FREE PAGE-16
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_last free page💞_
Ya hadeyi FADILA ta shigo cikin gidan cikin sauri ya furzar da abin da ke bakinsa, alokacin ya fara tuna wacece Fadila.
Ita kuwa jan hannun sa tayi ya bita kawai abaya ba inda suka nufa sai fadar mai martaba.
Hajiya ƙarama na ganin hakan cikin gaggawa ta bi bayansu cike da takaici.
Suna isa FADILA ta fada gaban mai Martaba cikin Muryar kuka take fadin, "Uncle wallahi ba na son Fahad ni FU'AD na ke so dan Allah kar ku Aura min Fahad in aka aura min shi mutuwa zan yi,ni FU'AD na ke so." Ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Da mamaki mai martaba ke kallon FADILA domin duk bai san abun da ake ciki na cewa ba ta son Fahad ba, atunaninshi ta amince da shi kamar yadda ta amince da FU'AD a farko.
Dagon numfashi ya ja kan ya ce, " 'lallai Amini bai kyauta mun da boye wannan lamari ba 'Yata dago ki kalle ni, daman bakya son Fahad?"
Cikin sauri ta dago tare da fadin, "Uncle wallahi bana son Fahad ni FU'AD nake so kuma ni shi zan aura."
Hajiya ƙarama dake gefe sai ƙara kumbura take tamkar famfas din yaran da ya jiƙe da fitsari.
Mai martaba ya ƙalli FU'AD kan ya ce, "Na san dai Ɗana baya son ɓacin raina, kuma ya na bin umarnina,kamar afarko da ka amince zaka auri FADILA yanzu ma ina so ka kara amincewa na san ayanzu kam ka tunata tunda har ka iya zama wajen da take, ka min alƙawarin da ke za a yi aurennan."
Kan FU'AD ya yi magana karaf Hajiya ƙarama ta fara saukar masifa, "wallahi bazata sabuba na fada na kara fada kamar yadda aka ce Fahad zata aura ko taki ko taso sai ta aure shi."
Wata firgitacciyar tsawa mai martaba ya yi,wanda ba ma Hajiya ƙarama ba hatta sauran yan fadan sai da suka firgita.
"Ki ficemun dagani in kika kara magana anan a bakin aurenki."
Tsaki tai kan ta fice ba tare da ta ce uffan ba.
Mai martaba ya juyo kallon shi da FU'AD tare da fadin, "in ka share hawayen FADILA tamkar ka share nawane FU'AD, ina so ka ci gaba da kasancewa mai bin umarnina a kullum."
FU'AD ya ce, "In sha Allah ina mai bin umarninka mai Martaba."
Haka kuwa akayi ba karamin Farinciki FADILA tai ba,shi ko FU'AD sam ran shi ba dadi amman ya ya iya Farincikin Mahaifinsa na gaba da na shi.
Hajiya ƙarama kuwa Fahad ta kira tare da rattaɓa masa abun da ke faruwa.
Sam bai ji dadi ba domin ya gama kulla kitumurmurar muguntar da zai yi wa FADILA duk da kasancewar ba sonta yake ba amman tabbas yana takaici da rashin jin dadin hakan.
Kukan munafurci ya fara tare da fadin, "Hajiya nikam dai ina ga ba dan gidannan bane taya za ace wai ace in aure Yarinya yanzu kuma ace FU'AD za aba shi da yake gudun ta ma,wallahi ni mutuwa ma zanyi da zaman wannan bakar masarautar." Ya kara fashewa da kuka.
Tuni hankalin Hajiya ƙarama ya kara tashi fiye da karin farko domin da ta rasa danta gwanda ita ta rasa ranta.
"Ina raye! Ina duniya hawayenka ba zai ci gaba da kwarara ba nama alƙawarin nan kamar kullum,ban da iskanci ace yanzu har FU'AD na iya kallon FADILA? Tabbas wani makircin munafukar uwarsa ta hada kuma ina dai-dai dasu." Cewar Hajiya ƙarama.
Niko nace meyafi karfin Allah? Ko alokacin da FU'AD ke gudun FADILA asirin da aka mai ne bai gama barin jikinsa ba,yanzu kuma da taimakon Allah da adduo,baya shakkar kallonta ko ganinta.
ALLAH KENAN! YANA TARE DA BAYINSA AKULLUM KUMA A KO DA YAUSHE.
Ta ci gaba da fadin, "in ka ga ba ka Mallaki abubuwa biyunnan ba kamar yadda nake fada ma akullum sarauta da kuma auren Fadila tabbas sai dai in bana numfashi."
******
FU'AD na nan hankalinsa ya gama ta shi, ba komai ke damusa ba illa tausayin FADILA da ke tsantsar zuciyarsa.
Kamar ta sani kuwa sai ga kiranta ya shigo.
Amasawa ya yi jiki asanyaye nan take ta fahimci cewa akwai matsala.
Nasiha ta fara mai.
"Kayi hakuri da duk yanayin da ka tsinci kan ka, kada ka taba tunanin cewa Allah baya sonka ne koda na rana daya,duk da kasancewar bana tunaninma zaka kawo hakan aranka,amman ina so ka ci gaba da tawakkali ga dukkan lamuranka komai ya yi zafi maganin shi Allah kuma ina tabbatar maka da cewa komai zai yi dai dai, kuma zai tafi kamar bai faru ba, rubuta aranka cewa yanayinka na yau jarabawace daga Allah,daure ka amsata kuma ka cinyeta yadda za abaka maki mai inganci,kaji?"
Nan take FU'AD ya ji wani sanyi na Ratsa zuciyarsa, numfashi yai mai fidda dumi tamkar ya fidda damuwarsa haka nan ya ji nan take.
"Alhamdu Lillah, Alhamdu Lillah, Alhamdu Lillah, FARIDA ke tamkar maganice arayuwarta dan Allah ki mun alƙawarin komin rintsi ba za ki taɓa guduna ba ko na rana ɗaya,ina sonki FARIDA dan Allah ki so ni,kar ki bar ni,ki mun alƙawari ba zaki gujeni ba,kin ji FARIDA?"cewar FU'AD.
FARIDA ta sake murmushi tare da fadin, "ya ma za ayi in bar numfashi na? Tamkar numfashi ka ke gareni da na rasaka tamkar na rasa rayuwatane,ina sonka ADO nima dan Allah kar ka bar ni ka tausayawa marainiyar da ke dakon soyayyarka azuciyarta ina so na rayu da kai,Ina so na kasance da kai."
Wannan kenan a takaice FU'AD da FARIDA sun yi Alkawarin rayuwa tare duk rintsi duk wuya.
*****
A safiyar yau laraba mai Martaba ke sanar da ahalin fada dama mutan gari gabadaya auren dan FU'AD tare da FADILA yar Amininsa aran Juma'a,wanda ya kama saura kwana uku kenan cif.
Shirye shiryen biki ake ta ko ina ban da ango da bai ma san anayi ba harkar gabansa yake kawai ba abokai gare sa ba illa doctor , doctor kuwa shi ma gun mai martaba ya ji labari ko da ya tsokani FU'AD murmushi kawai ya mai batare da yace komai ba.
adarenn Alhamis FU'AD gabadaya ya rasa walwlarsa niyarsa kiran FARIDA domin sanar da ita gaskiyar lamari ammman ina ya gagara.
Hajiya ƙarama kuwa na nan tana fafutukar neman hanyar dakile wannan auren.
****Safiyar Jumaa da ta kasance ranar daurin FADILA da FU'AD da sassafe ya tashi domin nufar gidansu FARIDA dan sanar mata da gaskiya ba tare da kowa ya sani ba hatta ado illa Hajiya ƙarama da ke bibiyar motsins hakan ya sa ta sa mutanenta bin bayan sa tana zumudi domin ta san FU'AD ba zai dawo gidan da rai ba.
FARIDA zaune da gudu Farisa ta tawo tare da fadin, "Aunty FARIDA Zo ki ga hoton YAREEMA FU'AD na samo mana a jarida zai yi aure yau."
FARIDA na ganin jaridar nan gabanta ya fadi domin tabbas ba ta ga maraba ba tsakanin FU'AD da Adonta
Hanunta na rawa ta fara nuna tana fadin, "Addd..... Ta kasa karasa wa illla hawaye da ke zubowa daga idanunta.
Lokaci guda kuma ta ji anyi sallamar ana kiranta.
Afusace ta ta shi ta fita.
Tana ganin shi kuwa yau acikin shigar shi ta sarauta ya zo nan FARIDA ta kara firgicewa nuna shi tai da yatsa kan tai magana ta fadi sumammiya awajen.
Dai dai lokacin da mutanen Hajiya ƙarama suka dumfaro FU'AD kenan domin kashe shi.
*KUNA GANIN FU'AD ZAI RAYU KUWA?*
*SHIN KUNA GANIN FARIDA ZA TA SO FUAD KUWA?*
*YAYA RAYUWAR FADILA DA FU'AD ZAI KASANCE? SANNAN YA FARIDA ZAKA KARE AYANZU?*
AMSOSHIN NA GA WA INDA SUKA SIYA.
KADA KU MANTA DUK WADDA TA SAI WANNAN LITTAFIN ZA TA ZAƁI DAYA CIKIN LITTATAINA NA KUDI DANA KAMMALA TA KARANTA A FREE *JAMEEL KO MATAR POLICE*
300NE KACAL
KO KATIN MTN KO TA ACCOUNT
1453215759 acess bank Aisha abdullahi sani
Ko kati tanan
***
Domin turo da shedar biya WhatsApp me with dis no
***
🥰🥰Ku nuna mun soyayyarku ta siyan Nobel dinnan kamar sauran
Xayyeesherthul-humaerath💞