mik'a kukanmu ga Allah mahallici shi zai share mana hawayenmu, in Sha Allah muna Kan yiwa FU'AD addu'o'i Kuma ba za mu fasa ba zamu ci gaba akullum a ko da yaushe Kuma,duk da kasancewar a yanzu dai Kam lafiyarsa lau illa lamarin Fadila Amman ba za mu fasa ba,Kuma Ina sa ran cewa komai zai daidaita ba za mu fidda Rai ga rahamar ubangiji ba,kamar yadda ya farfado in Sha Allah zai dawo normal a yadda ya kasance ada ga Fadila,"

Dadyn FADILA ya ce, "To muna Fatan hakan Amman tabbas na Fara tsorata da wannan lamarin Sam mun kasa gane Kan Fadila."

Mai Martaba ya ce, "Ni ina da wata shawarar ma ko da ace Fadila ba ta samu FU'AD ba,Mai zai Hana a hada ta da Fahad? Tun da na ga dai Kam ba bambanci tsakanin FU'AD da Fahad illa na shekaru." Dadyn FADILA ya gyara zama tare da fadin, "Tabbas da hakan zaiyu zan fi kowa jin dadin hakan in dai FADILA za ta so Fahad tamkar FU'AD."

Mai martaba ya ce, "In Sha Allah za ta so shi."

Da haka su kayi sallama tare da tsaida maganar cewa Fahad zai je su gana da Fadila.

Bayan rabuwar Dadyn FADILA da Mai martaba, sai Mai martaba ya kira Hajiya ƙarama ya sanar da ita hukuncin da suka yanke, Nan take ta nuna farin cikin ta sosai. Sai take ce ma Mai martaba, "gaskiya na ji daɗin hakan sosai da Fahad da Fu'ad duk ɗaya ne ai, Allah ya dai dai tasu." Mai martaba ya Amsa da cewa "Ameen ya Allah." Ita ko Hajiya ƙarama tayi farin ciki ne saboda burin ta zai cika akan hakan.

Hakan ya sa ta kiran Fahad tun alokacin ta sanar masa, ta bangare guda ya ji dadin hakan domin yana daya daga cikin burinsu shi da mahaifiyarsa, ɗayan ɓangaren kuwa zuciyarsa ban da tunanin FARIDA ba abun da ta ke.

Katse masa tunani tai da fadin, "ko ba komai dai burina ya fara cika tabbas abun da naso yi ba shi ne ya faru ba Amman wannan din ma wata karamar mafitace Allah ya aiko mana da ita babbar ma na gaba in sha Allah."

Hajiya Babba kuwa ko da mai martaba ya sanar da ita hakan fadin Allah sa hakane ma fi alkairi kawai ta yi.

****Ɓangaren Fadila kuwa Dadyn bai sanar da ita komai ba tun da su ka samu ta dan dawo hayyacinta shi ke nan, Momy ka dai ya fa ɗa wa yadda su kai da mai martaba, sam ba ta ji dadin hakan ba, domin ta kudiri niyar Aurawa Ɗiyarta zabin da ta ke so ne komin rintsi.

"Haba Alhaji mai ya sa za ku yi gaggawar yanke hukunci haka? In FADILA bata son shi fa? Sannan ina ganin ai karamar matsala ne na FU'AD ina da tabbacin yana son Fadila sai dai wani abun aka yi dan araba su." Cewar Momy cikin fushi .

Alhaji ya kalleta cikin hasala kan ya ce, "Dakataa ki je can da canfin shirmenku na manta,sannan ke kin fimu sanin abun da ya dace ne? Kar ki kuskure ki Ƙetare iyakar ki, mun yanke hukunci kuma ba fa shi ban ga bambanci tsakanin FU'AD da Fahad ba duk jini dayane,sannan ina so ki sanar wa da FADILA za ta yi baƙo da gobe in sha Allah." Yana karasa maganar ya ta shi ya bar ta wajen.

Duniyar gajeren tunani Mumy ta faɗa garin nemo ƙiba an samo rama, FU'AD bai so FADILA ba sai kin ta,ji take tamkar alhakin hakan ne akanta kamar Yadda 'Yar ta ta ke fadi ita ta bata komai,babbar damuwarta a yanzu shi ne FADILA sam ba ta son ganinta ko magana tai mata ba ta amasawa.

Ko da taje ta sanar da FADILAn cewa Dadyn ta ya ce za ta yi baƙo ko kallo mahaifiyarta ta ba ta ishe ta ba.

Wa she gari Fahad ya shirye tsaf cikin kaya irin na alfarma, da ka ganshi kaga jinin sarauta don shima ba baya ba gurin kyau, da iya ɗaukar wanka, bayan ya kammala shiryawa ne ya shi ga sashin Hajiya ƙarama, ya jima a ciki kafin su gama tattaunawar da su ke yi ya fito tare da fadawa suna take mi shi baya, in da ka fin ya ƙaraso har an buɗe mai wata haɗaɗɗiyar Mota yana isowa ya shi ge aka mai da kofar aka rufe, sannan suka fice daga gidan.

Sun isa Gidan su FADILA, bayan sun shi ga ciki aka gabatar musu da kayan ciye-ciye, da su drinks, bayan kamar Minti goma da zaman shi ne, ya fara jin kara step da wani sassanyar ƙamshi da ya ke doso shi Alamun cewa wadda yazo gani ne take isowa, yanayin ƙamshi da ya ke tamkar ya taɓa shaƙar kalan shi hakan ya sa shi lumshe lumsassun idanuwar shi yana da buɗe Hancin shi da ya samu ya ci gaba da jin wannan daɗɗan kamshin.

Hakan ya yi daidai da isowar ta falon, duk da tana tafe ne kan ta a ƙasa bai sa ta daina jin yanda Zuciyar ta take bugawa da ƙarfi ba, tun daga kan kafufuwar shi ta fara kallon shi har ta iso kan fuskar shi, wanda yayi dai-dai da buɗe idon shi, Miƙewa ya yi ci ke da Mamaki ya yin da ita kuma taja baya da sauri tana nunashi da yatsa tana faɗin cewa, "Kai ne,? meya kawo ka Gidan mu."? Duk a lokaci guda ta yi mai wannan tanbayar cike da Mamaki.

Murmushi Fahad yayi mai cike da ma'anoni.

Kan ya ce, "....

***********************

FARIDA ce Zaune Abun duniya ya dameta, Saboda rashin kiranta da Ado bai yi ba, karar wayar ta da ta ji ne ya katse mata tunanin da ta ke yi, ta tashi cikin hanzari ta ɗauki wayar har jikin ta na rawa saboda ganin mai kiran nata, take farin ciki da Annashuwa ya wanzu akan ƙyakkyawar Fuskar ta, cikin sanyin ta ta ɗauki wayar tana mai Amsa sallamar da yake mata, "Yanzu don Allah ina ka shiga kasa zuciya ta cikin maraici da tunanin ka,? gaba ɗaya hankali na ya kasa kwanciya tattare da natsuwar zuciya ta, na kira wayar ka yafi a ƙirga baka ɗauka ba." Ta ƙarasa maganar tana mai ɓa ta rai tamkar yana kallon ta. "To ranki ya daɗe uwar gida kuma Amarya a gidan Ado Allah ya huci zuciyar ki, kwana biyu bani da Lafiya ne shiyasa ki ka jini.....

*** Xayyeesherthul-humaerath

*ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_