ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-14

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_Feji biyu ya rage free pages su kare😊_

Shiru."

FARIDA taja wani dogon numfashi sannan ta ce, "Alhamdu Lillah tun da dai yanzu ka samu lafiya,Allah dai ya kara sauki."

Da Ameen ya amsa daga nan Dukansu kuma su kai shiru.

FU'AD ne ya katse shirun tare da fadin, "Yau baki je Chemist ba ne?"

Murmushi ta yi kan ta ce, "Eh Jikina ne ba kwari ina jin numfashina na sama-sama hakan ya sa ban je ba, amman da yarda za ayi in ganka yau? Ina fatan dai ka sha magani kuma jikin da saukii?."

Duka tambayoyin nan ta jero masa cike da yanayin damuwa.

FU'AD ya saki murmushi tamkar yana ganinta, "Sannu Fatan dai ba ciwonki ke kokarin ta shi ba ko? Ni fa na ji sauki sosai,umarninki shi ne abun da zan yi in Sha Allah zan zo anjima."

FARIDA ta ce, "Alhamdu Lillah, In Sha Allah ma ba ciwon bane,daman damuwar rashin jin kane tun da kuma na ji ka Alhamdu Lillah ko mai zai tafi daidai,ka samu kazo dan Allah ina son ganin ka."

"Ina nan tafe in sha Allah gimbiyata." Cewar FU'AD.

Murmushi FARIDA tai domin kuwa tana matukar jin dadin kasancewa da masoyin nata.

A haka har su kai sallama.

******************Fahad da FADILA kuwa ana nan anata gumurzo.

"Yanzu ina tunanin kin san ni waye? Kuma kin san wa ki ka mara awancen ranar ko? Ina tabbatar mi ki da cewa kamar anyi an gama kin aureni kuma nabi da ke yadda raina ke so."

Tsaki Fadila ta yi tare da fadin, "To sai me dan na mare kan? Na mari dubunka wa inda su ka fi ka a komai bare kai,kuma wallahi ka sa aranka ba za ka taba samuna ba,ko da mafarki ka ke to na tabbatar ma ka da cewa karyane ka yi saurin farkawa, tabbas zan shigo cikin gidan ku kuma a matsayin siriki ga iyayenka, sannan kai kuma a matsayin Yaya ko ince Aunty duk daya dai gare ka."

Ta nuna shi da yatsa kan ta ci gaba da magana, "Ka sa aranka cewa sai na mai da ka tamkar bawa agidan ubanka."

Juyawa tai ta haye kan stairs din ba tare da ta tsaya ko juyowa gare shi ba.

Suman tsaye Fahad ya yi agun na mamaki da takaici, domin FADILA ta wuce dukkan tunaninsa, sak'e-sak'e ya fara yi a zuciyar sa, "shin da me FU'AD ya fi shi da za ta ce ita FU'AD take so? Wanda bai ma iya soyayyar ba bare kalaman da zai sace zuciyar mace,mutum da magana ma wahala ta ke masa bare kuma zancen soyayya, tabbas a da zan auri FADILA ne dan bin Umarnin mahaifiyata tare da cikar burinmu a yau kuwa na kudiri niyar aurenta ta kowanni fanni domin azabtar da ita tare da nuna mata ni wanene."

Yafi minti biyar yana ta saƙe-saƙen nan kan ya fito daga falon tare da shiga mota fuskar nan sam ba annuri.

Ita kuwa Fadila tana shiga ɗakinta ta wuce ta kulle ƙofa ban da kuka ba abun da take,tun Mumy na ƙwanƙwasawa tana ba ta hakuri ta buɗe har ta gaji ta tafi na ta ɗakin kasancewar Dady ba ya nan.

Fahad kuwa ya na isa gida ya sanar da Hajiya ƙarama duk yadda su kai da FADILA a karshen ne ya ke fadin, "Hajiya Wallahi na dau aniyar auren yarinyar nan ko ta wani fannin ne yanzu ne ma na kudiri hakan azuciyata."

Fara zageye ɗakin tai ba tare da ta ce komai ba, cen kuma ta ce, "Tabbas Hajiya Babba ba ta bar wannan yarinyar a banza ba,ina da tabbacin ta yi ƙulle-ƙullen da ta saba akanta, amman ta yi na banza domin duk iskanci da badalar bokanta ai bai kan *Inmutu* ba ,"(inmutu shi ne sunan bakon Hajiya ƙarama).

Ni ko na ce in daman mutum na abu gani yake kowa ma yi yake.

Ta ci gaba da fadin , "Duk yadda za ayi in shiga in fita sai ka Auri FADILA Fahad ka sa aran ka ma cewa ka aure ta anyi an gama."

Wani shu'umin murmushi Fahad ya yi tare da fadin, "Tabbas ni na san ba mai karawa da ke Hajiyata, shi yasa na ke kara alfahari da ke akullum."

****

Misalin karfe takwas na dare Fahad ya je ya sanar da mai martaba cewa ya na son zuwa gun *Hamid* likitansa ko ince likitan masarautar gabadaya,ba musu mai martaba ya nemi da dakarai su raka shi domin kula da lafiyar shi.

Motoci biyar ban da wadda yake ciki.

Biyu a gabansa uku a baya.

Hajiya karama kuwa ban da leƙe ba abun da ta ke damuwarta ta san in da FU'AD ya nufa amman ina ba ta samu fuskar wannan tambayar a gun mai martaba ba.

Asibitin da Hamid ke aiki kuwa suka fara zuwan domin FU'AD har ya saba da Hamid sun zama tamkar abokai da ke sa'anni ne.

Bai jima ba suna gaisawa ya fito tare da fadawa Ado gidansa fa za su ya canja kaya zai je gun FARIDA.

Yadda ya fada kuwa a ka yi.

Amman ado ya ba sauran motocin umarni da dukan su tsaya can gefe in da ba mai gane tare da FU'AD suke ,shi ya tafi shi daya, ba yadda suka iya haka su ka bi umarnin Ado domin yana gaba da su sannan kuma shine shugaban su ta wannan fannin.

FU'AD na zuwa ya kira FARIDA awaya.

Kamshin ta da ya daki hancinsa ne kawai ya isar da shi cewa ta fito ba tare da ya ɗago kai ba.

Duk da kasancewar kayan jikin ta sun sha jiki duk akoɗe suke amman tsaf-tsaf take ban da ta shin kamshi ba abun da take.

Da sallama ta karasa gare shi tare da mika gaisuwa.

Murmushi FU'AD ya yi, "Yo ai ban amsa sallamar ba ma aka jefo mun gaisuwa ko duka zan haɗa in amsa ne."

Girgiza kai ta yi kawai alamar eh.

FU'AD ya kara sake murmushi kan ya ce, "to wa'alaiki Salam,lafiyalau,kin ga nima na amsa mi ki yadda ki ka yi."

"Uhumm ya jikin? Ina fatan dai ka samu sauƙin da za ka iya tsireni afilin gudu." Cewar FARIDA.

Sai da ta gama maganar Take mamakin kan ta ga yadda take iya yiwa FU'AD magana fiye da kowa.

Dariya FU'AD ya yi kan ya ce, "ko dai za agwada ne ma ki gani ina ganin in aka yi na tsereki za ki fi yarda ai."

Ita ma dariyan ta yi kan ta ce, "Aa na ma yarda ba sai anyi ba."

Da haka su ka ci gaba da hirarsu cikin nishadi

Kallon agogon wayar ado da ke hanunsa ya yi tare da bude baki, "har goma ta gota muna waje, gaskiya ya kamata ki koma gida ma yi waya."

Mika masa abu tai .

FU'AD ya ce, "wannan fa?"

FARIDA ta ce, "Ni dai ka karba."

Mika hannunsa ya yi ya karba da mamaki ya ga dubu daya.

Kallonta yai yana, "wannan kudin kuma na miye?.

Kan ta akasa ta ce, "Ka kara akudin magani na san ka kashe kudi da yawa watakila yanzu ba bu wadatacce wajenka."

Kan ya yi magana ta tafi sai da take bakin kofar gida kan ta juyo tare da sa ke mi shi wani hamshakin murmushi.

FU'AD kuwa suman tsaye ya yi.....

*** Xayyeesherthul-humaerath

*ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_