FARASHIN RAYUWA

BABI NA BAKWAI

by @rasheedasdirector

Washegari

Bayan Ramlat ta idar da sallar Asuba tare da gabatar da azkar, ta fito domin ta haɗa wa yaranta abin karin kumallo da kuma abin da za su tafi da shi makaranta.

Kamar yadda ta saba, ta raka su har bakin ƙofa.

Kasancewar makarantar ba ta da nisa da gidan, tana tsaye daga ƙofar gida tana iya hangota.

Sai da ta tabbatar sun shiga cikin makarantar lafiya, sannan ta juya ta koma cikin gida.

Tana shiga, idanunta suka sauka a ƙofar ɗakin amaryarta, Amina.

Da sauri ta ɗauke kai tana ƙoƙarin wucewa zuwa ɗakinta.

Sai dai kafin ta yi nisa, ta ji muryar Mustapha cike da raha yana cewa,

"Meenat tawa... kina kashe ni da daɗi, wallahi."

Dariyar Amina da ta biyo bayan maganar tasa ta tsaya mata a zuciya.

"Yaya, ka bari haka mana... ko fa sallah ba mu yi ba."

Ramlat ta runtse idanu da ƙarfi, sannan ta hanzarta shigewa ɗakinta.

Lokaci ya kusa ƙarfe bakwai da rabi na safe, amma har yanzu ba su yi sallar Asuba ba.

Ta lura tsawon wata guda da yin aurensa, duk lokacin da yake ɗakin Amina, jam'i kan wuce shi. Ba ya fita masallaci, balle ya samu jam'i.

Yanzu ma abin ya fara wuce gona da iri.

Har lokacin sallah ya wuce, amma bai yi ba.

Shiru ta yi tana dafe da mararta, inda cikin nata ya sake dunƙulewa ya cure ƙasan cikinta.

Kai ta dafe da ɗaya hannunta, tana jin irin yanayin da ya addabeta a daren jiya yana sake bijiro mata.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ta furta cikin rauni.

Me yake faruwa da ita ne?

Wane irin fitinanniyar sha'awa ce wannan da take ƙoƙarin kunce mata lissafi?

"Ya Allah, Ka kawo mini ɗauki."

Ta faɗa tana runtse idanunta da ƙarfi..

Haka ta shafe kwanaki biyu cikin matsananciyar azaba.

Ranar da Mustapha zai dawo ɗakinta kuwa, maimakon ta yi fushi da shi, sai ta tsinci kanta cikin farin ciki da kuma matsananciyar ƙwadayin kasancewa tare da shi.

Da wuri ta sa Mashkur da Muhsin suka yi barci, sannan ta kai su ɗakinsu.

Ta yi wanka, ta shafa turarukanta masu ƙamshi, ta shirya tsaf, tana zaman jiran isowarsa.

Lokaci zuwa lokaci sai ta ɗaga kai ta kalli agogo.

Sai dai ba shi ya shigo ba sai wajen ƙarfe goma sha ɗaya na dare.

A lokacin har ta fara gajiya da jiran nasa.

Da ta gan shi, ta hanzarta tararsa.

"Abban Mashkur, sannu da zuwa."

Ba tare da wata fara'a ba ya amsa,

"Yauwa."

Ta yi nuni da abincin da ta tanadar masa.

"Za ka ci abinci ne, ko sai ka yi wanka?"

Ya zauna bakin gado yana cewa,

"Na koshi. Kuma tuni na yi wanka kafin na shigo."

Maganarsa ta soki zuciyarta ƙwarai.

Amma duk da haka ta daure, ta yi murmushi ta ce,

"Abin da ka fi so na girka maka kuwa. Ko Lipton ma ba za ka sha ba?"

Ya girgiza kai.

"Yanzu kam barci nake ji."

Ya faɗi haka yana kwanciya gefen gadon.

Ba ta ƙara cewa komai ba.

Ta miƙe ta rage hasken ɗakin, sannan ta dawo ta haye gadon.

A hankali ta matsa kusa da shi, ta rungume shi ta baya.

Da sauri ya janye jikinsa.

"Don Allah ki ƙyale ni. Barci nake ji. Ke ma ki yi barci."

Ta runtse idanu, sannan ta sake matsowa jikinsa.

"Abban Mashkur... ko ka manta ina da haƙƙi a kanka? Bai kamata ka riƙa yi mini haka ba."

Da sauri ya katse ta.

"Yanzu barci nake ji. Ki bari zuwa gobe, ko wace irin magana ce sai a yi ta. Idan kuma so kike ki hana ni barci, sai na tashi na ba ki wuri, na koma parlour."

Nan take ta yi shiru.

Ba ta sake cewa komai ba.

Sai ta matsa can gefe, tana riƙe cikinta cikin wani irin raɗaɗin zuciya..


Washegari ma abin ya maimaitu.

Da dare ya sake ce mata barci yake ji.

Sai dai ita, a wannan karon, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba.

Ta riƙa matsawa jikinsa, tana kwanciya a ƙirjinsa tare da shafa shi cikin wani yanayi na roƙo da ƙauna.

A ƙarshe dai ta samu ya amsa buƙatarta.

Sai dai bai wuce mintuna kaɗan ba, ya zare jikinsa ya koma gefe.

A gare shi, tamkar komai ya ƙare kenan.

Amma a gare ta kuwa...

A lokacin ji tayi tamkar an ƙara hura wutar buƙatar da take addabarta.

Ta ji jikinta ya sake motsawa fiye da yadda yake a da.

Ta yi ƙoƙarin sake jawo hankalinsa, amma ko kallonta bai yi ba.

Ya juya baya, ya rufe idanunsa, ya bar ta cikin halin da take ciki.

Ba ta sake cewa komai ba.

Sai dai ta kwanta tana murƙususu cikin azaba, hawaye na zuba a hankali daga gefen idanunta.

Tun daga wannan lokacin, rayuwarta ta sauya gaba ɗaya.

Duk ranar da Mustapha yake ɗakinta, idan ita ba ta nemi kusancensa ba, ba zai taɓa nemanta ba.

Idan kuma ta neme shi, ya amsa mata na ɗan ƙanƙanin lokaci ne kawai, kafin ya janye ya juya mata baya.

Ko mintuna biyar cikakku ba ya iya ɗauka tare da ita.

Ta ci gaba da rayuwa cikin wannan hali, tana ɓoye raɗaɗinta a zuciya, tana fama da azaba da babu wanda ya san tana ciki sai Allah kaɗai....

★★★★

"Tirkashi! Ramlat, wannan shi ne halin da kike ciki?"

Cewar Nafisat, ƙawarta kuma aminiyarta, wacce ta kawo mata ziyara a wannan rana.

Ta matsa kusa da ita, ta riƙo hannunta, fuskarta cike da tausayi da damuwa.

"Wallahi na taɓa shiga irin wannan yanayin lokacin da nake ɗauke da cikin Shuraim. Hankalina ya tashi matuƙa a lokacin."

Ramlat ta girgiza kai a hankali, sannan ta sauke wani dogon numfashi mai cike da gajiya.

"Nafisat, wallahi lamarin ya fi ƙarfin da zan iya ɓoye shi. Tun farko na yi ta daurewa ina ɓoye wa Mustapha abin da nake ji. Da na ga abin ya gagare ni, sai na tattara ƙarfin hali na gaya masa komai.
Amma wallahi, wannan lalurar ta ishe ni.
Tun bayan da ya ƙara aure, rayuwata ta koma ta haƙuri da jurewa kawai. Yanzu kuma ga wannan sabon jarabawar da ta same ni...
Ina rantse miki da Allah, da ba don cikin nan ya yi girma ba, da tuni na cire shi... ko zan hutar da kaina daga wannan baƙar fitinar da take addabata."

Tausayin Ramlat ya cika zuciyar Nafisat.

Ta matsa kusa da ita, ta dafa kafaɗarta cikin lallashi.

"Ki kwantar da hankalinki, Ramlat. Ki gode wa Allah ma naki ya fara ne bayan cikin ya tsufa.
Ni kuwa, tun farkon shigar cikin Shuraim na fara fama da wannan matsalar. Wallahi sai da na haihu sannan na samu sauƙi.
Da farko ban san abin da ke damuna ba. Sai wata dattijuwa ta ce min,
Ke ba ciwo ba ne. Wasu mata idan suna da ciki, sha'awarsu tana ƙaruwa fiye da yadda suka saba.'
A lokacin ma ban yarda ba. Amma daga baya sai na gane gaskiyarta.
Domin kafin cikin, ban taɓa fuskantar irin wannan yanayin ba. Sai bayan na ɗauki ciki ne komai ya sauya."

Nafisat ta ɗan yi murmushi.

"Wallahi, sha'awar ba ta kwanciya, sai na yi tarayya da Kabir na tsawon awa huɗu ko fiye da haka.
Wallahi sharrin ciki ne. Kina haihuwa duk wannan sha'awar za ki nemeta ki rasa.
Sai dai ni lokacin Kabir yana iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya samar mini da nutsuwa.
Gaskiya ya kamata ku zauna ku yi magana ta fahimta da Mustapha.
Domin wallahi wannan matsalar ba ƙarama ba ce. Na taɓa na ji yadda abin yake.
Idan ba ki sami biyan buƙata ba, ji za ki yi kamar za kiyi hauka ko za ki mutu."

Ramlat ta sauke numfashi mai nauyi.

"Hmmm Nafisat... Mustapha ya ƙi ya fahimce ni. Na kasa gane kansa yanzu kwata-kwata.
Ko hira ma yanzu ya daina yi da ni, bare ya san damuwata.
Wallahi Nafisat, kamar an canza Mustapha."

Wayar Nafisat ta yi ƙara alamar shigowar kira.

Ta miƙe tsaye tare da dafa kafaɗar Ramlat.

"Ramlat, Kabir ya iso. Ga shi yana kira na.
Babu isasshen lokacin da za mu ƙara magana.
Amma zan dawo.
Ki daure, yau ku zauna da shi ku yi magana ta fahimta.
Wannan lamari ba ƙarami ba ne.
Ya kamata ya fahimci cewa ke mace ce wacce aka halatta wa namiji ɗaya.
Idan shi yana ganin yana da wata matar ne, to ke me yake tunanin makomarki?
Ki yi haƙuri. Za mu yi waya idan na koma gida."

Ramlat ta yi mata rakiya har ƙofa, sannan ta dawo ciki da damuwa fal a zuciyarta...


Kamar yadda kawar ta Nafisat ta bata shawarar suyi maza da shi.
da daren daya kasance daren kwanan ta.
yana kwance yana daddanna waya kamar yadda yanzu, yafi to da sabon hali.
duban sa ta yi zuciyarta na rad'ad'i.
ta mike ta dawo gefen sa ta dube sa murya a kasa ta ce
"Abban Mashkur ina son muyi magana da kai."
"Uhum ina jin ki."
ya amsa batare da ya kalli in da take ba.
kai ta girgiza duk da hakan bai yi mata dad'i ba ganin yadda ya nuna ko in kula da abun da take son fad'a masa,
 ta danne zuciya sannan ta ce
"Da ka saurare ni ka aje wayarnan muyi maga."
"Kunne ne ke jin magana ko ido? ina jin ki ai."
wasu hawaye ne suka ciko idanunta tana soma magana suka soma gangarowa kan kuncinta, cikin sheshsheka take fad'in
"Mustapha ka sauya ga ba d'aya ka sauya, wannan ba Mustapha'n da na sani a baya bane, 
mai kauna ta wanda baya son ganin damuwa ta,
dama ashe duk fad'an da kake a baya,
babu wata macen da zatazo ta sauya ka duk karya ce!
ina adalcin da kace zakayi.
ashe dama duk wasu maganganun da kake min a baya yaudara ce,
kace zaka auro wacce zatazo ta tayani aiki da kula da 'ya'ya kafin ciki na ya tsufa, ka gaya min badun baka sona zakayi aure ba sai dun sabo da na sami mai taimaka min a gida.
wlh Mustapha sauyawan ka na bani mamaki,
yanzu baka damu da damuwa ta ba, duk halin da nake ciki bai sa ka tausaya min ba,
tun ina b'oye maka damuwata a matsayi na na mace mai kunya. kai kuma a matsayin ka na miji na, bai sa ka gane ba har sai da na fito fili na gaya maka,
amma ko sau d'aya baka tab'a tunanin ka samo ni daga halin da nake ciki ba,
alhalin kai ne sila domin wannan cikin ka ne, kuma shi ya jefa Ni cikin halin da na tsinci kaina yanzu."
ta fashe da kuka sosai tana cigaba da fad'in
"So kake naje nayi iskanci a waje?."
katseta ya yi  "Ke fa Ramlat na fuskanci wata jaraba ce kika koyo yanzu,
ke ma ai ba haka halin ki yake ba da, sai da kikaga nayi aure kafin kika soma wasu fidda fice.
 ina ta fad'a miki wannan hanyar bazata b'ulle da ke ba, ita fa yarinyar nan bata damu da damuwar ki ba, ke kike so ki sawa ranki damuwa."
"Ya isa haka Mustapha! kayi duk abun da kake ganin dai-dai ne, Amma ka sani hakkina dai-dai da d'igo d'aya yana rataye a wuyanka.
ban nimi jin wata magana ba dama ni ma ce maka nayi na damu da damuwar ta, magana nake sakanin ni da kai,
kada ka sake sako min ita cikin magana, da kai nake ba da ita ba."
ta mike ta janyo pillow ta matsa can kuryar gado ta kwanta, tana mai rumtse idanun ta......!



Mommyn Twins ce