ASHE HAKA SO YAKE

FREE PAGE-15

by @xayyeesherthulhumaerath

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

Kallonta yake sai da ta shige gidan kan ya juyo tare da kallon kudin da ta ba shi.

Daga kudin ya yi tare da shekar sanyayyen kamshin turarenta da ya taba kudin.

Dogon numfashi ya ja tare da ajiyar zuciya tamkar wanda ya sha gudu.

Fuskar fal walwala ya iski su Ado, sai da suka je ya canja kaya kan suka nufi masarautar ta.

Suna isa Hajiya ƙarama idonta kan FU'AD damuwarta ta ji ina yaje amman har yanzu ba ta samu fuskar tambayar kowa ba.

Wa she Gari.

Da safe FU'AD bayan ya gaishe da mai martaba ya ke yi masa maganar kai kayan abincinnan unguwanni talakawa, ba musu kuwa mai martaba ya sa aka shirya rabon abinci ga talakawa da sunan YAREEMA cikin gaggawa.

FU'AD kuwa Ado ya samu ya mai Maganar lallai atabbatar kayan abincinnan ya je gidansu FARIDA.

Hajiya ƙarama na jin labarin cewa FU'AD zai yi rabon abinci ga talakawa ta fara ban bamin masifa

"Gaskiya na gaji da tuzartar da ake yi mana agidannan, wallahi ba za ta sabu ba ina laifin ace FU'AD da Fahad ke rabon abincinnan,ohh wato saboda neman duniya asiye zuciyar talakawa tun yanzu ko?"

Ta nuna Hajiya Babba da yatsa kan ta ci gaba da fadin, "Sumi-sumi mugun maciji, tabbas bokanki ya shahara Amman.......

Kan ta karasa ji tai kawai an sake mata wani gigitaccen mari

Mai Martaba ne yake magana cikin bacin rai, "Shin wai ke ba za ki taba hankali bane arayuwarki? Duk hakurin baiwar Allah nan so ki ke ki kaita bango? An raba kayan abincin da sunan FU'AD domin shi ya bukaci hakan ku kun bukatane? Sannan kibar kawo batun cewa Fahad zai gaji sarautata ko da wasa ma acikin garinnan ,daga ke har lusarin ɗanki ku fita a harkata na fada maku."

Hawayene kawai ya fara Zuba daga idanun Hajiya Babba wanda daman sam arayuwarta ba ta son rikici ko kadan hakan ya sa ta tafiya ba tare da ta ce komai ba.

Hajiya ƙarama kuwa wani ihu ta sake tare da fadin, "wallahi na rantse ba kaffara in ka ga Fahad bai zama sarkin masarautar nan ba to bana numfashi ne."

Ta tafi fuuuu .

Dafa kai mai martaba ya yi tare da fadin, "Wannan ita ce ƙaddara ta ,Allah ka dubi lamurana."

Cikin gari kuwa gabadaya ya gama daukan cewa Yareema FU'AD na rabon abinci,ko FARIDA da ke Chemist Sai da taji labarin ba ko karamin Farinciki tai da jin hakan ba, ji tai kawai ta tsinci kanta da son jin muryar Adonta.

Number sa ta danna tare da kira.

FU'AD da ke kwance kan katafaren gadonsa ya sa kudin da FARIDA ta ba shi agaba yana kallo ban da murmushin ba abun da yake sakewa.

Ringing din wayarsa ne ya katse masa tunani.

Ganin NUMBER FARIDA ya sa shi saurin ta shi tare da katsewa kan ya kuma kira.

Sallama ta mai da sanyayyar muryarta tare da gaisuwa.

Shi ko numfashi ya ja kan ya amsa .

Cikin shagwaba ta fara magana, "Shi ne ka ƙi ɗauka ka kira ko? Ni fa na san ai ba ka da katin ne shiyasa na ƙira kuma ni ina da kati."

Murmushin FU'AD ya yi kan ya ce, "Yoo kin manta cewa nima jiya kin bani kuɗi ne? Ai nima na sa katin shiyasa ban dauka ba."

Shiru tai bata ce komai ba.

FU'AD ya ce, "Amman dai ko yau naji muryarki ta fito fiye da koyaushe."

Murmushin tai kan ta ce, "Ba ka da labarin YAREEMA FU'AD na rabon abinci ne? Ni kam dai yana birgeni wallahi, tamkar mahaifinsa ya ke,Allah ya sa shi za a nada asabon Sarkin mu nan gaba,duk da ban taba ganinsa ba amman ina da burin ganin shi , domin kyakkyawa zuciyarsa,ummm duk da cewa na san ma ba zan taba ganinsa ba ko da kuwa zan gan shi watakila sai dai daga nesa."

FU'AD ya ja dogon numfashi kan ya ce, "Ko dai YAREEMAN nan kishiyatane ban sani ba?"

FARIDA tayi dariya kan ta ce, "rufamun asiri ni awa? Abun da na san ko amafarki ba samu zan ba."

FU'AD ya ce, "To a misali ki dauka cewa ni shine ,yana sonki kuma da niyar aurenki zaki amince?"

FARIDA ta ce, "Aa."

"Meyasa?" Cewar FU'AD.

FARIDA ta ce, "Ba zan same shi ba fa kuma bana fatan samun shi koda menene kuwa yana birgeni sosai amman nafi so in rayu ayarda na taso na samu dai dai ni ba wanda yafini fa,ina tsoron masu kudi domin sune sanadi ko ince silar......

Kukane ke kokarin kufce mata hakan ya sa ta yin shiru tare da katse wayar cikin gaggawa.

Shiru FU'AD yaya nan take yana yinsa ya canja, yana tausayin FARIDA domin ya san dalilinta na kin masu arziki, sannan yana tunanin ta inda zai bulowa lamarin fada mata shi waye watakil ta tausaya ta so shi wata zuciyar na fadin aa kada ka yarda ka bari har sai ka aureta a boye.

Wasi-wasi kala kala ya dun ga tsarawa azuciyar shi domin neman mafita .

A karshe ya yanke shawarar fada mata gaskiya tun Yanzu.

Hakan ya sa shi shirya wa aboye daga shi sai Ado suka nufi Chemist din.

Suna shiga kuwa ita kadai numfashi na sama gabadaya ta fita a hayyacinta ko karin dauko abun shakkarta take amman ina ba dama hannunta ya yi nisa da gun ga karfin jikinta duk ya tafi.

FU'AD na ganin yana yin da FARIDA ke ciki ya burkice inda hannunta ke nuna ya yi saurin zuwa tare da dauko mata, da sauri dagata tare da kara mata, tana sheka kuwa numfashinta ya fara dawowa a hankali.

Idon FU'AD ya yi jajir tamkar wanda zai yi kuka ko ince ma kukan yake.

Tausayinta yake ji har cikin ranshi.

Ɗagowa tai ta kalli shi tare da sakar masa murmushi ,a hankali take fadin, "Na gode."

Shima murmushin ya sake mata duk da cewa na shi dai kam ba har zuci yake ba.

Kallonta ya yi kan ya ce, "Yanzu kin ga yakamata ki koma gida ki huta ko?"

"Aa zan iya har lokacin ya karasa, Daman nasaba kuma dana sheka shikenan." Cewar FARIDA.

Ba Yadda FU'AD bai yi da FARIDA ya rakata gida ba taki,hakan ya sa shi taya ta zama a shagon ko anzo siyan magani tare suke sallamar mutane, atakaice dai shi ya yi jinyar abarsa aranar, karfe hudu nayi kuwa ya sa ta dole ta kulle sai da ya rakata har gida kan hankalin shi ya kwanta.

Ya so ace yau kam ya sanar da FARIDA shi wanene amman ba dama.

***FADILA kuwa Mumynta na ta shige da fita kan cewa sai FU'AD ya cigaba da son 'yarta haka ma Hajiya Ƙarama burinta dai FADILA ta so fahad,sannan ta kashe FU'AD.

FADILA kullum kunshe adaki ban da kuka ba abun da take domin dadynta ya ce tabbas magana ta kare Fahad zata aura,har an fara shagalin biki ta kowanne bangare zuciyar Hajiya karama fal da farinciki ita kuwa Mumyn FADILA tamkar ta hadiye kanta.

Soyayya tsakanin FU'AD da FARIDA kullum karuwa take amman aduk sanda ya yi niyar fada mata shi wanene wani abun zai zo da dole sai anbar batun...

**** Wata safiyar Asabar anata shirye-shiryen biki Hajiya karama ta tashi da niyar kashe FU'AD ta hanyar sa mi shi guba a abinci.

Dake shi kullum da safe girkinsa daban ake masa baya wani cin abinci in ba indomie ba.

Hakan yasata shiga kitchen din tare da aikan mai girkin.

Cikin sauri ta zuba maganin kan ta fice.

Idonta na kai har aka kaiwa FU'AD indomie .

Ya kai baki har ya ci,kan.......

***

_second to the last free pages😊_

ASHE HAKA SO YAKE!!*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

_*ASHE HAKA SO YAKE!!* Salon na mussamanne, labarin Soyayya Mai cike da k'ayatarwa,, tausayi tare da taimako ,, Tsantsar Izza da Mulki irin na jinin Sarauta,cike da sadaukarwa Kan so *kadan kenan daga cikin Ashe Haka so yake!*_

_*ALKALAMIN✍️*_ _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ 6STARS INDEED✨ *SADAUKARWA*

_Daga Farkon Littafinnan Har Zuwa Karshe Na Sadaukar da shi gareku *YAYANA Jameel Nafseen,ANTYNA Farida Sweery, ANTYNA Farida Momyn Suhaan,YAR UWATA Ameena Abubakar* Bazan iya maku So kadan ba🥰_

*TUKWICI*

_*TUKWICI* gareka NURA SADA NASIMAT_